Channels Television station, Abazie Ifeanyi Close, Guzape, Abuja.
Wata baƙar mota ce ta ƙetara babban gate ɗin station ɗin, ta wuce har zuwa parking lot. A lokacin da motar ta faka kuma ba jimawa aka buɗe ƙofarta… Ba tare da ɓata lokaci ba wani dogon baƙin mata shi mai cike da haiba, kamala da kwarjini ya fito yana saisaita sakin hullar Zanna Bukar dake kansa, sanye yake da wani plain yadi milk color, babu aikin komai jikin rigar yadin.
A hankali ya kai hannunsa na hagu ya buɗe gidan baya na motar, sannan ya sunkuya ya ɗauki wata bag da kuma wasu ‘yan tarkace dake wurin, yana ɗauka ya miƙe tare da rufe ƙofar motar, sannan kamar kullum, cike da kuzari ya nufi ƙofar shiga station ɗin.
Duk inda ya ratsa sai an gaishe shi ko an ɗaga masa hannu, ba wai dan shi ne shugaba ba, ko dan ya fi kowa, sai dan sanin ya kamatansa da iya mu’amalantar al’umma yasa yake da farin jini a duk inda zai zauna. Lokacin da yake taka stairs ɗin da zai sada shi da office ɗinsa dake sama aka ƙira shi.
“BILAL!”
Hakan tasa ya dakata, sannan ya juyo a hankali. Ganin abokinsa Aliyu ne yasa ya yi murmushi yana binsa da kallo har ya iso inda yake, sannan ya miƙa masa hannu suka gaisa.
“Wai ina ka je wajen sati guda ke nan rabon da na ganka?”
Ba tare da Bilal yace komai ba ya juya ya ci gaba da tafiya, yayin da Aliyu ya biyo shi yana faɗin.
“Na san duk yadda aka yi case ɗin ‘yan matan nan ne ba ka rabu da shi ba!”
Bilal ya kalle shi, kafin ya kuma girgiza kansa yana murmushi, haka Aliyu ya matsa masa kan sai ya sanar da shi dalilin ƙin zuwansa wurin aiki a kwanakin da suka wuce, domin ya san abokinsa Bilal ƙuli-ƙuli ne, ba shi gaba, duk yadda ka kai ga wayonka ba lallai ka iya gane inda ya sa gaba ba, akwai shi da zurfin ciki da kuma wayo na ban mamaki, hakan tasa duk wani labari da ya samu ba ya bari a yaɗa a gidan TVn nasu ba tare da ya tabbatar da shi ba, kuma ko shi kansa ba ya kawowa labaran da ba su da tushe, duk kuwa da yanda yake saka rayuwarsa a haɗari wurin samo labaran a wasu lokutan.
“Why don’t you tell me abin da kake ɓoyewa?”
Cewar Aliyu lokacin da Bilal ya buɗe office ɗinsa suka shiga ciki, amma har ya aje kayan da ya shigo da su a kan table bai tanka masa ba, sai da ya ja kujera ya zauna, sannan ya buɗe wata jaka da ya shigo da ita, ya fito da wani flashdrive, ya cillawa Aliyu, shi kuma ya cafe, kafin ya shiga kallon flashdrive ɗin yana juyawa.
“Ga amsar tambayoyinka nan!”
Kawai Bilal ɗin yace, sannan ya fito da system ɗinsa ya fara sarrafata.
“Ban gane ba”
Faɗin Aliyu yana jan kujera tare da zaunawa, Bilal ya ɗaga idonsa ya kalle shi.
“Tambayoyin da kake min game da rashin zuwana aiki tsawon sati guda! Duka suna cikin nan… Kamar yanda mu ka yi hasashe tun farko cewar wannan ƙungiyar ta GKL suna ɗaukan ‘yan mata da sunan za su sama musu aiki a ƙasashen waje, daga baya sai su ɓige da safararsu suna cinikinsu zuwa wasu ƙasashen da ban da waɗan da aka alƙauranta musu hakan ta tabbata!”
Cikin irin mamakin da Bilal ya saba jefa kowa a ciki idan har ya bankaɗo wata gaskiya da ake ganin wuyar tonuwarta Aliyu ya sake kallon flashdrive ɗin.
