Unguwar Samaru, Gusau, Zamfara state, Nigeria.
08:22 na dare.
FALAK POV.
Zaune take a falo, hannunta na dama riƙe da smoothie jar, yayin da take juya straw ɗin dake ciki a hankali da hannunta na hagu… Jin takun mutum ta wurin stairs bai sa ta kalli wurin ba, dan kowa ya yi wa Falak shaidar shariya da rashin kunya, wai kuma hakan ma ko kaso biyar cikin ɗari na halin ɗan uwanta Faisal ba ta ɗauka ba…
“A dawo lafiya Bilkis, dan Allah ki kula, ki duƙufa ki yi karatu sosai!”
Muryar Mama da ta ji ce ma tasa ta samu arziƙin kallon wurin da suke tsaye ita da Bilkis, ta sha dogon Hijab har ƙasa, domin da ma ita ba ta da shigar da ta wuce dogon Hijabi, a wasu lokutan ma idan za su fita tare da Falak sai tace ba za ta je da ita ba, don ita ba za ta bita da dogon Hijabi kamar matar takaba ba…
“Inshaallah Mama”
Faɗin Bilkis kanta a ƙasa, sai da Mama ta gama mata nasiha, sannan tace mata ta tafi, ta gaban Falak ta zo ta wuce tana mata sai da safe, wani ɗan iskan kallo Falak ta bita da shi, wanda yasa lokaci guda Bilkis ta kama kanta, sannan ta fita daga falon da sauri.
“Falak! Kallo ake ne?”
Mama ta tambaya yayin da take zaunawa a kan settee, Falak na zuƙar smoothie ɗin dake cikin jar ɗin hannunta ta kalli Mama, kafin ta ciro straw ɗin daga bakinta tana murmushi.
“Umm kallo nake”
“Ke ba za ki yi karatun ba?”
“Wani karatu kuma Alaji?”
Ta furta ba tare da ta damu da zancen karatun ba, domin a yanzu ba shi ne a gabanta ba, a duniya idan tana da maƙiyi to bai wuce karatu da makaranta ba, shi yasa a wasu lokutan take haura sati ba tare da ta leƙa makarantar ba, duk kuwa da yanda Kawunsu Alhaji Sammani wanda ya ci gaba da kula da kasuwancin mahaifinsu bayan rasuwarsa yake kashe mata kuɗi sosai a kan makarantarta.
A wani ɓangaren ma za ta iya cewa damuwar karatu ce ta saka ta fara shaye-shaye, ba wai dan ba ta gane karatun ba, haka kawai take jin cewa ta tsani makaranta da duk wani abu da ya shafeta, a lokacin da tace ba za ta ci gaba da zuwa makaranta ba Hajiya ta balbaleta da faɗa, har ta kai ga tace idan ba ta maida hankali kan karatunta ba sai ta tsine mata, kuma daga lokacin ta fara shaye-shaye.
“Ba exams za ku fara ba?”
Ta ɗan kalli Mama kaɗan, kafin ta girgiza kanta.
“Na sani, amma ni ba yanzu zan fara nawa karatun ba…”
“Sai zuwa yaushe ke nan? Uwar malalata”
Muryar Hajiya ta katse mata hanzari, dubanta ya kai kan Hajiyar dake tsaye jikin banister.
“Ai in dai ba za ki maida hankali a kan karatunki ba mun yi ta samun matsala da ke”
Ita dai ba tace komai ba, jar ɗin hannunta kawai ta aje a kan center table, Hajiya ta ƙaraso cikin falon, lokacin da Mama ke faɗin.
“Haba Hajiya? Ai ba haka za ki riƙa mata ba! Cikin lallami za ki na mata nasiha, ki kuma nuna mata hanyar da kike son ta bi”
“Humm! Maman yara ke nan! Yanzu Falak ba ta yi hankalin da za ta yi wa wani faɗa ba? Da wannan girman nata zan wani zaunar da ita ina lallaɓata?”
