Yini Na Bakwai
Da sassafe kuwa wadanan dakaru suka hallara a kofar fada cikin sulke. Haka kuma kusan kafatanin dabbobin da ke dajin manya da kanana suka zo suka yi wa fadar tsinke. Wasu suna bankwana da dangi wasu da abokai da makwafta, yayin da wasu kuma suka zo don addu’a kawai, a matsayinsu na masu kishin dajin nasu. Su ma tsirarin ‘yan ba wa idanu abinci ba a bar su a baya ba.
Jim kadan Basaraken ya fito, shi ma cikin sulke, ga kwalkwali a kansa, yana rike kuma da wata kantamemen kansakali! Wanda ganin hakan ya sa wasu suka yarda cewa tabbas da shi za a yi tafiyar. Bayan ya yi gajeren bayani na maraba da kafatanin dabbobin da suka hallara a wurin, ya kuma kara kebantar dakarun da marhaban tasu ta musamman. Sannan ya kalli Kahuhu ya ce. “Bisimillah.”
Kahuhu ya mike tsaye, ya yi bisimillah, ya karanta hudubatul haja, sannan ya ce.
“Kafin mu fara addu’a, akwai ‘yan kallomi da ya dace in fada muku. Ba wai kuma ina so in ce ku ma ba ku san su ba ne, ina so in tunatar da ku ne kawai. Ga shi kun fito cikin sulke, ku kadan, in an kwatanta ku da yawan al’umar da ke cikin wannan daji. Kuma za ku yi wannan tafiya ne don kare mutumci da dukiya da haibar wannan masarauta da al’umarta baki daya. Ina so in kara tuna muku cewa, tabbas kun shiga wani tarihi na musamman, wanda ba za a taba iya manta shi a wannan masarautar ba. Ina tabbatar muke cewa kodayake ba tare za mu rankaya mu tafi muna ganin juna ba, amma tabbas muna tare da ku kullum a cikin zukatanmu. Don haka dukkan abin da za ku yi, ku yi shi da kishi a ranku. Ku dauaka muna tare, muna kallon ku, in wurin wuya ne tare muke sha, haka ma in wurin dadi ne.”
Ya dan dakata, ya kara bin su da kallo daga farko har zuwa karshensu. Sannan ya ce. “To zan fada muku wata kalma, wadda za ku rika a matsayin makami, wanda duk abin da ya tunkaro ku, da yardar Al Karim ba zai iya cin galaba a kanku ba. Wannan kalma ita ce; ‘Husbunallahu wa ni’imal wakil.’
“Tun a can baya, lokutan kakanninmu, Ubangiji Al Karim Ya aiko wa mutanen wannan lokaci wani annabi mai girman daraja, da ake ce masa Ibrahimu, aminci ya tabbata a gare shi. Yana kiran mutane zuwa ga bautar Ubangiji, sai suka ki. Har daga karshe ya karya gumakan da suke komawa gare su da zummar bauta. Don haka su kuma suka dauki dogon lokaci suna rura wuta, har sai da ta kai wani mai rai bai isa ya rabe ta ba. Sannan suka samu majaujawa suka sa shi a ciki, suka harba cikin wutar. Abin da kawai ya fada kafin karasawarsa cikin wutar shi ne; ‘Hasbiyallahu wa ni’imal wakil.’ Nan take sai wutar ta kasance wuri mafi dadi da ya taba shiga a rayuwarsa. Daga baya sai kawai aka gan shi ya fito, ba tare da ko gefen rigarsa ya ci wuta ba!
Wannan kalma harwayau, Annabin wannan al’uma Muhammadu dan Abdullahi (tsira da aminci su tabbata a gare shi) da sahabbansa masu girma sun kasance sukan furta ta yayin da wani razani ko abin da zai sa fargaba ya tunkaro su. Kuma sai Ubangiji Ya kubutar da su, da buwayarSa. Don haka, har a yanzu, kuma har a cikinmu, ba wai sai cikin bil’adama kadai ba, duk wanda ya fadi wannan Kalmar yayin da yake cikin garari, Ubangijin Al Karim zai ije masa wannan masifa.”
Daga nan sai Kahuhu ya waiwayo ya dubi Dila, yana mai alamta masa cewa shi fa ya kammala nasa jawabin, don shi ma ya dora. Dalli ya dan yi wani gajiyayyen murmushi, game da cewa.
“Akaramakallahu ai ita dabara tana zuwa kafin ilimi ne, yayin kuwa da duk ilimi ya bayyana ai an kai karshe kenan.”
Kahuhu ya yi masa wani irin kallo mai alamta neman karin bayani, wanda hakan ya sa shi ya kara cewa.