“Ke nan duk tsawon satin nan kana Lagos?”
“Eh ina Lagos! Kuma ban dawo ba sai da cikakkiyar hujja a kan abin da shuwagabbanin ƙungiyar suke aikatawa! Wannan flashdrive ɗin na ɗauke da videon ‘yan matan da ake safara yayin da ake sakasu cikin container a tashar jirgin ruwa dake Lagos! Ba wannan kaɗai ba, hatta da videon cinikayyar ‘yan katan da suke akwai! Na ɗauko komai, kuma na samo komai”
Aliyu ya ƙyafta idonsa yana ƙarewa Bilal kallo, kawai sai ya yi dariya, domin ya tuna da wani lokaci can baya da ya taɓa cewa anya kuwa Bilal Mutum ne? Domin abubuwan da yake sun zarce tunani, duk yadda ƙungiyar GKL ke ƙoƙari wurin ganin ta kare sunanta dan kada ya fito a cikin waɗannan harƙallolin na cinikin ‘yan mata daga Nigeria zuwa ƙasashen waje sai da Bilal ya bi hanyar da ya san zai iya tona musu asiri.
“Ban ma san me zan ce maka ba”
“Kawai ka ce Allah ya rayani!”
Faɗin Bilal yana murmushi.
“To Allah ya rayaka! Yanzu kuma mene ne next?”
Bilal ya jingina da kujerarsa yana juyata a hankali, kafin ya ɗaga hannayensa yana motsasu wuri guda, can kuma sai yace.
“Mu dai namu kawai shi ne mu binciko duk wasu abubuwan da ake zargin an binnesu a ƙarƙashin ƙasa, kuma an hanemu da yaɗa labaran bogi, yanzu kuma da na tabbatar da hakan za mu miƙa videon zuwa ga manager, sai manager ya tantance kafin labarin ya isa ga al’umma da kuma mahukunta, idan kuma ya fita ya rage ga hukuma su san abin yi!… Mu dai mun yi namu mun gama”
Aliyu ya girgiza kansa.
“Ni da kaina zan kai wannan bayanin zuwa ga manager!”
Bilal ya taɓe bakinsa yana gyara zaman hularsa.
“Ai tuni ya san da batun… Domin tun jiya da na dawo na sanar da…”
Bai rufe bakinsa ba wayarsa dake aje a kan table ta soma ringing, dan haka gaba ɗaya hankalinsa ya koma kan wayar, musamman ma da ya ga mahaifiyarsa wadda ke zaune a garin Gusau ce mai ƙiran. Kafin ya ɗaga ya yi wa Aliyu alama da zai iya tafiya kawai, kafin ya ɗaga ƙiran, ya soma magana cike da ladabi. Kana ganin yanda yake wayar za ka san cewa da wani mai matuƙar muhimmanci a gare shi yake wayar.
Sabon Titin Kwaɗo, Katsina state.
08:23 na dare.
ZAHRA POV.
A hankali ta rufe ƙofar kitchen, bayan ta fito daga ciki hannunta riƙe da bowl, wanda ta haɗa cereal a ciki. Sanye take da wide blue trouser, sai farar free size T-shirt, kanta ɗaure da wani farin viel, ƙafafunta cikin farin Crocs mai ado a jiki.
“Zahra kin sauƙe min miyar nan daga kan gas?”
Mummy ta tambayeta lokacin da ta iso cikin main falo tana shirin cire Crocs ɗin ƙafarta.
“Eh na sauƙe”
Ta amsa lokacin da ta zauna a kan carpet, sannan ta janyo center table gabanta, ta ɗora bowl ɗin hannunta a kai, ta ci gaba da kallon film ɗin da ake haskawa a Hijra Tv, tana yi tana cin cereal ɗin da ta haɗa, domin ita ba ta cika cin abinci da daddare ba, sai cereal ko abu makamancinsa.
“Amira!”
Mummy ta ƙira Amira dake kwance a kan kujerar zaman mutum uku, ta saka waya a gaba tana latsawa. Jin ba ta amsa ba yasa Mummy ta kalleta.
“Amira!”
Ta kuma ƙira tana binta da kallo.
“Na’am Mummy”
Ta amsa tana tashi zaune a firgice. Domin har ga Allah ba ta ji ƙiran farkon da Mummyn ta mata ba.
