Cikin wani irin salo take saukowa daga kan bene, ƙarar sarƙar ƙafarta da ƙarar takalmanta masu tsini sun cika Parlourn duk sun baza idanuwa su ga da wane sabon salo ta shigo, Sai da ta sauko ƙasa sannan ta cire gilashinta ta fara ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya.
Kyakkyawa ce sosai, ita ba fara ba ita ba baƙa ba, amma kalar fatarta da ka gani ka san hutu ya zauna mata, tana da ‘yar ƙiba kaɗan, ɗinkin Lace ne doguwar riga a jikinta baƙi da golden sai stones da suka ƙawata ɗinkin suna ta walainiya, ta yi kyau sosai, tun da ta ɗaura idanuwanta kan Nafi ta kasa janye su.
Hajiya Baturiya irin fitattun ‘yan duniyan matan nan ne da ba za a nuna musu wayewa ba, suna ji da dukiya suna tsula tsiya yadda suka ga dama. ‘Yan matan sun ruɗe da ganin kalar sarƙar da ke wuyanta da awarwaro da ‘yan kunnaye sai zobuna duka na zinare mai daraja, suka shiga rawar jikin gaishe ta, suna ta juyi suna karai-raya kowace fatanta ta yi mata.
Sai da Hinde ta zunguri Nafi sannan ta yi saurin ƙarasawa gabanta kamar yadda ta ga ‘yanmatan na yi ta gaishe ta, Hajjaju da ke gefe ta tsuke cikin riga da wando sai Kimono Light blue gabanta a buɗe hagu da dama an ƙawata da baza me kyau.
Ko gaisuwar ba ta amsa ba ta miƙa mata hannu alamun ta zo, sai tai tsaye sadamai-mai tana kallon ta cike da rashin fahimtar abinda take nufi. Sai kuma ta kalli Hinde ta yi mata alama da idanu alamun ta ƙarasa gare ta, Amma tsabar rashin wayewa ta gaza fahimtar me take nufi. Baƙin ciki kamar ya kashe ‘yan’matan kamar kuma su tsire Nafi dan ganin ita Hajiya Baturiya ta zaɓa.
Cikin muryar gayu Hajiya baturiya ta ce “zo mana! ke ce Yarinyar da Hinde ta kawo miye sunanki?” Cikin jin tsoro Nafi ta ƙarasa kusa da ita tana faɗin “Nafi”. Janyo ta da ta ji ta yi ta rugeme ta ta matse ta kamar wani zai ƙwace ta hakan ya sa jikin Nafi ya mutu ta yi shiru tana rarraba idanuwa Hajjaju ce ta yi mata raɗa cikin kunne sai ta yi saurin sakin Nafin tana musu magana, “Za ku iya tafiya ku duka ku sake shiri zuwa dare.”
Duk suka fara tafiya cike da jin haushin Nafi da tsanarta. Hinde ce ta tsaya tana ma Nafi magana cikin kunne “Nafi dan Allah kar ki yi abinda zai yi silar komawarki ruga wallahi idan kika musu kuskure za ki gane kuskurenki kar ki musa ko me aka saki ki yi, maza ki bi ta”.
Ta yi saurin jinjina kai, ita kuma Hinden ta bar Parlourn Hajjaju ta jawo ta suka nufi Up-stairs da ita. Wani ƙaramin ɗaki suka shiga da ita, Ba tsaitsayawa Hajiya baturiya ta matso ta jikinta tana wani murmushi tana taɓa jikinta, ita dai Nafi duk abin da take mata ta yi shiru ta kasa magana ba za ta ce tana jin daɗi ba kuma ba za ta ce ba ta ji ba. Jin hannu da ta yi cikin Rigarta ya sanya ta zabura ta fara tuna maganganun da mahaifiyarta ke yawan yi mata da gargaɗi. Ta yi saurin ƙwace jikinta, Hajjaju da ke Rage kayan jikinta ta Kalle ta, tana faɗin “Lafiyarki?” Ta ɗaga mata kai jikinta na wata irin karkarwa lokaci ɗaya, ga zufar da ta fara jiƙa ta, sai ji take yi jikinta na chanzawa. “Hajjaju Ba ki mata bayani ba ne ta ya na fara ɗaukar chaji za ta kwafsa min”.
