Ya yi yawo sosai cikin rugarsu Nafi amma bai ga bafullatanin da suka yi magana da shi ba. Sai wajen ƙarfe tara da wani abu ya dawo gidan. Ammi na ganin shigowar motarsa ta tashi Imaan dan har ta fara barci Ta ba ta Coffee ta ce ta je ta kai masa, amma kar ta nuna wani ya ba ta ta kawo ta nuna masa ita ce ta haɗa, kuma ta tabbatar ya sha.
Ta karɓa jiki a sanyaye haka nan take jin zuciyarta babu daɗi, ta nufi Parlournsa ta yi sallama har sau Biyu amma shiru bai amsa ba, ta nufi bedroom ɗinsa tana sallama ta shiga ciki. Zaune ta same sa Kan Gado ya dafe kansa da hannayensa duka biyun ya yi shiru. Gabanta na faɗuwa ta ƙarasa gabanshi a ce “Yaya ina wuni” Ya ɗaga mata hannu yana murmushi. Ta miƙa mishi Kofin hannunta na kyarma. Ya ɗan tsare ta da idanuwa ta rikice kamar marar gaskiya sam hankalinta bai kwanta da Coffee ɗin da ta kawo masa ba. Su ka yi shiru su duka tsoro ya hana ta magana jira take yi kawai ta ji ya tuhume ta amma ta ji shiru da ƙyar ta yi ƙarfin halin faɗin “Yaya ga Coffee nan na haɗa maka ni zan je na kwanta dan ALLAH ka sha”. Ya miƙa hannu ta ba shi ya karɓa ya ce “Thank you Dear”. Ta yi murmushi ita ma ta ce “Good night” tana ficewa daga ɗakin. Tun da ta fito daga ɗakin take jin babu daɗi a ranta miye dalilin da ya sa Ammi take ta fushi da shi kwana biyu. Kuma ta ce kar ta nuna ba ita ce ta haɗa ba. Tana waɗannan tunane-tunanen ta shiga Parlourn. Gani ta yi Ammi na ta kai-kawo ta yi saurin tamabayarta “Ya karɓa ya sha??” Ɗaga kai ta yi tana faɗin “Umh Ammi do you know something?” Ta girgiza kai Imaan na hawaye ta ce “Wallahi Ammi I really dont know why i’m feeling somehow, like i’ve done something wrong or…” Katse ta Ammi ta yi da sauri gabanta na faɗuwa ita ma hankakinta ya kasa kwanciya ta ce “Imaan what do you mean i can’t understand what you saying go straight to the point” Ta goge hawaye ta ce “Ina gani kamar na aikata wani abu marar kyau wa Yaya, kawai ina jin faɗuwar gaba hankalina ba a kwance yake ba. Ammi kin ga idanuwan Yaya wallahi na ji tsoro da na gan shi I dont think he’s okay i believe that i love him i love him he’s my Happiness!!” Ta fashe da kuka jikinta na wata irin rawa zuciyarta na bugawa. Duk yanda Ammi ta so daurewa sai da hawaye suka zubo mata. Ta share su tana ɗan murmushin ƙarfafa kanta, gefe ɗaya kuma ta fara nadamar abubuwan da ta yi masa kwana biyu da kuma fushin da take yi da shi. Ta ce “Ban san yaushe kika zama raguwa irin haka ba, Yayanki yana lafiya babu abin da zai same shi, in sha Allah. don’t think about bad things, oya go and sleep don’t forget to pray nd Off the light”. Ammi na gama faɗar haka ta yi saurin Nufar bedroom ɗinta ta bar Imaan ɗin nan. Ji take yi kamar ta koma ta dubo sa amma ta daure ta koma ɗakinta ta kwanta tana ta kukan da ba ta san dalilinsa ba…Imaan na fita ya ajiye Cup ɗin ya ɗauko DIARY ɗinsa ya daɗe yana rubutu sosai kafin ya rufe ya ajiye. Ya shiga duba saƙonnin da aka turo Ya tura wa duk ma’aikatan Companies ɗinshi salary da ƙarin kuɗaɗe masu tsoka, sannan ya suba Account details ɗin da Kuku ya turo masa suma duk ya tura musu nasu. Sai wajen sha biyun dare Ya kwanta, har barci ya fara ƙoƙarin ɗaukar sa ya tuna da Coffee ɗin da ta kawo masa ya tashi duk da ba zafi ya ɗaga kofin ya shanye.
