Yini Na Biyar
Washegari da sassafe zababbun wakilai daga kowane sassa na dabbobin da aka ayyana a matsayin wadanda za su yi wancan taren aradu da ka suka bayyana a fada, suna jiran fitowar Sarkin. Sai bayan wani lokaci manyan malaman fadar suka iso. Bayan sun gaisa da wadannan wakilai a matsayinsu na masu ido da tozali a fadar suka matsa can gaba-gaba suka kama wuri suka zauna, duk a ka ci gaba da dakon fitowar Basaraken.
Dila ya dubi Kahuhu, ya fashe da dariya, tare da cewa.
“Wato kai ma fa Alaramma ba ka da dama, in ka so.”
Kahuhu ya yi dube shi cikin sakin fuska, ya ce.
“Na san inda ka nufa to, amma fa ni ma kamar kai, ba fa na yin kwai sai da zakara.”
Dila ya ce. “To amma Alaramma cewa fa ka yi wanda yake zaune a gida da sunan ribadi sai ma ya iya fin wanda ya je jihadin lada.” Ya tintsire da dariya.
“Kwarai kuwa,” In ji Kahuhu, “sai dai kar ka manta na ce in har bai kyautata niyya ba.”
Dila ya ce. “Af e, kwarai an yi haka.”
Kahuhu ya dan yi dariya, sannan ya ce.
“To ai duk lokacin da aka zo batun ayyuka da ake yi da sunan ibada, babu kuma wani abu mai muhimmanci kamar niyya. Domin da zarar niyyar nan ta samu tasgaro, to gara ma fa wanda bai yi aikin ba da kai.”
Dila ya ce. “To fa.”
“Kwarai kuwa,” Kahuhu ya ci gaba; “domin ai shi wanda bai yi aiki ba, yana nan a matsayinsa da laifinsa na wanda bai yi ba ne, don haka ba zai samu ladan wannan aikin ba. Amma shi wanda ya yi ba tare da kyakkyawar niyaya ba, bayan ba zai samu ladan wannan aiki ba, zai kuma samu alhakin yin riya, ko ma na shirka!”
Dila ya ce.
“Assha, harka ta baci!”
Kahuhu ya ce.
“Mummunar baci ma kuwa.” Ya dan tsahirta sannan ya kara cewa. “In ba ka labarin wadanda Allah zai fara sawa a jefa a wuta?’’
“Eh, a ba mu mana.” Wata murya ta amsa, katsam ba tare da tsammaninsu ba.
Nan take kuwa suka mike tsaye zumbur da zummar girmamawa. Zaki ya dubi Kahuhu ya ce.
“Wato Allah shi gafarta Malam abin naku ya zama ya ku ya ku kenan? Yanzu fadakarwar ma sai kun ware ku biyu kuna kuskus babu wanda yake jin ku?”
“Allah Ya kara maka yawan rai,” in ji Kahuhu, “wato ainishi dai magana ta gaskiya ba da niyyar karatun muka fara magana ba. Hira ce kawai ta yi hira, har kuma bukatar wannan ta taso, don buga misali.”
Zakin ya ce. “Af to, to yanzu na ji batu. Ai na dauka rowar ilimin a ka fara yi.”
Ya daga kai ya kalli sashen sauran dabbobin da ke gurfane a fadar. Wadanda su kuma ganin hakan ya ba su damar matsowa su kwashi gaisuwa, tare da gyara zaman jiran ba su umarnin su fada abin da ke tafe da su. Amma Basaraken bai yi wannan ba, ya waiwaya ga wadancan masana. Ya dan yi murmushi, sannan ya ce. “Ai tun da mun riga mun fito mun riski maganar sai a jiyar da mu baki daya.”
“Ubangiji Ya kara maka yawan rai.” Dukkansu suka hada baki.
Ya ce. “Su wa ne wadanda Allah zai fara konawa? Ina fatan ba a cikin mu dabbobi ba ne.”
