Skip to content
Part 14 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Ammi na ajiye wayar ta ɗauki Hijab da Mukullin motarta da jaka ta saka wayar ciki. Ta ƙwala ma Imaan kira, Ta ƙaraso jiki a sanyaye ta ce, “Ammi ga ni” “Fita zan yi Police station yanzu” Ta zaro idanu waje ta ce, “Police station kuma Ammi What happen?” Ta gayar Hijab din ta ce “Nothing Imaan idan na dawo za ki ji, ki kula ba zan daɗe ba in sha Allah” Ta gyada kai kawai ta ce, “Allah ya tsare” Ta amsa tana ficewa waje, Mota ta shiga ta ba d wuta, Gateman ya buɗe mata ta fice ta ɗauki hanyar Sabon Gari Police station, Ta shiga ciki ta yi Parking ta nufi ciki kai-tsaye, ‘Yansandan da ke duty lokacin ta yi ma magana, Ya amsa yana gaishe ta da tambayar dalilin zuwan ta, Ta ce “Dan Allah DPO fa?” Yay shiru sai kuma ya ce, “Lafiya dai?” Ta Dan murmusa ta Ce “E, idan da hali ka ce ya yi bakuwa matar Tsohon Sarki Abubakar Ahmaad Lamiɗo ce, mahaifiyar Dr Ahmaad” Ya washe haƙora yana faɗin “An gama Ranki ya daɗe” Wata ‘Yarsanda ita ma ta matso fuska a sake tana mata ta’aziya ta amsa, sannan ta nuna mata kujera Ta ce, “Ranki ya daɗe ko za ki zauna Kafin ya faɗa masa kina jira” Tana zama Ɗansandan da ya tafi Office ɗin DPOn ya ƙaraso da saurinsa ya ce, “Ranki ya daɗe ya ce Za ki iya shiga” Yanda ya ƙarasa maganar cikin girmamawa dole ya ba mutum dariya, Ya raka ta har ƙofar Office ɗin ta yi Knocking ƙofar ya bata izini ta shiga Ɗansandan ya koma Wajen sauran ‘Yan’uwansa.

Fuska a sake suka gaisa da DPO yana kuma mata Ta’aziyar mutuwar Ɗanta tana amsa masa, Ya nuna mata Kujera ya ce “Ranki ya daɗe ga wurin zama” Ta zauna cikin nutsuwa ta maida dubanta ga Abdul ta yi gyaran murya ta ce, “Yallaɓai Ashe abin da ya faru ke nan, Allah ya kyauta! amma mece ce matsayar Ɗana da kuka damƙe?’’ Yanayinta ya nuna ma DPOn sam ba ta da girman kai ko kuma nuna ɗagawa, Shi ya sa shi ma ya tattara nutsuwarsa ya maida kanta Ya fara mata Bayani, “A gaskiya ba za mu iya barinsa ya tafi ba yau, sai mun yi Bincike mun samu wata hujjar da za ta tabbatar ba shi da sa hannu ko wani abu, Tun da shi kaɗai aka sama a gidan, shi ma Abokinsa mun saka A tafo da shi, dan dole shi ma ya kasance ciki Suspects ɗinmu, In sha Allahu idan dai suna da gaskiya komai zai zo da sauƙi” Ta jinjina kai ta kuma faɗin, “To Shi ke nan, Dan Allah Yallaɓai ka ƙoƙarta a kan al’amarin, sannan ba za a yi masa wani abu ba ai ko tun da Ba a tabbatar yana da hannu a ciki ba” Ya jinjina kai tare da faɗin, “In sha Allahu babu wanda zai taɓa su” Ta sakar ma Abdul murmushi ta ce, Mun gode Ranka ya dad’e..In sha Allahu Abdul’aziz gaskiya za ta bayyana, ka ba ni wayarka n tafi da ita, Ubangiji ya tsare mini kai” Ya miƙa mata wayar yana faɗin, “Shukraan Ammi” Ta amsa tana sake yi masa Addu’o’i, DPO ya ce “Amma da wace Number aka kira ka aka ce ka je gidan Likitocin Jami’ai ne’’? “Da Lambar shi Akarsh mai gidan