Tare suka jero da Nafin da Hinde Suka samu kujeru suka zauna ‘Yan matan da ke zazzaune suna cikin abinci sai kallon banza suke musu, ba su wani maida hankali kan cin abincin ba sai latsa wayoyi da suke, da ƙyar Suka gaishe da Hinde ma kamar an musu dole, sai chanza fuska suke kamar sun ga kashi ga baƙin ciki da haushin Nafi da suke ji kamar su ci gaba da marin ta.
Ita ba ma ta su take yi ba, Abincin da Hinde ke zubawa ne ya ɗauke hankalinta ta ga soyayyen sankali da ƙwai sai doya da farfesun Ƙafar sa, ga Kuma Coffee da ke turiri. Teburin na da girma sosai shi ya sa suke a wale ba su takura ba, Hinde ta turo mata Abincin da Coffee ɗin gabanta, Da ma abin da take jira ke nan, ta duma hannuwanta cikin abinci ta fara nausawa cikinta kamar wacce ba ta taɓa cin abinci ba, duka hannuwan ta sanya haggu da dama tana yi tana tsotsewa tana lallashewa.
Wata dariyar rainin wayau ‘Yan’matan suka sanya sunan zaginta da mata habaici. Ba wai ba ta san da ita suke ba ko ba ta ji ba, ta yi shiru ne kawai dan tana jin hausa sosai kalmomi kaɗan ne ba ta ganewa amma hausarta ce marar daɗi ta fulani. Sai da ta tabbatar babu sauran wuri a cikinta sannan ta sarara tana nishi, dan ta cika cikin dan har ya ƙetare iyaka.
Zagin da suke mata ne tsakaninsu ne ya baƙanta mata, cikin ranta take faɗin, ‘shegu ba ku san wacee Nafi ba, za ku gane ne nan gaba kaɗan’ ta yi ƙwafa tana zura musu firgitattun idanuwanta masu susuta mutum. Har sai da Hinde tashe ta sa’annan suka bar dinning area ɗin.
Tabbas Kwanciyar Hankali hutu, Arziƙi, wadata, lafiya, sun fi komi daɗi, Allah ya tausaya wa Nafi a kwana ɗayan da ta yi, dauɗar Rugarsu da ƙazanta waɗanda suka dafar duk cikin ƙanƙanin lokaci ta jajor duk babu wannn wahalar. Lokacin da Salmerh me kwalliyar da ta gyara wa Nafi fuska ce ke ta yaba irin tsananin kyawun da ta yi, Ita kanta Nafi da taimakon Hinde ta gane kanta ashe ita ce sai wani mugun daɗi take ji ta tuna da Baffanta duk kuma sai ta ji ba daɗi, Salmerh ta taimaka mata ta sanya wata doguwa baƙa me kyau da inners ta sanya aka naɗe mata gashinta a yi wani irin sirrin kyau kamar ka gudu da ita don Kyau ta yi gwanin ban sha’awa. Tana gamawa ta bar ɗakin Hinde ta ci gaba da mata bayanin gidan da yanda al’amura ke kasacewa.
‘Yan’matan gidan duk sun yi mugun kyau sun fito a matsayinsu na wayayyu masu ji da class duk sun zazzauna a Parlour suna jiran fitowar Hajjaju da Hajiya Baturiya da ta zo.
Duk da Nafi ba wani shafe-shafe aka yi mata ba amma ta zama kamar tauraruwa ta yi mugun kyau, ba abin da za su nuna mata sai kwalliyar da aka chaɓa musu ta wayayyu masu ji da class duk sun zazzauna a Parlour suna jiran fitowar Hajjaju da Hajiya Baturiya da ta zo.
Duk an zazzauna ana jiran fitowar su har da maza su ma kowa ya yi ado ya yi kyau gwanin burgewa, su ma su Nafin zama suka yi suna jiran fitowar su.
Dr na zaune a Parlournsa yana tattara wasu bayanai duk da Air conditioner da ke Parlourn sai zufa yake yi, Ya nutsu sosai yana amfani da Laptop ɗinshi da ka ganshi ka san abin da yake yi yana da muhimmanci sosai.
Ƙwan-ƙwasa ƙofa aka yi, ciki-ciki ya ce ‘Yeah!’ Dogarin da ke buga ƙofar ne ya buɗe ya shigo dan dama suna kasa kunne su saurari maganarshi dan sun san baya magana me tsayi. Shigowa dogarin ya yi ya gaida shi ya fara magana a hankali da sauri dan ya san baya son hayaniya, “Ranka ya daɗe Hajiya ce ta ce a sanar maka tana nemanka yanzun nan a sashenta”.
