Sabon Titin kwaɗo, Katsina state.
Wata matashiyar budurwa ce zaune a cikin wani babban ɗakin da a kallon farko za ka shaida cewa na ‘yan mata ne… Domin ɗakin ya ƙunshi gadajen kwanciya har guda biyu, sannan dressing mirror ma biyu ne… Hatta da wardrobe biyu ce, yawan tarkacen dake cikin ɗakin bai sa ɗakin ya kasa yin kyau ba.
A hankali ta miƙa hannu ta janyo kwalin cart ears headphones, peaches color, ta kunna shi tana taunar cingam a nutse, sannan ta yi connecting da warta, ta saka a kanta tana gyara ɗaurin ɗan kwalin kanta… TikTok ta shiga, sannan ta soma recording video tana ta wani marfi kamar ‘yar tsana mai batiri. A ƙalla sau uku tana recording tana sakewa, domin duk ciki ba ta ga wanda yay mata ba… Tana shirin sake ɗaga wayar domin recording wani videon a karo na huɗu, aka buɗe ƙofar ɗakin da take ciki.
Hakan yasa ta sauƙe wayar tana amsa sallamar da aka yi, tare da kallon wadda ta shigo ɗakin. Wata farar matashiya ce, wadda take kama da ita sak, amma idan ka kallesu ka san cewa wadda ke zaune a ɗakin ita ce babba, domin alamun girma sun fi bayyana tattare da ita, sanye take da uniform ɗin Katsina State College of Health science and technology.
Hannunta na dama riƙe da wata teddy backpack, yanda ta jingina da garu, da kuma yanda take buɗewa tare da lumshe idanuwanta yasa ‘yar uwar tata ta gane cewa a gajiye take. ‘Yar dariya ta yi tana maida hankalinta kan wayarta, yayin da ita kuma ɗayar ta ƙaraso cikin ɗakin tana tafiya a gajiye. Yaraf ta zube a kan gado tana sauƙe ajiyar zuciya.
“‘Yan makaranta manya! Da wa ya gaya miki Borno gabas take?”
Cewar ta cikin ɗakin tana ci gaba da dube-dube a cikin wayarta, sannan tana taunar cingam. A gajiye ta kalleta ita ma, sannan tace.
“Wai fa hakan ma dan mota ake kaini ake dawo dani… Ba dan haka ba ai da na banu!”
“Ai duk abin da ake faɗa miki ba ki ji! Sai yanzu da kika fara zuwa kika gane ma idonki!”
“Humm! Ke dai bari! Calss ɗin 2-4 bai yi ba!”
Cewarta tana tashi zaune da ƙyar! Sannan ta sa hannu ta cire hijabin jikinta, kana ta cire takalmin ƙafarta.
“Amira! Amira!”
Wata murya ta shiga ƙwala ƙiran sunan tun daga ƙasa, hakan yasa Amiran ta amsa da sauri.
“Na’am Mummy!”
Ta aje wayarta dake hannunta ta miƙe tsaye, lokacin da ɗayar ke cewa.
“Ni na ma manta da tace na ƙira mata ke!…”
Ba ta kai ga rufe bakinta ba aka buɗe ƙofar ɗakinsu da ƙarfi, hakan yasa suka yi saurin kallon ƙofar, duk da sun san wa zai buɗe ƙofar… Wani irin kallo na ɓacin rai Mummy ta shiga binsu da shi. Hakan yasa Amira ta sha jinin jikinta ta kama susar wuya cikin alamun rashin gaskiya.
“Sau nawa na ƙiraki?”
Mummy ta tambaya tana haɗe rai.
“Yanzu ne fa na…”
“Rufa min baki! Tun sanda kika shiga wanka na ce miki idan kika fito ki zo ki ɗora mana abincin dare! Shi ne da kika fito daga wankan kika zauna ki kai kwalliya, sannan kika dasa camera a gaba kin video da ɗaukar hoto! Ko?”
“Mummy mana! Ki yi haƙuri!”
“Kar ki zo ki yi abinda na ce, ki ga yanda zan yi da ke!”
Mummy ta ƙarashe tana kallon ɗayar dake zaune a kan gado tana cire uniform ɗin jikinta.
“Ke ma ZAHRA! Idan kin.gama hutawar sai ki fito ki tayata! Domin ni ba zan zauna na sa ku a gaba ina kallo ba tare da kun iya komai ba! A kai ku gidan miji ba tare da kun iya tafasa ko fa ruwan zafi ba! Dan haka ki je ki yi wanka ki sauƙo ki tayata!”
