Skip to content
Part 3 of 6 in the Series Zarge by Fatima Rabiu

Room No. 19 Gamji Royal Hotel, Gusau, Zamfara State Nigeria

Ringing ɗin wayar a karo na uku ne ya sa su tsaida albidar da suke kan yi, da ƙyar kyakkyawar matashiyar ta miƙa hannu ta ɗauki wayar tana ɗan ɓata fuska kaɗan. Shi ko saurayin dake rungume da ita har yanzu bai fasa abunda yake mata ba sai kiss yake kai mata kota ina.

“Hello Mama me ya faru ne? Muna cikin aji ana cikin lecture kin sani fa”

Daga cikin wayar Mama ta ce “Haba Bilkis tun ɗazu fa nake ta faman neman wayarki amma ba’a ɗauka… Kuma ga shi har yamma ta yi ba ki dawo ba”.

“Mama kin san cewa idan muna aji ba’a ɗaukar waya, yanzu ma sai da na fito tukunna na ɗauki wayar taki”.

“To shikenan sai kin dawo, kuma dan Allah ki kula, karatun nan da aka sa a gaba a dage a yi shi!”.

Bilkis ta ɗaga idonta tana juya shi cike da gundura da maganar Mama a kan wani karatu, ƙasa-ƙasa tace.

“To inshaallah”

Daga haka ta yanke wayar tana jan ɗan guntun tsaki, kamar wacce tayi waya da ƙawarta ko abokiyar gabarta. Saurayin dake naniƙe da ita ya saki wani murmushin gefen baki yana cewa.

“Ke fa shegiyar kan ki ce Baby Bilkees. Uwar da ta haife ki, ki ke ma haka?”.

“Hmm kai dai kawai asha sha’ani. Duk ɗaukarsu fa school nake zuwa kullum, shi ya sa fa nasa aka raba mana school da Yaya Falak, saboda ba na son abin da zai kawo min cikas a harkata. Duk ɗaukarsu ni nitsatssiya ce mai jin magana wacce karatu kawai ta sa a gabanta, shi ya sa kullum nake riga Falak fita daga gida, a kan hakan kullum sai Hajiya ta mata faɗa, tana cewa ta riƙa yin ɗabi’u irin nawa, wai ko ta ga dai-dai a rayuwarta… Shi ko Ya Faisal da ya bawa Falak kyautar abu gara ya bani, kuma sai ya ƙirani sau biyar bai ƙirata sau uku ba, kullum gani yake cewar na fi Falak nutsuwa”.

Saurayin ya yi dariya.

“Gaskiya kin iya takunki, da ba ki bari an haɗa muku school ɗaya da ‘yar uwarki ba, da sai ta tona miki asirin cewa baki yawan zuwa school”.

“Ai ko da na karya Shegiya, dan ita ma ƙarara take nuna ƙiyayyata dake zuciyarta, ni ma dannewa kawai nake ina kulata, domin na sa a ga laifinta, amma Wallahi ko ni ba na sonta, ita ma ga shegen baƙin halin tsiya”.

Saurayin nata ya ƙara ja musu bargo yana cewa. “Manta da zancen kawai… mu hole kawai kan ji?”.

FALAK POV.

zaune take a tsakiyar samari Maza da Mata, can nesa kad’an dasu kid’a ne ke tashi sosai ‘yan mata da maza sai rawa suke suna chashewa. Wasu kuma a zazzaune suna shan giya da sigari da wasu ƙwayoyin maye.

Daga inda suke Falak da Khamis na zaune waje ɗaya, sai lallaɓata yake kan yauma ta sha ƙwaya, amma ta ce ita fa yau ba ta jin za ta iya shan wani abu, domin yau saura kaɗan asirinta ya tonu wajan Hajiya.

Kallonta ya yi yana kamo hannunta, da sauri ta fisge tana cewa “No Khamis na sha gaya maka cewa ba na so kana yawan taɓani, a tsaya iya shan kayan maye kawai, amma ba na jin zan iya baka kaina, ka sani kuma ba na so kana yawan kawo hannunka jikina please”.

Ta ƙare maganar fuskarta a murtuke, da sauri Khamis yace

“Ohhh I’m so sorry Baby luv, na manta ne, Amma…”

Dakatar da shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu, za tai magana wani abokin Khamis ya zo wajen, ya ja hannun Khamis suka ɗan bar wajan.