Ɗaga kansa kawai ya yi alamun amsawa dogarin ya fice ya bar sa. Numfashi ya fesar da ƙyar yana nishi aikin da yake yi yana da matuƙar muhimmanci a rayuwarsa, ya ajiye ya miƙe ya fito. Masu tsaron ƙofar ne suka shiga gaishe shi sai dai ya yi murmushi kawai ya ɗaga hannu, Har ya shiga cikin ɓangaren Iyayen Sarki bayi da dogarai sai gaishe shi suke yi, Ya ƙarasa bakin ƙofar Parlournta kai-tsaye aka buɗe masa ya shiga ba neman iso dan Hajiyar ta gaya musu ba ya buƙatar neman iso a bar sa ko yaushe yake son shigowa.
Ya yi sallama ciki-ciki kamar yadda ya saba, kishingiɗe ya same ta a kilisarta ana tausa mata jikinta, Ya tsaya ya kasa ƙarasowa saboda Aman da ya yunƙuro masa, ya fara kiran sunayen Allah da ƙyar ya iso gabanta ya zuƙunna yana murmushin ƙarfin hali.
Ɓata fuskarta ta yi ta sallami masu mata hidima ta harare sa cike da damuwa dattijuwar ta ajiye Alqur’anin da take karantawa ta yafito shi da hannu. Ya ƙarasa ya zauna dab da ita yana lumshe idanuwansa, “Likita ai na yi fushi da kai, yaushe rabon da ka zo ko gaishe ni ka yi duk ka bar ni cikin damuwa.” Kama hannuwanta ya yi, yana ƙoƙarin magana da ƙyar dan shi kaɗai ya san irin yadda yake jin jikinsa ga lokaci ɗaga jikin ya yi mugun zafi rau.
Zabura ta yi saboda tsanani zafin jikinsa da ta ji, ta ce “me ke damunka ba ka da lafiya ne, jikinka ya yi zafi sosai?” Buɗe baki ya yi zai yi magana wani irin amai me haɗe da raɗaɗi cikin maƙoshinsa ya kufce masa ya kwararo shi kamar ruwa Jikinsa da na Hajiya, sai wani irin wahalallen kakari yake yana fitar da dunƙulallen baƙin jini, daga farko ba ta tsorata sosai ba da ta ga wani tsanwan abu da ya amayo me ruwa sai da ta ga dunƙullalen baƙin jinin ne sannan zuciyarta ta ji wani jiri na neman rufa mata idanuwa, ya ci gaba da aman jini ba ƙaƙƙautawa idanuwansa sun yi ja sosai lokaci ɗaya da ka gansa za ka tabbatar yana tsananin wahaltuwar sai jufa ke ziraro masa duk da Air conditioner da ke kunne.
Gabaɗaya Fulani ta rikice ta ruɗe sai kiran sunansa da take yi kawai, “Ahmaad! Ahmaad!!” Ganin yana neman ficewa daga hayyacinsa gabaɗaya me ya sa ta dawo cikin ‘yar nutsuwa ta shiga ƙwala kiran Jakadiya, Da gudu ta shigo saboda ta girgiza a kan yadda ta buɗe murya sosai, turus ta yi ta tsaya saboda mugun ganin da ta yi na Yarima dafe da Zuciyarsa yana fitar da numfarfasjhi ga kuma aman da ya yi da jinin da ya ɓata ɓasa kaya.
“Hajiya Amm lafiya Yarima??” duk a ruɗe ita ma Jakadiya ke tambayar Hajiya jikinta na kyarma “Jakadiya ki kira su galadima da Tareeq ki ce su so da mota yarima babu lafiya yanzu.” Da gudu Jakadiya ta bar ɓangaren Jikinta na ɓari ta ƙaraso fada kowa ta wuce sai ya kalle ta saboda gudun da aka ga tana yi. Ana yi mata iso ta shigo fadar duk ta rikice ta manta Sarki da sauran ‘yan masarauta na nan ba ko gaisuwa ta fara bayani ana haki. Duk shiru suka yi aka ƙyale ta saboda sun san babu lafiya shi ya sa za ta shigo haka.
Suna gama sauraron taƙamaimai abin da ya kawo ta suka ruɗe da sallalami, Sarki ya miƙe a ruɗe ya ma fi kowa shiga ruɗani, ya yi magana dogarai da su galadima suka fice zuwa sashen Hajiyar.
Al’amarin ya sake rikitar da su lokacin da suka ga yanayin da yake ciki da yawansu zuciyoyinsu suka karye, ita ma Hajiyar tsabar irin yanayin da ta shigo ko motsi ƙwaƙƙwara ba ta yi ba, su galadima suka kinkime shi dogarai da na baza manyan rigunansu suna kare su aka fito da shi aka saka shi mota, lokacin idanuwanshi sun lumshe, Cikin gaggawa aka kira Abdul aka faɗa masa halin da ake ciki, sannan aka tada motoci kusan bakwai aka nufi Asibitinsa.
