Ƙauyen Gyaza, Kankia Local Government, Katsina State, Nigeria.
ZAHRA POV.
Bacci suke hani'an a wani ɗaki da aka ware musu ita da Amira, yayin da Amira ta jibga mata ƙafafunta, dan da ma can Amira mummunar kwanciya gareta, hakan yasa ma aka raba musu gado tun suna yara... Tsaki ta ja cikin magagin bacci ta kai hannu ta ture ƙafafun Amiran dake kan cinyoyinta. Amma ba a fi minti uku da yin hakan ba Amira ta sake lafta mata ƙafafun nata a karo na bayu.
Tsakin da ta ja a wannan karon ya fi wanda ta ja da farko. . .