Falak dake bin ko ina da kallo, idonta na gane mata yadda wata budurwa da saurayi dake nesa da inda take zaune suna kissing juna. Wani dogon tsaki Falak ta ja, tana kauda idonta daga garesu, har hakan ya jawo hankalin wasu kanta.

Dan ita kam kwata-kwata ba za ta iya yarda da wannan ƙazantar ba, ta fi gane kawai ta sha tayi mankas abinta, amma fa bata yarda wani shege ya raɓeta ba.

Wasu ‘yan ƙwayoyi ta ɗakko tasa a baki ta kora da wani maganin mura kwalba guda, tsabar yadda take jin ranta a ɓace yasa ta ɗauki ƙwayoyin da Khamis ya mata tayinsu ɗazu amma ta ƙi sha. Bayan wasu mintoci ta fara jin kanta ya fara juya mata, idonta na lumshewa a hankali.

Lokacin da jikinta ya saki ta kwanta a kan kujera tana jin duk hayaniyar da ake a wurin na tashi sama-sama. A lokacin kuma wani matashi ya shigo wurin, kuma yana shigowa ya wuce wurin abokansa da suka gayyato shi. Bai jima da tsayawa kusa da su ba ya hangi Falak, wadda ta ji duniyar ta mata nauyi, hakan yasa ta tashi zaune kanta na juyawa.

Ba tare da ya bari kansa ya kulle ba kawai ya nufi wurin da take, domin har ga Allah ya ɗauka cewar ita ma kamar sauran ‘yan matan dake wurin ce, ma’ana mace mara kamun kai, domin ba shi kaɗai ba, duk wani wanda zai ga wata mace a wurin haka zai ɗauketa, domin da ma wurin ba na ‘ya’yan mutunci ba ne.

A kusa da ita ya zauna yana kallon yanda take ta layi daga zaunen da take, kansa ya juya ya kalli mutanen wurin, sannan ya sake matsawa kusa da ita, hannunsa ya ɗaga ya kai jikinta zai taɓa hannunta yana lasar baki kamar maye.

“‘Yan mata barka da yamma!”

Ya faɗa yana taɓa hannunta, duk da Falak na jin jikinta ya yi nauyi sosai hankalinta bai gushe ba, domin ba ƙaramar ƙwaya za ta sha ta sa hankalinta ya gushe gaba ɗaya ba, kuma hakan ya samu nasaba ne sakamakon jininta da yake da ƙarfi. Ba wai mayen ne ba za ta yi gaba ɗaya ba, a’a za ta yi maye, amma hankalinta na jikinta, so duk abin da za’a mata ko a furta kusa da ita za ta ji, kuma za ta riƙe a kwakwalwarta kamar tana cikin hayyacinta.

“Kyakkyawa kamarki bai kyautu ace kina zaune ke kaɗai ba, ya kamata ki bani dama a yau ɗin nan na nuna miki soyayya!”

Ya kuma faɗa yana taɓa damtsen hannunta, a lokacin kuma ta yi ƙarfin halin bige hannunsa daga jikinta, tana watsa masa jajayen idonta.

“Kar… Kar ka sake…!”

Ta haɗe kalaman da ƙyar tana nuna shi da ɗan yatsanta a kasalance. Saurayin ya yi murmushi, sannan ya sake kaiwa hannunsa jikinta a karo na uku, ganin ba za ta iya jurewa ba yasa ta tattaro duk waji guntun ƙarfi da ya rage mata, sannan ta ɗaga hannunta ta kwaɗa masa mari.

“Kar ka… Ka sake taɓani na ce… Ɗan akuya kawai!”

Marinsa da ta yi, da kuma kalaman da ta furta yasa gaba d’aya hankali ya dawo kansu, shi kuma saurayin ya miƙe tsaye yana tunanin irin abin da zai mata, yana shirin rama marinsa da ta yi wata budurwa cikin waɗan da suka gayyace shi wajen ta zo ta ja hannunsa suka bar Falak kwance.

