Zango Na Hudu (Rayuwar Zinariya)
Dajin Jazamana ya rikiɗa yayi baƙi ƙirin, dabbobi sai kuka suke yi suna wani gunji, Juhaina ta diro cikin wani baƙin mayafi tafin hannunta ya dafa ƙasa mayafin ya sauka ya mamaye kaso ashirin cikin ɗari ya filin wurin, zakuna da kuraye suka zagaye ta, yayinda tsuntsaye suka cira sama suna zagayen sararin samaniya, hannunta ɗaya ta saka ta yaye mayafin da ya lulluɓe mata fuska, a hankali ta fara ɗago fuskarta wanda ƙwallayen idanunta suka fito waje kamar za su faɗo ƙasa duk jajjayen jijiyo yi sun fito raɗo-raɗo kan su, haƙoranta guda biyu na gefen bakinta na sama sun sauko har suna iya taɓa gemunta, mayafin ya tashi sama saboda tsananin iskan da ke kaɗawa gashin kanta ya bayyana wanda ya ware kamar zai tashi sama sai juyawa yake yi, ta ware hannayenta biyu faruttanta suka fito dogaye ta wane banƙare jikinta ta ɗage kanta sama ta saki wata mahaukaciyar ƙara mai ɗauke da guguwa “ahhhhhhhhh” duk wata jijiya ta jikinta ta fito cikin launin baƙi, ƙasa ta fara girgiza, dabbobin suka ƙara yawa fiye da na ɗazu, ta sake yin wata ƙara wadda ta fi ta ɗazu, nan take macizai suka fara fitowa daga cikin ramukansu suna zagayeta “Abar bauta ki albarkace” ta faɗa, sannan ta miƙe hannayenta da ta ware ta gaba, ta juyar da hannunta wata jar wuta ta soma fita “ki farmaki rayuwar Zinariya da gaggawa ” ta faɗa tana sakin wutar, wutar da Jahida ta saki ta dunƙule kanta ta shiga juyi kamar ba wuta ba ta miƙe tsaye, Jahida ta sake sakin wata wutar, har sau bakwai tana yin haka, sannan ta rufe idonta ta turo ƙirjinta ta ƙara banƙarewa kanta yana kallon sama ta buɗe bakinta wata Koriya kala ƴar siririya mai matuƙar ƙyalli ta fito, sai kuma ta fara sakin wuta daga idonta, ta cira sama tana juyi, ita ba sama ba , ita ba ƙasa ba.
Zinariya na tafiya zata je wurin Hibshiyana kawai ta ji shigar wani abu kamar mashi a jikinta, take ta faɗi jini yana bin hancinta da baki, ɗaya daga ciki hadiman masarautar Jasra ta nufo ta da gudu ganin yadda ta sulale ta faɗi tana faɗin “ranki ya daɗe Abar bauta ta taimake ki “, idon Zinariya tuni suka kafe, tana rawar sanyi, jikinta har wani ciccira yake yi, Jasra ta miƙe ta nufi fadar Sarauniya, bayan mintuna da ba su wuce biyar ba ta dawo tare da wasu mata suka ɗauki Zinariya zuwa fadar Sarauniya Jahiyana. Jikin Zinariya ya canza launi zuwa tsanwa, wata farar kumfa na fita a bakinta, dan sosai take jin jikinta na mata ƙuna, cikinta kamar babu komai a ciki sai wuta, ga wani irin mugun ciwo da zuciyarta ke mata. Sarauniya na ganin halin da Zinariya Take ciki ta yi saurin miƙewa tana miƙa hannunta Saman cikin Zinariya tare da rufe idonta gam tana ƙoƙarin cire wutar da ke ci cikin jikin Zinariya, ta sani ko ba a faɗa Mata ba wannan aiki Juhaina ne, idon Sarauniya yayi matuƙar yin ja, ƙwayar idonta ta fito kamar zata faɗi, cikin tsananin fushi kira sunan Juhaina “Juhaina!”
Sautin muryar Sarauniya Jahiyana ya daki dodon kunnen Juhaina da ƙarfi ta ɗago bakinta na zubar da jini ta ɗaga murya da ƙarfi tana faɗin “faɗan nan ba naki ba ne Mama Sarauniya, ki cire kanki, dan yau sai na kawar da Zinariya daga doron ƙasa.”
Ran Sarauniya ya ƙara ɓaci jin abun da ƴar tata ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai ta ɗaga hannunta sama nan take wata ƴar ƙaramar kibiya ta bayyana, hannu ta sa ta kamata, ta ce “Juhaina zan yanka jikina na ba Zinariya zuciyata, zan ga yadda zaki kashe ta.”
Juhaina ta ce “Mama Sarauniya ko gangar jikinki zaki bata sai na ga bayanta” ta faɗa idonta na fitar da wani haske mai matuƙar kaifi.
Jahiyana ta kalli Zinariya, sannan ta kalli bangon fadarta ta saki wani haske nan take ya tsage ta cira sama ta bi ta Bango ta fita.
Zinariya ta fara juyi, tana kuka. tana fitar da jini, tana wulle-wulle, Jamina ta shigo fadar tana haki dan yanzu labari ya je kunnenta Zinariya na can kwance kamar matacciya, cikin tashin hankali ta janyo Zinariya jikinta ta rungume ta sosai, sannan ta rufe idonta tana ƙoƙarin Mayar da ciwon jikinta, amma Ina abun ya ci tura, iya yadda tayi ƙoƙarin rage ciwon iya yadda yake ƙaruwa.
Sarauniya Jahiyana ta dira a dajin Jazamana, Juhaina na ganinta ta ƙara cirawa sama, Sarauniya ta yunƙura zata cira sama Juhaina ta miƙe hannunta wata ƙaramar sanda ta bayyana a hannun nata, ta nuna Sarauniya da shi, ai kuwa Sarauniya ta kasa cirawa sama, rufe idonta tayi ta buɗe bakinta cikin wata Ƙatuwar murya ta ce “Birtani! ” nan take yanke wata tsuntsuwa Ƙatuwa ta bayyana gaban Sarauniya, hawa tayi kan tsuntsuwa suka cira sama, Sarauniya ta ce “Yanzu zaki iya yaƙar Mahaifiyarki akan mulki”, Juhaina ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin “Sarautar kogon kawai nake so mi ya sa ba za a ba ni ba? ” tana faɗin haka tayi ƙasa da kanta ta nutse cikin ƙasa. Sarauniya ta yi ƙwafa ta ɓace ɓat.
Yinin ranar gabaɗaya mutanen masarauta masarauta ba su zauna ba, an kira ma su magani ya fi a ƙirga. Har faɗuwar rana, Zinariya ta shiga cikin tashin hankali da azaba mara misali, dan yanzu ba ta da wani zaɓi da ya wuce na mutuwa, Jamina kuwa sosai wutar ƙiyayyar ƴar’uwarta Juhaina ta ruru, Sarauniya ta yi zugum dan abun duniya ya sha mata kai, dama cikin ƴaƴanta Juhaina ce mai haɗarin cikinsu, Yarinya ce da tun tana ƙanƙanuwa ba ta barin wani ya shiga gabanta, idan wani ya shiga to tabbas za ta kawar da shi, ko da kuwa hakan na nufin za a rasa rayuka a cikin kogon gimatuwa.
Ma sha Allah Allah Ya kara basira yarinya