Wani mahaukacin burki ya taka, har sai da gabanta ya faɗi, ta ɗago tana kallon sa, hankalinta a tashe, shi ma kallonta ya yi cikin wani irin yanayi.
Cikin jin tsoro ta ce, “Hamma kana lafiya?” lumshe idanuwansa ya yi ya ce, “Akwai matsala Fulani..” A ruɗe ta ce, “Matsala kuma hamma?”
Bata ankara ba ta ga hawaye na zuba daga idanunsa. A karo na farko ya ruƙo hannayenta ya ƙura mata idanuwa yana sauke ajiyar zuciya. Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi ta shiga jero masa tambayoyi lokaci ɗaya.
“Hamma meke faruwa ka faɗa min kar zuciyata ta fashe..” Murmushi ya yi me kyau, sannan ya sake ta ya jingina da kujera, ya lumshe idanuwa kamar ba zai yi magana ba cikin gur’batacciyar hausarsa ya ce, “Fulani zan mutu ne”
Duk da ta san baya magana me tsayi da hayaniya amma ta rikice ta fashe da kuka tana faɗin “Hamma kar ka mutu do Allah idan ka mutu nima mutuwa zan yi.” wani irin tausayinta ne ya kama shi ya rasa me zai yi, cikin murmushinsa ya ce, “Fulani me yasa kike min ihu a kunne? Ke matsoraci ce” Shesshekar kuka ta ci gaba da yi, ya sanya hannayensa yana goge mata fuska, sannan ya ɗauko ruwa masu sanyi ya bata ta sha ta ci gaba da ajiyar zuciya, sannan ya tada motar suka ci gaba da tafiya.
Bai yi tafiya me nisa ba ya ƙaraso bayan lambun da yake aje ta, ta ɗauki ƙwaryarta duk jikinta babu kuzari har ta buɗe motar zata fita ya kira sunanta a hankali, “Nafisa” cikin jin kunya ta amsa, “Hamma.” Wani zobe ya ciro daga cikin aljihunsa ya mi‘ko mata ya ce, “You can leave, ki kula zoben ki boye.” Jinjina kanta ta yi, bata ce komai ba dan idan ta yi magana kuka zai iya ƙwace mata ta rufe masa motar, tana gani ya bar gurin.
Itama cikin rashin kuzari ta juya ta ci gaba da tafiya haka nan take jin zuciyarta babu daɗi, har ta fara wuce bukkokin wasu fulani, tun kafin ta iso gidan ƙirjinta ke dukan tara-tara gabanta sai faɗuwa yake, tana ƙarasowa gidan ta yi sallama a hankali ta ɗaga asaberin da yake matsayin ƙofa ta shigo ciki.
Cikin sauri wata mata ta fito daga wata bukka, tana faɗin, “Sannunki da gantali” ta sunkuyar da kanta kasa, cikin harshen fillanci ta gaida ta, maimakon ta amsa sai cewa ta yi, “Ina kuɗina kin siyar duka?” ɗaga kai ta yi, ta kwanto kudi daga zaninta ta mika mata.
Shewa ta yi, cike da masifa ta ce, “Nafi mutuwa kake so kenan, yanzu Nafi gidan uwarwa ka sami kuɗi sabo haka iye? Nafi anya ba maganar Jummai gaskiya ba ne ka faɗa min kafin na kashe ka.” Nafi ta tsorata dan ta san zalunci irin na Inna Hure ta ce, “Na rantse inna shinikin nono da fura ne kawai.”
Ƙwafa kawai inna ta yi, bata ce komai ba ta nuna mata wanke-wanken da zata yi ta koma ɗakinta. Sai da duhu ya fara sannan ta gama wanke-wanken uwayen kwanonin, tana gamawa ko hutawa bata yi ba, inna hure ta miƙo mata tuwo da miyar da take talla, ta ɗauka ta fice tana hawaye.
Bayanta sai ciwo yake yi saboda tsananin gajiya tun asuba idan ta tashi bata komawa sai dare ya raba. Haka ta iso inda take tsayawa siyar da tuwon, sai da dare ya raba sannan ta komo gida da sallamarta. Muryar Inna hure ta ji tana masifa, “Yo Malam idan ban tura ta talla ba ta samo kuɗi ba da me zan cida ka kai da ita? Ashe munafurcin da take kawo ma kenan tambadadden yarinya, Yauwa ga ta nan ma munafuka kika saya kina kallon mutane zo nan!”
