Skip to content
Part 3 of 9 in the Series Zinariya by Queen-Nasmah

Zango Na Uku (Da Muguwar Rawa)

“Mine ne dalilinki na sakar wa Zinariya guba a jiki ? ” Sarauniya Jahiyana tayi maganar tana kallon bangon ɗakinta, Juhaina da ke tsaye bayan Sarauniya domin amsa kiran da ta mata ta ce “Mama Sarauniya kiyi min adalci, mun kawar da duk wani jinsi mai ƙarfin iko a cikin kogon Gimatuwa, kwatsam kika kawo Zinariya masarautarmu, na yi duban taurarinta hakan ya nuna min ita ce Sarauniya ta gaba bayan ke, a da babu wata Sarauniya da zata yi mulkin garin nan sai ni, amma zuwanta yana neman sauya min ƙaddarata, ba zan jure ko da Jahida ba ce a ce ta ƙwace matsayina ballanta bil’adama.

“Sarauniya ta juyo ta zuba zara-zaran idonta a kan Juhaina ta ce “Da muguwar rawa, gara ƙin tashi Juhaina, idan har kika yi yunƙurin kashe ta za a jarabce mu da annoba mara ƙarshe, kuma dole kiyi haƙuri da wannan tsarin, Zinariya ce magajiyata”, Idon Juhaina suka canza launi zuwa tsanwa, jijiyoyin jikinta gabaɗaya suka fito ta buɗe bakinta cikin tsananin fushi wuta na walwali daga cikin bakinta ta ce “ba zan lamunce wa kowace irin hilitta a doron duniya ba, babu wannan ranar da ni Juhaina zan yi rashin nasara, sai na kashe Zinariya ko da haka zai janyo kowa ya mutu ” ta na gama faɗin haka ta ɓace. Sarauniya Jahiyana ta saki wani farin haske daga idonta tana murmushi ta ce “ina fatan ki canza shawara. Kafin ki janyo mana tashin hankali”.

Bitarmash

Mutanen Gimatuwa na matuƙar girmama ɗakin bitarmash , nan kowane mutum ke zuwa domin bautawa abar bautarsu wato Bizani, an gina wannan ɗakin a cikin masarauta, sannan aka ware ranaku uku na zuwa wurin bauta, ranar kowace litinin a garin wanda yake ranar sa’a a irin wannan ranar mutanen garin sukan yi shiga cikin fararen kaya sannan su durƙusa gaban abar bautar Bizani su riƙa kai kukansu , sai ranar bauta wanda yake ranar Laraba a irin wannan ranar kuma sukan yi shiga cikin korayen kaya, sannan su sujada ga abar bauta su na jinjina mata tare da yaba mata , ranar Asabar kuma suna kai wa abar bautarsu kayan marmari, da kaututuka domin nuna godiyarsu gare ta.

Cikin ɗakin Bitarmash Juhaina ta shigo, hannayenta guda biyu ta haɗe wuri ɗaya tare da duƙar da kanta gaban abar bauta Bizani, ta rufe Idonta, sannan ta buɗe su ta sauke akan sassaƙen gunkin da suke kira abar bautarsu ta ce “Abar Bauta Bizani ki albarkace ni “, hannunta ta miƙa ta shafa ƙafar abar bauta sannan ta taɓa goshinta. Ta juya ta kara hannunta ga kasko wuta, sannan ta sake haɗe hannayenta biyu ta na faɗin “zan gusar da Zinariya daga numfashi a doron duniya, ni mabiyiyarki ce mai biyayya a gare ki, ki ba ni iko na kawar da Zinariya daga rayuwar duniya.”

