Skip to content
Part 7 of 7 in the Series Zarge by Fatima Rabiu

House No. 17, Aguiyi Ironsi Street, Off Ahmadu Bello way, Durumi District, Abuja.

10:33 na dare

BILAL POV.

Kai kawo yake a cikin falon da babu komai cikinsa sai hasken TV dake a kunne, domin ko kaɗan Bilal bai son hasken wani da daddare, shi yasa a ko da yaushe bulb ɗin gidansa suke a kashe.

Hannunsa ya goya a bayansa, zuciyarsa na masa ba daɗi. Domin har kawo yanzu ji yake hankalinsa bai kwanta ba game da lamarin budurwar Umar. Ga shi ba shi da contact nata ballantana ya ƙitaya ya ji wani hali take ciki.

A hankali ya shafa wuyansa yana haɗiyar wani abu a maƙoshinsa, wanda ya sa Adam’s Apple ɗinsa ya motsa sama da ƙasa. Kujera ya dafa, sannan ya zauna a kan kujerar yana furzar da huci kaɗan, duk ya rasa me ya kamata ya yi. Wani abu ya tuna, dan haka ya ɗauki wayarsa, sannan ya lalubo lambar Umar ya aika masa da ƙira.

“Barka da dare B. Liman! Da fatan kana cikin ƙoshin lafiya”

Shi ne abin da Umar yace daga ɗayan ɓangaren.

“Haka nake fata… Ya jikin Umma?”

Batun jikin Umma da ya ambata yasa Umar bai bawa maganarsa ta farko muhimmanci ba, dan haka yace.

“Umma ta ji sauƙi, dan zuwa gobe they can discharge her”

“To Allah ya ƙara lafiya… Na ce ko ka ƙira girlfriend ɗinka ka ji yanda ta sauƙa gida?”

Bilal ya tambaya zuciyarsa na rawa, na kokwanton amsar da zai iya samu.

“Eh to! Da yake ka san jirgi ta hau yasa ban ƙirata ba, kuma har zuwa yanzu da nake tabbacin tana gida ma ban ƙirata ba, saboda na bata lokaci ne ta huta, zuwa gobe sai na kirata, amma duk da haka na yi mamaki da ita ba ta kirani tace min ta sauƙa lafiya ba!”

Bilal ya rintse idonsa, sannan ya saka hannunsa ta riƙe kansa.

“Lafiya kake tambaya? Ko wani abu ya faru da ku ne a hanya?”

Umar ya sake tambaya jin Bilal ya yi shiru, a hankali Bilal ya buɗe idonsa, sannan ya girgiza kansa yana ajiyar zuciya.

“Flight ɗinmu zuwa Sokoto bai tashi yau ba, sanda na je bata jakarta aka sanar da cewa an soke tashin jirgin… A lokacin ban san dalilin hakan ba, sai ɗazu nake jin an ce wai an samu labarin an kai hari ne a wani ƙauye dake kusa da Sokoton, shi yasa suka soke tashin jirgin…”

“Wait a minute B. Liman, ban gane ba? What are trying to say?”

Umar ya katse shi.

“Ina so na faɗa maka cewar Yabintu ba a jirgi ta tafi ba, bayan an soke tashin jirgin take shaida min cewar ita ba za ta iya jira sai zuwa gobe ba, fan haka za ta je ta hau motar haya!…”

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un!”

Umar ya furta, ba tare da ya bar Bilal ya sake furta komai na ya katse ƙiran, Bilal ya aje wayarsa a gefensa, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi, domin yanzu alamu sun nuna cewa yarinyar nan tana cikin matsala. Duk kuma sai yake ganin laifinsa, domin ya kamata ace lokacin da ta nuna son tafiyar ya bata shawarar kada ta tafi, ko bai hanata kai tsaye ba sai ya sanar da Umar. Amma bai yi hakan ba… Yanzu ga abin da ya faru da ita!.

*****

Umar na katse ƙiran Bilal ya shiga naiman lambar Daddyn Yabintu. Amma jar ta gama ringing ta katse bai ɗauka ba, hankalinsa a mugun tashe ya miƙe tsaye, ya soma safa da marwa a cikin ɗakunsa yana sake dialing lambar. A wannan karon ya yi sa’a Alhaji Haruna Bakura ya ɗaga wayar.