Hankali Tashe Nafi ta fara bata haƙuri cikin hausarta da bata fita sosai, “Inna na rantse ban faɗa komai komai ba.” Cikin fushi ta iso kusa da Nafi ta riƙe ƙugu tana faɗin, “Dan uwarki ni ke karya ko? Taimako ɗaya zan miki na ƙyale ki in kin sayar min da tuwona kin ƙaro da kuɗi, in ba haka ba…”
Tana jim furucinta jikinta ya ƙara yin sanyi, ta san dole saita dake ta, matsalarta ɗaya cinyoyinta da har yanzu basu warke ba tun dukan da ta yi mata. Dukan da ta ji ne ya sa ta dawo duniyar mutane, cikin daka tsawa ta ce, “Karka bari na sake maimaita maka Nafi.”
Cikin shesshekar kuka take fad’in, “Inna kiyi haƙuri, ba kashuwa tuwon bai kare ba, Kuma Baffa ya hana na kai dare.” Finciko wuyan Nafi ta yi cikin rashin imani ta janyo ta har gaban Malam Iro ta fara dukanta tana haɗa mata da zagiggika iri-iri da gori.
“Dan uwarki ba zaki kashe min ciniki ba saboda nakasasshen ubanki wanda zuciyarshi ta lalace, kema kina son zama kamar uwarki kenan, saina miki dukan yawon karuwancin da kike yi yau, an faɗa miki hauka nake bana gane inda kike sato kuɗin ba? da karuwancin da kike yi.”
Saida ta jigatar da ita da ita sosai sannan ta ƙyale ta bayan ta ƙwaƙule kuɗaɗen da Nafin ta ɓoye cikin jikinta. Tun Nafin na kuka da ƙarfi har muryarta ta disashe, duk da irin wulaƙancin da Inna hure take yi Baffa be ce komai ba kuma yana nan zaune. Saidaata gaji da mita da masifar dan kanta sannan ta shige Bukkarta ta rufo ta bar Baffa da Nafi a waje.
Da ƙyar Nafi ta miƙe jikinta babu kuzari sai ciwo kanta ke yi, ta ɗauko ragowar tuwon ta ajiye, sannan ta gyarawa Baffa shimfiɗarsa, ta yi masa jagora zuwa makwancinsa, Sannan ta dawo bakin ‘yar bukkarta marar kyan gani ga ƙwari da datti ciki, haka nan ta kwanta kan wani yagaggen buhu. Ta daɗe tana kuka tana kiran sunan Babarta sannan barci ya ɗauke ta.
*****
Tana tsaka da wahalallen barcin da ya ɗauke ta ta ji saukar ruwa a jikinta. Cikin gigita ta farka tana sauke numfashi da ƙyar. Muryar Inna Hure ta ji tana faɗin, “Zaki tashi ne ko kuwa?” Ai bata san lokacin da ta wartsake ba, Ta tashi zaune tana hamma idanuwanta Jajir gwanin ban tausayi. Ƙwafa ta yi, ba tare da ta ce komai ba ta fice. Duk da har lokacin barci be bar idanunta ba haka ta miƙe da ƙyar jikinta sai ciwo yake yi kanta sai sarawa yake, ga mugun sanyin da ke ratsa ta, Ta fito tsakar gidan ɗan ƙarami, ta fara wanke-wanke, sannan ta fara ƙoƙarin haɗa wuta, lokaci ɗaya fuskarta ta yi face-face ta yi jajir, idanuwanta sai zubar da ruwan hawaye suke yi saboda hayaƙi, da ƙyar ta samu wutar ta kama saboda itacen ɗanyu ne. Ta ɗaura Ruwan Zafi sannan ta ɗauki tsintsiya ta fara sharar gidan, sai da ta share tsaf, ta dama koko, bata ɓata lokaci ba ta sauke Ruwan ta ɗumama tuwo, saida gari ya fara haske sannan ta kammala, ta ɗauki tuwo da kokon ta fito waje. Yanayin tafiyarta kaɗai zai iya tabbatar da bata da zubin cikkakkun mutane, tafiyar a lanƙwashe take yinta. Ɗai-ɗaikun mutanen da suka fara fitowa ne suka fara gulmarta, da chanza hanya idan sun ganta.
Har wajen ƙarfe tara na safiya babu wanda ya siyi komai daga gurinta, kuma shiru-shiru Hammanta bai zo, damuwa ta ishe ta, jiki ba kuzari ta miƙe da ƙyar ta dawo cikin gidan. Sallama ta yi ta shiga gidan cikin shaƙaƙƙiyar muryarta, maimakon amsa sai wani mugun zagi da Hassatu ɗiyar Inna hure ta yanko da harshen fulatanci. Kamar tana jira ta fito daga Kewaye tana faɗin, “Ke da wa hassatu?” Zubda miyan barcin da ya tarar mata a baki ta yi, ta ce “Inna wai ke baki ga Nafi ba?” cikin sauri ta kalla inda Nafi take, bakinta har rawa yake ta ce, “Zancen banza kai Nafi! ni ba zan ɗauki iskancinka ba, bana tsoronka ni ba irin mutanen rugar nan bane, ko ba maye ba? babu ruwana da wani iskanci, ka kashe mana kasuwa hassatu ta dena sana’ar kai da ka fara kai ma kana son denawa to me kake nufi?”
