Skip to content
Part 6 of 6 in the Series Zarge by Fatima Rabiu

Channels Television station, Abazie Ifeanyi Close, Guzape, Abuja.

BILAL POV.

Zaune yake a office ɗinsa yana wasu rubuce-rubuce, sosai ya maida hankali kan rubutun da yake, lokacin da ya ɗiga aya ya miƙa hannunsa na dama ya ɗauko wata takarda, kamin ya fara wani rubutu a kanta, shigowar Aliyu office ɗin ce ta sa ya dakatar da rubutun da yake, na tattara wasu bayanai game da binciken da yake son farawa.

Kuma kallo ɗaya ya masa ya sake maida hankalinsa kan rubutun da yake. Aliyu dake kallonsa tunda ya shigo ganin yadda aiki ya sha masa kai, yasa shi zama kawai.

Ƙara kallonsa Bilal ya yi, ganin yadda ya yi shuru ya sa Bilal ture tarin takardun dak gabansa, kamin ya ɗan murza goshinsa yana runtse idonsa, kamin ya ware hannunsa ya d’auki wata takarda yana ta kallonsa, jin shirun ya yi yawa yasa shi ya fara magana.

“Me ya faru ne na ganka a haka?”.

Ya tambaya ba tare da ya kalle shi ba, A hankali Aliyu ya aje masa fallan jaridar da ya shigo da shi a kan table ɗinsa. Bilal ya bi takardar da kallo, kuma kafin ya kai ga karanta abin da ke rubuce a jiki Aliyu yace.

“An kama shugaban ƙungiyar GKL hukuma tace za su gudanar bincike a kansa da ƙungiyarsa”

Bilal ya sa hannu ya ɗauki jaridar, sannan ya bi hoto haɗe da rubutun dake jiki, ya miƙe tsaye yana ci gaba da kallon jaridar.

“Ban sani ba ai, saboda tun da na tashi yau wani aiki ya sha min kai… Alhamdulillah”.

Ya faɗa muryarsa ɗauke da murnar yin nasara, ya koma ya zauna yayin da Aliyu ke murmushi.

“Ɗazu Victor ke sanar min cewa wai ka ɗauki hutun sati guda… Yanzu kuma wani sabon aikin za ka yi?”

Bilal ya aje jaridar da yake ta riƙe da ita, sannan ba tare da jin komai a ranaa ba yace.

“Bincike a kan ‘yan bindigar cikin daji! Waɗan da suka addabi mahaifata da maƙotanmu!”

Ido waje Aliyu yake kallonsa, ya tabbatar Bilal ba zai bar aiki ba sai ya jawowa kansa da ma su gabaki ɗaya mutuwa.

“Lallai ka d’auko bincike mai tsananin had’ari tare da rikitarwa, domin kuwa shi ma wannan akwai sa hannun wasu hafaffu da mai a ƙasa, me yasa wai kai ba ka da aiki sai binciko abubuwa maau haɗari irin waɗannan?”.

Bilal ya yi murmushin gefen baki.

“Kawai addu’a za ka min, ku sai ku tsaya a matsayarku, amma ni dai na sa a raina cewar sai na binciko duk wata badaƙalar da ake a ban ƙasa… Zuwa gobe zan wucw Zamfara”.

Bilal bai tanka masa a kan maganarsa ya farko ba, domin ya san maganarsa ba ta isa ta sa Bilal ya fasa abin da ya yi niyya ba… Tun da har yace zai yi to zai yi, dan haka ya tsallake wannan maganar yace.

“Za a je duba Mama ke nan?”

“Eh ka san na kwana biyu ban je ba, kuma idan na je can zan fi samun wasu bayanai daga wurin mutane”

“Gaskiya kam, to Allah ya tsare, ya kaika lafiya, a miƙawa Mama saƙon gaisuwata, sai mun yi waya”.

“Yeah, amin thank you”.

Daga haka Aliyu ya tashi ya fita ya bar shi zaune yana nazarin ta inda zai fara aikin da ya ɗauko.

*Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, Nigeria.*

YABINTU POV.

Zaune take a cikin motar Umar, isowarsu ke nan filin jirgin, kuma dalilin da ya sa ba ta fito ba wai sallama suke, kuma lokacin tashin jirgin da saura, dan wajejan awa ɗaya sauya.

Kallon Umar ta yi, ganin yadda yake kallonta kamar zai cinyeta, murmushi ta saki tana ɗan gyara zamanta a cikin motar ta ce.

“Ya da wannan kallo kuma? Sai kace wacce ba za ta dawo ba?”.

Umar ya sauƙe ajiyar zuciya, yana ɗan shafa sumar kansa kamin ya ce.

“Ji nake kamar kar ki tafi ne, kuma sai da muka zo filin jirgin na fara jin hakan”.

Wani murmushin Yabintu ta saki tana cewa “Uhum kamar fa yau ne za ka ga na dawo, ai hutun ba mai yawa bane, it’s just 1 to 2 weeks… And whenever you missed me you can give me a touch abi?”.

Ba ta san sanda ya kamo hannunta ba, sai ji ta yi yana murza shi kaɗan-kaɗan, haka kawai yake jin kamar idan ta tafi za su rabu ne har abada… Tun da Yabintu take da shi bai tab’a gigin koda tab’a d’an yatsanta ba, shi ya sa take kallonsa cike da tsananin mamakinsa.

“Hayati na ga jikinka ya yi sanyi, ka daina damuwa please lafiya lau zan dawo inshaallah”. Cewar Yabintu ganin duk jikinsa ya yi sanyi.

Lumshe idonsa ya yi, kafin ya buɗe ya shiga binta da wani kallo wadda bai tab’a mata irinsa ba, muryarsa a sanyaye ya ce.

“Na sani ba dad’ewa za ki yi ba, amma wallahi haka kawai nake ji kamar a fasa tafiyar nan taki”.

A hankali ta d’an murza hannunsa dake cikin nata tana kallon cikin kwaryar idonsa.

“Ba na so ina ganin damuwa a kan fuskar nan taka fa please, ni da zan tafi a jirgi, kuma insha Allahu ‘kalau zan dawo ka ji?”.

Daga haka ta yi saurin janye hannunta daga cikin nasa, a hankali tasa hannunta na dama ta murɗa murfin motar ta fita, shi ma fitar ya yi yana kallon terminal, ya zagoyi inda take, suka fara tafiya, a ƙofar Terminal suka rabu, suna ta waving ma juna hannu kamar kar su rabu. Daga ƙarshe ma dai tace masa ya zo su ɗan zauna a ciki kafin lokacin tashin jirginsu, bai ƙi ba, domin har ga Allah shi ma bai gaji da ganinta ba.

A kan wasu kujeru suka zauna, Yabintu sai baza idonta take, domin hatta ita kanta zuciyarta ba ta mata daɗi. Suna zaune a wurin wayar Umar ta yi ƙara. A hankali ya zaro wayar ganin mai kiran nasa yasa shi ɗauka da sauri.

“Okay ga ni nan zuwa yanzu insha Allah”.

Abin da ya ce ke nan bayan ya gama sauraron abin da na wayar yace. Kallonsa Yabintu ta yi ganin yadda ya tashi da sauri yasa ta ce “Me ya faru?”.

“Wai Umma ce taƙi shan magani, tace dole sai na zo na ba ta da kaina, na san duk salon kar ta sha maganin ne, saboda na san ba son maganin take ba, ga shi jikin nata sai a hankali har yanzu. I’m so sorry cuz I have to leave before you leave”

Yabintu ta saki murmushi, sannan ta miƙe tsaye tana kallonsa.

“Haba ba komai, ka je kawai, tun da kai ka kawo ni har airport”.

Murmushi ya sakar mata yana ƙara jin ƙaunarta har cikin ransa, sai da ya furta mata i love you kamin ya bar wajan.