Abokinmu” ‘Okay’ ya ce ya koma jikin kujerar, Ya ce, “Saboda case ɗinka yau ba zan tafi gida ba sai na sama maka tsayayyir mafita. Hajiya za ki iya komawa ko me ke nan za mu turo a sanar da ke, in kuma yana da Numbernki zan kira” Ta mik’e tana mishi godiya ta fice. Ba ta tsaya ko ina ba ta dawo gida, Parlour ta iske Imaan ta yi jigum da alamu ita take jira ta miƙe jikinta babu kuzrin kirki ta ce, “Ammi me ya faru?” Ta kamo hannayen Imaan d’in idanuwanta har sun yi ba ta fara magana, “Imaan na so a ce kun Rayu da mahaifinku, kun samu gata rayuwarku ta imganta, kun taso cikin Danginku, Ban burin Ku yi rayuwa irin wadda na yi, Amma Alhamdulillah duk da Allah ya ɗauki ran Mahaifinku da nake da, yana tare da mu, Rayuwarku ba ta Lalace ba Allah ya albarka ce ku, kun zama komai nawa, Ba ni da kowa sai ke da Ahmaad Amma Ubangiji yana sane kuma ya fi mu son Ahmaad shi ya sa ya amshi rayuwarsa Alhamdulilllah..”, Kasa ci gaba da magana ta yi, sai da ta haɗiye wani Abu sannan ta ci gaba da maganar “A yanzu ke kaɗai kika rage mini sai Abdul’aziz, na sani ko da a ce Yau na bar duniyar nan Abdul’aziz zai kular mini da ke fiye da yanda zai kula da ke, shi kaɗai ke ƙoƙarin share min hawayena bayan ku ‘Ya’yana sai shi Ina ƙaunarsa sosai, Damuwa ta min yawa ina so na share dattin da ya taru A Zuciyata amma ba ni da wanda zan faɗawa damuwata ba ni da kowa” Fashewa da kuka Imaan ta yi wani irin tausayin kansu ya kama ta, ta ƙanƙame Ammi sosai tana shessheka, “Ammi gani nake kamar ni ma ba zan rayu ba, Kina ji Likita ya ce Wani abu aka saka masa cikin Coffee ɗin da ya sha shi ya sa Cup ɗin ya yi baƙi kuma shi kanshi ya san an saka ya she ne kawai, Ammi Yaya ya san da cewa ke nan Coffee ɗin da na kai masa An zuba wani abu, amma Ammi saboda ya yarda da ni shi ya sa ya sha, ya san ba zan taɓa cutar da shi ba har Abada, Gani nake tamkar ni ce na yi sanadin mutuwarsa shi ya sa na yanke hukuncin Bankwana da farin ciki, da wane ido zan dube sa idan da ace yana da rai, Waɗanne irin kalamai zan faɗa masa na kare kaina mutumin da yake so na fiye da yanda yake son kansa, yana hana kansa farin ciki saboda ni, Yana takura kansa saboda ni Yana sadaukar da komai nasa a kaina, I love him he’s my happiness I won’t change my mind love him, he’s my dream..” Kuka ne ya ƙwace mata ta ci gaba da yi tana jan majina, Ammi daskarewa ta yi tana mamakin Kalaman Imaan da kuma tasirinsu gare ta, ba tare da ta sani ba ta ji hawaye na bin kuncinta ta share su tana faɗin, “No Imaan! ya za ki ce haka, ni ce na ba ki Coffe ɗin kika kai mishi, karki ga laifinka ki yi blaming ɗina yanda kike so, Amma wallahi! wallahi! Imaan har Abada ba zan iya cutar da ku b..” Ta yi saurin cewa “Ammi ni na sani, Ba sai kin ce komai ba, Har gaba da Abada ba zan taɓa kawo ma Zuciyata kokwanto a kanki ba, Haba Ammi idan na yi haka ina da tabbaci sai ubangiji ya yi fushi mai tsanani da