A matsayinsa na likita ɗanɗanon Coffee ɗin da ya ji, ya san an sarrafa da wani abu na daban ba mai kyau ba, Ya ajiye Cup ɗin, ya gyara kwanciya. Cikin dare ya dinga jin raɗaɗi da Wani irin dunƙulallen abu, a zuciyarsa ga kuma zafin da jikinsa ya ɗauka Zuciyarsa ta shiga wani irin bugu, Ya rasa wata irin azaba yake ji har wani huci me mugun zafi yake saki Zuciyarsa kamar ta tsage tsabar irin tururin azabar da yake ji gabaɗaya jikinsa ya ɗau wata irin rawa. Tun yana iya tuna wasu abubuwa ya lumshe idanuwa har ya kasa jin sa da ganinsa suka ɗauke.
Daren wannan Ranar mutane da yawa masu alaƙa da Doctor Ahmaad Abubakar Yusuf Lamiɗo ba su rintsa ba.
Cikin wannan daren Galadima ya ɗauki waya ya kira Doctor Akarsh. Sai dai a mamakinsa bugu biyu ya ɗaga da alamu ma ba barci yake ba, sun jima sosai suna tattaunawa Kafin daga Ƙarshe suka yi sallama. Sam Ammi ta kasa rintsawa Barci ya ƙauracewa idanuwanta. sai kai-kawo take a ɗakinta daga Ƙarshe ta shige Toilet ta yi Alwalla ta fito ta fara jera salloli tana ta addu’o’i. Abdul ma sam ya kasa rintsawa da ya rufe ido sai ya ga fuskar Ahmaad yana masa murmushi lokacin da ya yi masa wani hoto.
Tun da Nafi ta ji Hajiya ta ce mata ta kwan ɗakin Tala hankalinta bai kwanta ba har are ya raba barci bai ɗauke ta ba. Jin ta take cikin wani irin da ba za ta iya fasalta shi ba, Zuciyarta ba daɗi.
*****
Tun da safe wajen ƙarfe Takwas Abdul da doctor Irfaan suka zo gidan, Parlourn Ammi suka karya, sannan Abdul ɗin ya miƙe jiki ba ƙwari ya ce bari ya je ɓangaren Ahmaad ɗin ya gano shi, dan Ammi ta ce ko sallar asuba ba ta ga fitar shi ya je ba. Ya yi sallama a Parlourn ya ji shiru, hakan ya sa ya kusa kai cikin bedroom ɗin na shi. Kwance ya hango shi kan gado, ya kunna fitila haske ya gwauraye ɗakin. Yanda ya gan shi kwance kan gadon kamar gawa ba ƙaramin bugu zuciyarsa ta yi ba, lokaci ɗaya kuma ya ji ƙafafuwansa na gagarar ɗaukarsa. ya ƙarasa gaban gadon da sauri yana kallon sa. Ba shi da maraba da gawa, idanuwansa ne kawai a buɗe yana kalle-kalle amma ko motsa kansa ba ya iya yi. Abdul ya kira sunansa A hankali “Ahmaad!” Bai amsa ba sai lumshe idanuwansa ya yi waɗanda suka rine suka yi wani irin ja sosai. Hankalin Abdul ya kai ƙololuwar tashi zuciyarsa na wani irin bugu ya miƙe jikinsa ba ƙwari yana jin fargaba da wane ido zai dubi Ammi. Ya durƙushe nan ya kasa tafiya gabaɗaya jikinsa ya gama yin sanyi. Jin da Ammi ta yi shirun ya yi yawa bai dawo ba ya ƙara sanyaya jikinta, suka nufi Ɓangarenshi ita da imaan da Dr. Irfaan, Tun kafin su ƙarasa take jin faɗuwar gaba sosai da wani irin yanayi me wuyar fasaltuwa. Ammi ta yi sallama a Parlournsa, jin shiru ya sa ta tura ƙofar bedroom ɗin sa a hankali. Abin da idanuwanta suka gano mata ne ya haifar mata da wata irin bugawar zuciya lokaci ɗaya kuma kanta ya sara, ta lumshe