“Ke wai haka kullum rayuwarki za ta ƙare a kan waya? Baki da aiki sai na latsa waya? Wallahi Amira a kan wayar nan za mu samu matsala da ke?”
Amira ta sauƙe kanta ƙasa tana ɓata fuska.
“Ki tashi ki je ɗakina ki ɗauko min wayata, na ji kamar tana ringing”
Ta miƙe da sauri ta yi sama, sannan ta je ta ɗauko wayar da ƙira yake shigowa a karo na uku. Ta dawo falon ta miƙawa Mummy, da yake wayar mai muhimmanci ce yasa Mummy ta tashi daga falon, domin mahaifiyarta ce ta ƙirata.
“Kin san jiya sau biyar wannan Kamal ɗin yana ƙiran wayata?”
Faɗin Zahra tana kallon Amira wadda ta ci gaba da aikin da ta saba, wato latsa waya. Amira ta dubeta.
“Kuma me ya sa ba ki ɗaga ba?”
“Na ɗaga na ce masa me? Me zan ce?”
Amira ta kwashe da dariya, har da tafa hannuwa. Ta aje wayarta tana bin Zahra da kallon mamaki.
“Oh yarinya! Wai ke ba ki san yanda ake magana da saurayi ba ko?”
Zahra ta girgiza kanta.
“Sanin me zai amfane ni da shi? Saboda ni dai yanzu karatuna na saka a gaba! Ba zan ɗauki zancen wata soyayya ba”
Amira na shirin sake faɗar wani abin wayarta ta shiga ruri, ganin me ƙiran yasa ta ja tsaki ta saka wayar a silent mood.
“Waye?”
Zahra dake kaiwa spoon bakinta ta tambaya tana kallon wayar Amira da ta kuma kawowa haske alamun wani ƙiran ne yake shigowa. Amira ta juya idonta.
“Zai wuci wannan mara mutuncin!”
“Haba Yaya! Yanzu fa ya kusa zama mijinki, ki daina ce masa mara mutunci mana”
Amira ta ƙanƙace idonta tana kallon Zahra.
“Ba ki san abin da yace mini jiya ba! Wai na ɗora video a status yace na yi maza-maza na sauƙe! As if shi ne Ubana!”
“To a hakan kike cewa na fara soyayya? Ku dai da kuka ga za ku iya sai ku yi, amma mu kam ba yanzu ba, kuma ta wani ɓangaren ya fiki gaskiya Yaya! Dan ba ko wani saurayi ne zai yarda ya riƙa ganin video ko hoton matar da yake son aure a duniya ba!”
“Duniya? Yanzu dan na ɗora a status shi ne zai baza duniya?”
Zahra ta yi murmushi mai sauti, sannan ta jinjina kanta.
“Kin san Allah kar ki yi mamakin ganin videon ki a Instagram ma, domin dan kin ɗora a story yanzu wani zai iya sauƙewa a kan wayarsa, wani ya gani ya tura, shi ma waji zai iya tura daga wayarsa, daga haka za ki ga yana bazuwa har ki ganshi a inda ba ki yi zato ba”
Wayartata suka sake kalla, sakamakon wani hasken da ta kuma kawowa dalilin shigowar ƙiran Mahmud saurayin Amiran. Wanda ake sa ran zai zama mijinta nan da wasu wattani, domin hatta kayan aurenta an kawo, an kuma yanke ranar auren tun bayan da ta gama karatunta na gaba da secondary.
“Allah sarki bawan Allah! Ki ɗaga, ba ki san abin da zai faɗa miki ba, wata ƙila ma zuwa ya yi”
Amira ta yatsina fuska tana hararar wayar, kamar da aka ce ita ce Mahmud ɗin.
“Ai Wallahi zai yi ya gama, amma ba zan ɗaga wayarsa ba, zai gani idan ina da mutunci ko a’a”
Zahra ta yi dariya.
“Wallahi yana ƙoƙari da halinki Yaya…”
Kafin Amira ta kai ga bata amsa aka buɗe ƙofar shigowa falon. Daddynsu Alhaji Musa Gyaza ya shigo falon yana gyaran murya. Sanin cewa shi ne yasa suka miƙe da sauri suna amsa sallamar da ya yi, kafin suka masa sannu da zuwa. Daddy ya amsa yana murmushin ganin ‘ya’yan nasa mata biyu kacal a duniya.
