Skip to content
Part 3 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Tana daga cikin ɗakin ta jiyo sallamar Baffanta. Wani irin kuka ne ya kufce mata ta yi saurin toshe bakinta, tana jin zuciyarta babu daɗi kwata-kwata. Ta share hawaye ta kwashi ‘yan tsummokaranta ta ƙulle sannan ta fito.

Kallon Baffa ta yi cike da tausayawa ta ce “Ina yini Baffa.’’ Murmushi kwance kan fuskarsa ya amsa mata, “Lafiya lau Nafisatu ke ce?” cikin sanyin jiki ta amsa saboda hararar da Inna Hure ke banka mata. “Eh Baffa ni ce”.

Baffan zai sake magana Inna Hure ta huro hanci ta ce, “to me ɗiya! kar ka ɓata mini lokaci gwara da ka zo ku yi sallama da ita, dan birni Hinde zata tafi da ita aikatau.”

Cike da mamaki ya ce “Hure aikatau hwa kika ce?” a masifance ta bashi amsa “malam ina tunanin kai ba kurma ne ba, ka ji na ce aikatau ai ba wasa nike ba, dan ni ba zan iya zama da ita ba baƙin jininta ya shafe mu ni da Hassatu, ko kuma ta ci gaba da janyo mini bala’in fillon rugar nan ba, idan kuma ka ce sai ta zauna billahillazi sai na cikin maciji ya fita ‘yanci da komi”.

Shiru Baffa ya yi yana tunani, Zuciyarsa ce ta dinga ayyana masa gwara Nafi ta nisanta da fulanin rugar ko ta samu ‘yanci a matsayinta na ‘yar Adam, ta kuma huta da fitina da masifar Inna Hure da Hassatu.

Bashi da zaɓi da kuma ɓulalliyar mafitar da ta wuce ya bita da fatan alkhairi da addu’ar tsari hakan ya sa shi faɗin, “Nafi ki kula sosai Allah Ya tsare ki a duk inda kike Allah Ya zama gatanki, Ubangiji ya albarkaci rayuwarki”.

Hawaye ne suka shiga zubowa daga idanunta jiki a mace ta amsa “Amin Baffana na gode”.

Yadda ta yi magana murya a matuƙar sanyaye ne ya ƙara dagula lisaafin Baffanta, zuciyarsa ta raunata, kukan zuci kawai yake yi, A duniya babu wanda yake tsananin so da ƙauna da kuma tsantsar tausayawa irin Nafi.

Maganar da Hinde ta yi mata ce ta sanya kuka taho mata, “Nafi lokaci na ƙurewa ya kamata mu tafi” kuka ne ya ƙwace mata, Baffa ma duk dauriyarsa sai da hawaye suka zubo masa.

Tana kuka Hinde ta tasa ta gaba Inna Hure na bayanta suke fice daga gidan, Sai da Inna Hure ta yi mata gargaɗi sosai, sannan ta dawo, ita kuma Hinde ta umarce ta da ta chanza kaya bayan sun ƙaraso gidan ta chanza kayan sannan Hinde ta ɗauki abun da zata buƙata suka fito ta datse gidan.

Tafiya suka fara har suka ƙaraso cikin kasuwa nan ne suka hau babur su biyun dan a kai su tasha.

Bisa babur ɗin me masifar ƙara suka taho, ga su biyu ne kuma akwai nisa sosai da inda ake hawan motar.

Tun da me babur ɗin ya taho da su Nafi ta lula duniyar tunani, ita kaɗai take magana cikin ranta. ‘Yanzu kuma wacce ƙaddarar ke jiranta, wace irin masifar zata tarar a birnin, ya rayuwarta zata kasance me ya sanya take rayuwa kamar ba ‘yar Adam ba komai yana zo mata banbaraƙwai. Yanzu kuma ita ce da ina mahaifiyarta take, wace irin rayuwar maraici da rashin gata da ƙunci take yi haka. Allah sarki Baffanta abun alfaharinta sai yaushe zasu sake ganawa da shi???.’ Waɗannan sune tambayoyin da ke danƙare a zuciyarta.

Tafiyar kusan mintuna Arba’in suka yi, suka ƙaraso Inda ake hawan motar da za a fice daga rugar ta su. Sallamar me babur ɗin Hinde ta yi, suka matso inda yagwalgwalun motocin suke, an yi sa’a mutum biyu ake jira, suna biyan kuɗi suka shiga mota ta tashi zuwa garin Katsina.

Ƙarfe 5:37 Dr A ya fito daga wanka ya shirya tsaf, sannan ya dawo parlour inda ya bar Abdul shi ma ya zauna.

Miƙa Abdul ya yi yana aje wayarsa ya ce, “mutuniyar nake ji fa.” tabe baki ya yi, ya dauki wayar da ke gefensa karama ya dannawa wata number kira tana ringing ya miƙa masa ba tare da ya yi magana ba. Ya karɓa ya kara a kunne, jin muryar Sale kukun Dr ya sanya shi faɗin, “Hello Sale nine ba Yarima ba, kana ji na, ina son a kawo mini abinci yanzu ko ma wane kala ne ina jin yunwa”. Daga chan bangaren Sale ya amsa, “Ai ho ranka shi daɗe ashe kai ne, yanzu kuwa zaka ganni” ko amsar Abdul be tsaya ji ba ya yanke wayar.