Da ƙyar Umar ya iya saita kansa suka gaisa da Daddy lafiya-lafiya, amma duk da hakan sai da Daddy ya fuskanci akwai matsala tattare da shi. Duk da su ma yau sun yi busy da yawa, na jiran zuwan Yabintu amma shiru har yanzu da dare ya yi. Kuma ko sun ƙira wayarta ba ya shiga, shi yasa ma suka fara tunanin ko dai ta fasa tafiyar ne.

“Umar fatan lafiya? Dan na ji yanayin naka kamar ba lau ba”

Cewar Daddy. Kamar mai jira Umar yace.

“Daddy Fatima ta iso gida?”

Dimmm! Kunnuwan Daddy suka yi, domin tun da ya ji haka ya san cewa Yabintu ta baro Abuja.

“Daddy kana ji na?”

Umar ya sake faɗa jin shirun ya yi yawa.

“A’a har yanzu ba ta ƙaraso ba, idan an ƙirata ma wayarta ba ta shiga, shi yasa ma muka fara zargin ko dai ta fasa zuwan ne?”

Gwajab! Umar ya koma ya zauna a kan kujera, saboda wata irin zufa da ta keto masa.

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un!”

Ya furta yana kama kansa da ya sara nan take.

“Me yake faruwa ne Umar?”

Daddy ya kuma tambaya.

“Daddy yau aka soke tashin jirgin su Yabintu, hakan yasa ita kuma ta yanke hukuncin tafiya a mota, kuka ta tafi ɗin, amma yanzu da kake sanar da ni cewar ba ta isa Gusau ba yasa na fara tunanin ko dai wani abin ya sameta a hanya!”

Duk dariyar Daddy sai da ya ji wani abu ya soki ƙahon zuciyarsa, domin babu tantama kan lalle a halin yanzu ‘yarsa tana cikin haɗari… Amma me ya sameta? Haɗarin mota suka yi? Ko kuma Bandits ne suka sacesu a hanya? Wannw daga ciki hankalinsa zai kama? Wanne?

Gusau, Zamfara state

MARYAM POV.

Kwance take tana bacci a ɗakin hotel ɗin da suka kama, ƙaran wayarta ne ya tasheta a bacci, dan haka ta miƙa hannunta ta janyo wayar, da ƙyar ta buɗe idonta ta kalli mai ƙiran, a zabure ta miƙe zaune tana murstika ido. Sannan jiki na rawa ta amsa ƙiran ta kara a kunnenta.

“Barka da safiya Major”

Na cikin wayar bai bari ta gama magana ba ya dakatarta cikin alamun dake nuna cewa ransa a ɓace yake.

“Me kike da har na jera miki ƙira 2 ba ki ɗauka ba?”

Maryam ta juya idonta cikin takaici, wai dan ya mata ƙira biyu shi ne yake faɗa kamar wanda ya jera mata ƙira sittin… Ita yanzu ya fara gajiya da halin Faisal, ba dan ita tace ta za ta iya ba da tuni ya rabu da bawan Allahn nan.

“Wato ga ɗan iska ko? Na miki magana shi ne kika min shiru?”

Wannan karon a tsawace ya yi maganar, dan sai da ta zabura kamar wadda ke tsaye a gabansa.

“Na… Na shiga wanka ne! Ka yi haƙuri dan Allah!”

Ya yi shiru kawai, can kuma yace.

“From now till Saturday zan iya shigowa Gusau! Na faɗa miki ne kawai dan kina yawan min ƙorafi kan ba na sanar miki da zuwana!”

Maryam ta yi murmushin jin daɗi, kafin tace.

“To Allah ya dawo da kai lafiya My Major!…”

Ya kuma yin shiru, kuma hakan yasa a gane cewa ya gama magana, amma ba ta isa katse masa waya ba tun da ta san hali, dan haka ta aje wayar a gefenta tana kallo, har ya gaji dan kansa ya katse ƙiran. Wani dogon tsaki ta ja tana jan rigarta da ta yar a ƙasa.

“Ai kuma shikenan, yanzu zai dawo ya ishi jama’a da tsirfa da bala’i”

Ta ƙarashe maganar tana saka rigar a jikinta.

“Ke da wa kuma?”

Wani baƙin Alhaji mai ƙaton ciki da ya fito daga bayi ya tabayeta yana binta da kallo.

“Saurayina Faisal”

Allhajin ya yi dariya yana zaunawa a kan gadon, yayin da ita kuma take mayar da tufafinta da ya cire ɗazu.