Ita dai Falak ƙala ba tace musu ba, dan idan ta faɗa ɗin ran Hajiya ne zai ɓaci nan take, kuma za ta iya yin kanta da faɗa, wata ƙila ma ta bugeta, yawan faɗan Hajiya yasa gaba ɗaya ba su yi wata shaƙuwa da ita ba, kullum cikin tsare gida take, babu wani lokacin samun kusanci irin na ‘ya da uwarta a tsakaninsu, ita kuma ba ƙawa gareta ba ballantana idan damuwa ta mata yawa ta samu wani da za su tattauna da shi domin samun mafita…
Shi ko Faisal kar ma ta soma tunkararsa da batun shawara ko wani abu, mutumin da sai su yi wata ba su ga farin haƙorinsa ba, saboda sam shi dariya ba ta dame shi ba, kullum fuskar nan a ɗaure tamau, kamar haddarin da ya so zubar da ruwa, wasa na wa da ƙaninsa ma ba ya haɗata da shi, ballantana har ta kai su ga hira, kuma shi in zai yi magana umarni yake bayarwa, ka ƙi bi kuma jikinka ya gaya maka.
“Ina Bilkis ne? Ban ji motsinta ba”
Faɗin Hajiya, Mama ta yi murmushin jin daɗi.
“Ta tafi makaranta, tace yau a hostel za ta kwana saboda suna da exams gobe, so tana so ta yi karatu sosai…”
Hajiya ta wurgawa Falak dake latsa wayarta harara.
“Kin ji fa? Yarinyar kirki, wadda ba ta sa shashanci a gaba ba, ita karatun ne kawai a gabanta…”
“Ai ita ma Falak ɗin tana karatun Hajiya, kawai dai sai san barka”
“Ina fa…”
Ƙofar falo da aka ƙwanƙwasa yasa hirar tasu dakatawa.
“Falak tashi ki duba waye”
Falak ta aje wayar hannunta, sannan ta nufi ƙofar ta buɗe, tana arba da wanda yake bayan ƙofar ta ja tsaki a fili tana ɗauke kai.
“Falak waye?”
Hajiya ta tambaya tana zaune daga cikin falo.
“Sirikarki ta gobe ce”
Ta faɗi maganar cikin shaguɓe, tare da buɗe ƙofar gaba ɗaya, Maryam budurwar Faisal kuma ƙanwar Mama ciki ɗaya ta bayyana ga su Hajiya. Lokaci guda Hajiya ta washe baki tana miƙewa tsaye.
“Maryam? Ke ce tafe?”
Maryam dake tsaye a bakin ƙofa ta shiga ciki, yayin da Falak ke binta da wani kallon rashin kunya, duk da ta lura sai ta ɓoye, da yake ita ma ‘yar bariki ce sai ta matsa kusa da ita za ta rungumeta tana faɗin.
“Ohhh my little sister…”
Dakatawa ta yi, lokacin da Falak ta ɗaga mata hannu alamun ta dakata.
“Ja jikinki a nawa!…”
Kawai tace, sannan ta juya ta ɗauki wayarta ta yi sama, shi ma wannan Maryam ta shaƙa, amma ganin Hajiya da Mama yayarta yasa duk ta shanye komai, ta nufi wurin Hajiya tana gaisheta kamar ta Allah. Hajiya ko kamar ta saka zani ta goyata, dan ita kanta ba ta ce ga dalilin da ya sa take son Maryam ba, kuma soyayyar da take mata ce tasa lokacin da ta nuna cewa tana son Faisal Hajiyar ta yi Uwa ta yi makarɓiya ta tilasta Faisal amincewa da soyayyar Maryam, duk kuwa da shi ɗin ba ya sonta.
“Amma dai a nan za ki kwana ko?”
Cewar Hajiya lokacin da ta kawowa Maryam drink. Maryam ta yi sipping drink ɗin, kafin tace.
“A’a, yanzu ma zan koma, mun yi magana da Major ne a kan wani book da na daɗe ina naima, yace mini shi kuma yana da shi, shi yasa na zo karɓa”
Hajiya ta kama baki tana ‘yar dariya.
“Ikon Allah! Ai kuwa kin ga bai barwa kowa keyn ɗakinsa sai Bilkis, ita kuma yanzun nan ta fita!”
Kamar da gaske Maryam ta ɓata fuska cikin rashin jin daɗi.
“Oh oh, amma ban ji daɗi ba Wallahi”
“Ah haba Maryam? Kar ki ji ba daɗi mana, bari na saka Falak ta zo ta duba miki”
“Za ta yarda kuwa? Kin san halin Falak fa?”