Girgiza kai kawai Abdul ya yi, dan shi tsakaninsa da Allah dariya Salen ke bashi. Ya juyo ya kalli yarima kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, mintuna bakwai tsakani, sai ga knocking ɗin ƙofar ana yi, Abdul ya miƙe yana hamma ya doshi ƙofar ya buɗe ɗaya daga cikin masu tsaron ƙofar ne ya faɗa masa Sale na waje, umarni ya basu da su bar shi ya shigo ya dawo aikinsa ne. Shigowa Salen ya yi yana ‘yar mita ƙasa-ƙasa. Ya jera masa abincin da ya kawo a dinning, yana gashe da su, amma Yarima ko kallon inda yake ma bai yi ba kawai dai ya ɗaga masa hannu. Har zai yi saving ɗinsu Abdul ya dakatar da shi ya ce, “Bar shi ma zuba ka ji Sale mun gode haka ma.” Cike da walwala kan fuskarsa ya amsa masa ya fice.

Zuba tuwon shinkafa da miyar Kuka da ta ji tsoka dafaffiya Abdul ya yi, ya ci sosai yana ta rausaya kai saboda yadda abincin ya yi daɗi sosai, ya kalli Dr ya ce, “gaskiya girkin ya yi dadi ya kamata ka ci fa”. Girgiza kansa ya yi kaɗan alamun ba ya jin yunwa, bai takura sa saboda kar ya sa mishi gajiya ya kammala ya dawo ya zauna.

Tun ɗazun yake son ya yi masa maganar da ke cinsa, ya daure dai ya ce “Dr Please ina so mu yi magana”. “Umhum” ya bashi amsa a takaice. Cikin lalama Abdul ya fara masa magana, “Ahmad na roƙe ka dan Allah ka amince ayi aikin nan ka ga Akarsh 1week ya bamu kuma yanzu sauran six days idan kuma ba a yi ba akwai matsala sosai fa, Please Ahmad muna buƙatar Rayuwarka.”

Murmushi ya yi me matuƙar kyau, wanda Abdul ya daɗe bai ga ya yi irinsa ba sannan ya fesar da numfashi ya ce, “Oh Abdul!! Da ace hakan zata kasance da zan fi kowa farin ciki yadda zan kama enemies buh zuciyata bata yin aiki an riga da an chanza ta, ina tabbatar maka asarar lokaci ne da dama kawai za a yi, idan ta kasance Akarsh ya matsa zasu yi aikin ko da anyi babu nasara”.

A wannan karon har hawaye sun fara taruwa a idanun Abdul jikinsa ya yi sanyi laƙwas gani yake yi ma yarima ya mutu ne, ya yi ƙarfin halin faɗar “Me fada ba za a yi nasara ba ka manta da ubangiji ne??” Silently ya haɗa hannayensa guri ɗaya kamar yadda ya saba cikin nutsuwa ya ce, “please mana Abdul try to understand me, ka bari gobe zamu yi magana zuciyata tana ciwo yau na yi surutu da yawa”. Daga masa kai kawai ya yi yana kallonsa, Allah ya sani a duniya yana yiwa Ahmaad ƙauna ta tsakani da Allah ne kuma yana tausayinsa sosai.

Hancky ya miƙo masa yana ɗaga masa gira ɗaya, karɓa ya yi ya goge hawayensa, still bai daina kallonsa ba, sai da ya ɗan harare sa sannan ya yi murmushi ya kawar da kansa dan ya san saboda kallonsa da yake ta yi ne.

Miƙewa ya yi Ya shiga ya yo alwalla ya dawo, shima Abdul ya shiga ya yi, Saboda lokacin sallar magrib ya kusa bai fi 20mnts ba.

Tun da suka fara wuce rugar ta su, Nafi ke kalle-kalle har tafiyar ta su ta miƙa sosai sun yi kusan awanni uku suna tafiya, har barcin wahala ya ɗauke ta. Tashinta Hinde ta fara yi, “Nafi fito muyi sallah mu ci abinci”.

Ta wattsake sannan ta amsa mata da ‘To”. Ita Nafi sai a lokacin ta tuna da rabonta da sallah tun jiya da mutuwar yaron, da kuma rigimar da aka yi, duk da bata nan. Ta fito daga motar suka yi sallah sannan Hinde ta siya musu Wainar tsala suka ci suka sha ruwa sannan suka komo cikin mota sauran mutanen ma haka, aka ci gaba da tafiya.

Tafiyar awanni biyu da ‘yan mintuna suka ƙara duk saboda motar da ba mai kyau bace, cikin birnin Katsina suka shigo, me mota ya nufi tasha da su.

Nan ne fa Nafi ta saki baki da hanci ta baza idanu tana kalle-kalle kamar idanuwanta zasu faɗo, ta wani lambu mai kyau suka zo wucewa mai ni’ima da sanyi, Nafi Ta lumshe idanuwanta ta buɗe zuciyarta ta buga, tunanin hammanta ya bijiro a zuciyarta. ‘Shin dama nan ɗin ne birnin da yake faɗi mata, yana ina lafiyarsa ƙalau rabon ta da shi tun ranar lahadi yau gasu talata??’.

Tasha me motar ya ƙaraso ya yi parking fasinjojin suka fara fitowa, sai da Hinde ta yiwa Nafi magana sannan ta ɗauko ‘yan tsumman kayanta ta fito itama. Hinde ta ruƙo hannayenta suka fito suna tafiya.

Kallon da wasu daga cikin mutanen da ke tashar ke bin Nafi da shi ne, ya hanata sakewa ta ci gaba da kalle-kallen duk inda suka yi sai an bita da idanuwa riii.

Bakin titi suka tsaya suka tsayar da Napep, Hinde ta kwatanta masa unguwar da za a kai su suka shiga.

<< Zuciya 2Zuciya 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.