“Tun yaushe nake cewa ki rabu da shege? Da ace ke me jin magana ce da tuni kin rabu da shi kin zo na aureki!”

Maryam ta yi murmushi tana taɓe bakinta.

“Ai ba za ja gane ba Alhaji Sadi, ba na jin zan iya rabuwa da Faisal, ko da kuwa zai riƙa yankar naman jikina yana cinsa ɗanye!”

“Yo ai kima a banza man kare! Tun da mun riga shi samun wurin”

Ta juyo ta kalleshi.

“Idan ka gama bani kuɗina zan wuce”

Ganin kamar ba ta son zancen yasa shi ma ya share, yace ta je zai mata transfer. Da haka suka yi sallama ta fito daga guesthouse ɗin Alhaji Sadi da suka saba haɗuwa suna sheƙe ayarsu lokaci zuwa lokaci.

Tana shirin tsaida napep a bakin titi wayarta ta shiga ƙara, ganin Mama ce mai ƙiran yasa ta ɗaga wayar ta kara a kunne.

“Wai kina ina ne?”

“Na je wurin aiki”

“Wurin aikin ubanki? Wallahi ko kaffara ba zan yi ba kan wurin wannan mayen Alhaji Sadin kika je ki! Wai Maryam sau nawa zan ce da ke sai kin kama kanki kafin ki mallaki Faisal a hannunki?”

Cewar Mama daga cikin wayar cikin faɗa. Maryam ta juya idonta irin kanki ake ji ɗin nan.

“To wai sui Faisal ɗin wa ya san tsiyar da yake shukawa a Lagos ɗin? Waye bai san sojoji da shegen biye-biyen matan banza ba? Ni Wallahi ba zan daina ba sai aurena da shi ya kusa? Haka kawai zan hana kaina jin daɗin rayuwa saboda wanda bai damu da ni ba!”

“To shikenan! Ki zauna kina kallon ruwa har kwaɗo ya miki ƙafa, ke shaida ce kan yanda muka sha wahala na bin malmai, kafin muka karkato da hankalinsa kanki, idan ba ki yi wasa ba Wallahi Faisal sai ya kufce miki!”

Maryam ta ja tsaki.

“Ni karki tara min jama’a, yanzu ina bakin hanya, ɗazu ya ƙirani yace zai iya dawowa daga yanzu zuwa Saturday, dan haka zan zo sai mu tattauna a gida!”

“To sai kin zo”

Daga haka ta katse wayar yana rantsuwa a ranta har da Allah kan babu mai hanata holewa da samarinta, tun da auna bata kuɗi yanda ya kamata.

Ikorodu Barrack, Lagos, Nigeria.

Zaune a farfajiyar wasu gajerun gine-gine na ofisoshin manyan sojoji dake barrack ɗin, wani farin mata shi ne, sanye cikin complete Nigerian camouflage uniform (kakin sojoji). Ya jingina bayansa da jikin kujerar da yake kanta, kansa a sama, yayin da ya saua idanuwansa cikin shade, yayinda ya ɗora ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya, hularsa kuma a kan gwiwar ƙafarsa wadda take sama.

Nauyin manyan boots ɗin dake ƙafarsa ba su sa ya fasa jijjiga ƙafarsa ba, hannunsa na dama kuma riƙe da fidget spinner (Ban san sunanta da hausa ba, amma na ji ana cewa katantanwar hannu). Duk da idanuwansa a rufe suke haka yake kaɗa sppiner ɗin, yayin da kunnuwansa ke jiyo masa wata waƙa dake tashi a can nesa da inda yake.

“Major Makama”

Take ya ja tsaki jin ƙiran da aka masa. A hankali ya daina jijjiga ƙafarsa, sannan ya sauƙeta daga kan ‘yar uwarta yana gyara hularsa dake aje a kan gwiwar tasa, sannan ya ɗago yana saka ɗan yatsansa tare da gyara glasses ɗinsa da ya zamo. Kuma har zuwa lokacin bai daina kaɗa fidget spinner ɗin dake hannunsa ba.

Major Khalil abokinsa da ƙira shi ya iso wurin da yake zaune yana shan iska, ya ja ɗaya daga cikin kujerun dake wurin ya zauna. Murmushi kawai ya yi yana kallon sppiner ɗin dake hannunsa.