Wadda aka ƙira da ZAHRA ta jinjina kanta, sannan ta sake bajewa a kan gadonta tana susar wuya. Ita kuwa Amira da sauri ta sauya kaya, sannan ta sauƙa ƙasa ta shiga kitchen, gudun kada ran Mummy ya ɓaci a kan wannan girki! Domin in ba ta yi ba na lahira sai ya fi ta jin daɗi, ita ma Zahra ba ta ga ta zama ba, duk yadda take a gajiye haka nan ta daure ta fito suka yi girkin tare da ‘yar uwarta Amira.
*Nigerian Law school, Bwari, P.M.B 170, Garki, Abuja Nigeria.*
“YABINTU! YABINTU! YABINTU!”
Cikin tarin dandazon ɗaliban shari’a da suka fito daga ajin Trots Law… Wata baƙar matashiya ta shiga ƙwala ƙiran sunan tana tattage, wai ko za ta samu danar hango YABINTUn da take ta ƙira.
“Yabintu! Khadija na ƙiranki!”
Faɗin wata budurwa dake sanye da baƙar mini skirt, tare da farar shirt, wadda ta ɗorawa baƙar suit a sama, wuyanta saƙale da legal collar a maimakon tie, ta riƙe legal gown a hannunta da kuma legal wig, yayin da take kallon wata farar budurwa, wadda ita kuma take sanye da dogon baƙin matching trouser, da farar riga, sannan akwai suit a saman dress shirt ɗin, kamar sauran ɗaliban shari’ar ita ma legal collar ne saƙale a wuyanta… Sai da ta yi rolling wani farin mayafi a kanta, sannan ta ɗora legal wig a sama, hannunta na dama na riƙe da legal gown ɗinta, na hagun kuma na riƙe da wasu ɗima-ɗiman litattafai…
Ba ta cika tsayi ba, amma tana da dirarren jiki, kuma fara ce, fari irin mai kyau ɗin nan, tana da kyakkyawar fuska, abar son kallo, gwanar birgewa ga mutane!… Cike da nutsuwa ta juya ta kalli Laura da ta mata magana, kafin fararen idanuwanta suka juya daga kan Laura zuwa baya. Hakan ya bata damar ganin Khadijan dake ƙwala mata ƙira, lokaci guda kuma ta dakata, ganin Khadijan ta nufosu tana gudu.
“Bar tab Ɗinki kika manta!”
Cewar Khadijan tana haki, yayin da take miƙa mata bar tab ɗin, Yabintu ta saki wani sassanyan murmushi, sannan ta saka hannu ta karɓa.
“Kin kuwa kyauta! Dan da ba ki bani ba da wata ƙila sai zuwa gobe zan yi ta naimansa na rasa! Na gode”
Khadija ta yi dariya tana girgiza kanta.
“Ba komai ai! Ina ku ka yi ne?”
Ta tambaya yayin da suka jera su uku suna tafiya a tare.
“Ni dai cafeteria nake son zuwa!”
Cewar Laura.
“Ni kuma a gajiye nake, da hostel nake son wucewa”
“To me zai hana mu fara zuwa mu ci wani abu, sai mu wuce hostel ɗin, dan na san ke ma a gajiye kike liƙis! Ba lalle ki iya girka komai ba”
Cewar Khadija.
“To ba damuwa, mu je ɗin…”
Yabintu ba ta gama rufe bakinta ba suka jiyo horn ɗin motar da duk duniya mutum ɗaya ta san yana yin irinsa, da sauri idanuwanta suka zarce zuwa wurin da ta san ya saba aje motarsa… Kuma kamar yanda ta yi zato, motar tasa na fake a wurin, ya buɗe ƙofar driver seat, ya fito da ƙafarsa ɗaya waje, yayin da ɗayar kuma take cikin motar, hannunsa ɗaya na kan sitiyari yana kallonta ta saman baƙin glasses ɗin da ya saka.
“Ai fa! Da ma na san ba lallai ace ya bar ki kin je ba! Dan haka mu mun wuce, sai mun haɗu a hostel”
Cewar Khadija, sannan da sauri ta ja Laura suka nufi wata hanyar da ban… Yayin da Yabintu ta nufi wurin da motarsa take fake murmushin kan fuskarta na yalwata. Tun kafin ta ƙaraso ya fito daga cikin motar, ya rufe ƙofarta sannan ya jingina da ita yana kallonta har ta ƙaraso inda yake.
“Barka da rana Habibi!”
Ta faɗa cikin muryarta mai daɗin saurare. Umar ya girgiza kansa yana ƙare mata kallo.
“Barka da rana Hayati! Ya rana ya gajiya?”