Jikin Nafi na rawa ta ce, “Na rantse inna mutanen rugar nan basa son siyan komai daga..” Hassatu bata bari ta ƙarasa faɗar abinda take son faɗa ba ta katse ta da faɗin, “Ƙarya kike munafuka, wallahi kece ke yin maitar har aka dena siya.” Ta buɗe baki zata yi magana cikin hanzari Inna hure ta hankaɗa ta, tana faɗin, “Duk inda zaki je ki tafi ka siyar da shi, ko yau na kashe ki Nafi” jin haka yasa Nafi ficewa cike da tsoro.
Babban tashin hankalinta yau da Hammanta bai zo ba, bai turo a kira ta ba. Ta fara tafiya tana hawaye ga rana ga yunwa da ke cinta, duk inda ta wuce sai an yi zunɗenta an aibanta ta. Ta je duk inda ta san suna haɗuwa amma bata ganshi ba. Lokacin ne ta fara jin jiri-jiri, ta nemi wata bishiya ta zauna ta ajiye tuwon da kokon da ƙudaje suka daddaɓe ba kyan gani. Ta daɗe nan zaune cikinta sai karta yake tsabar yunwa, ganin bata da mafita ya sanya ta tashi ta fara tafiya. Sai da rana ta buɗe sosai sannan ta iso babbar kasuwarsu, ta fara yawo, haka ta ƙarashe yawonta bata siyar da komai ba, yunwa ta jigatar da ita ta zauna ta ci tuwon sannan ta miƙe, ta ci gaba da tafiya.
Wata Hamshaƙiyar mata Kyakkyawa ce ta zo wuce wa, ta sha ado me kyau, kwata-kwata bata yi kama da ‘yan Rugar ba, da ganinta hutu ya zauna mata da arziƙi hanunta riƙe da jaka me kyau. Suka yi ido huɗu da Nafi, Har matar ta tafi sai kuma ta dawo Ta kalli Nafi a karo na biyu ta ce, “Y’an’mata dan Allah tsaya mana.”
Tsayawa Nafi ta yi, tana kallonta ba tare da ta ce komai ba, matar ce ta sake fadin “Dan Allah Ina so ki kwatanta mini Inda mazaunin me garinku yake.” Jim ta yi, tana tunani cikin jin tsoro ta ce, “Ban san ina yake ba, ka tambayi wasu.” Tana gama faɗin haka ta juya da sauri zata tafi, matar ta ruk’o hannunta tana murmushi ta ce, “Kuma baki faɗa min sunanki ba?” kamar ba zata amsa ta ba, ta zame hannunta daga nata ta ce, “Nafi.” “Nafi!” matar ta maimata sunan a hankali.
Kafin ta yi wani yunkuri Nafi ta bar gurin, ta yi murmushi kawai ta juya ta bar gun itama. Tun da Nafi ta taho take jinta wani iri ta kasa fasalta yanayin da take ciki. Tana Tsallakowa cikin rukunin bukokinsu, wani Ƙaramin Yaro ya rugo da gudu, Karon da za suyi da Nafi Yaron ya faɗi itama haka tuwonta da kokon duk suka zube, Rintse idanuwanta ta yi, da ƙarfin cikin ruɗu, ta fara ƙoƙarin miƙewa.
Ihun wata Macce ta ji tana faɗin, “Taimako! Taimako!! Mayya zata kashe min yarona” Kafin wani abu matan da ke kusa wad’anda suka ji suka fara firfitowa. Ƙarasowa Uwar yaron ta yi, A kiɗime tana kiran sunan shi, amma sam babu alamun ma yana da rai sai jinin da ta gani yana fita ta hanncinsa. Ai Nafi na ganin matar ta fara ihu da sambatu, matan kuma suna nufo ta, ta kwasa da wani irin mugun gudu. Suna ganin ta gudu suka dawo, aka fara ba wa ywar yaron baki, da ƙyar aka samu ta amince aka nufi gun mai magani da Yaron. Tun a kallo ɗaya da me maganin ya yi wa yaron ya ce musu, Mayya ta yi abinda ta saba, yaro ya mutu!