“Kallo kuke ne?”
Daddy ya tambaya yana ƙarasowa cikin falon.
“Eh Daddy!”
Zahra ta amsa shi.
“To mashaallah… Aminatu”
Daddy ya ƙarashe da ƙiran sunan Amira na gaskiya.
“Na’am Daddy”
Amira ta amsa tana matsawa kusa da inda yake.
“Mahmud ya zo tun ɗazu yana waje yana ta jiranki! Yace wai idan ya ƙira wayarki ba ta shiga!”
Zahra da Amira suka haɗa ido, na jin yanda Mahmud ya ɓoye laifin Zahra a idon Daddy, duk dan kar ya san abin da ta yi ya mata faɗa.
“Ya na ga kuna kallon juna? Ko ba haka ba ne?”
Daddy ya katsewa ko waccensu zancen zucin da suke. Dan haka Amira ta yi saurin kallonsa.
“Eh, eh haka ne Daddy”
“To sai ki fita ki je ki same shi, dan Sani Mai gadi yace ya daɗe a compound tsaye yana ta jiranki!”
Ta amsa da to, sannan ta yi sama ta ɗauko mayafi ta sauƙo ta fita, lokacin kuma Daddy ya zauna a falon, yana tambayar Zahra ina Mummy, tace masa tana sama, dan haka ya umarceta da ta ƙira masa ita.
Nigerian Law school, Bwari, P.M.B 170, Garki, Abuja Nigeria.
YABINTU POV.
A karo na uku, Khadija da suke zaune ɗaki ɗaya ta sake kwashewa da dariya, har da guntuwar ƙwallarta. Cike da mamaki Yabintu dake zaune kan gadonta na kwanciyar mutum guda ta ɗaga kai ta kalleta, yayin da take duba wani abu a cikin system.
“Wai ke dariyar me kike ne tun ɗazu? Sai ka ce wadda ta samu taɓin ƙwaƙwalwa?”
Dariya ba ta gama cin Khadija ba ta tashi zaune a kan gadonta, tana riƙe da cikinta tace.
“Littafin FULANI na Khadeeja Candy nake karantawa!… Wallahi daga ɗan iska sai Faɗime, wai Shattima ne ya bata waya, kuma ba ta faɗawa Inna ba har ta dawo gida waya na ringing, Inna tace kamar ƙaran waya take ji, Faɗime tace ba waya ba ce… Inna tace in ba waya ba ce mene ne, buɗar bakin Faɗime sai cewa ta yi wai Memory ne ta haɗiye, da Inna tace a ina aka taɓa jin memory na waƙa a cikin mutum sai cewa ta yi da ta je birni ne ta tsince shi, sai ta haɗe da ruwa, shi yasa yake waƙa a cikinta!”
Lokacin da ta ƙarasa bawa Yabintu labarin ita kanta sai da ta yi dariya, domin abin ne akwai ban dariya.
“Allah ya kyauta”
“Humm! Dan ma ba ki ji abin da ta yi wa Iya mayya ba…”
Khadija na shirin ci gaba da bata wani labarin ƙaran wayarta da aka ƙira ya hana ƙarasa labarin, dan haka ta ɗauki wayar ta amsa ƙiran da yake shigowa da sauri. Domin mahaifiyarta ce ke ƙira.
“Mummy ina yini?”
Daga ɗayan ɓangaren Hajiya Ramatu ta amsa da.
“Lafiya lau Yabintu! Ya makaranta ya karatun?”
Yabintu ta yi murmushi tana rufe system ɗinta, kafin tace.
“Komai yana tafiya yanda ake so Mummy!”
“To mashaallah Allah ya taimakeku”
“Anti Bint!”
Ta jiyo muryar ƙaninta Khalid ta cikin wayar, alamun dai yana kusa da Mummy ne.
“Ni ina ruwana da kai? Kai da na fi wata uku da dawowa, amma ko sau ɗaya ba ka ƙirani ka ji ya nake ba”
Tana jin sanda ya karɓi wayar a hannun Mummy, kafin yace.
