Yini Na Sittin Da Daya
Dukkan dabbobin da suka saba zuwa fada, kuma suka ci gaba da zuwa tare da Sarkin ba ya iya halartar zaman, yau ma haka suka kara hallara. Kodayake dama dai suna cike da dokin ci gaba da sauraren wasiyyoyin Sarki daga bakin Malam Kunkuru.
A irin sa’ar da Zakin ya saba bayyana a fadar daidai shi ma ya bayyana, cikin shirbace da rawani. Hannunsa rike da kandiri yana taku daidai cikin takama. Yana zuwa kuwa ba tare da ko dar ba ya haye karagar Sarkin! Kafatanin dabbobin da ke fadar suka cika da mamakin al’amarain, shi kuwa ko a jikinsa.
Bai ko nuna ya damu da rashin gaisuwa irin wadda aka saba yi wa Sarki da suka yi ba. Ya gyara zama ya fara bayani,
“Abu mafi ban sha’awa game da ku da Sarkinku ya fada min shi ne soyayyarku ga ilimi. Don haka ne ma ya tabbatar min da cewa babu wanda za ku yi wa biyayya kamar masani. Idan kuma ana maganar masani, to ba jago-jagon masana da kuka saba gani a baya ba. A’a, masani da ya san ilimi ya san rayuwa ya san abin da ya shafi wajen duniyar dabbobi da tsintsaye.”
Yana cikin wannan bayani bai aunai ba, hankalinsa ya yi nisa cikin kwadayin cimma burinsa, da yake tsammanin yana daf da cika. Har aka shigo da Zakin da rakiyar Dila da Kahuhu cikin fadar ta wata barauniyar kofa! A daidai lokacin kuwa har ya zo inda yake cewa, “Don haka, akwai dakaru ma da Sarkinku ya tanada cewa duk wanda ya yi min tawaye su kashe shi! Kuma suna cikinku, amma ba ku san su ba. Shi ma wanda yake cikin rundunar kansa kawai ya sani, bai san shi da su wane a cikin rundunar ba. Saboda haka ina umartarku da mika wuya gare ni, domin Sarkinku ba zai kara tashi ba har abada.”
Tare da ishara da Zakin ya yi musu cewa su yi shiru, amma da aka zo wannan gabar, sai Zomo ya harzuka ya ce. “Ban da wannan da ke tsaye a bayanka, munafikin Ubangiji?”
Kunkuru ya waiwaya cikin wani sauri da ba a taba gani ba a tarihin Kunkuraye, ai kuwa sai ya ga Zaki kikam da tawagarsa a tsaye! Ya yi tsalle ya fado kasa tim, yana cewa, “Ka yi min rai Ranakashidade wallahi dama can ina da tabin hankali, kuma yakan motsa min. Shi ne ma yake kora ta daga duk inda na je.”
Kafin wani ya bude baki ya yi masa magana kuma sai aka fara jiyo kara da koke-koke da gudu duduf-duduf a wajen fadar, ihu ya karade iyakar inda kunnensu zai iya jiyowa! Nan take kowa ya shiga razani, masu jarumta daga ciki suka shiga gyara damara. Wasu Bareyi biyu da suka shigo a guje cikin firgici ne suka shaida wa fadar cewa. “Wadannan Karnukan da ake ta magana ne suka karaso, sun fi su dubu cikin shirin yaki, kuma nan suka nufo gadan-gadan!”
Daga jin wannan dukkan dabbobi suka kara rikicewa, kuma rufe bakin wadancan Bareyi ke da wuya Karnukan suka rika malalowa cikin fadar ba ko kakkautawa! Take kuma ganin su ya sa wasu dabbobin suka fadi sumammu!
Zakin wanda da kyar yake iya tsayawa a kan kafafunsa, sakamakon tsawon lokacin da ya kwashe yana jinya, shi ne kuma yanzu ya yi tunga a gaba, cikin shirin ko ta kwana. Sauran dabbobi da suke da ragowar laka a jiki suka tsaya a bayansa.
