Skip to content
Part 4 of 15 in the Series Zuciya by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Yanayin Unguwar shiru-shiru ba hayaniya, kuma unguwar da ka shigo zaka fahimci ta masu matsakaicin ƙarfi ce.

Bakin wani shago Hinde ta ce wa Mai Adaidaita sahun ya tsaya suka sauko, ta bashi kuɗinsa, suka ci gaba da tafiya Nafi sai kalle-kalle take yi.

‘Yan tsirarun mutanen da ke wucewa da waɗanda ke zama bakin shaguna Sai bin ta suke da kallo, har suka ƙaraso wani ɗan lungu, gida na biyu me dakali da bulan fenti suka tsaya, Hinde ta fiddo mukulli ta buɗe, ita dai Nafi cike da ƙauyanci take kallon komai da Hinden ke yi, har ta cire kwaɗɗon suka shiga.

Nafi bata rufe baki ba ta ci gaba da kallo ta tsaya ƙiƙam ta ƙi ci gaba da tafiyar. Da ƙyar ta ci gaba da takowa kamar me tsoron wani abu, Suna tsayawa ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan ta tsaya, Hinde ta sake buɗewa, still tana ta kalle-kalle na ƙauyanci, ga tsoro da ya bayyana ƙarara kan fuskarta kamar a ce tak ta arce. Sai da Hinde ta ce mata “Ki saki jikinki kin ji yanzu wanka zan sake miki kiyi fes ki saka kaya irin na ‘yan birni sai mu je gidan Hajjaju wacce zaki wa aiki amma dan Allah Nafi ki bada haɗin kai komai aka ce kiyi kar kiyi musu, idan har kika kuskura kika yi musu mutuwa zaki yi babu ruwana.”

Tsoro ne ya kama ta gyaɗa mata kai suka shiga ɗakin. Akwati ta buɗe ta fiddo wasu riga da skirt masu kyau ba laifi, waɗanda zasu yi wa Nafi daidai. Ta fiddo sabulu da soso ƙarƙashin ɗan gadonta ta kai ruwa bayi Sannan ta dawo ta bata zane ta tuɓe kayan ta nuna mata yadda zata yi wankan ta bar ta. Ta dirje jikinta sosai fatar ta yi haske sosai, sannan ta dawo ɗakin Hinde ta bata man shafawa ta shafa, ta sanya kayan Hinde ta ɗaura mata ɗan kwali ta yi kyau tsaf hasken fatarta ya ɗan dawo.

Sai Ƙarfe bakwai na dare sannan suka fito daga gidan suka rufo ƙofar jikin Nafi duk ya yi sanyi hankalinta ya tashi zuciyarta sai harbawa take, suka tsaya bakin titi, ta tare musu mai Adaidaita Sahu suka shiga. Duk da dare ne amma akwai wadataccen haske wanda ya ba Nafi damar yin kalle-kallenta, Sosai garin ya bata sha’awa da mutanen kowa na ta harkar gabansa, sun wurwuce masu gashin nama da shagunan aski da sauransu Nafi sai al’ajabi take ta yi.

Yanayin Garin kaɗai da ka gani ka san cikin ƙayataccen Birni kake me cike da wayayyun mutane masu ilimi. Tsoro ne ya fara shigarta lokacin da suka Fara kusanto manya-manyan gine-gine da fitilu masu matsanancin haske suka ƙayata layin kamar rana ga kuma gidajen masu mugun kyau da girma. Sosai Nafi ta sake karaya zuciyarta ta shiga raya mata da ƙyar idan suna cikin duniyar mutane ma, ga kuma manyar motoci zuƙa-zuƙan da ke shige da fice daga wani danƙareren gida.

Muryar Hinde ce ta katse ta, ta kuma sake tsorata ta, “Ki fito mana Nafi” jiki a mace ta fito tana ƙanƙame jikinta, suka nufi bakin wani ƙaton gida Hinde ta ƙwanƙwasa. Mai Gadin ne ya buɗe yana ganin ta ya washe jajjayen haƙoransa yana faɗin, “Hinde ke ce tafe sannu” Cike da kwarkwasa ta amsa “E nice an wuni lahiya?” zai yi magana aka yi horn ya yi saurin buɗe gate ɗin suka shige motar ma ta samu nasarar shigowa ya maida Gate ɗin ya rufe.

