Shiru-shiru Ammi ta ji Ahmaad har safiya ta yi, wajen karfe tara, ta yi niyyar share sa amma ta kasa ta aika Imaan ta dubo shi ko yana lafiya. Tana shiga Parlourn ta gan shi kan kujera kwance, ta ƙarasa da sauri tana kiran sunansa “Yaya Kana lafiya?” Yana jin ta amma ba zai iya komai ba kansa ya masa nauyi sosai ko magana ba zai iya yi ba.
Ta ƙarasa kusa da shi ta ɗan taɓa shi, ta ji jikinsa ya yi mugun zafi sosai, ta fice da sauri ta koma ta faɗa ma Ammi. Sosai Hankalinta ya tashi, ta kira Abdul ta faɗa masa ya ce yana nan tafe. Duk yana jin su amma ya yi shiru.
Shi ma Abdul ya shigo Parlourn yana sallama, haka nan yana ganin Dr. ya ji wani mugun ɓacin rai ya ƙaraso ya gaishe da Ammi ta amsa cikin damuwa ya tambayi Ammi me ke damun sa ta ce ba ta sani ba, ya matsa kaɗan ya ɗan taɓa jikinsa ya ji zafi sosai rau. Ya koma cikin mota ya ɗauko wata jaka ya dawo, ya ce “Ammi ina tunanin zazzaɓi ne bari na sa masa ruwa ban zo da kayan awo ba da na auna shi”.
Ta jinjina masu kai Abdul ya riƙe hannunsa har ya saka cannula ko bai yi wani ƙwaƙƙwaran motsi ba. Sai da ruwan ya ƙare ya ɗan ji ƙwarin jiki kaɗan da zufa, cikin dauriya ya miƙe zaune fuskarsa a haɗe ya cire Cannular ba tare da ya tanka ma kowa ba har Ammin ya shige bedroom ɗinsa ya rufo ƙofa. Cikin ɓacin rai Ammi ta sallame su, suka bar sashen nasa, shi ma Abdul ya bar gidan ya koma office ɗinsa.
Cikin gaggawa ya shiga ya yi wanka ya sanya manyan kaya shadda light brawn sai hula kalar aikin shaddar coffee, ya yi kyau sosai ya ɗauko makullin wata motarsa da waya ya zo dinnig ya zauna. Kukunsa ya fito yana gaida shi ya amsa fuska a sake ya zuba masa abinci ya ci sosai.
Sai kallonsa Kukun ke yi dan ya yi wata irin muguwar rama ga kuma hasken da ya ƙara sosai, ya ɗan harare sa, shi kuma ya sunkuyar da kansa, ya jawo wayarsa ya ɗan latsa ya dube sa ya ce “ba ni account numbernka” ya karanto masa ya rubuta daga nan ya lallatsa, ya ce a taƙaice “Na tura maka kuɗi, ka amso mini Account Numbers ɗin masu aikin gidan nan duka” cikin murna ya shiga yi masa godiya da addu’a ya ɗan sunkuyar da kai ya ce “To Yallaɓai na gode albashina ne ko hasahin da aka saba mini??” Ya mike yana ‘koƙarin fita ya ce “idan ka duba za ka gani”.
Yana gama faɗin haka ya fice daga Parlourn Kai-tsaye ko Part ɗin Ammi bai kalla ba ya nufi Parking Lot ɗin gidan ya buɗe wata farar mota ya shiga, ya tada ya ba ta wuta sosai. Gabaɗaya yanzu abin da yake son aikatawa kawai yana so ya gana da Nafeesa kwata-kwata hankalinsa ya gaza kwanciya. Ya ɗauki hanyar rugarsu.
Ammi zaune a Parlournta hannunta riƙe da Ipad da alama video call suke yi irin yadda ta maida hankali a nutse tanamagana cikin girmamawa kaɗai ya isa ya nuna ta ba wa wayar muhimmanci sosai. Abdurrahim wanda take roƙo ya dan fesar da numfashi daga bisa kujerar da yake ya jujjuya kafin ya ce, “Shi ke nan Ammi! Amma fa saboda ke zan yi wannan alfarmar da kuma dear Imaan anyway ni ma zan shigo Naija nan kusa, zuwa dare zan saka agent ɗinmu na nan cikin Nigeria ya kawo muku, dama muna ajiye maganin incase of unexpected things. Zan turo miki Account Numbern.”
Ta amsa tana ta godiya cikin girmama lafuzanshi sannan suka katse kiran, Ya turo mata account numbern na Nigeria Access Bank. Take ba ta wani tsaitsaya ba ta tura masa zunzurutun kuɗaɗe Naira Miliyan Biyu da dubu ɗari Takwas da saba’in 27070 sai kuma Cash waɗanda ya turo mata text zata ba wa wanda ya kawo maganin Dubu ɗari Shida da hamsin. Imaan da ke zaune ɗan nesa da ita kaɗan Ta turɓune fuska ta ce “Ammi wai nawa kika tura masa? kuma a haka kike cewa ni in aure shi kam”.
“Bai shafe ki ba” ta ba ta amsa tana miƙewa tsaye ta bar parlourn. Ita dai Ammi yanzu ba ta da burin da ya wuce rayuwr Dr. ta gyaru komai ya zo ƙarshe ba wata damuwa ai ita a ganin ta Abdurrahim ba shi da wata matsala ko da ace ya so Imaan.