 “Kai kuwa me ya kai ka zuwa wajan budurwar Khamis? Wadda duk wajan nan an san cewa ba ta da mutunci, to ko shi Khamis ɗin yana son ɗanata amma taƙi ba sa damar hakan”.

Cewar budurwar da ta jan ye shi.

“Shi ya yarda har yake lallaɓata, tana a bige ma zai iya mata illa ba ta sani ba”.

“Kayya! Ai ba zai taɓa iyawa ba ne shi ya sa, kamar ta mass asiri, hatta wannan shaye-shayen da take da ƙyar ya shawo kanta ta farasa, amma mu’amala da Maza, kam taƙi”.

“To wata ƙila sonta yake da gaske shi ya sa ba zai iya rage zafi da ita ba, ko kuma asirin ta mai, ni da ace ni ke da waccan ai Wallahi da tuni na gama da ita ta wannan wajan”

Sabon Titin Kwaɗo, Katsina State, Nigeria

ZAHRA POV.

Zama Amira tayi a kan gado, bayan ta dawo daga wurin Mahmud. Zahra dake kwance akan ɗayan gadonta, tana karanta wani book ɗinta na school ta tashi zaune tana cewa.

“Ya na ga kin dawo sai sakin murmushi kike, hala an shirya ba?”.

Wani murmushin Amira ta ƙara saki tana cewa.

“Uhum an shirya, kawai tausayi ya bani wallahi, bawan Allahn nan yana sona sosai.”

Zahra ta yi dariya tana rufe book ɗinta.

“Ai dole, ni ma wallahi ya birge ni, sai kuma ki ɗan rage ɗora hoton naki tunda dai kinga ba ya so, ki yi ƙoƙarin faranta masa kema… Kuma da ma kwana nawa ne ya rage ki shiga daga ciki?”.

Amira dake kallon Zahra tace “Ohhni ‘yasu wai yau kece ke bada shawarar a kula da saurayi, keda ba abin da kika sani a cikin soyayyar ma?”

Murmushi kawai Zahra ta yi tana ɗan gyara zamanta a kan gadon tana cewa.

“Hmm ba wani abu na ce ba ai, shawara ce na baki kyauta, ku da kuke soyayyar sai ku yi ta fama ai, kullum raine a ɓace kai da mutum shi ya sa kwata-kwata ba ta birge ni”.

“Hmm lallai yarinya, za ma ki yi ne nan gaba kaɗan, sanda zata kamaki ta kanainaye miki zuciya ba ma zaki sani ba”.

“Bana ganin ranar za ta zo kuwa”.

Da ɗan mamaki Amira ke kallon Zahra ta ce.

“Kambu! Anya yarinyar nan baki da iskokai a kanki kuwa? Yo idan ba haka ba, ta ya za ai ka ji dad’in rayuwa babu masoyinka a kusa da kai?, Kina da babban aiki fa a gabanki wallahi. Ko da yake Mummy zan sa ta rinƙa amso miki rubutu gaskiya ki rinƙa sha”.

Dariya kawai Zahra tayi tana girgiza kanta ta koma ta kwanta, domin gobe da safe zata fita, tana da lecture d’in safe. Yayin da ita kuma Amira ta tashi ta shiga bayi tana ta mitar halin Zahra, a lokacin wayar Zahra dake aje a gefen pillownta ta yi ringing, hakan yasa ta ɗauka ta duba.

“Hello Zahra Beauty”

Cewar wata murya wadda daga ka ji ta za ka san cewa mai ita ta iya tsiwa. Zahra ta yi dariya.

“Yane Kulsum mummuna”

Suka kuma yin dariya a tare.

“Wai A. Sani cewa tace gobe bayan mun gama class ɗin 8-10 za mu tafi Aldusar Parks mu je mu huta a can!”

Zahra ta girgiza kanta, dan da ma ta san zancen gizo ba zai wuce na ƙoƙi ba.

“Yanzu ku bayin Allah ana daf da fara exam kuna zancen zuwa hutu? Ina muka ga hutu a lokaci irin wannan?”

Tana iya jiyowa sautin tsakin Kulsum ta cikin wayar.

“Ke! Tsakanin mutuwa da hisabi babu wanda za a fasa, dan haka gobe kawai ki shirya mu tafi, kuma ki taho mana da shepherd’s pie… Na san kin iya yinsa sosai!”