Tsayawa Nafi ta yi, taƙi ci gaba da tafiya saboda tsananin tsoro gani take gidan ƴan kashe mutane ne aka kawo ta. Cikin faɗa Hinde ta ce, “miye haka Nafi Mts! na ce ki saki jikinki kar ki yi ƙauyanci ana kallon mu fa”. Bata jira cewar ta ba ta janyo ta suka ci gaba da tafiya tsirarun mutanen dake wangalelen Farfajiyan suka bisu da kallo, wasu suna zazzaune a Parking lot, bisa kujeru maza da mata.

Tafiya suka ɗan yi suka ƙaraso sashe na biyu wata babbar ƙofar main Parlour suka isa ta buɗe suka shigo, duk da ta riƙe Nafi amma jikinta sai kerma yake saboda tsananin tsoro ta ma kasa yin kalle-kallen ga uban hasken da ya dalle su.

Wani sassanyan ƙamshi ne me daɗi da sanyin Ac ne ya daki hancinansu suka shigo cikin ƙaton parlourn da ya ji kayan more rayuwa. ‘yan matan da ke zazzaune ne cikin kwalliya suka fara bin su da kallo wasu sai harara suke bin su da shi wasu kuma ba yabo ba fallasa.

Wani Ma’aikacin Hajjaju ne me kama da ɗan daudu ya matso yana rangwaɗa ya ce “Hinde sabuwar kaya aka kawo ne?”, “E Gaye ina Hajjaju ne?” Tana sama bari a muku iso. ya haye sama, bai jima ba sai gashi ya dawo, duk kallon banzan da ‘yanmatan ke wa Nafi ya sa ta tsargu.

Suka fara taka mattattakalar benen Nafi ta gurɗe zata faɗi Hinde ta riƙe ta sosai, ‘Yanmatan suka kwashe da dariyar rashin mutunci, har suka buɗe ƙofar suka shiga kan Nafi na ƙasa saboda tsoro da jin kunya.

Tun da suka shigo Hajjaju ta ƙurawa Nafi idanu tana kallonta, ita kuwa ta sake tsarguwa gabanta sai faɗuwa yake yi. Har suka shigo tsakiyar ɗakin jikin Nafi bai bar rawa ba, Hajjaju sai wani irin kallo take mata irin na ƙurilla wanda ya sake tsorata ta.

Tsaye suka yi ita da Hinden ba su zauna ba, saboda ƙa’idar Hajjaju sai ta bada izinin zama ake zama. Ta ɗan yamutse fuska ta ce, “Hinde wannan ce yarinyar?” Jiki na ɓari Hinde ta amsa mata “Eh ita ce”. Bata sake magana ba sai kujera da ta nuna musu Hinde ta mintsine ta suka zauna duk da Nafi a ɗosane take dan ƙiris ya rage ta fashe da kuka tsabar tsorata.

Hannunta ta miƙowa Nafi wanda yasha Jan lalle ya yi kyau aka yi mishi ado da zobunan zinare, Nafi ta ɗago suka haɗa ido da ita saboda mintsininta da Hinde ta yi. Cikin sa’a suka yi ido huɗu da Hajjaju hamshaƙiyar macce wacce a kallo ɗaya idan ka yi mata zaka fahimci arziƙi da wadata, hutu, gayu, jindaɗi, wayewa, isa, sun yi biyayya a wurin.

Ta juya idanuwanta da suka sha kwalli blue kan na Nafi. Irin yanda Nafi ta zaro nata idanuwan ya sa dukkansu Zuciyonsu suka buga, Nafi ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa. Gyaran murya da kuma mintsininta da Hinde ta yi ne suka sake bala’in tsorata ta kamar ta ruga da gudu sai lokacin Kewar Baffanta ta bijiro mata ƙwalla ta cika idanunta.

Cikin kunnenta Hinde ta raɗa mata, “Ke Nafi wannan wane irin busasshen iskanci ne haka? dan ubanki tashi kije shegiya kar ki ja min asara dan wallahi na rasa wannan damar sai kin ci uwarki tashi ki je tana kiranki!” Da fullanci take mata maganar ma saboda masifa ta turata, ta isa gaban Hajjaju. Hajajju ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita sosai cikin wani irin salo ta ce, “mi ye sunanki?” Bakinta na kyarma halshenta na datsewa da haƙoranta ta ce “Nafi”. Ta yi murmushi “You mean Nafeesa ko??” Ta ɗaga kai duk da bata san me take nufi ba ita dai a tsorace take, saboda bata taɓa barin yankin Rugarsu ba.

