Yini Na Tara
Da sassafe a wannan yinin Dila ya isa kofar gidan Kahuhu, ya rika rafka sallama. Zuwa wana dan lokaci Malamin ya leko yana murzar idanu. Ya yi mamaki bayan hada idanu da shi:
“Rankayadade kai ne da sassafe haka?”
Shi kuma ya ce.
“To Alaramma ina muka ga ta zama ba mu gan ka a fada da maraicen jiya ba?”
Ya dan yi murmushi tare da cewa.
“Af, af , to…” Ya kuma saki jiki, alamar ya fahimci ziyara ce ta kauna; “to ai Rankashidade jiyan nan ni dai wata mura ce mai tsanani da ciwon kai suka rafke ni.”
Dilan ya ce.
“Subhanallahi!”
Malamin ya ci gaba: “To kamar dai zan lallaba in fito, sai kuma sarautar gidan ta motsa ita ma.”
Dila ya yi dariya.
“Wato ka ce dai ku ma Malamai wataran ana yi muku wannan mulkin mallakar a gida.”
Kahuhu ya gyada kai, ya ce.
“Kai, kai, kai, ai wato, kodayake ba a bakina ya kamata ka ji maganar nan ba.”
Ai nan take sai maganarsa ta tuna wa Dilan maganar Zaki ta maraicen jiya. Ya ce. “Alaramma to a nan fa ina da tambaya.”
Kahuhu y ace. “Menene tambayarka?”
Ya ce. “Me ya sa maza ba sa son bayyana labarin zamantakewaru ciki da bai ne? idan ma sun fara dan fada sai kuma ka ji sun waske, amma dai ba za a bayyana dukka, yadda za a fahimci ainishin yadda take ba kwabo da kwabo ba?”
Kahuhu ya ce. “Ida nana kulla kawance ko tagwaitaka a tsakanin tambayoyi ka san da wacca tambaya za a yi wa wannan kawa ko abokiyar tagwaitaka?”
Dila ya gyara tsayuwa ya ce.
“Sai ka fada Alaramma.”
Ya ce.
“To kamar a duniyar mutane ne ka ga mutum ya fito waje a lokacin zuffa daga shi sai gajeren wando da single ko ‘yar-shara, yana shan iska. Sai ka ce masa ‘Wai me ya sa mutum ba zai rika tube kayansa dukka in zai fito shan iska ba?’”
Dila ya yi dariya tare da cewa.
“Alaramma nawa! Wato wani lokacin idan aka ce min ina da basira, in na tuno ka, sai in karyata zancen. Ni dai a iyakar sanina ban san wanda ya iya tsara zance sanka-sanka ba tare da tuntuben Harhe ba irin ka. Abu mafi muhimmanci kuma shi ne a yi zancen mai ji ya fahimta. Tare da cewa ba da kalmomin da ya zata za a isar da sakon aka yi amfani ba.”
Kahuhu ya ce.
“Wannan fa shi ne abin da ake cewa wai Gwano ba ya jin warin jikinsa.”Sannan ya yi girgigit ya waiga dama da hauninsa, ya juyo cikin sassauta murya ya ce. “Na sha’afa, ka san fa makwabcina ne, har ma iyalinmu suna kawo-kwarya.”
Dila ya ce. “Af to, to yau dai an yi gam da katar tunda ba ya kusa, sai dai a kiyayi gaba.”
Ya ce.
“Ba dolena ba. Ka san fa fada da makwafci yana daga cikin manyan bala’i da mai rai yake iya haduwa da shi a rayuwa. Wanda yake cukuikuye shi, ya rasa yadda zai yi ya samu sukuni.”
Dila ya ce.
“To ba dole ba kai kuwa, wanda kullum dolenka sai ka gan shi, ko ka ji shi, ko kuma dai ka ga wani abun da zai tuna maka shi.”
Kahuhu ya ce.
“Yauwa, to ka ji inda matsalar take. Shi abokin gaba ai idan ma dole sai ka yi shi, to kamata ya yi a ce yana can wata uwa duniya kai ma kana wata.”
“Yauwa, sai dai lokaci-lokaci ka rika tunawa da shi ba.” in j Dila.
Malamin ya ce. “To wannan shi ne dama-dama. Amma duk mahalukin da aka ce kullum sai ka gan shi, kuma kana jin haushin sa ai ya jefa ka a garari. Tun da kai kenan kullum sai ka ji bakin ciki a ranka.”
Sarkin Azancin ya ce.
“Kuma ni fa na taba ji ma ana cewa wannan yawaita bakin cikin, musammam wanda za a kwanta da shi, a kuma tashi da shi yana cikin abubuwan da suke saurin haddasa tsufa.”
Malamin ya ce.
“Yo tsufa kawai Rankashidade? Ai har da miyagun cututtuka masu saurin birkita jiki da tunani.”
Dila ya ce.
“Wato shi ya sa fa ni tun da muka yi fada da Dage, muka kwashe kwanaki uku ba ma yi wa juna magana, na ji na tsani batawa da wani.” Ya dan yi shiru, ya ciji yatsa. Sannan ya ce. “Wato Alaramman ka san wata asara ma da na lura ina yi a ‘yan kwanakin?”
Kahuhun ya yi dariya tare da cewa: “Sai ka fada dai.”