“Kai da wa kuma?”

Ya tambaya, dan ya san ba a rasa nono a riga, abu ne mayuwaci ka gan shi cikin walwala, shi ba a rasa abin da yake ɓata masa rai duk kwanan duniya. Kuma daga zarar ransa ya ɓaci za ka ganshi riƙe da fidget spinner ɗin nan, yana wainta, wai ko ya rage ɓacin ran da yake ciki. Tsaki kawai ya ja, sannan ya saka hannu ya cire shade ɗin da suka saya kyawawan madaidaitan idanuwansa, masu rikitar da ‘yan mata da kuma waɗan da suke ƙasa da shi.

Duk da a zaune yake za ka iya gane cewa shi dogo ne, amma faɗin da yake da shi ya ƙarawa hallitar tsayin nasa kyau, ba shi da wani jiki sosai, amma ko dantsensa ka kalla za ka san yana motsa jiki. Ba fari ba ne sosai, kuma ka zalika shi ba baƙi ba, amma hakan bai rage komai na daga kyawun hallita da Allah ya ba shi ba. Ba shi da gemu ko saje, amma ayana da wani ɗan siririn gashin baki dake tsakanin ƙofofin hancinsa da laɓɓansa. Kuma idan daga nesa sosai kange shi ba lalle ma ka ce yana da gashin bakin ba, sai in ka matso kusa, domin babu gashi sosai. Sumar kansa ba ya da tsayi, domin ya yi askin buzz cut ne, irin askin da sauran sojoji ‘yan uwansa ke yi yawan yi.

“Ba magana?”

Major Khalil ya sake tambaya yana binsa da kallo, Faisal ya ja tsaki yana ɗauke idonsa daga kan Khalil.

“Wannan mara kamun kan ne!”

Major Khalil ya yi dariya. Dan ba sai ya zauna ya masa dalla-dalla ba, ya gane waye mara kamun kan. Shugabansu ne General Audu Kazaure.

“Me ya faru?”

“Wai ɗazu ina zaune mutumin nan ya ƙirani yace na zo na same shi a office, da na je na iske shi da wata karuwa, duk da haka ban fita daga office ɗin ba na tsaya domin jin dalilinsa na ƙirana, amma wai sai ya kalleni yace na jw, idan an jima zai ƙirani… Ma’ana ba shi da lokacina sai ya gama da ita!”

Major Khalil ya Kuma yin dariya, ganin Faisal na matse spinner ɗin hannunsa da ƙarfi, kamar wanda ita ce ta masa laifin.

“Ban da abinka Bilal! Da ma shi General kowa da halinsa ya sanshi!”

“Idan bai yi wasa ba ai mata ne za su kashe shege!”

Shi ko Khalil yace me zai yi in ba dariya.

“Wallahi ba za ka kasheni da dariya ba… So nake mu je siyayya, tun da ka ga jibi za mu tafi”

Cewar Khalil yana miƙewa tsaye. Faisal ya bi shi da kallo, kafin ya sa hannu ya ɗauki hularsa dake kan ƙafarsa, sannan ya miƙe tsaye yana faɗin.

“Me za ka siyo?”

“Komai ma”

Faisal ya ja tsaki.

“Kai fa ba ka da hankali! Wato ba ma ka san abin da za ka siyo ba?”

Khalil ya kuma darawa, kafin ya dafa shi yana faɗin.

“Ni dai in za ka rakani ka ce min komai ma, tun da na saba!”

Da ƙyar dai ya samu ya shawo kansa ya yarda zai raka shi ɗin, duk da iyaka au kaɗai za su fita ba, har da masu tsaron lafiyarsu.

*Huda University Gusau, Eastern Bypass Road, Sokoto Road, Gusau, Zamfara state.*

Wata farar mota ƙirar Audi RSQ ta faka a bakin gate ɗin shiga makarantar. Daga cikin motar, wata farar bafulatanar yarinya ta ɗauki jakarta da sauri yana faɗin.

“Na gode ya FU’AD!…”

Bafulatanin saurayin dakw zaune a mazaunin direba, sanye da suit gray kala ya dubeta yana murmushi.

“To Allah ya taimaka!”

