Skip to content
Part 4 of 35 in the Series Yini Sittin Da Daya by Hamza Dawaki

Yini Na Hudu

Da sassafe, a wannan karon, dabbobin da su aka tarwatse aka bari a fadar, su ne kuma suka riga kowa dawowa gare ta yau. Kafin lokacin da Zakin ya saba fitowa ta al’ada, suka nemi iso gare shi. Ya kuma aminci da su riske shi a cikin gidansa. Bayan sun kwashi gaisuwa, an kuma tattauna abubuwa da suka shafi iyali, sama-sama, sai kai tsaye Dila ya ce:

“Rankayadade, wata shawara ce ke tafe da mu.”

Zaki ya ce. “Dama ai tun da na gan ku yanzu na san akwai dalili, banza ba ta sa Hawainiya sassarfa.” Ya dan yi shiru ya dubi kowannensu cikin sakin fuska, sannan ya kara cewa. “To bisimillah.”

Suka kalli juna, sannan Kahuhu ya yi wa Dila nuni da hannu, yana mai alamta ya ci gaba da bayani. Dila ya dan kara dukufawa ya ce.

“Wato Rankashidade, magana ce dai a kan zaman fada na jiya ne. Ina farawa da bayar da hakuri bisa laifin da muka yi. Ina kuma addu’ar Ubangiji Ya kara wa sarki juriyar hakuri da dawainiya da mu. Sannan daga karshe, ina kuma bayar da shawawa, cewa nan gaba idan irin wannan ta faru, a dena barin fadar. Musamman lokacin da marasa ladabi suke ciki.”

Zaki ya gida kai cikin alamta yarda da maganar, ba tare da furuci ba. Kahuhu ya ce. “Lallai wannan shawara ce mai kyau. Domin daga abin da muka samu a tarihi, wannan wata gaba ce mai sammatsi matuka, wadda sarakuna ba sa sakaci da ita. Shi ya sa lokacin da Sarki Hirakalu ya yi niyyar bayyana ra’ayinsa na gasgata sakon musulumci, sai da ya sa aka rufe duk kofofin fadarsa. Saboda kar ma wasu su fita, su yi wani kuskus a bayan idonsa.”

Zaki ya gida kai a karo na biyu cikin nuni da gamsuwa da batun. Sannan Dila ya ce. “To ai irin wannan sakacin ba wai a duniyar mutane kawai tasirinsa ya bayyana ba. Domin ko a nan ai shi ne sanadin kifar da sarautar iyalan Damisa.”

Zaki ya dube shi ya ce. “Ina lissafawa, ina bin ka labarai kusan shida yanzu. Kuma idan wannan dambarwar ta lafa duk sai ka zauna ka zayyana min su, kaf.”

Dila ya risina tare da cewa. “Ubangiji Ya kara maka yawan rai.”  Sannan ya kara cewa. “Hakika ina yi muku godiya. Domin na san wannan shawara masoyi na gaskiya ne kawai zai iya bayar da ita. Kuma ina tabbatar muku da cewa ba za a kara maimaita hakan ba.”  Dukkansu suka risina cikin ladabi. “Muna matukar godiya bisa daukar shawararmu da aka yi. Hakika wannan ba karamar girmamawa ba ce gare mu.” 

Bayan wani dan lokaci, suna shirin tashi, Zaki ya ce da su. “Amma wane darasin rayuwa ku ka dauka a cikin sha’anin wadannan jama’a biyu?”

Kahuhu ya ce. “Ai akwai darussa kam da yawa. Na san Dila zai bayyana mana su.”

Dila ya yi wa Kahuhu wani kallo mai kama da harara, sannan ya ce. “Me ya sa sai ni zan bayyana?”

Zaki ya yi dariya, sannan ya ce. “To ni bari in fadi abu daya wanda watakila shi kuke tsoron bayyanawa. Daga abin da na fahimta shi ne, yawanci kananan dabbobi sun fi nutsuwa. Watakila suna ganin suna da rauni a wai fanni, don haka sai su mayar da hankalinsu wurin samun wasu dabaru da za su amfane su. Amma manyan ganin suna da girma da karfi, ya sa babu abin da suka iya sai wauta, tsagwaronta.”

Kahuhu ya ce. “Da gaske ne kananan sun fi manyan azanci, kuma watakila raunin da suke da shi ne ya gadar musu wannan. Domin na ji wani mawaki yana cewa:

                              “Baiwa kowa da irin tasa,

                              Wasu karfin damtse ba nakasa.

                              Sai sun zance ka ji fal tawaya

                              Harshen wasu zai iya ruda kasa,

                              Kuma ga shi jikinsu akwai nakasa”

                              Wataran biyu ba ta tadda daya.”

