Nigerian Law school, Bwari, P.M.B 170, Garki, Abuja Nigeria.
YABINTU POV.
Cikin hanzari take shiryawa, domin sun yi da Umar kan zai zo ya ɗauketa dan ya kaita ta duba jikin mahaifiyarsa dake kwance a asibiti ba lafiya. Gaggawar da take ta yi ce ta sa Khadija da Laura da ta kawo ziyara ɗakin nasu suka shiga dubanta.
“Wai Umar ɗin ya zo ne?”
Laura ta tambaya tana kama baki. Ba tare da Yabintu ta kallesu ba ta saka clip ta riƙe veil ɗin da ta yafa a kanta, kafin tace.
“Ya kusan ƙarasowa dai! You all know that I don’t want keep him waiting”
Laura da Khadija suka yi dariya, har da tafawa.
“Oh soyayya ruwan zuma…”
Cewar Khadija, ba ta ƙarasa ba Laura ta caɓe da.
“In ka sha ka ba masoyi”
Ita dai Yabintu murmushi kawai ta yi tana kallon fuskarta a mirror. Lokacin kuma wayarta ta shiga ƙara alamun shigowar ƙira, da yake da ma ƙiran nasa take jira sai ta yi saurin ɗaukan wayar ta amsa.
“Hello Hayati gani nan a ta wajen babban gate!”
Faɗin Umar ta cikin wayar, dan haka Yabintu ta yi murmushi tana juyawa a jikin mirror.
“Okay gani nan fitowa”
Tana gama faɗin hakan ta sauƙe wayar, sannan ta ɗauki handbag ɗinta, ba ta fita ba sai da ta kuma gyaggyara jikinta, kafin ta fita, su Laura na mata dariyar shaƙiyyanci.
A inda yace mata ya faka ta same shi, shi da kansa ya fito ya buɗe mata motar ta shiga, yana ta yabawa da irin kyan da ta yi.
“Wai me ya samu Umma da faja’atan ta kama rashin lafiya?”
Ta tambaye shi lokacin da ya ɗauki hanyar zuwa asibitin da aka kwantar da mahaifiyarsa. Umar ya dubeta yana driving da hannunsa ɗaya, yayin da yake shafa sumarsa da ɗayan hannun nasa.
“Jininta ne ya hau ba gaira ba dalili! Amma dai su likitocin sun ce da alama ta ci ɗaya daga cikin abubuwan da hawan jinin ya haramta mata ne”
Cike da tausayawa Yabintu ta girgiza kanta.
“Allah ya bata lafiya”
“Amin ya Rabbil izzati”
Har suka isa Abuja Continental Hospital yana bata labarin yanayin ciwon mahaifiyar tasa. Shi ya mata jagora har zuwa ɗakin da aka kwantar da ita, lokacin da suka shiga kuma suka iske ƙannensa huɗu a cikin ɗakin, Mata uku na miji ɗaya. Su huɗun gaba ɗaya sai da suka gaisheta cikin girmamawa, ta amsa tana ta murmushi, kafin ita kuma ta miƙa tata gaisuwar ga mahaifiyar su Umar ɗin.
“Lafiya ƙalau Fatima Bintu! Ya makaranta ya karatu! Ya kuma wajen su Umman taki?”
Mahaifiyarsu Umar tace yayin da suke gaisawa da Yabintu. Kan Yabintu a ƙasa tana murmushi ta amsa da.
“Wallahi komai lafiya Umma, su ma suna lafiya, nan da jibi ma zan je hutu gida…”
“Ahhh to mashaallah! Allah ya taimaka…”
Ta jima a asibitin suna ta hira da ƙannen Umar, domin da ma can sun saba da ita. Sai da lokaci ya fara ƙurewa sannan tace za ta tafi, ƙannen Umar mata sai da suka rakata har zuwa parking space dake ƙasa, kafin suka koma, shi kansa Umar a hanya sai da ya tsaya ya mata siyayyar guzirin da za ta kai gida. Kafin ya dawo da ita cikin hostel ya tafi.
