Skip to content
Part 6 of 9 in the Series Zinariya by Queen-Nasmah

Zango Na Shida (Tutar Masauta)

“La ilaha ilallahu Muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam.” Zinariya ta faɗa wannan karon bayan Hibshiyana ta maimaita mata kalmar sau goma sha bakwai, a razane cikin nuna rashin tsammani da abunda Zinariya ta ambata Hibshiyana ta ja baya tare da kallon Zinariya, Zinariya ta ce “E na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzonsa ne,” Hibshiyana ta saukar da kanta ƙasa ts kalli gabas ta yi sujjada tana faɗin “ Alhamdulillahi,” sannan ta ɗago ta rungume hannun Zinariya, Jamina ba ta yi mamaki ba, dan dama ta san za a yi haka, Zinariya ta ɗan ɗago ta jingina da bango tana faɗin “na yarda addinin islama garkuwa ne, ki ce min saboda me?, Hibshiyana ta ce “ko saboda me?” “da kika fara maimaita kalmar la’ilaha illallah sai na ji wani sanyi da ƙarfi sun ziyarci zuciyata, na ji na samu sassauci daga cikin azabar da nake ji, kaso hamsin cikin ɗari na raɗaɗin da nake ji ya ragu, sai na kamanta shi da kwanakin da ƴan masarauta suka kwashe gaban Bizani “, Jamina ta miƙe ta dawo gab da Zinariya ta ce “kin fara kwaɗaita min addinin ki Hibshiyana” Hibshiyana ta yi murmushi ta ce “addinin kowa ne ranki ya daɗe”, Jamina ta ce “to nima dai a yau ɗin nan bayan abun da ya faru na shaida cewa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma annabi Muhammadu manzonsa ne “, sosai Hibshiyana ta ji daɗin hakan, nan suka yanke hukunci cewa za su shiga makaranta bayan Zinariya ta warke, saboda ƙara sani akan addinin islama.

Bayan ta ƙarar da ruwan Jinin, ta juya ta ware hannayenta rigar jikinta ta ɓare ta faɗi ƙasa, ta juya ta fara tafiya a bisa umurnin Bokanya , Tafiya take yi tana rikiɗa zuwa mage, damisa, da zaki, duk ta girgiza kanta sai ta sauya kamanni, ta buge awanni ɗaɗɗaya har awanni biyar sannan ta shigo cikin dajin Gimatuwa, ta yunƙura zata ɓace ‘ba za ki iya ɓacewa a wannan yanayin ba, dole ki tun kare su da kaifin ƙafafunki’ maganar bokanya ta dawo mata, saboda haka ta matse jikinta ta kutsa cikin kogon.

Zinariya ta miƙe zaune ta ce, “Na ɗan samu ssuƙi, ku bar ni na yi tattaki “, Hibshiyana ta kama hannun Zinariya ɗaya, Jamina ta kama ɗaya suka nufi hanyar fita waje.

Sarauniya Jahiyana na zaune gaban abar bautarsu ta haɗe hannayenta wuri ɗaya, kamar an tsikare ta ta buɗe ido da sauri ta miƙe sanadiyyar abun da idonta suka gano mata. Da sauri take tafiya amna da ta fahimci tafiyar ba za ta mata ba kawai ta tashi sama ta ɓace.

Juhaina kuwa na shigo cikin masarauta wani irin iska ya taso mai ɗauke da wani kalar yanayi mai sa garin lushi, hasken rana ya gushe duhu-duhu ya soma lulluɓe garin. Hibshiyana ta ɗaga kai ta kalli yanayin garin, Jamina ta ce “wani mummunan abu na shirin faruwa “, Zinariya za ta yi magana kenan suka tsinkayo Juhaina, baki Hibshiyana ta riƙe tana faɗin “Ranki ya daɗe, Gimbiya ce”. Tun daga inda ta tsinkayo su ta ɗaga murya ta ce “Zinariya ” tsabar ƙarfin da ta sakar ma muryar sai da farfajiyar masarautar ta amsa.