Kahuhu ya gyara murya ya ce. “Allah Ya kara maka yawan rai, na sami labari daga Kakana cewa. Za a zo da shahararren mai kudi, wanda ya yi suna cikin taimako da ciyar da al’uma da dukiyarsa. A karanta aikinsa na wannan ciyarwa da taimako da ya dauki tsawon lokaci yana yi a rayuwarsa. Wanda aiki ne da ya cancanci himilin lada. Amma sai a ce da shi. Duk wannan aikin ka yi shi ne a duniya don kawai mutane su ce ka yi, kuma sun fada. Don haka fadarsun ita ce sakamakonka, tun da ita ka nufa. Sai a jefa shi a wuta! Sannan a zo da mujahidi, wanda ya mutu a wurin yakin da aka yi don daukaka Kalmar Allah. Ya yi lissafin aikinsa; irin jarumta da bajinta da ya yi a wurin jihadin kafin a kashe shi. Har kuma aka zo aka kashe a wurin. Yana tsammanin za a tashe shi cikin shahidai. Amma sai a ce da shi, dama ai ka yi duk wannan aikin ne don ka nuna wa mutane jarumtarka, ba wai don Allah ba. kuma mutane sun fada, kamar yadda ka so su fada din. Don haka wannan kuma shi ne sakamakonka. Sai shi ma a jefe shi a wuta! Sannan a zo da Malami, mai tarin sani,” Ya tsaya ya karkata kai, kamar mai sauraren wani zance, sannan ya fashe da kuka. Kowa ya sunkuyar da kai, da yawa suka ci gaba da murzar idanu. Bayan wani dan lokaci kuma ya goge hawayensa ya dora:
“wanda suna da iliminsa suka shahara a duniya, saboda aikin da ya yi a cikin addini. Sai ya gama lissafinsa na ayyukan alkhairi da ya yi, na yada ilimi da ayyuka da shi. Yana tsammanin za a sa shi cikin Malamai nagari. Sai a ce da shi; ai duk wannan ka yi ne don mutane su ce ka yi. A ce kai isasshe ne, ka tumbatsa, kuma an fada a duniyar, kamar yadda ka yi buri. Don hakan wannan shi ne ladanka. Sai shi ma a jefa shi a wuta!”
Da ya kawo wannan gabar sai ya dakata na wani dan lokaci, sannan ya girgiza kai, ya kara cewa.
“Wadannan fa duk sun yi ayyukan, kuma ayyuka tukuru. Amma saboda ba su yi da kyakkyawar niyya ba, ina nufin ba Allah suka nufa kai tsaye ba, shi ya sa aka ki karba. Kuma ya zama laifi, maimakon aikin lada. Don haka duk ma yadda za mu yi ya kamata mu sa a ranmu cewa komai za mu yi, musamman in na ibada ne, ya zama mun nufi Allah kai tsaye da shi.”
“Na’am.” Wasu daga dabbobin da ke wurin suka hada baki.
Sannan shi ma Basaraken ya ce. “Allah Ya saka da alkhairi Malam, lallai lamarin akwai tsoratarwa. Tabbas akwai aiki a gaban al’umar wannan zamani, kuma aiki mai nauyi.” Sannan ya daga kai ya dubi waccan tawagar da suka dade a fadar tun kafin shigowarsa, ya ce.
“Me ke tafe da ku ne?”
Wakilan nan suka zayyana masa lissafin dukkan abubuwan da rundunarsu take bukata, tun daga kan makamai har zuwa abinci. Nan take kuwa Zaki ya yi umarnin a basu su kafatanin abubuwan da suka nema daga baitul mali. Nan take kuwa suka yi godiya, suka bar wurin.
Jim kadan ya dubi inda Dila da Kahuhun suke zaune, ya ce.
“Wato da gaske yau na fito da karsashi da kuma zummar yin magana, amma wannan karatu ya kashe min jiki matuka. Don haka ni zan koma gida, in samu cikakken lokaci in yi nazari a tsanaki, kafin zaman maraice.”
Dukkansu suka risina yayin da yake mikewa tare da addu’ar. “Allah Ya kara maka yawan rai.”
Bayan ya shige sauran tsirarin dabbobi da suka zo fadar suka tashi suka bar wurin da daidai. Sannan Dilan ya dubi Kahuhu ya ce.
“Wato Allah shi gafarta Malam ni ma fa kamar ta Sarkin.” Ya mike.
Da maraice manyan dabbobi suka yi wa fada tsinke, suka dauki lokaci suna jiran Sarki bai fito ba. Abin mamaki kuma ba Dila ba Kahuhu har zuwa wani lokaci mai tsayi. Suka tashi bayan gajiya da zamansu, da zummar tafiya, sannan Giyen da yake yi masa rakiya ya bayyana. Da ganin sa suka nufe shi da sauri:
“Lafiya kuwa yau?” Ya ce. “Wato akwai wani wa’azi da Kahuhu ya yi a zaman fada na safe, wanda ya yi matukar taba dukkan wadanda suke zaune a fadar. To daga wannan lokacin ya sanar da mahalarta fadar yadda jikinsa ya yi sanyi, ya kuma koma gida. To muna ta sa ran fitowarsa tun dazu, amma dai shiru. Don haka ina ganin yau dama sai dai mu hakura da zaman fadar nan, a tara gobe kuma. Daga nan ya yi sallama da su, ya juya su ma suka kama hanyoyin gidajensu.