idanuwanta ta sake buɗewa. Shesshekar Abdul kawai ke ta shi cikin ɗakin. Ammi ta zube nan ƙasa tana fitar da numfashi da ƙyar, tuni hawaye suka fara zubowa daga idanuwanta, ta fara raira kuka tana karanto addu’o’i gabaɗaya ranta a dagule yake ba ma za ta iya misalta irin mummunan yanayin da take ciki ba. Ta ja jiki cikin sarewa da Al’amarin Ahmaad ɗin ta isa bakin gadon da yake. Jikinta na wata irin rawa ta kamo hannayenshi ta riƙe, tana son karanto addu’o’i amma zuciyarta ta raunata sosai ta kasa, Ta rushe da wani irin kuka tana jijjiga shi tana ba shi haƙuri, magana take yi ita kanta ba ta san me take furtawa ba. “Ahmaad ka tashi dan Allah ba zan tilasta ka ba, na yafe maka ba zan sake fushi da kai ba..” Kamar daga sama Imaan ta faɗo ɗakin jikinta na rawa tana ganin halin da suke ciki ta fashe da kuka jikinta sai wata irin karkarwa yake ta rugo da gudu ta tsaya gaban Ahmaad wanda har lokacin yana yanda yake ta durƙushe ƙasa tana wani irin kuka mai raunata zuciya ta kamo hannayensa duka tana magana muryarta na shaƙewa, irin yanda hankalinta ya tashi dole mutum ya fahimta ko kallo ɗaya idan aka mata.“Yaya Please wake up! and say something, don’t brake our hearts, you’re our only hope and everything, i can’t even imagine it, Dan Allah Yaya ka tashi, ka ce wani abu Zuciyata za ta fashe, Ba zan iya rayuwa kana cikin wani hali ba a saboda ni! Na sani ni ce silar komai ka tashi ni ce na chancanci mutuwa!!” Imaan ta ci gaba da kuka mai tsayawa a ƙarƙashin zuciya. Duk maganganun da take yi da kukan da suke yi Yana ji, amma ba zai iya aiki da kowane sashe na jikinsa ba, Ya lumshe idanuwansa wasu hawaye masu ɗumin gaske suka zubo daga idanuwansa. Ta miƙe jiri na ɗibar ta Hankalinta a tashe kamar za ta faɗi ta fice tana ƙwala ma Dr Irfaan kira. Shi kanshi da ya shigo ya ga yanayin da suke ciki sai da ya yi hawaye. Cikin gaggawa ya fara kiran Asibiti. Mintuna goma bisani suka ji ƙarar Amblance daga Asibitin, da ƙyar ya samu Abdul ya miƙe suka kama Dr. A suka fito harabar gidan suka saka shi cikin Ambulance, Irfaan ya shiga suka bar gidan, suka nufi Asibiti. Kafin su ankara Ammi ta yanke jiki ta faɗi Tashin hankali da ruɗanin da suka shiga ɓata baki ne tsayawa misalta shi, Abdul ɗin ma ya rasa taƙamai-mai mai zai yi. Kuku da ya shigo tuntuni komai ya faru kan idanunshi shi ma sai hawaye yake, dan dama godiya ya zo ya yi akan maƙudan kuɗaɗen da Dr A ya turo masa Naira dubu ɗari biyar. Sai kuma ya ci karo da wannan tashin hankalin. Driver ne ke tuƙa motar Abdul na gaba Imaan da Ammi sun baya. Suna ƙarasawa Asibitin suka nufi Office ɗin Abdul da Ammi, ya kira wani Likita ya ba ta taimakon da ya dace, dan a irin yanayin da yake ciki ba zai iya taɓuka komai ba. Sai da ya tabbata an yi wa Ammi allurar barci kuma numfashinta ya daidaita sannan ya bar imaan gurin ta.