Kulsum ba ta damar cewa komai ba ta katse ƙiran, murmushi kawai ta yi ta aje wayar, tana yo wa Kulsum ɗin addu’ar shiriya.

Channels Television Station, Abazie Ifeanyi Close, Guzape, Abuja Nigeria

BILAL POV.

A hankali ya sauƙe wayar dake manne a kunnansa yana ɗan juya kujerar da yake zaune akai. K’arar bud’e k’ofar Office d’insa ne ya sa shi d’an d’aga kai yana duban mai shigowa, ganin Aliyu ne yasa ya miƙe tsaye ya soma tattata kayansa yana faɗin.

 “Zan wuce gida, gaskiya yau da wuri nake son tashi”.

Aliyu bai zauna ba yana tsaye ya ce “Oga ne yake son ganinmu gaba ɗaya fa”.

Ɗan kallon Aliyu Bilal ya yi kafin ya saki ƙaramin tsaki yana faɗim “Cewa za kai ɗan rainin wayo ke son ganinmu, hala wani abu ya ji dan gane da binciken da na ke yi ko?”.

“Naga alamar hakan daga garesa. Amma dan Allah Bilal kar ka nuna irin zuciyarka a wajansa, ka bi komai a hankali please, na san halinsa bai wuce ya ce, kwata-kwata ka cika shiga abin da bai kamata ba, ko kana son basu matsala a gidan Tvnsu ba, ka san abin da ka binciko abu ne babba sosai, wadda ya ƙunshi ɗaya daga cikin manya-manyan ƙasar nan, so da ma dole ka fuskanci matsaloli tare da k’alubale”.

Bilal ya sauƙe kansa yana ɗan lumshe idonsa sai kuma ya buɗe, dan har sun sauya launi sunyi ja kaɗan, saboda matsalar k’asar da take yawan ci masa tuwo a ƙwarya.

“Shin idan shugabanni na haka sai zuwa yaushe ci gaba zai wanzu a ƙasar nan Aliyu? Taya za a yi ka binciko gaskiya ga abu k’iri-k’iri, an san cewa gaskiyar ce amma a tauyeta?, A gaskiya ba zan ci gaba da lamuntar hakan ba, kuma shi yasa muke samun matsala da Sir, domin shi duk abin da za a binciko sai yasa an rage wani abu daga cikin binciken da aka yi, saboda yana tsoron bada rayuwarsa ne?, Ko kuwa cin hanci suke kawo masa? Ni na rasa gane inda ya dosa”

Da sauri Aliyu ya ce “Haba Bilal wane irin cin hanci kuma, gara ma dai kace ko tsoro yake ji kar mutanan suje har inda yake su ce za su cutar da shi, domin ba Allah a ransu, duk wani abu da zai basu matsala kawar da shi suke, shekara nawa suna aikata irin haka, ka ji an taɓa kawo ƙarshen abin?”.

Bilal ya ɗan saki murmushin da ya fi kuka ciwo ya ce “To mi ye aikin Jaridar da ma?, ba taimakon al’umma da hukuma ba ta hanyar bankaɗo abubuwan da aka ɓoye ba ne?, Kuma in dai kana da tsoro ko shakka a ranka to ba za ka tab’a aikin jarida yadda ya dace ba, in dai kuma baka da gaskiya shi ma bazaka tab’a aikinka yadda ya kamata ba, za ayi ta cutar jama’a ne, kai kuma mai gaskiyar tsoro sai ya saka ka danne gaskiyar taka, ka bada dama ke nan domin a cuci jama’a, komi kake fa Allah sai ya tambaye ka ranar gobe?”.

Jikin Aliyu ya yi sanyi ya ce “To Bilal Sir fa ba zai tab’a fahimtar wannan ba, amma ban sani ba ko ya fahimta idan ka masa bayani kamar yadda kake min haka, amma mu ma kanmu muna kasada da rayuwarmu ne Wallahi”.

“Ni ko zan rasa rayuwata a wannan aikin ba na jin zan damu, burina shi ne, na bankaɗo gaskiya komai ɗacinta”.

Yana idasa maganar ya nufi k’ofa, shi ya fara fita kamin Aliyu ya take masa baya.

<< Zarge 2Zarge 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×