Zinariya ta tsaya cak tana kallon ikon Allah, Hibshiyana ta ce “ki riƙa maimaita innalillahi wa’inna ilaihir raju’un”, Zinariya ta fara maimaita abunda Hibshiyana ta faɗa mata , Juhaina ta yi kukan kura ta tashi sama, tare da sakin wani dogon mashi zuwa ƙasa, mashin na gab da isa wurin Zinariya ta rufe idonta tana maimaita innalillahi wa’inna ilaihir raju’un , Sarauniya Jahiyana ta shiga gaban Zinariya mashin ya daki gefen ƙirjinta na hagu, “haaaaa…. ” Sarauniya ta faɗa idonta na kafewa ta faɗi ƙasa cikin jini, da sauri Zinariya ta buɗe ido jin ƙara kusa da ita, dan ita har ta sadaƙar mutuwa za ta yi,  Jamina ta nufe tana faɗin “Mama!”, ba shiri Juhaina ta sauko ganin Mahaifiyarta kwance cikin jini.

“Mama Sarauniya ki tashi” Juhaina ta faɗa, Jamina ta sa hannu ta ture ta “kar ki kuskura ki sa hannunki a jikin Mama “, Sarauniya Jahiyana ta riƙo hannun Jamina, Bakinta na fitar da jini ta ce “ki… Ki. Ki….”, Zinariya ta nufo ta tana kuka ta ce “ke ce kawai gata nan, Dan Allah kar ki bar ni, ki tashi Mama, dan Allah ki tashi “, hannu Mama Sarauniya ta kai gefen kuncin Zinariya tana shafawa cikin jin zafin mashin dake jikinta ta ce “ki tashi ki je, kar ki bari tutarmu ta faɗi ƙasa, ki je gare ta ni ki bar ni lokacina ya riga yayi” ta nuna mata tutar masarauta da ke shirin faɗuwa, Zinariya ta juya ta kalli Tutar, sannan ta juyo ta kalli Sarauniya, idon Sarauniya suka cika da hawaye da gaɗa mata kai, cikin Zafin Nama Zinariya ta tunkari Tutar da ke ta yin ƙasa, a hankali alkhairan Mama Sarauniya gare ta suka riƙa dawo mata a kai, ta tuna yadda take rungume ta, ta rarrashe ta, Juhaina tayi kukan kura tana faɗin “ko ta wane hali, ni ce zan karɓi sarautar Gimatuwa” ta tashi sama idonta na fitar da wuta, “Allahu akbar! ” Hibshiyana ta fara faɗa, tana ɗaga hannunta sama, Jamina ta ɗauka ita ma “Allahu akbar”, hakan ya ƙara ma Zinariya ƙarfi, Juhaina ta kai hannu zata riƙe tutar, Jamina ta saki wani haske ya kafe hannun Juhaina, Zinariya ta daka tsalle ta cafke tutar da ke shirin faɗowa, ta faɗa kamar yadda ta ji su Jamina na faɗi “Allahu akbar ” tare da juyowa ta kalli Sarauniya Jahiyana dake kwance cikin jini, murmushi Sarauniya ta mata tana gaɗa mata kai alamar ta taka ta ɗora tutar, murmushi ita ma ta yi wa Sarauniya hawaye na bin kuncinta ta juya ta taka wani ƙarfe ta hau zata liƙa, Juhaina ta taso ta buɗe bakinta wata wuta ta fito dunƙule ta yi sama, Jamina ta buɗe bakinta wutar ta dawo ma Juhaina duk ta ƙone mata fuska, ta faɗi ƙasa tana ihu tana gunji.

Jahida ta fito da gudu ta nufi Mahaifiyarta, tana isa kusa da ita, aljanun masarauta suka fito rututu kamar ƙudaje, ko ina mutane ke fitowa yayinda Sarauniya ta rufe idonta kuf, Zinariya kuma ta ɗaga tutar sama tana kuka, kowa a gurin yana ɗaga hannu alamar sun yi mubayi’a.

<< Zinariya 5Zinariya 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×