“Duk ba wanda babu, dan yanzu haka ma cafeteria za mu je mu ci abinci, daga nan sai mu wuce hostel!”
“Ai bai kamata ki je cafeteria ba ina nan! Dan haka kawai ki zo mu fita waje mu je mu ci abinci!”
Da mamaki Yabintu tace.
“Da waɗannan kayan?”
Umar dake shirin buɗe ƙofar motarsa ya fasa shi ma yana binta da kallon mamaki.
“Eh! Mi ye aibin kayan naki?”
“Ai da ka bari na koma hostel na ciresu, sannan na watsa ruwa na sauya wasu!”
Umar ya rufe motar baki sake.
“Hayati kin san irin kyan da kayan nan suke miki kuwa? Allah da ace kin sani da ba lalle ki ci gaba da saka wasu kayan saɓaninsu ba, ni da ma da su na fara ganinki, har na ji kin kwanta min a rai, dan haka kayanki ba su da wata tawaya!”
Yabintu ta yi murmushi tana rufe bakinta da books ɗin dake hannunta.
“Ki yi sauri mu tafi kafin rana ta gama gasa mini ke a nan”
Wani murmushin ta sake, sannan ta zagaya zuwa inda ya buɗe mata ta shiga, sannan shi ma ya zagayo ya shiga ya tada motar ya ja suka fice daga Law school ɗin.
Fatima Haruna Bakura ke nan, wadda aka fi sani da Yabintu, matashiyar budurwa wadda ta taso da burin zama lawyer tun a yarinta, kuma burin nata ya samo asali ne sakamakon mahaifinta Alhaji Haruna Bakura babban alƙali ne, wanda a halin yanzu ya yi retire. Su biyu ne kaɗai a wurin iyayenta, kuma ita ce ta farko, sai ƙaninta Khalid dake bin bayanta. Asalinsu ‘yan jahar Zamfara ne, kuma har zuwa yanzu suna gudanar da rayuwarsu a cikin garin Gusau.
Yabintu da Khalid sun samu gata sosai a wurin iyayensu, domin mahaifinsu mutum ne mai kula da duk wani da ahalinsu suke so. Hakan tasa ko a lokacin da Yabintu ta fara tasowa tare da burin zama lawyer ya tsaya kai da fata wurin tayata cimma wannan burin nata. Kuma shi da kansa yake ƙarfafa mata gwiwa kan hakan abu ne mai matuƙar kyau, wanda idan ta yi shi za ta saka shi alafahari.
Kuma tun daga lokacin da ta taso har zuwa sanda ta gama jami’a, ta shiga law school ba ta samu wata tangarɗa daga iyayenta ba, ga shi yanzu tana daf da gama law school ɗin. Sun haɗu da Umar saurayinta ne wattani takwas da suka wuce, lokacin tana sabuwar zuwa a law school, kuma daga wannan lokacin suka fara soyayya har ta kai ga manya sun shiga maganar, domin ana jiran ita Yabintun ne ta kammala Law school ɗinta sannan a yi aurensu.
*Unguwar Samaru, Gusau, Zamfara state, Nigeria.*
Gwan! Gwan! Gwan!
A karo na uku aka sake ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da wata budurwa ke ciki, kwance take a saman gado, ta yi kwanciyar rubda ciki, yayin da kanta yake a ƙarshen gadon, ƙafafunta kuma suna ta saitin allon gadon. Bacci take hankali kwance, har da su minshari, babu ko alamar tana jin bugun ƙofar da ake.
“Falak! Wai ba za ki buɗe ƙofar nan ba?”
Wata farar dattijuwa ta faɗa a ƙufule, cikin fushin dake nuna cewa tana daf da fasa ƙofar ɗakin. Sai a wannan karon ta motsa ƙafafunta, kafin ta buɗe idonta da kalarsa ta sauya zuwa ja, ba ta haura sakan guda ba ta sake lusmhe idon nata, dan ji take kamar wani abu ke janta kan ta rufe idon nata.
“Falak! Wallahi idan ba ki zo kin buɗe ƙofar nan ba sai na ci ub*nki!”