Ya nufi Emergency room ɗinsu. Akarsh da Doctor Danial ma duk sun iso Asibitin suna Emergency room. Abdul ya chanza kaya, ya saka hula da nose-mask ya tura ƙofar gabansa na faɗuwa ya shiga. Jigum-jigum ya gansu tsaitsaye kowanensu na iya bakin ƙoƙarinsa, gabaɗaya sun kasa shawo kan matsalar duk yanda suke tunanin tsauri da tsananin Tasirin maganin da kuma tasirinsa me matuƙar hatsari ya zarce tunaninsu, Tun da suka shigo su ke ɗirka masa allurori daban-daban da yi masa aune-aune kala-kala, ZUCIYArsa ba ta buga ba tana aiki, Tsananin zafin jikinsa da yanda zuciyar ke bugawa ne ya yi bala’in sake rikitar da su. Ba su taɓa tunanin hatsarin abin ya kai haka ba. Abdul ɗin shi ma ya yi iyakar yinsa da ƙoƙarinsa amma al’amarin ya girmi tunaninsu, Duk da Akarsh, Irfaan, Abdul, Uwa uba Doctor Danial ƙwararrun likitoci ne na gaban kwatance amma kaf ɗinsu sun kasa taɓuka komai. Doctor Danial ne ya fito daga Emergency room ɗin yana goge zufa, ya koma Office ɗin Abdul ya buɗe Laptop ɗinsa da take nan Ya shiga searching akan matsalar, Bai jima ba ya koma Emergency Room ɗin.
Wata allura Dr Saleem abokinsu ya ɗauko Pharmacy da garin da ake kwaɓa ta, ya shigo Babban Ɗakin da ke cike da Na’urori sai gadajen Marassa lafiya me girma guda biyu, ɗaya Dr. A ɗin na kwance a kai. Ya kawo Allurar, dan da nan suka kwaɓa aka tsira masa ita, suna gani Ya lumshe idanuwansa lokacin da suka zare syringe. Allurar za ta ba shi damar ci gaba da rayuwa idan har Ubangiji ya nufi hakan, kuma yana da rabo, kuma zai samu barci. Daga nan kuma su ci gaba da ƙoƙartawa a kan lamarin. Amma kusan Mintuna Talatin da yi masa ita babu alamun komai, ba wani ci gaba, illa ma wani jini da suka ga ya fara zuba da hancinsa. Ficewa Dr. Saleem ɗin ya yi yana goge Hawaye sai lokacin ne ya fahimci dalilin Kyautar zunzurutun kuɗaɗen da Ya yiwa Ma’aikatan, da shi kanshi da kuma yafe ma duk wani mara lafiya kuɗin magani da komai. Sai lokacin ya sake tuna dalilin da ya sa Shekaranjiya ya ce musu a kai Ziyara asibitoci aka yi hidima sosai an taimaka musu, asibitoci da Na gwamnati da na kuɗi da na ƙauyuka kusan Talatin duk sun je cikin Satin har kuɗaɗe sun raba, Amma da ya faɗa masa Sai kawai ya masa godiya da nuna jin daɗinsa sosai, ya sake tura masa kuɗeɗe. Kafin wani lokaci hatta ƙananan likitocin da ke Aiki a babban asibitin sun san Halin da yake ciki, Asibitin ko ina ka gitta sai addu’a ake masa da kuma fatan samun sauƙi, Wasu har da kuka. Sam Al’amarin ba sauƙi babu wani ci gaba, ga uban jinin da yake ta zubarwa. Abdul ya kira har masarauta ya faɗa wa Iyayensu da kowa. Ana ta addu’o’i.