Shiru Hajjaju ta yi, kuma ta fara mata magana cikin harshen turanci “Baturiya ni fa ban shirya yin komai da yarinyar nan ba, kin ga duka-duka yaushe ta zo, akwai rashin wayau sosai tattare da ita sannan ba ta san komai ba, ina so na fara gyara ta sosai na fi son na ɗan fara gyara tukun, amma za ki iya nuna mata abin da za ta miki” Ta jinjina kai kawai, Slsai ta koma kan gado ta zauna tana sauke numfashi, Ta janyo Nafi da ta yi tsaye tana mata raɗa a kunne, Duk sai Nafin ta ji tsigar jikinta ta tashi, ta daure ta yi abin da ta ce yadda ta ga tana nuna mata.
Hannunta ta sanya yana kyarma kamar yadda ta ce ta fara taɓa zip ɗin irin yadda ta ce ta yi, ta zuge ƙasa, sannan ta fara ƙoƙarin cire mata rigar Ta kwanta ta juyo tana kallon Nafin ta miƙo mata hannu ta matsa dab ita. A hankali ta sanya hannu ta fara warware mata mayafin jikinta, Sannan ta kai hannu kan doguwar rigarta ta fara ƙoƙarin taɓawa, tana kai hannunta kan ƙirjinta ta ji wani mahaukacin shock har cikin ƙwa-ƙwalwarta, ta yi ƙara tana ja da baya, hakan kuma ya bawa rigarta damar saɓulewa ta ida yin ƙasa. Ɗago idanun da za ta yi suka haɗa ido da Nafin ta ga idanuwanta suna kamar wuta kamar tartsatsi, ta yi wata irin zabura dan gabaɗaya ƙwayar idonta ta chanza launi, Hajjaju da ta shiga toilet ta fito da ɗan Towel tana kallon su fuskarta da alamun mamaki, ta ce ‘lafiya B?.’ Ta yi saurin saukowa daga gadon tana girgiza kai “ki ce ta tafi..”. Hajjaju ta ce “Wai me ya faru ne?” ba ta saurare ta ba, ta yi saurin faɗawa Toilet, Hajjaju ta ce Nafi ta fice, ita dai ba ta lura da irin yadda launin ƙwayar idonta ta yi ba. Tana jin an ce ta tafi ta yi saurin ɗaukar mayafinta ta chukurkuɗa ta fice tana ta kyarma.
Washegari da wuri aka kawo Allurar da za a yi wa Dr. Babban likita ya yi masa. Mintuna Talatin da yi masa Allurar abubuwan suka fara sauƙi, numfashinsa da bugun zuciyarsa ya ɗan fara daidaita. Hakan ya sa hankalinsu ya ɗan kwanta, Ammi ta koma gida su kimtsa su dawo ita da Imaan daga masarauta ma an ɗan rage doctor ya ce nan da ko awa biyu zai iya tashi. Hajiya ce kawai ta ƙi tafiya tana masarautar ita dai. Abdul ya sa aka gyara wani room me kyau kusa da Office ɗinsa tsaf aka maido shi nan.