“Amin”

Yarinyar ta amsa tana buɗe ƙofar motar ta fita, tana fita ta rufo masa ƙofar motar, sannan ta nufi gate da sauri-sauri, yayin da shi kuma matashin da ta kira da Fu’ad ya tada motar ya soma ƙoƙarin barin wurin, sai da yavkusa barin layin kafin ya ankara da wani book da ƙanwar tasa ta manta a kotar. Murmushi ya yi kawai yana girgiza kai, kafin ya dawo baya, wannan karon har cikin makarantar ya shiga. Ya fito daga motarsa riƙe da littafin nata, ya nufi faculty of Law, inda ya san cewa a can ƙanwar tasa take.

Tun daga nesa ya hango wata budurwa sanye da abaya blue, tashin farko zuciyarsa ta raya masa cewar ƙanwarsa Umaima ce. Dan haka ya soma ƙwala mata ƙira yana nufar inda take, amma ba ya juyo ba har sai da ya isa kusa da ita, ua saka hannunsa ya riƙo damtsen hannunta, ya juyo da ita yana faɗin.

“Ke wai ba ki ji ne ina ta ƙwala miki…”

Bai kai ga ƙarasa furtawa ba saboda wani lamari da ya faru unexpected.

FALAK POV.

Kasancewar yau Khamis yace mata ba ya gari yasa ta shirya ta tafi Makaranta, ba wai dan tana so ba sai dan ya zame mata dole. Kuma tun da ɗazu Hajiya ke faɗa mata cewar Faisal zai dawo ta hango kamawar watan tashin hankalinta na shirin kamawa. Domin idan yana nan dole ta rage wasu abubuwan, sannan dole ta yi wasu da ba ta yi a baya.

Tsabar murɗɗaɗen halinta yasa ba ta da ƙawa ko kaɗan, ba a makarantar ba ba a gida ba. Ita kaɗai take tafiya a cikin makarantar, tayin da ta nufi Library, dan ba ma ta jin za ta iya attending class ɗin. Kamar daga sama ta ji an riƙo damtsen hannunta hannunta, sannan aka juyo da ita, ɓacin ran rainin hankalin da ta ga ana shirin mata yasa ba ma ta tsaya ta ji abin da mutumin ke faɗa ba, ta rufe idonta ta ɗaga hannunta ta shararawa matashin marin da yasa ya ɗauke wuta.

“How dare you touch me this way?”

Ta furta idanuwanta zare a kansa, ba ta duba girmansa ba, ba ta duna kamalarsa ba, ba ta duba kimarsa ba ta zage ta ci mutuncinsa yadda taso. Shi ko Fu’ad kuncinsa kawai ya dafe yana kallon yarinyar da ya san ba ta kai Umaima ƙanwarsa a haife ba, amma gata tsaye a gabansa tana ci masa mutunci, tasa jama’a na ta kallonsu.

“Ke! Falak! Kar ki sake furta wata mummunar kalma a kan yayana! Dan Wallahi idan har kika sake ni ma sai na mareki!”

Umaima da ta ga abin da ya faru ta faɗa, tana isowa wurin, wani irin kallo Falak ta yi wa Umaiman dake sanye da abaya blue, kusan shigen wadda ke jikinta.

“Shi yayan naki ba shi da ɗa’a ne? Ko gyatuma ba ta koya muku a gida ba? Ya kamata ace kin ba shi labari cewar babu wani ƙazamin saurayi da ya isa ya yi gigin taɓa Falak…”

“Ke har kin isa!…”

Umaima ta faɗa tana ɗaga hannunta za ta mari Falak, amma sai Fu’ad ya riƙe hannun nata.

“Ya isa Umaima! Tana da gaskiya, kin mance book ɗinki ne a car, shi ne na zo zan baki, da na ganta da farko na ɗauka cewar ke ce, shi yasa na riƙe hannunta a bisa rashin sani, dan Allah ki yi haƙuri!”

Ya ƙarashe yana kallon Falak dake binsu da kallon sama da ƙasa. Wani dogon tsaki ta ja, sannan ta juya ta barsu tsaye a wurin ana ta kallonsu.

“Ka yi haƙuri Ya Fu’ad! Kowa ya san halin Falak kan ba ta da mutunci!”

Cewar Umaima tana duba gefen fuskarsa da ya yi ja, alamun a nan ya sha marin, abinka da farin mutum. Fu’ad bai amsata ba, saboda bayan Falak kawai ya bi da kallo, sakamakon wani abu da ya karanto a cikin idonta, wani abu! Wani abu! Tabbas wani abu!.

<< Zarge 6

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×