*****

Jahida na zaune gaban madubi ta shafa wannan ta shafa wancan Jamina ta shigo ta zauna gefen gado tana faɗin “wai anya rayuwarki ba a madubi za ta ƙare ba? “, Jahida ta yi murmushi ta ce “idan ke zaki ƙarar da ita ga madubi ai sai ki zo”, Jamina ta ce “ to na ga kullum kina zaune gaban madubi “, Jahida ta ce “nakan ga abunda duniya take ciki ne idan na kalli madubi”, “ga shi ke baki da wani aikin yi sai kallon rayuwar wasu ko? ” Jamina ta tambaya, Jahida ta Harare ta, ta ce “ban sani ba, yanzu dai kafin ki dame ni ina mara lafiyarki?”, Jamina ta numfasa ta ce “ta fita yawon miƙe ƙafa, wai zata gaida ƴan masarauta “, Jahida ta ce “haka yana da kyau, da kin sani kin bi ta ko na huta da sa idonki “, ɗan murmushi kawai Jamina ta yi ta sulale kan gado sai barci. Jahida ta ce “a dai rage mugunta kar a sha jini da yawa ” dan ta san halin ƴaruwarta , idan ka ga Tayi barci da rana to jini zata sha, kafin ta tashi sai an rasa rayuka uku ko huɗu.

*****

A ɓangaren Zinariya kuwa zagayen masarauta take tana gaida hadimai da bayi na masarauta, ƴar wata raga ta leƙa ta ga Hibshiyana Zaune riƙe da alƙur’ani tana karantawa, zagawa tayi ta shiga ɗakin da Hibshiyana take. Ta samu wuri ta zauna. Ganin Zinariya yasa Hibshiyana rufe ƙur’anin bayan ta kai aya. Sannan ta kalli Zinariya tana murmushi ta ce “Amincin Allah ya tabbata a gare ki ranki ya daɗe “, murmushi Zinariya tayi ta ce “wai shi wannan littafin miye sunansa?”, shafa alƙur’anin Hibshiyana tayi ta ce “littafi ne mai tsarki, wato alƙur’ani, an saukar da shi ne ga shugabanmu annabi Muhammad saw zuwa gare mu mutane”, “ wane ne shi Muhammad? ” Zinariya ta tambaya, Hibshiyana ta ce “shi ne cikamakon annabawa, an aiko shi zuwa gare mu domin ya sanar da mu musulci”, Zinariya ta gaɗa kai ta ce “to ta ya zaki koya min wannan littafin, ya na min daɗi idan kina karantawa “, Hibshiyana ta ce “zan koya miki idan har kin shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne”, Zinariya ta ce “ita fa abar bauta Bizani? “, Hibshiyana ta ce “Ranki shi daɗe addinin musulunci shi ne gaskiya, Bizani fa sassaƙen gunki ne da ƴan garin Gimatuwa suka sassaƙa da kansu, shi ubangiji Allah ba a ganinsa, bai barci, bai angaje, bai da ɗa, ƴa, mata ko jika, shi ne Allahu, Al’azizu, Al-jabbar, sarkin da babu kamar sa “, Zinariya ta ce “ni na tashi ne akan tafarkin bautar bizani”, Hibshiyana ta ce “nima na karɓi musulci ne bayan rasuwar iyayena, Sarauniya Jahiyana mai adalci ce shi ya sa ba ta taɓa tilastawa ko da tsuntsu ba ne ya yi abunda ba ya so, kar ki yi zaton zata hana ki . Na fahimci ubangiji yayi ni’imomi da yawa ga bayinsa masu biyayya ga dokokinsa, addinin musulunci ya kare haƙƙin ɗan adama, ya haramta jinin ɗan’uwanmu akan ɗan’uwanmu (zubar da jini/kashe-kashe), ya haramta zinace-zinace, dalilai da yawa suka janyo ra’ayina ga addinin musulunci, na fahimci an ƙawata musulunci da abubuwan jin daɗi, idan kika shiga musulunci zaki fahimci daɗin da rahamar Allah take da shi “, Zinariya da tayi shiru tana sauraren Hibshiyana ta ce “bari na tashi na tafi, idan na sake zagayowa sai mu ci gaba”, Hibshiyana ta ce “to shi kenan a sauka lafiya”, Zinariya ta miƙe ta tafi, Hibshiyana ta ci gaba da karatunta.

<< Zinariya 2Zinariya 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×