“Su wane ku, kuma me kuke nema a nan?” Ya tambaye su cikin daga murya.
Sai wani garjeje mai bakin baki, wanda da alama shi ne jagoransu ya ce, “Mu ne Karnukan Walle, kuma muna neman Sarki ne.”
Ya bugi kirji ya ce, “Ga ni nan, ni ne Sarki Asad dan Hafsin!”
Da mamakinsa sai ya ga jagoran nan ya fadi kasa a gabansa yana gaisuwa, sauran ma duk sun yi koyi da shi!
Cikin tsananin ta’ajibi ya tambaye su, “Mene ne sha’aninku?”
Jagoran ya dago kai ya ce, “A baya can mun kasance a wata daddadar daula karkashin wani adalin Sarkinmu. Katsam watarana muka yi wani bakon Kunkuru, ya zo ya yaudare mu da malumta…” Da ya kawo nan, sai dabbobin can suka shiga waige-waigen neman Malam Kunkuru a cikin fadar. Ya ce. “sai bayan mun amince da shi, Sarki ma ya amince da shi, zuwa wani dan lokaci muka ga Sarki ya fara rashin lafiya, ya sha fama da doguwar jinya, sannan daga bisani ya rasu. Har ya zo ya dare karagar Sarkin ashe wani Bera a fadar yana ganin duk abin da ake yi, shi ya tona asirinsa. Muka kama shi muka ajiye a magarkama, ya kara yi wa masu gadin dadin baki, ya gudu ba su sani ba.”
Zaki yana ta faman gyada kai a hankali yana tuno yadda wasu abubuwa suka rika faruwa tsakaninsa da Kunkurun.
Jagoran nan ya ce, “Mun jarraba sarakuna da yawa, sun kasa rike mu bisa adalci. Shi ne wani Rahibi daga bil’adama da mukan je neman fatawa gare shi ya ce mana duk fadin duniyar nan in dai adalin Sarki muke nema da zai maye mana gurbin tsohon Sarkinmu sai dai mu taho gare ka!”
Zakin ya yi masa kallo na mamaki.
Shi kuwa ya karasa, “Kuma ga shi mun same ka da sunan da kuma suffofin da ya lissafa mana game da kai.”
Zakin nan ya waiwaya ya dubi mukarrabansa, sannan ya juyo ya dubi wannan Jagora ya ce masa. “Yanzu da za ku samu wannan Kunkuru, wane hukunci ne ya dace da shi a shari’arku ta can?”
Ya ce. “Za mu yanke masa hannu daya da kafa daya mabambanta, sannan mu tsire shi da mashi. Daga baya mu karasa shi ta kowace irin siga ma.”
Zaki ya dubi dabbobin fadar. “Ina yake ne?”
Suka ce, “Ai tun dazu muke duban sa Rankashidade mun rasa.”
Sai da Zakin ya yi wata kara mai sa rasani, kowa na fadar ya tsorata. Har dabbobin da dazu tsabar tsoro ya sumar da su suka mike zumbur. Sai ga Malam Kunkuru, ashe wata katuwar sumammiyar Bauna ce ta danne shi. Zaki ya ce musu, “Ga shi nan.”
Suka kuwa damike shi ba wanda ya saurari magiya sa soki-burutsunsa, suka guntule masa hannun dama da kafar hagu, yana ta faman rafka ihu, suka kara soka masa mashi ta cikin kokon bayansa har sai da ya fita ta kasa. A haka kuma suka rika taka shi da cizo da yakushi a bainar jama’a, har sai da ya mutu!
Sannan Zakin ya kara yi musu maraba ta musamman, tare da tabbacin samun nutsuwa a cikin zaman da za su yi a masarautar tasa. Da kira gare su da sauran dabbobin da ke masarautar kan a girmama juna, kuma a dauki kowa a matsayin dan’uwa, ba bare ba.
ALHAMDULILLAHI!
Masha Allah