Zaki ya ce. “To ai ga shi ma mun gani ra’ayil aini.”  Sannan ya dan kara muskutawa ya fuskance su da kyau:                          

 “Amma duk da haka sai kun ci gaba da hakuri da ni ku ma. Domin wani abin za ku ga kamar ina gardama ni ma akwai abin da nake hangowa. Kuma daga cikin abubuwan da watakila ku ma za su ba ku mamaki  shi ne, wannan fitar da za a yi don tarar abokan gaba, ba zan tura ko daya daga manyan dabbobin nan ba!”

Dila ya rike baki, shi kuwa Kahuhu ya karkata kai, dukkansu cikin tsananin mamakin abin da suka ji.

Ya ci gaba. “Domin magana ta gaskiya ni duk wani aiki da za a gina shi bisa doron wauta ba na taba sa hannuna a ciki. Ni nasara na sani, a tarihin gidanmu ita na ji ana bayar da labari, ban samu akasinsa ba. Don haka duk inda na lura babu nasara to ba na sanya hannuna a ciki. Don kuwa hakan tamkara karya alkadari da tarihin gidan namu ne.”  

A haka suka fito fada tare, a lokacin kuma tuni da yawa daga kananan dabbobin sun hallara.

Zakin ya zauna, mazauna fadar suka duka suka kwashi gaisuwa.  Sabanin sauran ranaku majalisar babu armashi har tsawon wani lokaci. Domin Basaraken bai yi irin waccan tambaya da ya saba yi, ta neman jin labaran da suke tafe da su ba. Haka kuma bai bayar da uwarnin ci gaba da jin shawarwarinsu game da tunkarar waccan balahira ta dabbobin da ke fuskanto su ba.

Sai dai bayan jigum-jigum din ya dan tsawaita ya ce.

“Tururuwa da Mikiya da Biri da Zomo da Kurege duk ku fara shiru. Domin da ku za mu yi amfani wurin tunkarar waccan kalubale. Idan kuma daga baya mun ga akwai bukatar a kara muku wasu ayarin to za a yi hakan.”

Dukkan wadanda ya ambata suka cika da murna. Yayin da a gefe wadanda bai ambata ba alhali suna son tafiyar suka yi jugun-jugun cikin alamta takaici. Ba tare da ko nuna ya san halin da suke cuki ba, ya kara cewa.

“Ina fatan daga yau zuwa jibi ya ishe ku, ku tattauna ku zabi wadanda za ku wakilta daga cikinku, kuma ku kammala dukkanin wani shiri da za ku yi zuwa jibi.”

Suka hada baki.  “An gama Rankashidade.”

Bayan wannan bai kara cewa lomai ba, sai bayan kusan rabin sa’a ya kara cewa:

“Ko akwai mai wata magana?’’

Kowa ya yi kamar ruwa ya ci shi. Sannan ya mike tare da kara cewa. “To a je a ci gaba da shiri. Duk abin da kuma kuke bukata kwa iya yin magana.”

Sai bayan ya juya ya tafi ne Dila ya kara fuskantarsu, ya ce.

“To, kun ga dai yau zaman fadar ya yi banbarakwai, ba yadda aka saba ba. Sai dai na san ko da ba a ce da ku komai ba, na san za ku iya fahimtar girman darajar da kuke da shi a wurin Sarki. Domin waccan tafiya fa da ya ambata ku kadai ya zaba zai tura, saboda tsananin son ku da yake. Tare kuma da cewa manyan dabbobin dajin nan sun ma fi ku son zuwa.”

Ya dan waiwaya ya dubi sahen wadanda jikkunansu suka yi sanyi, ya kara cewa.

“Abin alfahari ne wannan ga kafataninku, ba wai wadanda kawai aka zaba ba. Domin arziki ne a gidanku baki daya, wataran in an dau wancan gobe kai za a dauka. Kuma idan za ku iya kwatanta kanku da wadancan manyan dabbobi, to tabbas ba ku da dalilin damuwa.”

Sai bayan fuskokinsu sun washe, alamun damuwa sun kau, sannan ya yi sallama da su suka tafi. 

Da maraice manyan dabbobi suka hallara fada cikin sanyin jiki. Bayan zama na dan wani lokaci Basaraken ya fito, irin fitar da ya saba yi a kullum. Da zamansa suka kwashi gaisuwa kamar yadda aka saba. Sanan ba tare da bata lokaci ba ya ce.

“Bayan nazari da muka yi game da tunkarar wadancan dabbobi da aka ba mu labarin suna tunkaro mu, mun amince da tura musu kananan dabbobi. Wadanda muna ganin su suka fi dacewa su tunkare su.”