Dattijuwar ta sake faɗa a ƙufule, tana jin kamar ta ɓalla ƙofar, ta finciko Falak ɗin dake ciki, sannan ta lakaɗa mata duka. Kuma maganar da ta yi a wannan karon yasa Falak ɗin ta sake buɗe idonta, ta tashi zaune tana hamma, kafin ta shiga sosa wuyanta, tana jin kwata-kwata ita baccin ma bai isheta ba. A daddafe ta miƙe ta nufi ƙofar ɗakin tana layi, alamun kayan da ta ja jiya ba su gama sakinta ba, kuma da ma ita ta san za a rina, shi yasa tacewa Khamis ba za ta iya shanye kwalabe huɗu ba, amma haka ya tilasta mata ta shanyesu tas, duk kuwa da ta nuna ƙin amincewarta kan hakan…
Wani matsiyacin kallo Hajiya ta bi Falak ɗin da shi, lokacin da ta buɗe ƙofar tana buɗe idanuwanta da ƙyar a kan mahaifiyarta, domin ji take kamar za ta faɗi.
“Baccin ub*n me kike bayan kin san yau akwai school?”
Cewar Hajiya tana binta da kallon sama da ƙasa, cikin ƙarfin hali Falak ta buɗe jajayen idanuwanta a kan Hajiyar, sannan ta furta.
“Ayi haƙuri Hajiya, ban san baccin ya ɗaukeni ba!”
“Kin yi sallahr Subhi?”
Hajiya ta sake cillo mata tambayar tana nazarinta, Falak da idanuwanta ke gaf da rufewa gaba ɗaya ta yi saurin buɗesu, sannan ta jinjina kanta ba tare da ta san ma wace tambaya Hajiyar ta mata ba, tsayuwar da take yanzu haka ji take kamar za ta faɗi, ba dan ƙofar da ta riƙe ba da tuni ta faɗi ƙasa.
“Sai ki je ki yi wanka ki shirya ki sauƙo ki yi breakfast ki tafi school! Dan ita Bilkis ta jima da tafiya abinta, ba kamar ke ba da kika kwanta baccin asara!”
Hajiya ta ƙarashe tana wurga mata harara, Falak ta sake jinjina kanta.
“To Hajiya!”
“Tun wuri ma gara ki raba kanki da wannan lalacin, dan Wallahi idan FAISAL ya dawo ya iskeki kina wannan lalacin ba za ki ji da daɗi a hannunsa ba…”
Ita dai Falak kanta kawai take jinjinawa, domin ba komai take ganewa a cikin kalaman Hajiyar ba, burinta kawai Hajiya ta bar ƙofar ɗakin, domin ta daddafa ta shiga bathroom ta watsa ruwa a jikinta domin hayyacinta ya dawo. Cikin ikon Allah kuwa Hajiya na gama banbamin nata ta tafi, hakan ya bata damar garƙame ƙofar ɗakin, tana layi ta nufi bathroom, kafin ta kai cikinsa sai da ta faɗi ƙasa sau biyu, da ƙyar da jiɓin goshi ta shiga ciki, ta samu ta watsa ruwan kamar yanda take fata, kuma sai ta samu ɗan kuzari, domin ba gaba ɗaya mayen ya gama sakinta ba.
Tana fitowa daga bathroom ta gabatar da sallahr safiya, yo sallahr safiya mana, domin a ƙalla lokacin 10 na safiya, domin ba ta yi sallahr da asuba ba kamar yanda tace. Tana idarwa ta miƙe da sauri, sannan ta shirya cikin wata abaya maroon color, ba ta yi kwalliya ba, sneakers kawai ta saka a ƙafarta, ta fesa turare mai sanyin ƙamshi, ta ɗauki wasu abubuwanta na buƙata ta fita.
Lokacin da ta sauƙa falon ƙasa, Hajiya tare da Mama ne zaune a falon, yayin da suke hira a kan wasu kaya da aka siyo. Da kallo suka bita har ta iso inda suke, har ƙasa ta tsugunna tana gaishe da Hajiya da Mama.
“Hajiya ina kwana”
“Lafiya”
Hajiya ta amasa, Falak ta kalli Mama dake murmushi.
“Hajiya ina kwana!”
“Lafiya lau Falak! Fatan kin tashi lafiya”
Hajiya ta faɗa tana ta fara’a, kamar ta saka zani ta goya Falak. Ta amsa tana miƙewa, ganin ta nufi ƙofar fita yasa Hajiya faɗin.
“Ba za ki karya ba kafin ki fita?”
A hankali ta ɗan juyo ta kalli Hajiyar, sannan tace.
“Na makara sosai, zan ci a waje”
“Ai da kin tsaya kin ci”
Cewar Mama, dan yadda take kula da Falak ya fi yanda take kula da Bilkis ɗiyar cikinta.
“A’a Mama, kada ki damu zan ci a can… Na tafi”
“To a dawo lafiya, Allah ya tsare, ya bada sa’a”
Ta amsa da amin, lokacin da ta fita waje, maimakon ta hau ɗaya daga cikin motocin gidan sai ta fita waje tana amsa wata waya.