Faɗa ko misalta tsananin tashin hankalin da makusantan Yarima da waɗanda suka san shi suka shiga ɓata lokaci ne. Masarauta ta ɗauka sai addu’a ake masa, da yawa sun shiga damuwa sosai, yayin da wasu ke cikin farin ciki sosai amma ba su bayyana ba.
Tun da aka isa asibiti da shi ƙwararrun likitoci suka karɓe sa dan dama sun shirya kawai jiran isowarsu suke yi sun duƙufa sosai suna son su daidaita bugun zuciyarsa amma gabaɗaya al’amarin kamar almara ya gagara hankalin likitocin ya tashi sosai ba su taɓa ganin rikitaccen al’amari irin wannan ba numfashinsa ma a sassarƙe yake fita shi ma da taimakon na’urori. Ga zafin jikinsa da ya zarce iyaka suna ta bakin ƙoƙarinsu amma abun ya ci tura.
Wata irin jijjiga gadon da yake kwance ya fara kamar zai faɗo, Na’urorin da ke amfani a ɗakin waɗanda aka Sanya suka haɗu da yadda bugun zuciyarsa yake da kuma waɗanda umfasinsa yake suka fara ƙara sosai, tun likitocin na mamakin abun har ya fara ba su tsoro, sun kwashe tsawon awa biyu amma babu ci gaba.
Motar Amminsa na shigowa Doctor Mu’az ya fito daga Emergency-room ɗin da aka shiga da Dr. Ko nutsattsen Parking Ammi ba ta yi ba suka fito ita da Imaan suka shigo cikin asibitin suna tafiya sauri-sauri gudu-gudu fuskar Imaan chaɓe-chaɓe da hawaye, suka ƙaraso bakin Emergency Room ɗin inda Mutanen masarauta ke zazzaune jigum-jigum, Daidai lokacin kuma Doctor ya gama wanke hannayensa ya cire Nose-mask ɗinsa yana goge zufa ya Ƙaraso inda suke, tun kafin ya daidaita tsayuwa suka yi saurin haɗa baki wajen faɗin “Doctor miye matsalarsa an dace??” Huci Dr Ya sauke ya fara musu bayani, “gaskiya akwai matsala! har yanzu ba mu gane taƙa-mai-man abin da ke damunsa ba, amma Zuciyarsa ba lafiya ba, Al’amarin ya ɗaga mana hankali ba mu taɓa cin karo da irin wannan matsalar ba abun tamkar almara, gaskiya yana buƙatar addu’arku, yanzu muna son kiran babban likita ne ya zo ko zai iya wani abu a kai.”
Wani irin ƙunci ne ya ziyarci Amminsa ta share hawaye fakaice tana jera masa addu’o’i cikin ranta.
“Subhanallahi, innalillhi wa inna ilaihi raji‘un”. Kawai suke maimaitawa tuni Imaan ta sake fashewa da kuka sai haƙuri ake ba ta. Dr ya yi saurin barin wurin shi ma ƙwalla na cika idanuwansa.
Kiran gaggawa aka yi Dr Hassan Usman Tafida akan matsalar Yarima, bai ɓata lokaci ba ya shigo cikin asibitin, kai-tsaye ya shirya ya shiga E-room ɗin, abu kamar wasa sun kwashe 1hour suna abu ɗaya amma babu ci gaba, Dr Hassan ɗin ya girgiza sosai. Wani likita ne da Abdul suka fito su biyu kowane fuskarsa na fallasa tsananin damuwar da yake ciki, Dr Irfan ne ya fara magana cikin harshen turanci “Abdul ya kamata zuwa yanzu Family ɗin Dr su san me ke damunsa tun kafin matsalarsata ta kai matakin rashin magani ka sani ba za mu iya aikata komai a kai ba kuma lokaci yana ƙurewa kwanakin da suka rage mana ba su zarce huɗu ba, ga shi Akarsh ya tafi.”
Shiru Abdul ɗin ya ɗan yi na ‘Yan mintuna sannan ya ce “maganarka gaskiya ce, sai dai ka san Dr ba ya son kowa ya san maganar, amma za mu iya faɗawa mom ɗinsa kaɗai dan ta san halin da ake ciki” Dr Irfan ya amsa da “Gaskiya ya kamata”.
Daga nan suka koma office cikin sauri ya ɗauki waya ya dannawa Akarsh kira. Kusan 5 miscalls bai ɗaga ba, sai a na shida sannan ya ɗaga cikin muryar barci . “Dr please ka tashi mu yi magana Ahmad ba lafiya” yana jin furucin Abdul ɗin da ya yi masa magana da harshen Turanci ya wartsake yana tambayar me ya sami Dr Abdul ya yi masa bayani, nan take ya ce zai masa typing ɗin Vaccine ɗin za a masa.