Yana niyyar saka key ya tayar da motarsa domin tafiya kawai kamar an ce ya waiga ya hango wata jakar Yabintu da ta manta ta, hannu ya miƙa ya ɗauko jakar, ya fito dai-dai da wayarsa na sake ringing. Yana fitowa daga motar su kai k’aro da wani, tsabar saurin da Umar yake bai ma lura da shi ba. D’agowa ya yi domin bawa wanda ya bige haƙuri, sai idonsa ya gane masa wani tsohon friend ɗinsa Bilal B. Liman.

Murmushi kowanne d’auke a kan fuskarsa Umar ya ce “Ah-ah B. Liman?”.

Bilal ya gyara zaman hular dara dake kansa yana murmushin ganin tsohon abokinsa.

“Na’am Faruk Yola”

Dariya suka yi, sannan suka yi musabihi.

“Ya na ganka a nan? Ko aikin jaridar ne ya kawoka?”

Bilal ya girgiza kansa.

“Ko kaɗan, ganin gida zan je?”

Umar ya yi dariya.

“Sai ka ce wata mace… Za a leƙa Zamfara ke nan?”

“Wallahi da yake na d’an kwana biyu ban je ba”.

Umar zai sake magana ya sake jin k’arar wayarsa, da sauri Umar ya kalli Bilal ya ce.

“Ohhh sorry friend dan Allah ga wannan jakar ka bawa Yabintu, wallahi sauri nake Umma ba lafiya, za ka ganta zaune wajan waiting chairs, ba mu gaisa sosai ba, Allah ya tsare hanya Kuma”.

Yana damƙa masa Umar ɗin ya yi saurin buɗe motarsa ya shiga, ko damar tambayar wace ce Yabintun ma bai ba shi ba, domin shi bai san wacece budurwar Umar ɗin ba.

Bilal ya bi abin da ya basa da kallo. Shi ya za’ai ya gane ta, tunda ba wani saninta ya yi ba, koda yake ya yi masa uzuri da alama jikin Umman nasu ne ya sake tashi, kuma Mahaifiya ai ba abar wasa ba ce, shi ya sa Umar d’in duk ya bi ya rud’e, “Uwa mai dad’i.”

Cewar Bilal a zuciyarsa. Murmushi ya saki sanda ya fara tafiya yana nufar inda waiting chairs ɗin.

Dai-dai lokacin da ya iso wurin, aka fara wata sanarwa cewa jirgin da zai tashi k’arfe 9AM, wadda zai tashi daga Abuja zuwa Sokoto an soke tashinsa sakamakon wasu ‘yan dalilai da ba su bayyana ba, suka kuma ƙara da bawa fasinjojinsu haƙuri game da wannan tangarɗar da aka samu.

Hankali a tashe Yabintu ta mik’e, sai kuma ta saki wani dogon tsaki, a dai-dai lokacin, a wannan wurin, zuciyarta ta ƙissima mata wani abu da ya zama sanadiyyat faruwar ƙaddararta ta rayuwa. Tunanin take kan ba za ta iya jira sai zuwa gobe ba, ta riga ta yanke cewar yau a kan gadon ɗakinta na Gusau za ta kwana, dan haka gara ta hau motar Kaduna daga Abuja, idan an sauƙeta a Kaduna kuma sai ta hau motar Gusau.

Duk da da ba haka tsarin yake ba, idan ta hau jirgi zai sauƙesu ne a Sokoto, daga nan kuma za ta hau kota zuwa Gummi, daga Gummi kuma za ta hau motar Gusau.

Mutane da yawa sun ji haushin tsaida masu tafiya da akai, wasu kuma sun bada uzurin ko jirgin ne akwai matsala ko kuma sun dai hango wani abun ne.