“Duk wani abu da ka ji ana neman dabarun da za a gudanar da shi, ai kafin a samu ainihin ilimin yin sa ne. Domin ita dabara lalube ce, amma da zarar an samu ainishin ilimin yadda ake gudanar da wannan al’amari, to sai kuma a jingine ‘yan dabaru. Domin shi ilimi tabbas ne.”
Kahuhu ya ce.
“Na’am.” A wannan karon cikin alamun fahimta. Dilan kuma ya dora:
“To da kafin bayaninka ya gabata ne, sai in ce ga wata dabara da za a je a gwada. Amma a yanzu dabarar kawai da zan dora jarumanmu a kanta ita ce, su rike wannan bayani naka da kyau. Domin dama ainishin al’adar masu dabara ita ce, su yi tsai, su auna abu bisa nutsuwa da kaifin basirar da Ubangiji Al Karimu Ya hore musu, su kardadi abin da ya fi kama da daidai. A haka, sau da yawa sai Ya datar da su hanya mafi dacewa. Amma da zarar masu dabara sun riski wani abu wanda ilimi ya dabbatar da shi, to a wannan halin sun yarda cewa rungumar wannan ilimin shi ne kololuwar dabara.”
Kahuhu ya yi murmushi, ya ce.
“Wato dai kamar Malamai ne da sukan yi istinbadi; su fitar da hukunci mafi kama da dai-dai a cikin al’amura. Amma da zarar an samu wani nassi da ya yi magana game da wannan mas’ala, sai a jingine batun wani istinbadi a rungumi nassi.”
Dila ya ce.
“Yauwa Malam, to ka isa har inda nake son kai ka!”
Daga nan Kahuhu ya daga fukafukai sama, ya fara jero addu’o’i, kafatanin dabbobi suna amsawa da “Amin, amin, amin ya Karim, amin ya Karim.” Lokaci mai tsayi. Sannan ya shafa, kowa ya shafa. Daga nan da Zakin ya kara kallon rundunar abin da kawai ya kara ce musu shi ne.
“Ku sani, ina alfahari da ku. Don ina so ku tabbatar min cewa ku ma kuna alfahari da ni.”
Dukkansu suka daga makamansu sama tare da daga murya a lokacin da suke cewa:
“In sha Allah!”
Suka kama hanya.
Wuri ya yi tsit, babu abin da ake yi sai kallon matafiyan ba tare da furta komai ba. Kowa yana karafkiya da himilin sake-saken da ke cikin zuciyarsa, har zuwa lokacin da suka kule, idanu suka dena hango su. Sannn hankalin kowa ya dawo ga Sarki, wanda yake tsaye kyam cikin sulke, kai ka ce rufa musu baya zai yi. Shi ma ya kara duban taron dabbobin da kyau, sannan ya daga murya, ganin yadda yawansu ya kai matuka, yana cewa.
“Ina so ku sani, faruwar wannan al’amari ya faranta min rai kwarai, ya sa ni jin alfahari, kuma ya dawo min da tsohon kuzarina. Wanda a baya na bi hanyoyi da yawa don dawo da shi, amma ban yi nasara ba. Saboda ya bayyana min karara wasu tarin ni’imomi da Ubangiji Al Karim Ya yi mana, wadanda a da dukkanmu ba mu san da su ba. Ya nuna min yadda kuke da tsananin kishin wannan daji namu, da biyayyarku ga wannan masarauta.
“Na tabbata ganin dakarun can kawai ya isa alfahari gare ku, kuma ya isa razani ga dukkan abokan adawarku. Kuma kuna sane da cewa wannan runduna ta kananan jaruman wannan dajin ce. Muna da manyan jaruman a kasa,” Ya kalli bangaren da manyan dawan suka fi tattaruwa; “ga su nan kuna gani. Wadanda su in kun gam mun fito da su, to so muke kawai mu muttsike duk rundunar da muka nufa cikin ‘yan dakiku kadan ne.” Nan take wuri ya yi armashi, aka ci gaba da murna da sowar farin ciki, kowa yana jin karfin jikinsa gani da jin yadda suke da tasiri da daraja a wurin Sarkin nasu. A haka Basaraken ya yi musu fatan alkhairi tare da sallama, ya koma gida. Sannan Dila ya fuskanci al’umar ya yi musu guntun jawabi; cewa tun da ga shi an kai har tsakar rana a wannan wuri, Sarki ba zai fito fada da yamma ba. Ba wai kuma don gazawa ba, don a ba wa kowa ma daga manyan dabbobin damar zagaya wa neman kalacinsu, ko kuma su shimfida hakarkaransu su huta a gida. Daga nan shi ma ya yi musu sallama ya nufi gida, haka shi ma Malam Kahuhu ya kwata. Su ma sannu a hankali suka tarwatse, kowa ya nufi nasa matsugunin.