Hajiya ta ja tsaki.
“Ita ta haifi kanta?”
“A’a Hajiya, amma bari dai na ƙira wanda zai iya sakata ko da ranta bai so ba”
Ta ƙarashe tana latsa wayarta, a cikin contact list ta naimo lambar ‘Heart beat’ sannan ta aika masa ƙira.
Falak na shiga ɗakinta ta kwanta a kan gado, damuwar Hajiya da abin da mata duk sun bi sun hanata bacci… Da ta ga ba za ta iya ba sai ta tashi zaune, sannan ta sauka daga kan gadonta ta sunkuya a ƙasan gadon, ta miƙa hannunta ta janyo wata jaka dake ƙasan gadon, ta fito da wasu kwalaban kayan maye guda biyu, ta mayar jakar ƙasan gadon, sannan ta zauna a kan gado, ta buɗe kwalba ɗaya tana shirin ɗurawa cikinta wayarta ta dakatar da ita… Tsaki ta ja, sannan ta rufe kwalbar tana miƙa hannunta saitin wayar, ganin sunan ‘MR. BEAST’ ya fito ɓaro-ɓaro a kan screen yasa ta zaro ido. Ta yi saurin aje kwalbar, ta goge bakinta, har da su kimtsa kanta kamar wadda ya ƙira videocall.
“Assalamu alaikum! Ya Faisal ina yini”
Ta faɗa a salihance, domin ko kusa ba ta son abin da zai haɗata faɗa da Faisal, dan sai ta gwammaci barin zaman gidansu gaba ɗaya a kan Faisal ya yi fushi da ita. Daga cikin wayar, wata murya mai kauri, wadda ta ƙunshi zallar kamewa da kwarjini ta fito ta doki dodon kunnenta.
“Da ban wuni ba za ki jini haka? Kina ina?”
Falak ta juya idonta, a ranta kuwa faɗi take. _”Masifaffe”_
“Ina zan je a lokaci irin wannan? Ai ina gida?”
“Ok! Maryam ta zo, ki je ɗakin Bilkis ki ɗauko keys ɗin ɗakina, ki je ki buɗe, a cikin wannan shelf ɗin da yake kusa da desk za ki ga wani book mai suna ‘The Inner Child’ ki ɗauka ki bawa Maryam”
Cike da takaici Falak ta cije leɓenta na ƙasa, dan ta san da gangan Maryam ɗin ta aikata mata haka. In dai kuwa haka ne yanzu za ta gasa mata maganar da za ta hana mata sukuni.
“Shikenan yanzu zan je na ɗauko mata… Yaushe za ka dawo ne Yaya?”
Abin ka da ɗan uwa, sai ta samu kanta da tambayarsa hakan, duk da ta san ba lalle ta yi gwaninta ba, dan wata ƙil ma gwasaleta zai yi, kuma sai ya yi abin da take hasashen.
“Ban sani ba”
Kawai yace a dake, dan haka ita ma ba ta sake cewa komai ba ta aje wayar tana kallonta, duk da bai katse ƙiran ba, shi a rayuwarsa ba a yanke masa ƙira, ko da kuwa kai ka ƙira shi ba shi ya ƙiraka ba, saboda a wasu lokutan ya kan manta abin da zai ce, sai bayan wasu mintoci kuma zai tuna, sai ka ga ya faɗa maka, wani lokacin kuma maganar ta ƙare, amma saboda isa da gadara ba ka isa ka kashe masa waya ba sai in shi ya kashe. Har bayan shuɗewar wasu sakkani, kafin Falak ta ga ƙiran ya katse, a bayyane ta ja tsaki, sannan ta ɓoye kwalaban da ta fito da su, ta ɗauki wayarta ta kuma fita.
Ɗakin Bilkis ta shiga, ta ɗauki keys ɗin, sannan ta sauƙo ƙasa tana bin Mama da Maryam dake hira da kalll, dan zuwa lokacin Hajiya ba ta falon, wani ɗan iskan kallo ta wurgawa Maryam, kafin ta yi ƙwafa ta fice daga falon. Part ɗin Faisal dake gidan ta shiga, sannan kamar yanda yace mata haka ta yi, har ta samu book ɗin. Lokacin da ta fito take kulle part ɗin nasa ta ji muryar Maryam a bayanta.