Shi ko Bilal dake tsaye kusa da Yabintu bai ji wani abu ba, Allahn da ya yi hau shi ya yi gobe, kuma goben ma kamar yau take… Tsayawa da ya yi sauraron sanarwar ya mantat da shi saƙon da aka ba shi, juyowar da zai yi suka kusan cin karo da Yabintu da ta ɗauki bags ɗinta.

Kuma hakan ya sa ya tune da saƙon da aka ba shi, sai ya dubeta yayin da ita ma shi take kallo.

“Oh sorry Pleas”

Bilal ya girgiza kansa alamun ba komai, kafin yace.

“please ko ke ce Yabintu girlfriend d’in Umar?”.

Da ɗan mamaki Yabintu ta ƙara kallonsa, dan ba ta sansa ba, shi ina ya santa? Sai kawai ta samu kanta da d’aga masa kai kawai.

Murmushi ya saki yana mik’a mata jakarta dake hannunsa yana cewa “Ga wannan Umar ne ya bada ya ce a baki, kin manta tata ne a cikin mota, yana sauri, shi ya sa ya bani na baki. Kuma gashi an samu matsalar tashin jirginmu”.

Murmushi ta d’an sakar masa, jin wajan Umar ya santa ta amsa tana godiya ta ƙara da. “Eh amma ni ba zan iya jira har sai gobe ba, yau zan wuce gaskiya”.

“Ohh amma baki tsoron hanya?… Saboda akwai hatsari sosai fa”.

“Ba wani abu da yardar Ubangiji lafiya lau zan isa”.

D’aga k’afad’arsa ya yi kamin ya bata bata waje yana mata fatan sauƙa lafiya, lokacin da ya fito faga terminal ya shiga motarsa sai ya ƙira mahaifiyarsa ya sanar mata da cewa an soke tashin jirginsu, sai zuwa gobe zai zo.

A lokacin kuma Yabintu ta fito daga terminal da kayanta, ta tare taxi wadda za ta kaita tashar motar da za ta hau ta Kaduna… A kan idonsa ta shiga taxi ɗin, kuma har taxi ɗin ta bar wurin bai gama wayar ba, sai da ya gama sannan, ya sauk’e numfashi, yana jin kamar bai yi dai-dai ba, da ya bar ta ta tafi, kuma ya san motar haya za ta hau, mi ya sa bai hanata ba? Ko ma ya bita su tafi tare, haka kawai yake jin kamar bai kyauta ba.

*Ƙauyen Gyaza, Kankia Local Government, Katsina State, Nigeria.*

*12:44 na rana.*

ZAHRA POV.

A hankali Zahra ke matsama Hajiya kakarsu k’afarta.

Amira kuma na zaune kusa da Hajiyar tana cin kwaɗon rama da aka musu, duk sun zagaye Hajiya suna mata hira. Hatta Mummy na kusa da Hajiyar suna ta lallaɓata, domin yanda suke son tsohuwar sosai. Shi ko Daddy yana can wurin ‘yan uwa, abin ka da mutan ƙauye, akwai son sada zumunci.

“Wash! ke ki bi min k’afa a hankali fa, ja’ira karki k’arasa ni”.

Hajiya ta k’are maganar cike da wasa da zolaya. Turo baki Zahra ta yi tana cewa.

“Haba Hajja? yanzu ai sai kisa amin dariya, ina malamar asibiti guda?”

Ai kuwa dariyar Amira ta kece da ita, tana cewa “Yo da ma ke mai yima Hajiya gwaninta ai saiya shirya, ke ce da gulma wai sai kin mata tausa, na san hakan sai ta faru ai, shi ya sa ban ma yi gigin cewa zan yi mata ba”. Ta ƙarasa tana cusa rama a bakinta.

Hajiya dake dariya a hankali ta jawo Zahra jikinta tana cewa “Ke rabu da ita dan Allah, wasa nake miki fa, ci gaba da min tausar jikalle, da ma so nake na gane masu jin yaushin ana min tausa kuma na gane ki”.

Ta k’are maganar tana mintsinin cinyar Amira. Amira ta janye jikinta, sannan ta miƙe riƙe da robar da take cin ramar da ita tana faɗin.