House No. 17, Aguiyi Ironsi Street, Off Ahmadu Bello way, Durumi District, Abuja.
Da misalin 09:13 na dare.
BILAL POV.
Cike da kula ya ɗaga electric kettle ɗin dake ɗauke da tafasasshen ruwan zafi, ya tsiyaya ruwan zafin a cikin wani mug da ya saka ganyen shayi, sai da ya zuba ruwan yanda zai isheshi, kafin ya mayar da kettle ɗin ma’ajinta ya aje. Ya kashe socket ɗin da kettle ɗin ke jone a jiki, kafin ya koma kan sandwich ɗin da ya haɗa. Duk da dare ne ba ya jin zai iya cin wani abu bayan sandwich ɗin, domin bayan tarin gajiya da ayyukan da suka shige masa ba ya jin yana da lokacin zama ya girka wani abin mai nauyi.
Fitowa ya yi daga kitchen hannunsa riƙe da plate mai ɗauke da yankan sandwich biyu da kuma mug mai ɗauke da tean da ya haɗa. Lokacin da ya ratso ta falon da babu hasken komai cikinsa sai na Tv ya yanke shawarar zama a falon domin ya ci sandwich ɗin a nan. Sanda ya zauna ya janyo center table ya aje mug tare da plate ɗin da yake riƙe da su a kan table ɗin.
Sannan ya ɗauki remote control ya sauya channel daga StarPlus zuwa Channels Tv, domin yana so ya ga ko za a saka rahoton da ya kawo bayan yin cecekuce tsakaninsa da shugansu na wurin aiki, duk da sun tsaida magana kan za a fitar da rahoton tunaninsa bai gama yarda kan za a saka ɗin ba, gara ya gani da idonsa.
Remote control ɗin ya aje, lokacin da ya ga har an yi nisa a rahoton ƙarfe tara na dare da ake haskawa, ya ɗauki mug ɗinsa ya kai baki ya yi sipping tea ɗin dake ciki kaɗan, hankalinsa gaba ɗaya yana kan Tvn, rahoton da yake ta tuƙuburin gani shi ne na ƙarshe a cikin rahotannin da aka gabatar, sai dai duk da haka ya yi farin cikin ganin labarin, domin babu abin da aka rage na daga wanda ya kawo.
Sai da aka gama haska labaran bai ci ko rabin sandwich ɗin da ya haɗa ba, duk kuwa da muguwar yunwar da ya kwaso daga wurin aiki. Sai da aka gama ɗin ne ma kafin ya samu sukunin cinyewa, ya ɗauke kayan ya kai kitchen, bai fito ba sai da ya wanke duk abubuwan da ya ɓata. Lokacin da ya fito daga kitchen ɗin wayarsa dake gurzawa a kan sofa ta ja hankalinsa.
Ko da ya ɗauki wayar har ƙiran ya katse, a nan ya ga 3 missed call daga Aliyu, kasancewar wayar a vibration mode take yasa ƙaran wayar bai fito ba. Murmushi kawai ya yi, ganin ƙiran Aliyu ya sake shigowa wayar a karo na huɗu, kuma ya san me yasa yake ta jera masa wannan ƙiran kamar wanda yake binsa bashi.
“Yane?”
Kawai yace yana ɗaga wayar.
“To! Buri ya cika, an haska labarai kuma an bada rahoto, yanzu sai mu koma gefe mu ga abin da zai wakana!”
Wani murmushi mai kyau Bilal ya yi yana shafa kwantaccen gashin sajensa, kafin yace.
“Inshaallah komai zai tafi kamar yanda muke fata, ko hukuma da gwamnati ba su ɗauki mataki ba wannan rahoton ya isa ya wayar da kan al’umma game da illar tura yaransu mata ƙasashen waje zuwa aikatau! Kuma ka ga ko ta nan ma mun yi nasara!”