“Nafeeesa!!” Hajiya Safee ta kira sunan Nafi cikin wani salo tana jan sunan tare da kashe mata ido. Ba ƙaramar razana Nafi ta yi ba, har wani fitsari ta ji tana ji, cike da fargaba muryarta har tana rawa ta amsa “Na…nnnNaam” Jin yadda muryar Nafin ke rawa ya sa Hajiya Safee sakin wata dariya irin ta shahararrun ‘yan duniya gogaggu. Ita kanta Tala sai da ta ɗan dara, Hajiya ta sake faɗin, “Wai me ke damunki ne haka ki saki jikinki mana”. Ta girgiza kai alamun babu komai, Hajiyar ta sake cewa “Okay ci Abincinki”. Ta ɗaga kanta, da dole ta fara tura abincin bakinta. Da gani cin na dole ne take yi, ga Idanuwa da Hajiya Safee ta tsare ta da su, ta turo mata kofin ruwa gabanta, ta ɗauka ta fara sha har tana ƙwarewa. Hajiya ta ce, “Idan kin koshi za ki iya zuwa daki, Tala za ta buyo ki daga baya”.
Kamar jira Nafi ke yi jikinta na ɓari ta miƙe ta bar Parlourn ta shige ɗakin da aka kaita, ta wuce bedroom ɗin ta kwanta kan gado ta ja bargo ta rufe har kanta. Ta jima na kwance shiru sai hawaye kawai take yi, jikinta duk ya yi sanyi gabaɗaya kewar Baffanta ta ishe ta tana ta nadamar yarda da Hinde da ta yi, ga shi ta kawo ta inda za a kashe ta, sam hankalinta ba a kwance yake ba, komai ya fice a ranta.
A haka Tala ta shigo ɗakin ta kunna fitila da Ac ta ce “Nafi ki tashi! wai ke ko zafi ba ki ji.” Ta yaye bargon ta zauna tana bin ta da idanuwa, Tala ta sake faɗin, “taso mu je Yau zan zagaya da ke cikin gidan nan ne” ta fito suka fice daga Parlourn Hajiya, Tala na gaba suka fito Harabar katafaren gidan danƙarere me tsananin kyau da girma, Nafi ta baza idanuwa tana kallon tsarin gidan kamar ba a duniya ba, hankalinta ya sake tashi sosai kanta sai juya mata yake gidan ya yi biyun na Hajjaju wajen kyau da girma.
Parking Space ɗin gidan kanshi abin kallo ne, tsarin gidan ya yi sosai, idan ka ga ɗakin mai gadi kaɗai da masu aiki daga wajen sai ka ce Tabarakallahu saboda haɗuwa, dan ka kalli zubin ginin yake ma haka sai ya burge ka sosai saboda haɗuwarsa.
Ɓangarori uku ne na ɗaya na biyu sai na ƙarshen da ya ke ɗan ƙaramin wanda Su Nafi suka fito daga cikinsa. Securities sai kai-kawo suke yi riƙe har da bindigu ga maigadi da wasu samari zaune kan benci. A zubure ta kalli Hannunta da Tala ta riƙe sai kuma ta saki ajiyar zuciya ita ma Tala ta ga wani zanen star me kyau a hannun Nafi ta yi shiru ta ƙura wa zanen ido tana raya abubuwa da dama cikin ranta sai kuma ta basar ta ja ta tana magana “In kin gama kalle-kallen mu je ko”.
Ta ja ta suka fara shiga ɓangaren da ke kusa da nasu, Nafi ta ga Ikon Allah dan babu kowa a ciki tsit amma ya fi na su haɗuwa da tsaruwa sosai dan ba a haɗa su ma. Daga ƙarshe suka nufi bayan Ɓangare na ƙarshe wanda ba su shiga ba inda wajen shaƙatawa yake, suka nemi waje suka zauna kusa da Sweeming Pool, nan sai zare ido take tana ji bayanin Talar, amma ko maganar sashen da ba su shiga ba bata yi mata ba.
Ta dubi Nafi a tsanake ta ce “Humm! wallahi Nafi baki da wayau sam, yanzu in ban da abinki ke haka ake rayuwa kin kama kin fara wasu abubuwa ke da kanki za ki ja ma kanki matsala, wa ya ce miki ana ma Hajiya haka, to yanzu ki tabbata duk abin da za ki yi akwai Na’urar da ke naɗa komai da kika yi sai ta gani, dan haka ba za mu dinga magana a chan ba sai dai mu zo nan. Sannan kuma waɗannan ‘yan abubuwan da kike yi ban jin daɗinsu, ki saki jiki idan ba haka ba za ki sha wahala sosai gaskiya.” Ba ta iya cewa komai sai gyaɗa kai kawai da take yi dan bakinta ya mutu. Daga nan ita ma Tala ba ta sake cewa komai ba. Suka miƙe suka koma Ainahin inda suka fito, suka shiga Kitchen tare, ta nuna ma Nafi kujera ta zauna ita kuma ta ci gaba da aikace-aikace Nafin na bin ta da idanuwa.
Ƙarfe Tara na dare Akarsh Likitan Dr A. ya iso Nigeria ya sauka a gidansa shi da wani ƙwararren likita wanda ake ji da shi sosai da sosai a America Doctor Danial suka yi waya da Abdul akan yadda aikin da za a yi ma Ahmaad zai kasance.