Skip to content
Part 2 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Kafin faɗuwar rana maganar ta game rugar fulanin da suke rayuwa a rugar duk sun san abinda ke faruwa.

Hayaniya ce kawai ke tashi ƙofar gidan, matasan fulanin maza faɗi suke, a fito da Nafi su ƙona ta. Inna Hure ce ta leƙo tana masifa, “Ku je ku neme ta wani wuri bubu ita nan”. Ɗaya daga cikin matasan ya ce “A fito mana da ita ko mu shige mu duba da kan mu”.

Rigima ce ta barke tsakanin samarin da Inna Hure, ta kasa ta tsare ba wanda zai shiga, suna tsaka da rigima uban yaron ya bangaje Inna Hure ya shige gidan suma sauran matasan suka shigo, kaf sun duba ko’ina amma babu Nafi babu dalilinta.

Nan fa suka fara masifa suna faɗin an san inda aka ɓoye ta, inna hure ba haƙuri ta biye musu. Kamar abun arziƙi duka suka fice daga gidan. Inna Hure ta ci gaba da masifa faɗi take yi, Yau sai Nafi ta bar mata gidanta.

Ba a wani jima ba gabannin magrib sai ga su dawo da kalanzir me uban yawa, suka fara watsawa zasu ƙona gidan.

Hankalin Inna Hure da hassatu ya yi mugun tash ganin da gaske ƙona gidan za a yi. Ana cikin wannan yanayin sai ga Malam Iro mahaifin Nafi Da ƙyar ya kawo ƙofar gidan ya shigo kasancewar baya gani sosai bai zama makaho ba amma baya gani sosai. Haƙuri ya fara ba su, cikin tattausan lafazi, da ƙyar ya shawo kan matsalar suka fice zuwa Fada.

Maigari ne ya soma magana, “malam Iro ka ji abinda suka fada ko? A karo na ba adadi yarinyar nan tana ta kashe fulanin rugar nan da mutanen gari amma ka kasa daukar mataki, a wannan karon gaskiya ka yi mata gargadi na ƙarshe, mun Baku dama da yawa, Idan har ta sake aikata wannan laifin na kisan kai zamu kore ta daga rugar nan gabadaya ba za ta sake dawo mana ba, wannan shi ne adalcin da zamu iya yi maka.” Amsawa ya yi ya ce, “Hakan ba zata sake faruwa ba”.

Daga haka kowa ya kama gabansa duk da mahaifan yaron da sauran fulanin dam basu ji daɗin hukuncin me gari ba, hasalima ransu ya sake ɓaci ne kawai, sun gaji da matsalar Nafi bafullatanar mayyar da ke kashe musu mutane amma an kasa ɗaukar tsattsauran mataki tamakar ana tsoronta.

Ko da fulanin na tsoronta amma abun ya ishe su har sun fara bayyana fushinsu.

Shesshekar kukanta ne ke tashi kawai cikin jejin fuskarta ta yi Jajir ta jigata, sosai gabaɗaya ta gaji da rayuwa, sai yaushe ne za a dai na mata Kallon mayya, yanzu ana nufin ita ce ta kashe Idi wace kalar mummunar ƙaddara ke bibiyar rayuwarta haka? Tambayoyin da suka addabi zuciyarta kenan a kowane lokaci, musamman ma idan wani ya mutu aka ɗaura alhakin kanta.

Ɗago kanta ta yi, tana kallon hannayenta da suke lafce da jini, ta sake mayar da kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka me taɓa zuciya, Tun tana kukan yana fitowa har muryarta ta disashe, ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya.

Dariya ta fara ji me ban tsoro na tashi cikin dajin, lokaci ɗaya hankalinta ya tashi, wani mugun tsoro ya shige ta, ta ƙanƙame jikinta. Sunanta ta ji wata murya na kira da ƙarfi kamar kunnenta zai fashe, ta miƙe jikinta na kyarma ta fara gudu, da ta kusa fita da dajin sai a maido ta inda take.

Cikin tsananin Ruɗu ta miƙe zata sake guduwa, ta ji wani irin abu, kan ƙafarta, kallon da za ta yi taga wani danƙareren Maciji fari tas, yana nannaɗe ta, irin yadda ta gigita ya sanya komai nata ya tsaya ta sume, macijin kuma ya nannaɗe ta har wuya.

Ciki-ciki ya yi sallama ya shigo ɗakin da suke, Ammi ce ta amsa masa tana murmushi, sai da ya zauna kusa da ita sannan ya ce, “Ammi zan koma masarauta”. Wata irin ƙwarewa ta yi, cikin sarƙewar murya ta ce, “Saboda me?” kamar ba zai yi magana ba ya yi shiru, sai da ya fesar da iskar bakinsa sannan ya ce “Haka”.