ni, I have already know who are you so there’s no need to yo to say anything i trust you nd my Brothers more than i trust myself and anybody in this world” Ta rungume ta sosai ita ma Ammin kuka take an asa mai lallashin Ɗan’uwansa. Sun kai 5mnts a haka kafin Ammi ta yi ƙarfin halin faa tsaida nata Hawayen, sannan ta fara goge ma Imaan nata, ta ce, “Kin san me?” Ta girgiza kanta ta ce “No!” ta lumshe idanuwanta ta ce, “Ina ƙaunar Abdul’aziz da yawa kamar dai yanda nake sonku ke da Ahmaad, Yanzu haka duk saboda ƙoƙarin da yake yi da mu, yana Police station an kama shi, ba za a sake shi ba yau ma, sai dai mu yi ta Addu’a” Lokaci ɗaya Imaan ɗin ta ruɗe ta ce, “Yaushe?? Me ya aikata?” Cikin tsananin damuwa ta ce, “Imaan wai ana zargin ya kashe Dr Daniel da Akarsh, yanzu haka Akarsh na hospital shi bai mutu ba Dr Daniel kuma ya mutu” A firgice ta ce “Kisa fa Ammi Innalillahi Wa’inna ilaihi Raji’un ya Rabbi!!” Ta ɗaga mata kai ta ce, “Ki yi masa Addu’a kar ki yi kuka kin ji, Yanzu lokacin barci ya yi mu je mu kwanta” Shiru kawai ta yi saboda Damuwa ba ta ce komai ba suka miƙe zuwa Bedroom.

Waiwaye

Wace ce Nafi ‘yar Fulani.
A ƙarƙashin ƙaramar hukumar Sandamu (Fago). Rugar Fago ta kasance ɗaya daga cikin rugogin fulanin da ke a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Sadamu. Tafe matshiyar Bafulatanar take tana ‘yan tsalle-tsalle da waƙoƙi, a ƙiyasi ba za ta haura shekaru goma sha biyar ba, Dajika suke ta wucewa ita da saniyarta, Da ka gan ta ka san hankalinta kwance ya ke, Har ta fara ratso bukkokin fulani. Tana gab da wuce wata bukka ta ga wani ƙaton Maciji mai kyan jiki sosai, yana da baƙaƙen idanuwa da kaurin jiki sosai da mugun tsayi, Tana ganin shi ta yadda ɗan karanta ta zuƙunna kaɗan ganin bai sulale ya bar wajen ba, Ta sanya hannu ta ɗauko ahi duk da ɗan nauyinshi da sulɓi cike da Nishaɗi, sai ta ga ashe ciwo ya ɗan ji, ta ɓata fuska cike da shiririta ta kalli shanuwarta tana mata magana, “Choummo za ni wajen mai magani na kai macijin nan ba shi lahiya, ka zo mu tahi” Ta ƙarashe maganar da saita shanuwar hanyar da za su ɗauka ta cikin Rugar. Ko a yanayin tafiyarta za ta iya tabbatar maka da ita ba cikakkiyar mutum ba ce ga kuma ƙaton maciji riƙe a hannunta babu abin da ya yi mata, Lokacin da suka fara wuce fulani, Wata tsohuwa tana tsaka da shan Kindirmo mai kyau ta ga wannan tashin hankalin Nafi riƙe da maciji ta kurma ihu ƙwaryar da kindirmon ya ke ciki ta faɗi, Jikinta ya ɗau kyarma ta kasa tafiya don ba ta taɓa ganin irin ƙaton maciji haka ba. Nafi na ganin yanda tsohuwar ta tsorata ta wani haɗe rai cike da mugunta, tunowa da ta yi da zagin da matar ta yi mata jiya ta shiga kasuwa da kiran ta mayya da ta yi bainar nasi ya sa ta yi wata irin zabura cike da rashin mutunci da iya sarrafa harshe wajen masifa ba ko kunya, Ta sakar mata macijin a jiki. Ihu matar ke yi ganin macijin ya harɗe bisa