Zango Na Takwas (Masarautar Bishtimal)
Bayan Zinariya ta fito daga cikin masallaci, ta tsaya gaban wasu mata guda biyar da kullum suke tsayawa gefen masallacin su amshi sadaka, hannunta ta sa cikin aljihun rigarta fara wadda aka ƙawata da duwatsun zinari ta ciro dunƙulen zinari guda biyar ta miƙa musu kowacce ta ɗauka ta na murna, har sun ayyana kuɗin da za su samu idan suka siyar da zinarin, ita kuma Zinariya ta juya tana murmushi, a ranta ta ji daɗi sosai ganin farincikin dake shimfiɗe a fuskarsu, daga nesa tana jiyo irin addu’ar da suke mata, wanda hakan ya wadatar da ita sosai.
Kukan wata tsuntsuwa ne ya sa Zinariya ɗaga kanta sama, tsuntsuwar ta sauko zuwa ga Zinariya, wata hadima ta tara hannunta tsuntsuwar ta sauka kan hannun nata, hadimar ta kalli tsuntsuwar sannan ta kallo Zinariya ta ce “Allah ya ja zamaninki, aiko ta aka yi, ga takarda nan rataye a wuyanta “, Zinariya ta ce “ciro takardar”, hannu hadimar ta miƙa da niyyar cire takardar amma sai tsuntsuwar ta kauce, ta yi yunƙurin hakan har sau uku, amma sai tsuntsuwar ta kauce, Hadimar ta ce “Allah ya ja da ran Sarauniya, wannan takardar fa ba zai yuwu a cire ta ba “, Zinariya ta ce “in ji wa?”, Hadimar ta ce “na ga ina ta yi amma tsuntsuwar ta kafe “, Zinariya ta ce “wataƙila saboda saƙon ba naki ba ne nawa ne shi ya sa ba za ki iya cirewa ba”, hannu Zinariya ta sa ta cire takardar dake rataye a wuyan wannan tsuntsuwar, tana cire takardar tsuntsuwar ta tashi sama, hadimar ta karɓi takardar ta riƙe, suka nufi masarauta.
Suna zuwa masarauta Hadimar ta buɗe takardar ta fara karantawa. _ina sanar da Sarauniyar Masarautar Gimatuwa cewa zan yaƙe ta gobe, ku zama cikin shiri.
Saƙo daga Masarauta Bishtimal
“Bishtimal?” Zinariya ta tambaya, Hadimar ta gaɗa kai alamar e. Zinariya ta ce “wace masarauta ce wannan?”, “Ranki ya daɗe wannan shi ne karo na farko da muka ji sunan Masarauta irin haka ” duka ƴan cikin fadar suka faɗa. Zinariya ta ce “ ku tashi ku sanar da duka ƴan masarauta ku zama cikin shiri, za a kwana ana gwaji “, tana faɗin haka ta miƙe ta nufi cikin gida.
Jamina na zaune gefen gado tana karatun ƙur’ani, Zinariya ta shigo cikin sauri ta zauna gefen Jamina tana faɗin “ƴar’uwa”, Jamina ta ɗago tana murmushi ta ce “na san da zuwan nan naki, Masarautar Bishtimal ce ta aiko da saƙo zuwa ga Zinariyarmu, ko ba haka ba? “, gaɗa kai Zinariya ta yi, Jamina ta ce “Na yi imani da Ubangiji da shi ya halicce ki, ya halicce ni, ya ƙaddara a yi Masarautar Gimatuwa, har ma da ita Masarautar Bishtimal ɗin, zamu yi nasara, ki kwantar da hankalinki”, Numfashi Zinariya ta sauke ta ce “amma ta yi kike ganin zan tunkari halittar da ba irin tawa ba, har na ce zan yaƙe su “, Jamina ta ce “Allahn da ya ƙaddari rayuwarki, har ya ƙaddara zaki jagoranci jinsin da ba naki ba shi zai baki kariya ya ɗora ki sama gare su”, Zinariya ta ce “Allah ka amince mana “, Jamina ta ce “Amin da girman Hasken al-ƙur’ani mai girma”, Zinariya ta miƙe ta ce “ina Jahida? “, Jamina ta ce “ta fita yawon miƙe ƙafa” ta kai ƙarshen maganar tana miƙewa. Ƙur’anin da ke hannunta ta aje inda ta ɗauko shi, sannan suka fita ita da Zinariya. Ɗakin gwajin yaƙi cike yake dab, kowa ya ɗauki takobi, nan suka fara gwaji bisa umurnin Sarauniyarsu.