“Yauwwa Sister, kin ɗauko mini?”
Ta juyo tana kallonta.
“Ga shi na ɗauko ƙuda sarkin naci!”
Ta faɗa tana danƙa mata book ɗin a hannunta, a karo na uku Maryam ta shaƙa, dan tun da ta zo Falak ke mata abubuwan da ba su mata daɗi.
“Kar ki damu sister, yayanki ya kusa zama nawa”
Falak ta yi murmushi mai sauti tana harɗe hannayenta a ƙirji.
“Idan ma bacci kike to ki farka! Domin jelar raƙumi ta yi nesa da ƙasa Maryam, kuma ko da girgiza kurna ta fi magarya, dan haka Ya Faisal ya fi ƙarfinki, na san kina ganin kamar kalamaina a matsayin shashanci ko wauta. Duk ki cire wannan, batu ne na gaskiya nake miki, Faisal ba zai taɓa aurenki ba”
Maryam ta yi murmushi tana juya book ɗin dake hannunta.
“Zan so ace na ga yanda za ki yi ranar da na mallaki yayanki a tafin hannuna!”
Falak ta yi taku biyu zuwa gabanta, sannan ta ɗaga hannunta dake riƙe da wayarta ta dafa kafaɗarta.
“Wannan ranar ba za ta zo ba Habibty ‘yar wahala”
Tana gama gasa mata maganar ta janye hannunta daga kan kafaɗarta, sannan ta raɓata ta wuce tana karkaɗe hannunta da ya taɓa Maryam ɗin, kamar wadda ta ɗauki buhu mai datti. Haka Maryam ta bi bayanta da kallo a kufule, tana hasaso kalar abubuwan da za ta yi wa Falak bayan ta shigo gidan a matsayin batar Faisal.
YABINTU POV.
Gaba ɗaya ƙawayenta ne suke zazzaune a ɗakinsu, yayin da suke hirar tafiyar da za ta yi, duk da wasu daga cikinsu su ma za su je gida.
“Ni fa ji nake kamar na biki mu tafi Zamfara tare!”
Cewar Khadija… Yabintu ta wurga mata hararar wasa.
“Kamar da gaske, ke ɗin da tsoro ya cika miki ciki kika kasa zuwa last time da muka yi za mu tafi da ke?”
“A’a ni fa ban ga laifinta ba! Yo ai ko ni ba zan iya zuwa yankinku a halin da ƙasar nan take ciki ba”
Faɗin wata daga cikin friends ɗin nasu.
“Kai duk fa wannan abubuwan da kuke ji ana yi bakinsu ƙauyuka… Ba su shiga cikin gari”
Cewar Yabintu.
“To ai ka fin a isa garin dole sai an ratsa ta ƙauyen ko?”
Cewar wata tana taɓe baki.
“Wallahi duk kallonku nake, kawai dan abin bai zama muku dole ba ne shi yasa!”
“Ke da ya zamewa dole sai ki je… Mu dai Allah ya yaye mana”
Yabintu ta yi dariya kawai.
“Amma dai da Umar za a je ya yi rakiya?”
Faɗin Laura a sigar tsokana.
“Ai shi ba rago ba ne kamar su o’o, tun da shi da ‘yan uwansa suka tashi tun daga Abuja har zuwa Zamfara suka je naiman aurena!”
Gaba ɗaya su shida suka sheƙe da dariya.
“Oh Yabintu da Umar soyayya kamar ba za a rabuba! Mu dai Allah ya kaimu lokacin bikin nan mu cashe!”
Faɗin Khadija tana ɗaura ɗankawalin kanta da ya since, Yabintu ta yi murmushin jin daɗi.
“Amin”
Ta amsa tare da sauran… Su da kansu suka tayata shirya kayanta, domin zuwa gobe za ta bi jirgi zuwa Sokoto, daga nan kuma za ta hau mota ta kaita cikin Gusau. Sai da aka gama shirya kayan kuma aka dawo aka ci gaba da hirar da rabinta ya fi karkata a kan karatunsu da suke daf da gamawa.