“Wai da ma Mummy ba ta gaya miki ba? Tun washe garin ranar da kika tafi phone ɗina ta lalace, kuma Daddy ya ƙi sauya min wata, yace wai dole sai na gama SS3”
Yabintu ta yi dariyar jin yanda Khalid ya ƙarashe maganar cikin alamun dake nuna cewa zaman rashin wayar ya ishe shi.
“Dan Allah Anti Bint ki sa baki ya sai min wata”
Ya faɗa ƙasa-ƙasa, kuma hakan yasa ta gane cewa duka suna zaune ne tare da su Daddy a falon.
“Ok give him the phone”
Da sauri ya matsa kusa da Daddy dake cin abinci a falo, sannan ya miƙa masa wayar, Daddy ya dube shi, kafin ya kalli wayar.
“Anti Bint ce take son magana”
A hankali Daddy ya miƙa hannunsa na hagu, sannan ya karɓi wayar ya kara bisa kunnensa.
“Daddy barka da dare! Da fatan kana cikin ƙoshin lafiya”
Cewar Yabintu daga ɗayan ɓangaren.
“Lafiya ƙalau Fatima! Ya karatun ya makarantar?”
“Komai lafiya yake tafe Daddy”
“To mashaallah haka ake so ai”
“Daddy magana ce a kan wayar Khalid! Yace tasa ta lalace, kuma kai ka ƙi sai masa sabuwa”
A jikinta ta ji cewar lokacin da ta gama maganar, sai da Daddy ya kalli direction ɗin Khalid, kafin ya bata amsa.
“Ai da yace miki na ƙi sai masa sabuwa ya kamata ace ya faɗa miki dalilina”
“Eh haka yace wai kace sai ya kammala secondary school”
Daddy ya girgiza kansa yana murmushi.
“To ai ba gaskiya ya faɗi miki ba… Gaba ɗaya Khalid ya tattare hankalinsa ya mayar kan waya! Ba shi da aiki sai chat, game da kuma kalle-kallen banza da wofi! Ko ta karatunsa ma ba ya yi, duk wannan maida hankalin nasa a kan karatu yanzu babu, abin takaicin ma shi ne, last exams ɗinsu C4 ya ci a mathematics, B2 kuma a English! Shi yasa lokacin da wayar tasa ta lalace na ji daɗi, kuma ko da ace ba ta lalace ba zan karɓeta, kuma ba zan ba shi ba sai zuwa lokacin da ya gane cewa karatu shi ne kaɗai gatan da zan iya ba shi a yanzu!”
Yabintu ta jinjina kanta.
“Ƙwarai kuwa Daddy kana da gaskiya, kuma hukuncin da ka yanke ya yi dai-dai. Amma kuma idan aka duba za a ga cewar ita ma wayar tana da amfani Daddy, domin ko karatun ma zai iya yinsa ta waya, assignment da sauransu… Dan haka ni dai da za bi tawa da an sai masa wata, amma kuma ba za a ba shi ba sai an kafa masa dokoki da ƙa’idoji, wanda idan ya kiyayesu to ya shafawa kansa lafiya, idan kuma ya ƙi sai a ƙwace wayar!”
Daddy ya kuma kallon Khalid da ya sunkuyar da kansa tun lokacin da Daddyn ya fara faɗawa Yabintu abubuwan da ya yi, kafin ya jinjina kansa.
“Shikenan Fatima, inshaallah za mu duba iyuwar hakan…! Zuwa yaushe za ki leƙo gida ne?”
“Yauwwa Daddy Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana… Batun zuwana kuma zan iya shigowa Zamfara nan da next week, domin mun kusa samum Mid-semester break, so zan zo na yi good 1 to 2 weeks a gida, kafin mu dawo a ci gaba da fafatawa!”
“To Allah ya kawoki lafiya, sannan a ci gaba da dagewa a kan karatun nan, tun da yanzu ƙiris ya rage a gama”
Ta jinjina kanta tana murmushi.
“Haka ne Daddy…”
Ba su jima suna magana da Daddy ba Mummy ta karɓa, ita kam sun ɗan sha hira, kafin suka yi sallama, Khadija ba ta ƙarasa bata labarin Faɗimen Bandalo ba ƙiran Umar ya shigo wayarta, dan haka ta jingine komai ta tsaya yin waya da shi kaɗai.