Ammi ta yi suma fiye da Biyar, yanzu haka ma tana Vip Room an yi mata allurar barci. Imaan ma Allurar barci Aka mata dan Abubuwan da take yi tamkar ta zare faɗi take ita ce dalilin ciwon nasa. Abdul na gama waya da mahaifinsa Jiri ya ɗebe shi ya yanke jiki ya faɗi. Duka likitocin sun yi iyakar iyawarsu an kira Manyan likitoci an yi Posting a social media Ƙwararrun likitoci na bada shawarwari, amma Lamarin ya zarce duk yanda suka zata. Hankulansu sun kai fiye da ƙololuwar tashi, Duk sun yi zuru-zuru. Still har lokacin idanununsa biyu yana bin su da kallo, abun ya tsorata su fiye da tunani ba su taɓa zaton akwai ciwon da ya fi ƙarfin ƙwarewarsu ba sai ranar. Sun ma rasa ta ina za su fara komai. Ba su taɓa cin karo da rikitaccen al’amarin irin wannan ba, da ace wani ya faɗa musu akwai irin wannan matsalar da hankali kan gaza ɗauka tabbas za su ɗauke shi fiye ma da abin da ya fi gawurtacce kuma shahararren maƙaryaci. Za su iya cewa a lokacin sun gama sarewa dan yana da ransa sun kira sunansa sun yi masa magana Yana ta lumshe ido alamun yana jin su, yana da rai kuma, zuwa lokacin sun saduda lamarin ya fi ƙarfinsu.
Tala ta gama komai ta jera Abinci a dinning Nafi dai ba ta yi magana ba. Har dare ya yi, ga mamakinta maimakon ta kwana ɗakinta sai ji ta yi Hajiya ta ce Ta je ɗakin Tala su kwana tare za ta ɗan yi tafiya sai jibi za ta dawo ita. Ta amsa suka shiga ɗakin Tare, Nafi ta yi wanka Talar ta ba ta kayan sawa ta sanya. Duk Nafi ta zama wata shiru-shiru lokaci guda. Tun da ta sanya kayan ta ga Talar na ta kallon bayan hannunta tafin fari tas da shi, sai fatarta da ke fara ita ma. Kafin wuyan hannun an yi wani zanen TAMBARI mai matsanancin kyau da jan rubutu, Kamar wata Star amma me kyau har sheƙi take yi, wanda sai ka lura sosai za ka gan ta. Ita dai zazzaɓi-zazzaɓi take ji, ba ta yi wani abu ba ta haye gadon Tala ta rufa mata Blanket ta fice. Wani irin ciwon Kai take ji, ga kuma zuciyarta ba daɗi sam.
Galadima ya sake duban Ummi a karo na biyu yana sheƙewa da dariya. “Hahhhaha!! Kina wasa da Galadima gaskiya, dan duk inda kike tunanin na kai na wuce nan! Dama Hatsabibi ya ce Yau sihirin zai bar jikinsa, zai dawo ya yi nadama marar amfani a banza…” Ya kuma tuntsurewa da dariya ita ma tana taya shi. “To Amma Zubaida fa, yau tun da aka sanar da maganar situation ɗin da yake ciki ta kulle kanta ta ƙi fitowa ko Breakfast ba ta yi ba dan ma na hana ta fita??” Ya murtuƙe fuska yana miƙewa ya ce, “Kar ki damu da ita. Ni zan kula da komai”. Yana gama faɗar haka ya fice.
Hatta masarautar Suna cikin damuwa a kan Halin da Yarima Ahmaad ɗin ke ciki. Duk wani makusancinsa me ƙaunarsa ƙarya yake ya ce ba ya cikin yanayi na ruɗu da karyewar zuciya.
Waziri ya fito daga Ɓangaren Hajja, Ya shiga motar tsakiya, Aka shiga fita da motoci daga masarautar, Biyu gaba biyu baya, sai wadda yake ciki a tsakiya. Aka tuƙa shi har zuwa asibitin da Dr A ɗin yake.