Miƙewa Hajjajun ta yi, ta sake ta. Ta shige Bedroom ɗin da ke cikin Parlourn ba ta wani daɗe ba sai ga Gaye ya shigo shi da wata macce da Trayn Abinci, su ka shigo Gaye ya kalli Hinde ya ce, “Hinde Hajjaju ta ce a kawo muku abinci ku ci da baƙuwa”. Washe haƙora ta yi ta ce “Godiya muke”.

Macen da ta riƙo ƙaton tire ɗin ta ajiye tana musu sannu sannan suka fice, suka bar su yadda za su sake sosai.

Kamar jira Hinde take ta fara ma Nafi bala’i kamar zata cinye ta. “Nafi kina son ja muna asara ko? Wai wacce kalar ƙwaƙwalwa ce da ke? Mts! sai da na roƙo ki, ki natsu amma kina abubuwa kamar wacce ta ga namun dawa, wallahi idan ba ki saki jikinki ba kika yi duk abin da aka saka ki ba ke zaki sha wahalar banza, komai fa dan ke nake yi…” Sai kuma ta sassauta murya ta ci gaba da mata faɗan, “Ki yi taka tsan-tsan fa, Hajjaju da kike gani mutuniyar arziƙi ce me ƙwatowa mata ‘yancinsu, me share wa kowace macce kukanta da Marayu, idan kika fahimce ta zaki ji daɗi amma idan kika ce haka zaki ci gaba da abubuwa wahala zaki sha, Dan Allah Nafi ki cire tsoro da ƙauyanci. Yanzu mu ci abinci zan sake miki bayani anjima.” Ɗaga kai kwai Nafi ta yi jiki a sanyaye.

Hinde ce ta sake faɗin, “Babu Wanda zai cutar da ke a nan ko dukanki, kar ki saka shakku a ranki ba wata matsala sai alheri dan suma mutane ne kamar kowa da kika sani”. Sai lokacin hankalinta ya ɗan kwanta, ta ce “To zan kiyaye”. Zamowa ƙasa Hinde ta yi, ita ma Nafi haka suka buɗe Abincin da aka kawo Soyayyun kaji ne daƙwa-daƙwa sai Maiƙon suke yi, sai kuma Furar Maidabino da aka ajiye ƙasa da cups, da kuma tuwon Masara miyar ɗanyar kuɓewar da ta ji kifi da Ganda. Sai kuma Ruwa sha.

Cikin Nafi ne ya hargitsa ta manta wane yanayi take ciki, Yawunta ya tsinke burinta kawai ta kai wa bakinta. Fidda plates da Chokulan Hinde ta yi, ta sa hannu ita ma Nafin haka suka fara kai wa bakunansu, wani ɗanɗano ne na zallar madarar daɗi ya ziyarci Nafi har cikin kwanyarta, ta tauna kazar da ke da ɗan yaji ga ta yi luɓus ta kuma ji suyar mutunci, ita kanta bata san lokacin da ta gyara zama ba ta duma hannayenta duka biyun cikin abincin ta ci gaba da nausa ma cikinta, cikin ‘yan mintuna suka gama fatattakar naman suka dawo kan tuwon shima, Nafi ta ji daɗi zai zauta ta, ta ce “ruwa”. tana suɗe yatsunta hada hannuwanta.

Furar Hinde ta zuba musu a cup sannan ta buɗe mata Bottle water ta ajiye mata. Ta ɗauki Furar ta kai baki ta sha ta ji zumar daɗi da garɗi, ta fara santi tana faɗin, “Hinde dama haka ake a binni jandi“ilso (Dad’n duniya na nan)”. Suɗe yatsu ta yi ta bata amsa ita ma daɗin girkin na ɗibarta “Hum! ai baki ji komi ba, ni kaina duk daɗewata ko da yaushe aka min haɗin ruɗewa nake saboda komi na Birni ya yi zarra.”

Ta kasa bata amsa saboda yadda take tauna gandar tana jin kamar ba da bakinta take cin daɗin ba dan kar gandar ta gudu ya sa ta yi tsit. Ɗan abincin da suka rage ba shi da yawa sun yi hani’an kowa ya yi lodin da ya ƙetare iyaka sun zubar da abincin har saman carpet baja-baja sun kasa tashi sai gyatsa da lumshe idanu, sun mimmiƙe ƙafafuwa.

<< Zuciya 3Zuciya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×