Jinjina kai ta yi cikin damuwa ta ce, “To Allah ya tsare ka Dr ka kula da kanka sosai, ba na son neman magana” jinjina kansa ya yi, budurwar da ke kwance ce ta turɓune fuska tana faɗin, “Ya Please kar ka tafi” Hararta ya yi, ya fice bai ce komai ba. Turo baki ta yi ta ce, “Ammi Please ki ce kar ya tafi” Ajiye Cup ɗin hannunta ta yi tana faɗin, “Auta kin cika rigima” Ta miƙe ta shige toilet ta bar ta tana ta mita.

Bai ɓata lokaci ba ya fito hannunsa ɗaya riƙe da mukullin mota ɗaya, ɗayan kuma ya kara waya a kunnensa, ya zauna bisa ɗaya daga cikin kujerun parlourn yana magana “idan ka ɓata lokaci ba zaka same ni ba” yana gama faɗar haka ya kashe wayar.

Bai fi 10mnts da gama wayar ba aka yi knocking ɗin ƙofar parlourn, “Yes,” kawai ya faɗa a daƙile ya lumshe idanuwansa.

Abdul da ke shigowa ya fasa ihu yana faɗin, “Dan Allah Dr kai ne da gaske? Wow wallahi ka yi kyau yau zaka haukata Babies, Please bari na maka photo ko guda biyu” Taɓe baki ya yi, a hankali kuma ya ce “kar ka fasa min kunne da ihu tashi” Ɗaukar Apple ɗin da ke gaban Dr ya yi, sannan Suka jero, a tare suka fito har suka iso harabar bai sake magana ba, Abdul sai ‘yan surutai yake shi ɗaya dan Ya yi amma ya yi banza ya ƙyale shi.

Parking lot suka ƙaraso ya miƙa wa Abdul key ɗin ba tare da ya yi magana ba, Buɗe wata Farar mota ƙarama suka yi me zubin machine suka shiga Abdul ya ja su. Har suka miƙo titi Bai yi magana ba, ƙaramin tsaki Abdul ya ja, ya ce “Dr A ni fa ba zan iya zama haka ban yi magana ba, a to kar ka ga laifina idan na yo ni kaɗai tun da kai bakinka ɗinkakke ne, Shi mutum ace kullum magana ta fi komi wahala gurinshi ba fara’a ba komi maganar ma babu haba mana” Still bai tanka masa ba, ya ƙulu ya sake faɗin, “kai fa baka san daɗin magana ba wallahi…”

zai ci gaba da surutu Dr ya yi tagumi da dukkan hannayensa ya zubo masa idanu “Surutunka ya yi yawa ka nemi magani” “Wane magani kenan?” ya tambaye shi cikin rainin wayo a hankali ya dago yatsansa ya nuna masa ya ce a hankali “double two fucks”. Sheƙewa da dariya ya yi, ya kunna waƙa ya ci gaba da bi yana tuƙin. Har suka shigo babban gate ɗin bangaren masarautar.

Ɓangaren karshe da ya kasance na Dr suka nufa, ya yi parking suka fito suka nufi ƙofar main parlour, ya latsa Security lock ɗin suka shige. Sai da suka nutsu sannan Abdul ya gyara zama ya fuskance sa sosai ya ce, “ka ce kana son mu yi magana me muhimmanci ina sauraronka”.

Ajiye wayar da ke hannunsa ya yi ya ce, “Good! Abdul kai ne kaɗai zan iya faɗawa matsalana, ba na son aikin da Akash ya ce dole sai an yi, Ammi zata shiga damuwa fiye da kowa and the king too…” sai da ya dafe saitin zuciyarsa ya numfasa, sannan ya ci gaba da magana, Abdul ba na jin daɗin komai please…take care of Ammi nd Imaan nd Fula..,” sai kuma ya yi shiru muryarsa ta sarƙe, ba a bina bashi sai dai company duk masu bashina na yafe musu, akwai kuɗi cikin bank ɗina na U.B.A, zamu fita da wuri gobe”.

Sai numfashi ya ke ja saboda magana me tsawon da ya yi, cikin fargaba Abdul ya ce “Dole ne fa ayi maka aikin, sannan waɗannan maganganun fa ka ruɗar da ni, ka ce Fula waye haka??” ya goge zufa da hancky ɗinsa duk da Acn dake ɗakin. “Dan Allah ka min magana A ina cikin rud’u”. Sai ya yi wani tsadadden murmushi Wanda ya sake sanyaya jikin Abdul sannan ya ce a hankali, “Just Forget about it” “Please Ahmad ina bukatar karin haske” Sai da ya ja numfashi sannan ya ce “Ohh Abdul! kana son sani surutu anyhow na gaji gobe zamu yi magana ko”.