“Baby Baby Babe! Kin tashi lafiya”
Muryar Khamis ta fito ta cikin wayar.
“Na tashi lafiya Baby! Amma yau asiri ya kusa tonuwa! Don Wallahi bacci na yi ta yi kamar gawa, yanzu haka maganar da nake maka ba su gama sakina gaba ɗaya ba, ji nake kamar zan faɗi! Allah ne ya rufa min asiri Hajiya ba ta ganeni ba”
Tana iya jin sautin dariyar da Khamis ɗin ke yi.
“Haba Babe! Sai ka ce ba wayayya ba? Ya ma za ayi ki bari ki yi abin da Hajiya ko wani na gidanku zai gane?”
Ta girgiza kanta lokacin da ta tsaya a bakin titi.
“Ba za ka gane ba ai! Yanzu kana ina?”
“Gani nan a bakin titi, ina iya ganinki ma”
Da sauri ta kalli wata mota ƙirar Honda Accord, wadda ta san cewa tasa, ba tare da tace komai ba ta katse ƙiran, sannan ta nufi motar ta buɗe ta shiga.
“Yaushe ka zo?”
Ta tambaya tana binsa da kallo, mutumin da ta danƙawa ragamar rayuwarta, mutumin da soyayyarsa tasa ta soma ɗabi’un da ba nata ba, mutumin da ya sauya duk akalar tunaninta.
“Na ɗan jima a nan, kuma ma san za ki fito”
Khamis ya bata amsa.
“Yanzu ina za mu je?”
“Mu je mu shana mana!”
“Woooo! Babe, kamar ka san yau ba na son zuwa school! Mu je kawai!”
Ta faɗa cike da jin daɗi, Khamis ya yi dariya, sannan ya tada motar ya ja suka bar unguwar, inda suka nufi gidan da suka saba sheƙe ayarsu dake cikin filin jirgi.
Alhaji Ali Makama haifaffan garin Zurmin jahar Zamfara ne, attajirin mai kuɗi wanda Allah ya masa rasuwa shekaru goma sha biyar da suka wuce… Ya mutu ya bar matansa biyu, Hajiya Aisha, wadda ake ƙira da Hajiya, da kuma Hajiya Laraba, wadda ake ƙira da Mama… Hajiya Aisha na da yara biyu tare da Alhaji Ali Makama, FAISAL shi ne na farko cikin ‘ya’yanta, kuma haka ma a wurin Alhaji Ali Makama.
Wanda a halin yanzu yake riƙe da muƙamin Major a hukumar sojan Nigeria. Kuma a halin yanzu yana Ikorodu Barrack dake Lagos. Duk da ana sa ran yana daf da dawowa cikin garin Gusau domin da ma can a Zamfaran yake, sauyin wurin aiki yasa ya koma Lagos ɗin. Mai bi masa kuma Falak ce, wadda ta kasance auta cikin ‘ya’yan Hajiya, Bilkis kuma ita ce auta a gidan gaba ɗaya, kuma ita ce tilon ‘yar Mama.
Kasancewar akwai fahimta tare da jittuwa a tsakanin matan biyu yasa bayan rasuwar mijinsu ba su yi ƙoƙarin barin gidan ba, sun ɗauki haƙuri, sannan suka rungumi ‘ya’yansu domin ba su tarbiyya mai kyau. Tsakanin Hajiya da Mama babu wani abu da za ka ce ga shi ya taɓa haɗasu, a zahiri suna zama ne kamar ‘yan uwa ba kishiyoyi ba, amma idan aka tona ba lalle hankali ya yarda da ƙulle-ƙullen da ake kan ƙullawa ba.
Bayan rasuwar Alhaji Ali Makama, FAISAL shi ne ya zama kamar uba ga su Falak! Domin akwai tazarar shekaru tsakaninsa da su sosai ba kaɗan ba, kuma a lamarin FAISAL babu ɗaga ƙafa ga duk wanda ya shiga gonarsa, tun tasowarsa yake da wani irin murɗɗaɗen mutum, sai kuma ga shi ta shiga aikin soja, wani abu da ya ƙara dagula ɗabi’unsa.
Sai dai duk da wannan zafin nasa bai san abin da ƙannen nasa ke aikatawa ba, domin hatta su Hajiya babu wanda ya san cewa Falak na shaye-shaye, a wasu lokutan ma ba ta kwana a gida ba tare da kowa ya sani ba. Kuma tarbiyyarta ta fara wargajewa ne a lokacin da ta haɗu da wani shaiɗanin saurayi wai shi Khamis.