Ya ji alamar Aliyu ya gyaɗa kansa, kuma ƙasa-ƙasa yake jiyowa muryar tilon yaron Aliyun yana wasa.
“Ina madam da Boy?”
“Suna lafiya gwauro!”
Bilal ya yi dariya yana zaunawa a kan sofa.
“Ka yi ka bar ni! Komai lokaci ne, kuma na Allah ne, mu ma inda rai da rabo namu na nan tafe”
“Allah ya nuna mana…”
Wayar tasu ba ta tsawaita ba ta ƙare, saboda ƙiran Adebisi wata abokiyar aikinsu da ya shigo ya kori na Aliyu.
“Yanzu na gama kallon labaran da aka haska yau! Gaskiya ka yi na mijin ƙoƙari B. Liman!”
Faɗin Adebisi cike da farin cikin abin da abokin aikin nata ya yi. Bilal ya shafa kansa yana faɗin.
“Ƙoƙarin ba nawa ne ni kaɗai ba, har da ke Ade, domin ke ma kin taimaka da taki gudunmawar!”
Ade ta yi dariya.
“Komai zan maka zai zama kamar na yi wa kaina ne B. Liman!”
Ta kuma ƙiran sunansa da ta saba ƙiransa da shi, wato B. Liman, cikakken sunansa kuma Bilal Bashir Liman, ana taƙaitawa ne da B. Liman ɗin kawai dan ya fi sauƙin faɗa ko a baki.
“Zuwa yaushe za ki dawo?”
Ya tambaya, dan yanzu haka ita Adebisi tana garin Enugu.
“Nan da sati mai zuwa zan dawo”
“Ki kawo min tsarabar doya”
Shi kansa da ya yi batun sai da ya yi dariya, ballantana kuma ita da ya shaidawa.
“Wa zai girka maka doyan idan na kawo? Ko Mama za ka kaiwa?”
Ya girgiza kansa yana taɓe baki.
“Ni zan ci abata!”
“To zan kawo maka, kar ka damu”
“To na gode, ni zan sauƙa a kan layi!”
“Okay bye”
Ya aje wayar a gefensa, sannan ya ɗaga kansa yana shafa sumar kansa, sabon aikinsa da ya saka a gaba yana yawo cikin tunaninsa.
Sabon Titin kwaɗo, Katsina state…
Mummy ta aje flask biyun da take riƙe da su a kan center table, kafin ta waiga ta kalli Daddy dake operating wayarsa.
“Ga abincin nan”
Ta idasa maganar tana zama kusa da shi, kafin ta ɗauki plate ta shiga zuba masa abincin, har sai da yace ya isa, ya aje wayar hannunsa sannan ya karɓi plate ɗin ya soma cin abincin.
“Su Zahra sun kwanta ne?”
Daddy ya cillowa Mummy tambayar, yayin da take zuba masa drink a cikin cup. A hankali Mummy ta aje cup ɗin da ta zuba masa drink ɗin next to plate ɗin abincinsa.
“Ba lalle ba, ita Zahra ɗazu ta dawo daga Aldusar Park, kuma na san a gajiye take, yanzu haka ba za ta kasa baccin ba, ita dai idon screen ina da tabbacin ba ta yi baccin ba”
Abba ya yi dariya jin sunan da ta ƙira Amira da shi.
“To ko zuwa gobe da safe ne ki sanar da su, zuwa gobe su shirya, tun da Saturday ce na san Zahra ba ta da class, za mu je Gyaza mu duba Hajiya!”
Mummy ta yi murmushi tana shafa cinyarta.
“Ai ba sai gobe ba, yanzu ya kamata na gaya musu, domin su shirya tun yanzu, duk da na san ba kwana za mu yi ba kamar yanda muka saba!”
Daddy yana taunar abinci ya jinjina mata kai.
ZAHRA POV.