Yana turowa ba su ɓata lokaci ba suka fara kiran pharmacies suna tambaya, kusan huɗu ba su samu ba, sai wani Pharmacy suka ce za a iya samu gobe amma allurar tana da side effect sosai da kuma tsada sosai, amma haka ya tura kuɗin da zummar gobe a kawo musu. Yana shirin yi wa Irfan bayani Ammin Ahmad ta faɗo Office ɗin ko sallama ba ta yi ba ta ƙaraso gaban Abdul tana magana muryarta na kyarma.
“Abdul na roƙe ka dan Allah ka faɗa min me ke damunsa yana lafiya zuciyata babu daɗi.” Ta ƙarashe maganar tana haɗe hannayenta Alamun Roƙo, shi ma Abdul hawaye kawai yake jikinsa ya yi mugun sanyi komai ya fita a ransa ya gaji da komai ma yake ji. Idanuwan Ammi sun ja sosai har jini ya kwanta, Irfan na ganin haka ya fice, da ka gan ta ka san tana cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali amma sam babu alamun hawaye ko ƙwalla cikin idanuwanta, Janyo ta Abdul ya yi ya zaunar da ita bisa kujera ya durƙusa ƙasa yana kallon ta ya kasa cewa komai. Sai hawaye ke fita daga idanunsa. Shi kanshi ya san a irin yanayin da Ammi ke ciki ba ta buƙatar sake jin abin da zai tarwatsa mata zuciya tana buƙatar samun nutsuwa, Amma ba shi da yadda zai yi wajibi ne ya faɗa mata komai. Katse shi ta yi tana share masa hawaye tana magana “Kuka kuma kai Abdul’aziz?” Ta ci gaba da girgiza tana share masa hawaye, cikin wata irin sassanyar murya ya fara mata magana. “Ahaad yana lafiya Ammi ki daina damuwa fa”. “Da gaske? Yaushe ka fara faɗin maganar da ba gaskiya ba? Dan Allah ka faɗa mini matsalar ko zan samu sassauci a zuciyata. Dan jikina na bata tun ba yau ba akwai abinda suke ɓoye mata na damunsa. Shi kanshi ya san ba shi da mafita ya fara magana gabaɗaya jikinsa ya saki. “Ammi kin san cewa tsawon shekaru uku Ahmaad yana da matsala kuma cutar ciwon zuciya wanda ya munana ya kai mataki na ƙarshe??”
A hankali kamar an zare mata lakkar jikinta gabaɗaya ta ɗago tana kallon sa ko ƙyafta idanu ba ta yi, Zlxuciyarta sai wani irin bugu take yi da ƙarfi. Ya ci gaba da magana “Ammi ciwonsa ya kai mataki na ƙarshe, yana buƙatar addu’arki, Akarsh ya faɗa mana Sati ɗaya kawai ya rage masa ya amince ayi masa surgery ko kuma ya rasa rayuwarsa bakiɗaya amma ya ƙi amincewa, ciwon ya chanza sa ya hana sa sakewar rayuwa baya jin daɗin komai…”
Sai kwai ya fashe da kuka idanuwansa sun yi ja sosai ya kasa iya fasalta irin mummunan yanayin da Amininsa yake ciki tsayin shekaru fiye da biyu yana rayuwar ƙunci. Ɗagowar da zai yi kawai ya ga Idanuwanta na kakkafewa ta fizge ta faɗi ƙasa. Wani irin sabon tashin hankali ya sake shiga, kanshi ya kulle ya rasa inda zai tsoma ransa ya samu salama, yayi jigum ya zuba mata idanuwa ya san ta suma ne, ya buɗe ruwan da ke saman table ɗin gabansa ya shafa mata amma ba ta farfaɗo ba, ya sake shafa mata bata farfaɗo ba, hankalinsa ya sake ɗunguzuma ya ruɗe ya rasa me zai yi, ya jawo rubbern ruwa me sanyi ya yayyafa mata amma ba ta yi ko motsi ba.
Kansa ya kulle ya rasa ya zai yi kwata-kwata ba ya cikin nutsuwarsa, sai kawai ya fara addu’o’i yana roƙon Allah ya kawo musu mafita ya ba Ahmad lafiya. Cikin ikon Allah wutarsa ta fara dawowa Ya yi saurin ɗaukar waya ya dannawa wata nurse kira, Ya ba su umurni su zo su biyu office ɗinsa. Nurses biyu ya sanya suka ɗauki Ammi suka ɗaura ta kan gadon da ke cikin office ɗinsa, Ya fara ba ta taimakon da ya dace.