ƙafafunta, “Jauro Jauro Jauro Maciji Hanɗ..” Jauro da ya je ɗibo musu ruwa ya jiyo Ihun Inna Hansai Ya ƙaraso da gudunsa kamar zai kifa, Wani irin ja ya yi ya tsaya chak kamar an dasa shi ya sauke wani wahalallen numfashi ganin Nafi tsaye ta riƙe ƙugu tana hararar mahaifiyarsa, Ya juya da mugun gudu ya koma Inna Hansai sai ihu take ta gama saɗakaswa haɗiye ta macijin zai yi. Ta turo ƙaramin bakinta, tana Zare mata rikitatun idanuwanta masu Rikita ƊanAdam ta ce ”Inna Hansai idan kika shake ce min mayya sai na sa maciji ya cinye ki” Ta duƙa ta ɗauki macijin da ƙyar ita ma, Suka ƙara gaba. Duk inda fulani suke ta tunkaro kowa watsewa yake yi, har ta shiga cikin Rugar ta fara tunkarar Gidan malam Sama’ila mai magani, Tun a ƙofar gidan Waɗanda ke zazzaune suka ganta kowa jikinsa ya ɗauki rawa suka fara neman hanyar guduwa, Ta wani murtuke fuska ta buɗe murya tana ƙwala ma Malam Sama’ila kira “Malan Sammamai’ii’ila hito” Daga cikin Bukkarsa ya jiyo kiran kuma ya san babu mai ɓata masa suna haka na rainin wayau Sai Nafi. Ya miƙe zai fito yana addu’a Allah ya sa ba wani abin ba ne ba na tashin hankali. Ya sadaƙar kawai ya fito waje, Ganin macijin hannunta da ya yi ne ya sa shi ɗan tsorata ya ce, da harahen fulatanci, “Nafi Baffa yau hadda ɗan rakiya ke nan?” Chillo mashi macijin ta yi a hannu ya chaɓe a tsorace ta ce, “Magani za ka yi me yanzu be lahiya” Ya tsorata sosai da jin furucinta, Ya haɗiye wasu yawu da ƙyar ya ce, ‘In ban da abinki Nafi ai ba a yi ma Maciji magani kin manta’, yanda ya ga ta giggimtse na ya sa shi faɗin, “Yi hakuri, bari na ba ki maganin ki shafa masa.” Ta ɗauki macijin shi kuma ya koma cikin sauri ya ɗauko wani ƙullin magani shi kanshi bai san ko na miye ba ya miƙo mata. Ta karɓa ta ƙara gaba. Ta sa ma macijin Magani suka ci gaba da tafiya, Ta ga har ya fara mutsu-mutsu ta sake shi ya sulale ya yi cikin ciyayi. Gidansu ta koma ko sallama babu ta shige cikin Bukkar Baffanta, Ta faɗa jikin Babarta da ke zaune kamar su ɗaya sak, ita ma Kyakkyawa ce sosai kamar ba mutum ba ga wasu idanuwa da baƙin gashin da kuma fari sosai. Ta faɗa jikinta tana Faɗin, “Babata na gaji fa, Amma ki kwo Kindirmonki” Ta ce, “Yawwa ɗiyar Baffanta, Mu da ke so mu fi kowa kuɗi a rugar nan” Ta miƙe ta ɗauko ƙwaryar Kindirmon ta ba ta. Ta ƙarsa gaban Baffa ya yi mata addu’a ta fice daga gidan, Har cikin kasuwa da take zuwa talla da ‘Yar shanuwarta ta ke tafiya. Ta shiga cikin kasuwar ta zauna inda ta saba cinikinta, Ko mintuna biyar ba ta yi ba da zama Aka rufe da ciniki dan Ƙa’ida ne dole idan fa kana da kuɗi ka siya san tana gane mai kuɗi da marar su, Idan ba haka ba ra ja maka abin kunya cikin Rugar. Ta gama saidawa ta juya cikin nishaɗi ta ɗauki hanyar Komawa gida, Wani costomernta da ke Ƙauyen Sandamu ya tsaida ita ya ce, “Yawwa Nafi ki faɗa ma Baffanki ku je fadar Mai Gari akwai tattunawa za mu tafi da wasunku birni.”