Ya ce. “Wato bayan irin lokutan da kuke horar da mu cewa ya kamata mu rika yawaita ibada a ciki. Akwai kuma wasu lokuta da nakan zauna kawai in yi shiru, ina kitsawa in warware, in dauki dogon lokaci ina sake-sakena, tare da kallo zuwa wasu halittu na Ubangiji Al Karim, in cika da mamaki da girman buwayarSa. Ko in tuna dukkan matsalolina da suka dame ni, sai kuma in tuna matsalolin magabata da na ji a tarihi, wadanda suka fi ni daraja a wurin Ubangiji. Nan take sai in ji dukkan damuwata ta tafi” Ya dan yi shiru, sannan ya dora: “Kai in dai takaice maka zance Malam, wannan al’ada ce ma ta mutanen gidanmu. Kowa yana da wani lokaci da yakan kadaita ya yi shuri na wani lokaci. Kamar kakanninmu suna ganin yana ta tasiri a rayuwa kwarai.”
Malamin ya ce.
“Yo kai ka ce ma wai kamar yana da tasiri, kai ba ka ga tasirin nasa ba ne?”
Dila ya yi dariya tare da cewa.
“Allah Ya gafarta Malam.”
Sannan Malamin ya ci gaba: “Ai kaso sama da saba’in na wadanda za ka samu da yawan azancin nan da kuma nutsuwa, to da yardar Ubangiji za ka taras masu karanta zance ne. Watakila kuma irinsu a cikin masa yawan surutun nan ca-ca-ca ba za su kai kaso goma sha biyar ba.”
Dilan ya kara cewa.
“To na yarda da wannan Malam.”
Kahuhu ya yi dariya, sannan ya ce.
“Ba dolenka ba.” Bayan ‘yar dariyar da suka kara yi a tare ya kara cewa: “To shi ya sa makwabci duk yadda za ka yi ka yi bakin kokarinka ka zauna da shi lafiya, duk kuma masifarsa.”
Dila ya ce. “Ni ai shaida ne,” ya dan yi shiru sannan ya kara; “kodayake fa akwai wadanda ballagazai ne, duk kau da kanka ba sa gani, sai sun jangwalo ka.”
Kahuhu ya ce.
“Da yawa ma kuwa, amma ai ba a biye musu. Yo kai da kake da tsari a rayuwa da burace-burace da kake son cimma kuma ga babbar manufarka ta burin haduwa da Ubangijinka cikin salama. Ina za ka tsaye biye wa wanda ka lura ba shi da manufa, wanda lissafinsa a kullum na yau ne kawai?”
Dila ya ce.
“Lallai fa.” Tare da gyada kai.
Kahuhu ya ce.
“Ai irinsu duk kumbure-kumburensu kana fitowa in ka gan su, duk yadda za ka yi ma ka yi ka samo wani suna da suka fi so a fada musu na girmamawa ko da kuwa irin sunan Sarki ne, ka kira su da shi. Sannan ka kakalo wani yake da zai sa a ga hakoranka bashar ka jefa musu.”
Dukkansu suka tintsire da dariya, suka tafa hannaye. Sannan Dilan ya yi wani duba zuwa sama, ya ce.
“Assha, ka ga ga rana har ta daga muna nan, yanzu na san tuni Sarki ma ya fito fada!”
Kahuhu ya ce.
“Af, to bari in dauko rawani in fito mu tafi.”
Suna cikin tafiya Dilan yana ce masa. “Wato ban fa manta ba, akwai kanun zantukan da muka dauko dukansu kuma ba mu karasa su ba.”
Shi ma ya ce masa. “Duk kuma ni ma ina sane da su.” Suka yi dariya.
A lokacin da suka isa fadar alamun da suka gani sun tabbatar musu cewa fadar ta dade da zama. Domin ta cika, gwargwadon irin cikar da ta kamata ta yi a irin wannan lokaci. Yayin da dukkansu suka yi gaisuwa suka koma wurarensu na al’ada suka zauna, sai suka fahimci ashe tuni Cakwaikwaiwa ta yi nisa cikin bayar da nata labarin. Sarki ya tambayi halin da suke ciki, musamman shi Kahuhu da bai zo zaman fadar na jiya da maraice ba. Ya sanar da shi larurar da ta tsare shi. Ya yi masa sannu, sauran mazaunan suka yi masa sannu. Sannan aka ba wa Cakwaikwaiwa damar dorawa a labarinta.
Cikin kankanen lokaci ta kawo karshen labarin. Wanda mazauna fadar suka nuna alamun nishadantuwa da shi matuka. Amma su biyun dai dayake ba su riski farkon ba, ba su tofa tasu a ciki ba. haka kuma aka ruka tambyaoyi iri-iri, tana bayar da amsa har zuwa wani lokaci. Wanda bayan shi zaman fadar bai yi wani tsawo ba lokacin komawa gidan Basaraken ya yi.
Haka da maraice da manyan dabbobi suka hallara. A wannan karon dai ba a bar Kahuhu a baya ba, balle Dila. Sai dai sabanin sauran ranaku, yau ko uffan ba su tofa ba, bayan gaiuwa da sauran umarni da hani da aka zaci dama wadannan ayyuka ne da Dilan zai iya yi. Sai bayan Basaraken ya yi sallama ya tashi ya nufi gida ne ma ya yi wa Dilan wani kallo, wanda kuma daga gani shi ma ya matsa kusa da shi cikin hanzari. Ya ce masa. “Lafiya dai ko?” Shi ma ya amsa: “Lafiya lau wallahi Rankayadade, yau dai kawai cewa muka yi za mu yi shiru mu kara nazartar ainihin dabi’ar manyan namu.” Zakin ya ce. “To, hakan ma daidai ne.” Ya shiga gida abinsa, Dilan kuma ya juyo ya nufi nasa.