A ɓangaren Zinariya kuwa ta zagaye duka Masarautar ita da Jamina, can ƙarshen gini suka sami Jahida zaune ta sanya ƙarfarta cikin ruwa, Jamina ta dafa ta ta ce “kukan me kike yi ƴar’uwata? “, Jahida ta ɗago tana share hawaye, Zinariya ta ce “au dama kuka Kike yi?”, Jamina ta ce “e tun da muka doshi inda take na ji hakan “, Zinariya ta zauna gefen Jahida ta riƙe hannunta tana faɗin “akwai abunda zai sa ƴan’uwa su ɓoye ma junansu damuwarsu?”, Jamina ta ce “babu abunda ke damunta, tana kukan…..”, Jahida ta yi saurin rufe mata baki tana faɗin “dan Allah kar ki faɗa”, Zinariya ta kalli Jahida, sannan ta juya ta kalli Jamina ta ce “me kuke ɓoyewa daga gare ni “, Jahida ta ce “ba wani abu ba ne, tashi mu je ɗakin gwaji”, Zinariya ba ta yi mamaki ba dan su Jahida sukan ga duk wani abun da ke faruwa cikin masarauta. Ɗakin gwaji suka nufa suna fira sama-sama.
Zinariya na shiga ta ɗauki takobi guda ɗaya da Marfin ƙarfe, Jamina ma ta yi kamar yadda Zinariya tayi, suka fara rafka takubbansu wuri ɗaya, Jahida kuwa ta koma gefe ta naɗe Hannayenta wuri ɗaya tana kallonsu. Sosai kowa a wurin suke amfani da dabarun faɗa, kowa yana gwada ƙarfinsa. Jamina ta ɗan juya ta kalli Jahida, daidai lokacin Zinariya ta ɗaga takobinta zata zari Jamina, Jamina ta tara takobinta sannan ta juyi tana murmushi ta ce “ina gani ta bayan ido fa “, Zinariya tayi dariya ta ce “na sani ai shi ya sa na yi hakan”, Jamina ta ce “Muguwa ke kika sani, mu je mu ɗauki kibiya mu ga ni idan Kin iya saiti”, Zinariya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce “hala me kika ɗauke ni, lokacin da na fara tasowa abunda mama Sarauniya ta fara koya min kenan, mu je ki gani.” aje takobin tayi, itama Jamina ta aje.
Jamina ta ɗauki mashi guda biyu ta miƙa ma Zinariya ɗaya, Juyawa Zinariya tayi tana murmushi ta saita mashin inda aka tanada domin gwaji, ta ɗage kanta sama kaɗan, sannan ta saita ta jefa mashin, ya tafi kai tsaye ya daki inda ta saita daidai, sannan ta juyo ta kashe ma Jamina ido, Jamina ta yi murmushi ta ce “bana haufi da koyarwar Mama, na san dama Kin iya tunda har kika ce ita ta koya miki ” ta ƙarasa maganar tana jefa mashin dake hannunta ya tsaya kusa da na Zinariya, Sannan ta ce “na koyi wannan ne daga ƴar’uwa Juhaina”, Zinariya tayi murmushi ta ce “Allah sarki “, Jahida dake can nesa da su ta matso ta ce “na lura kun maida gwajin fira, nima bari ayi da ni,” Zinariya ta ce “to ke me kika iya? “, Jahida ta ce “ni duk waɗannan abubuwan ba su dame ni ba, ni ko ƙarfina ban taɓa amfani da shi ba, a taƙaice ma bana faɗa, kuma bana shiga yaƙi, ina dai kallon yadda ake yi”, Jamina ta ce “kina kallo dai a madubi, ita fa ba abunda ta iya bayan kallon madubi “, Zinariya ta ƙyalƙyale da dariya, Jahida ta ce “Baki san ta madubi nake ganin komai ba”, Zinariya ta ce “shi ya sa idan kina ɗaki baki taɓa ɗagawa daga gaban madubi “, Jahida ta ce “Mama Sarauniya ce ma ta hana ni kwana gaban madubi”, Jamina ta ce “ni ce na zuga ta ai, ina mamakin yadda kike maƙale ma madubi “, Jahida ta yi dariya ta ce “ni kam madubi ne mahaɗin rayuwa ta.” haka suka ci gaba da fira har fitowar alfijir, yayinda sauran aljanu suke fafatawa da takubbansu.