Ta isa Bukkar Baffa ta sanar da shi, ta miƙa ma Babarta kuɗin Nonon ta fara azalzalarsa ya tashi su tafi, sai magiya ta ke masa kamar za ta cinye sa, ya ce, “Kai Nafeesa to mu je” Ta miƙe fuskarta cike da fara’a suka ɗauki hanya. Malamai Biyar ne suka baƙunci Rugar daga Makarantar kwana ta Sandamu Local government, Suna kira ga fulanin rugar a kan ilimin Zamani da na boko da zuri’arsu za su samu a makarantar, sun faɗa shuwagabannin Sandamu Local government ne suka wakilta su akan su zaɓi ɗalibai hamsin waɗanda za a tafi da su, su yi karatu Kyauta iyakacin iyaye siyan suturar da Ɗalibi zai saka da kayan karatu. Tsit Fadar ta yi kowa yay shiru duk taron fulanin Aka rasa wanda zai ce ga ɗansa a tafi da shi, Nafi ta yi wuf ta ce, “Ni za ni ina so ko Baffa?” Baffa ya jinjina kai ya ce Nawa ne kuɗin da ake buƙata a siya kayan karatun da kaya? Shi ma mai gari ya ce zai saka Ɗiyarsa ɗaya, haka taron Fulanin ya tashi mutum uku kawai suka amince, an ƙiyadde musu adadin kuɗaɗen da za su kawo fadar gobe, Jibi kuma sai a tafi da yaran. Malam iro mahaifi ne ga Nafi Yana da mata biyu Hure ita ce uwar Gida sai Hawwa. Baffulatani mai gaskiya da riƙon amana tare da tarin ilimi. A lokacin da aka yi fama da Mayu sosai da Aljannu a rugar suna fitowa Ta kowace sufa da suke so, suna kuma ɓanna da kashe-kashe, An rasa yanda za a yi da su sun addabi fulanin, Malam Iro yana da ilimi sosai dan haka ya fara amfani da baiwarsa yana magunguna kuma ana dacewa sosai, ya zamana babu wanda Mayun da Aljanun suke shakka irinsa, Fulanin kuma suna matuƙar ganin ƙimarsa.

Lokacin da abin ya gagara sosai ya bar Rugar zuwa Wani gari babu wanda ya san sunan garin ko wani abu, ya dawo da Magunguna kala-kala da kuma Mata da ya auro wacce zubinta ya girgiza Fulanin rigar sosai, sam ba ta da zubin mutane, ga tsananin kyawu mai fizgar zuciya, Allah ya ba ta baiwar Idanuwa rikitattu masu zautarwa.

Ga tsananin kyawu da Allah ya ba ta, Wato Hawwa mahaifiyar Nafi. Lokacin ne aka kuma samu wata Mayya mai suna Lohaj, sam ta gagari kowa da kowa a Rugar ko da yaushe fulanin cikin killace ‘Ya’yansu suke yi da dabbobinsu, Shi kan shi Malam iro ta gagare shi, domin ta shanye masa Ɗan cikin matarsa Hure ta yi ɓari, Ta hana kowa saƙat, babu wani maganin mayu da ke yi mata ko daidai da misƙala zarratin.

<< Zuciya 13Zuciya 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×