Yayin da Amira ke soyewa tana ƙonewa da Mahmud saurayinta a waya ita kuwa duk ƙauri ne ya cika mata hanci. Tana kwance a kan gadonta, ta kunna kallo a system ɗin Amira tana kallon wani indian series. Duk da a gajiye take daɗin Film ɗin ya hanata kwanta da wuri, don so take ta gama kallon wannan episode ɗin sai ta kwanta, saboda yau Kulsum da A. Sani wato Aisha Sani ƙawarsu sun bata wahala kamar me, dan bayan Aldusar Parks and Zoo da suka yi niyyar zuwa tun farko har Maryam Park suka ja ta.
Sai da ta yi nadamar binsu zuwa wannan yawon, kuma tsabar tijara duka da uniform suka fita, kowa ya gansu ya ga ɗalibai. Rabi da rabi hankalinta na kan wayar da Amira ke yi da Mahmud, wadda ke kwance tana wani juyi, alamun wayar tana kai mata har ka, ta wani kashe murya kamar ba ita ba. Ita har mamakin kalaman da Amiran ke amfani da su a wayar take, dan ita kam ji take ba za ta iya ba. A wani ɓangaren kuma zuciyarta ce ke raya mata cewar anjima kaɗan za ta shukawa Mahmud tsiya, domin Amira ba a abin arziƙi da ita, ko sun shirya to fa sai ta yi abin da zai sa su ɓata.
Har episode ɗin ya ƙara Amira ba ta gama wayar ba, da yake ta gaji sai ta rufe system ɗin, ta ɗorata a kan side drawern da ta raba gadonta da na Amira. Sannan ta ɗaga bargonta ta rufa a kan ƙafafunta, ta lalubo hula ta saka a kanta, sannan ta shiga yin addu’o’in bacci da na kariya.
“Ya Amira mu kwana lafiya”
Ta faɗa tana shirin kwanciya, shigowar Mummy ɗakin ce ta katse abubuwa biyu lokaci guda, kwanciyar Zahra da kuma wayar da Amira ke yi da Mahmud.
“Au! Har yanzu ba ku kwanta ba ke nan?”
Mummy ta tambaya tana binsu da kallo.
“Yanzu dai zan kwanta… Ya Amira kuma waya take”
“In ji wa? Ni ma kwanciyar zan yi ai!”
Cewar Amira tana harar Zahra, alamun dake nuna ke ke ba a rufin asiri da ke?. Mummy ta yi murmushi, kafin ta furta musu wasu kalmomi da za su zama sanadiyayyar rabuwarsu da juna na har abada.
“To! Daddynku yace ku shirya, zuwa gobe za mu tafi wurin Hajiya a Gyaza!”
Zahra ce ta fara zumbur ta tashi zaune tana kallon Mummy.
“Dan Allah Mummy?”
“Da ina muku wasa ne?… Sai da safe”
Ta ƙarashe tana rufe ƙofar, dan da ma ba ta gama shigowa cikin ɗakin gaba ɗaya ba. Zahra da Amira suka dubi juna, cike da farin cikin batun tafiyarsu Gyaza, domin gaba ɗayansu babu wanda bai son zuwa Gyaza, wato mahaifar Daddynsu, inda ‘yan uwansa da mahaifiyarsa suke zaune… Dalilin son zuwansu Gyaza shi ne, ana nuna musu gata sosai, duk sanda za su je suna ganin gata a wurin ‘yan uwan ubansu…
Kakarsu ma haka na matuƙar ji da su, duk da tun da yanzu lamuran tsaro suka ɓaci idan sun je ba sa kwana a can, zuwa suke su yini su dawo cikin garin Katsina. A cikin daren suka tashi suka fara shirya kayan da za su saka gobe idan za su tafi, kai kace zuwa za su su yi wata a can. Kuma tun a cikin daren Amira ta faɗawa Mahmud batun tafiyarsu zuwa Gyaza… Wata tafiya da za su yi nadamar yinta, a lokacin da nadamar ba za ta amfanesu da komai ba.