“Bari na tashi kar ki ƙarasawa saurayina ni”

“Ai sai na ƙwace saurayin naki ma! In ya so na ga ta tsiyar”

Ita dai Amira ƙin tanka mata ta yi, ta fita tana cin ramarta. Mummy ta yi dariya kawai tana firfita da muhuci, bawai dan gidan babu nepa ba, sai dan Hajiyar ba ya son iskar fanka, domin babu ta inda za ka ga gidan ka ce a ƙauye yake, domin gini aka yi mai matuƙar kyau. Sai wajejan yamma Daddy ya shigo tare da ƙannensa biyu.

“To Hajiya! Mu fa za mu kama hanya kin ga magariba ya kusa, kuma ina tsoron kwana a garin nan, bare ma na d’an zaga an san na shigo garin”.

D’an nisawa Hajiya ta yi kamin ta furta kalamomin da za su yi sanadiyyar wargaza farin cikinsu gaba d’aya.

“Shi ya sa ai ban so ka nausa cikin garin nan ba har wasu su san da zuwanka. Ga shi dare ya farayi, ni kuma ba zan bari ku tafi yanzu ba gaskiya, sai dai ku bari zuwa gobe”.

Daddy ya yi k’asa da kansa cikin bin umarnin Hajiyar ya ce “Shikenan Hajiya za mu kwanan zuwa gobe sai mu wuce”.

Ya faɗa ba wai dan hankalinsa ya kwanta da hakan ba, dan ya san zamansa a garin haɗari ne… Su ko su Zahra daɗi suka ji, domin sun sha roƙon idan suka zo garin kan ya barsu su kwana, amma bai bari, sai yanzu da Hajiya ta faɗa, suna ta murna ba tare da sanin abin da zai biyo bayan hakan ba.

“Yawwa insha Allah ba abin da zai faru. Duk da dai a kusa-kusa damu d’in nan ana ‘yan bindigar suna yawan shigowa, shi yasa abin sai a hankali”.

Cikin Amira ne ya bada wata k’ara tsabar tsoro ta ce “Hajiya to miye na bada labari kuma? Kawai ki yi shiru dan Allah wallahi ni dai har kin samin tsoro, har na fara jin kamar ma kar mu kwana Wallahi”.

Zahra tayi saurin cewa “To amma Hajiya kuke zaune a haka? Ku ma ai nake ganin duk masu kud’in garin sun tashi sun koma cikin birni, ke ma Wallahi kawai da yarda kika yi, idan za mu yafi mu tafi tare da ke”.

Wata dak’uwa Mummy ta jefa ma Amira da Zahra, hakan ya sa ba shiri suka kama bakinsu suka yi shuru. Hajiya ta d’an yi murmushi tana cewa.

“Kyaleta kawai, ai tana da gaskiya, ni kuma gara na mutu a garin nan da kuke gani, ai da zan tashi daga cikinsa da tuni na tashi, ga ubanku nan zaune, ba yadda bai yi i da ni ba domin na koma kusa da shi nak’i, ina dai nan inda nafi wayo, muna ta kuma addu’a a kansu, kuma cikin ikon Allah abin nasu ya yi sauk’i, amma kwanakin nan dai sai Addu’a domin ba ranar banza da za’a tashi da safe ba ki ji labarin cewa sun shiga wani gari nan kusa damu ba, an kashe wani ko an d’auki wani, amma nan dai gaskiya har yanzu ba’a tab’a shigowa ba”.

Ɗaya daga cikin ƙannen Daddy yace “Hajiya da za ki yarda yanzu ma zaku iya tafiya domin alamu sun nuna cewa hankalin Yaya Musa bai wani kwanta da ci gaba da zamanki a garin nan ba”

Hajiya ta girgiza kanta.

“Su dai sa tafi zuwa gobe, amma ni kam zama a garin nan yanzu na farasa”

<< Zarge 5

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×