Ba haka Abdul ya so ba amma ya yi shiru yana ta saƙe-saƙe a ransa ga kuma tausayin Ahmad da ya cika zuciyarsa..

Kwance take ƙasa cikin ciyayi, sai a hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta saboda zafin rana da kuma yadda ranar ta dalle ta sosai.

Buɗe idanuwanta ta yi waɗanɗa suka mata nauyi sosai, ko gama ware su bata yi ba ta rufe saboda tsananin hasken ranar. Sai da ta jima a haka da ƙyar ta miƙe zaune ta matsa gefe kaɗan sannan ta buɗe idanuwanta sosai.

Wata irin karta cikinta yake na yunwa ta miƙe tana layi kamar ta yi maye saboda yadda sassan jikinta ke kwankwatsa, abubuwan da suka faru ne suka shiga dawo mata take wasu hawayen baƙin ciki suka shiga zubowa da idanunta, tana tambayar kanta ‘Da gaske ita ɗin Mayya ce?’ da ƙyar ta iya takowa ta fito daga dajin zuciyarta ta yi wani irin nauyi fargaba ta cika ta.

Ta yi sallama a hankali ta shigo zuciyarta sai bugu take cike da tsoron fitina da masifar Inna Hure.

kamar jira Inna hure take ta miƙe tsaya ta karkace baki ta fara bala’i, “Lalataccen yaro ka dawo daga Findahon (Isakanci/Lalatar) to ka fita yanzu ba zaka sake zama ba, Hauwa ta bar min Bala’i, ki fice ni ba na tsoron iskacinka fa!”

Tsabar bala’in hausar ma bata fita sosai. Hinde ce ta taso cike da munafurci tana faɗin, “Haba Hure daɗina da ke rashin hakuri fa matso ki ji” kamar ba zata bita ba sai kuma suka ja gefe, ta janyo Inna Hure ta fara mata raɗa, tun kafin ta kai aya Inna Hure ta yi shewa cikin harshen fulatanci take faɗin, “Kudi fa Hinde, na zata kwana yau ba ku tafi tun yanzu”. Jan ta ta yi, suka sake magana “Ke Hure da Allah ba wannan ba yanzu ba ta abinci ta ci, sai ta yi wanka dan muji daɗin more kuɗi wallahi Hajiyar Birnin nan bata harkar tsiya kuɗi zamu samu, qur’anin Allah gidanta kamar a lahira” “Qur’an na yarda ke Hinde na kusa zama maikudin rugar nan kamar ki fa huuuu j`anniha(shagali babba) amma fa sai na daki tuwona da kununa ba zan bar ta haka ba ehe”

“Ba wannan ba, baki so a ganta da kirki yadda zamu wafci arziki, ki barta kawai ke da zaki mori kudi kawai ki yi yadda na ce, mu tafi da ita da kuzari”.

“Haka ne fa bari in kira ta, Ke Nafi zo nan” ta kwala wa Nafi kira. Cikin Nafi na kyarma ta amsa ta zo ta tsaya, Sai da ta harare ta, ta haɗa mata da zagika da tsinuwa sannan ta ce, ta je ta ɗauki abinci na nan madahwa ta ci ta yi wanka. Kamar a mafarki ta ɗago daga tsugunnen da take ta kalle ta bakinta ya kasa rufuwa saboda tsananin mamaki. Tsawa ta daka mata “Zaki tashi ki yi abinda na ce ne ko kuwa??” cikin sauri ta miƙe, duk jikinta a sanyaye tunani fal a ranta ta ɗauki abincin da yake rufe da fai-fai da kindirmon da aka haɗa, kamar kar ta ci saboda tsoro kar a ace inna Hure kashe ta zata yi, amma saboda mahaukaciyar yunwar da ke cinta ta manta da wani zargi ta ci ta yi nak.

Ta yi wanka ta shiryo cikin kayanta na fulani ta dawo ta tsaya gaban Inna Hure, ta ce “Inna na gama.” sai sannan Hinde ta tanka mata, “Yauwa Nafi, So nake na tafi da ke birni yau Aikatau Ki saki jikinki karki nuna ƙauyanci kin ji ki dangwali arziki.”

Hawaye ne suka cika idonta, ta san dama ba banza ba, ta ɗago cikin sanyin jiki ta san bata da zaɓin da ya wuce haka, Amma baffanta shi ne damuwarta. “Ba ki ji bane??” Inna ta faɗa cikin fad’a, a sanyaye ta amsa da “To”.

Umarni Inna ta bata da taje ta haɗa kayanta, ta miƙe jiki ba kuzari ta nufi ‘yar bukkarta.

<< Zuciya 1Zuciya 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×