Ai nan take aka fara kallon-kallo tsakanin dabbobin. Kusan dukkansu sun ji abin banbarakwai kuma ba yadda suka so ba. Amma a lokaci guda kuma kusan dukkansun suna tsoron maimaita laifin da suka yi jiya, shi ya sa suka ja baki suka yi gum. Bayan wani dan lokaci ya mike tare da cewa.

“Wanda duk yake da wata shawara game da lamarin zai iya ba mu nan da jibi.” Ya kada kansa ya nufi gida tare da haunawansa.

Kallon da suke yi wa Dila bayan tafiyarsan ya ishi kowa fahimtar cewa suna cikin tsananin bukatar fashin bakin dabi’ar da Basaraken ya nuna a yau. Dila ya matsa kusa, kamar wadda yake tsoron yin magana da karfi don kar a jiyo shi. Ya ce.

“Wato magana ta gaskiya lamarin nan ya fara ban tsoro, ni har na fara jin kunyar kananan dabbobin nan.”

Dukkansu suka kara zuro wuya gaba: “Yaya aka yi ne?’’

Ya ce. “Duk yadda muka so mu nuna bukatar a sirka da wasu daga cikinku in za a tafi tunkarar dabbobin can da ba a san yaya uke ba, ya ki yarda.”

Suka ce. “To wai saboda me?”

Ya ce. “Cewa yake yi ai wai ku dakarunsa ne da ba ya so ya rabu da ku daidai da taki guda. Kuma idan har zai bar ku ku tafi wani wuri mai hatsari ba tare da sanin balahirar da za a riska a wurin ba, ai gara ya fito ya tunkare ta da kansa. A ganinsa zai iya bayar da ransa saboda ku.”

Ya dan yi shiru yana karanta fuskokinsu, sannan ya ci gaba. “Yana ganin tun da dai wadancan kananan dabbobi su suka kawo kansu suka ce za su je, to kamata ta yi a yi amfani da su a matsayin abubuwan gwaji. Ya san da zarar sun je sun taras sun fi karfinsu, za su gudo. Kuma tunda akwai Mikiya da Tururuwa a cikinsu, to tabbas duk rintsi za a iya samun labari. Idan ma an ji musu rauni ko an kashe su, to to yanayin raunin da aka gani a jikinsu zai iya ba ku cikakken labarin yadda suke fadansu. Wanda sanin hakan zai sa tunkarar su ta kara zama mai sauki a gare ku.”

Da suka ji haka sai duk jikinsu ya yi sanyi, suka rika nuna gamsuwa game da soyayyar da Sarkin yake yi musu. Har Giyen nan yana tambaya.

“To yanzu ba ya tsoron kar su fahimce shi, su ce su ba ya yi musu adalci?”

Dila  ya ce. “Ko daya, ai sun san ba wanda aka gayyato. Dukkansu da kansu suka zo suka ce za su iya. Kuma an ma latsa su, ana nuna kamar ba a so su je, suka nace sai sun je. Daga karshe aka lamunce musu, su murna ma suke ta yi ai yanzu wai.”

Kahuhu ya ce. “Kuma wani dan karin bayani shi ne, ku ma din fa ba wai yana nufin ku sakankance ko ku shantake ku zauna a gida kawai ba. Ku ma zamanku a nan wani aikin ya zabar muku ku yi, aiki mai gwaggwaban lada kuwa, wato ribadi.”

Dukkan su suka mayar da maganansu ga Malamin, Karkanda ya ce.

“Alaramma ya ya ribadin yake ne?”

“Shi ne zama a gida, musamman a gefen gari cikin shirin ko-ta-kwana. Yadda duk abin da ya tunkaro za ka tare shi, ka hana shi afka wa al’uma.” In ji Kahuhu.

Suke ce.

“Na’am.”

Sannan ya ci gaba. “To wannan aikin da kuke gani, lada ne da shi da falala mai yawa. Kai idan ma har mai jihadi bai kyautata niyya ba, kai da kake zaune kusa da iyalinka da zummar ribadi ka fi shi lada.”

“Allahu akbar!” Ta fito daga bakin dabbobi kusan takwas a lokaci guda. Dila da Kahuhu dai ba su yi  sallama da dabbobin nan ba sai bayan sun tabbata sun kai matuka wurin gamsuwa cewa Sarki yana tsananin son su ne shi ya sa ya dauki matakin da ya dauka.

<< Yini Sittin Da Daya 3Yini Sittin Da Daya 5 >>

1 thought on “Yini Sittin Da Daya 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×