Ƙafafunsa ne suka fara motsi sai idanuwansa da ya fara ƙoƙarin buɗewa, daidai lokacin Abdul ya buɗe ƙofa ya shigo Ammi da Imaan suna bayanshi. Farin ciki ya kama su ganin ya buɗe idanuwansa ya kuma rufe, Imaan ta yi saurin ƙarasowa bakin gadon tana mishi magana “Yaya ka tashi ya jikinka?” Hararar ta Abdul ya yi ya ce “za ki fara ko Imaan wa ya ce miki ana wa marar lafiya ihu, idan kika yi wasa gida za ki koma” baya ta yo inda Ammi ke tsaye tana kallon sa tana murmushi, Ta marairaice fuska ta ce “Sorry Yaya ba zan sake ba fa” Ahmaad da ke jin su sama-sama ya buɗe idanuwansa da ƙyar, sai kuma ya yi saurin rufe su saboda dishi-dishin da ya gani, ya sake buɗe su kan Ammi.
A nutse ya fara ƙare wa ɗakin kallo, yana tuna abubuwan da suka faru sai yai saurin kallon hannun sa, ya kuma maida kallon sa gare su Yadda suka yi tsaye suka kafe sa da idanu, ya lumshe idanuwa yana jin zuciyarsa na masa nauyi da kuma wani ƙunci da yake ji da ɗaci a ransa, kwata-kwata bai san lokacin da hawaye suka zubo daga idanuwansa ba, Ya musu alama ta ido su ƙaraso, har rige-rigen tambayar sa ya jiki suke yi me ke masa ciwo, sai murmushi yake yi, Kafin da ƙyar ya ɗaga hannunsa ya dunguri kan Imaan a hankali. Cikin sauri Abdul ya fita,sai kuma ga shi ya dawo shi da Hajiya, ta shigo da sallama tana takowa riƙe da ‘yar sanda ta iso gaban gadon tana kallonsa fuskarta cike da fara’a Imaan ta tashi daga kujerarta ta ba ta gurin ta zauna. Cike da son ƙarfafa kansa ya fara ƙoƙarin jingina da gadon cikin ransa sai addu’a yake yi Ubangiji ya sanya Abdul be faɗa wa Ammi halin da yake ciki ba. Ya ƙawata fuskarsa da sassanyan murmushi ya ce, “Hajiya, Ammi good moirning” tare suka amsa masa sai Hajiya ta dubi Abdul tana faɗin, “Wai dan Allah me ke damun abokinka ne ko dai wani abu ya ci ne?. Gaskiya ya tada mini hankali ban sanya rai zai sake shaƙar iskar duniya ba, Aman jini fa ba wasa ba ne, Yayata da mu ke uwa ɗaya uba ɗaya da ita tun da ta yi aman jini aka kaita asibiti Allah ya amshe ta, Ni fa ban taɓa ganin wani ya yi Aman jini irin wannan ba ya rayu, jini ba kaɗan ba kuma kai, Allah me iko, Ina roƙon Allah ya kare ka Ahmaad Allah ya tsare ka.”
Dukansu shiru suka yi Har Abdul ɗin dan ba shi da abin faɗa, Jikin Ammi ya ƙara yin sanyi, ita kanta Hajiya da ka kalle ta za ka fahimci tana cikin damuwa. Cikin rashin sanin Abin faɗa Abdul ya buɗi baki zai yi magana, Amma Dr A ya yi saurin katse sa yana faɗin, “Kai Hajiya fa. kin san ana samun ɗan kuskure wani taste na je na yi shi ya sa, Amma mutane da dama sun yi aman sun rayu kin san ni yanzu garau nake jina zan iya faɗa da kowa.”
Duk sai suka yi murmushi lokaci ɗaya, Abdul ya harare sa “Kasan dai ba za ka fara tunanin had’a ƙarfinka da nawa ba ko?” “Kana tantama kenan, matso ka gani” Ya yi dariya ya ce “zan kyale ka ne kawai saboda Ammi”. Yana masa magana yana cire ƙarin ruwan da aka saka masa. Umurni Hajiya ta ba Abdul ya sanya hadimanta su shigo da Abinci, ya amsa yana ficewa daga Room ɗin. Su uku suka shigo sanye da Unifoarm ɗin Masarautar Suka ajiye Wani ƙaton tray da Flask da cup da sai breakfast suka fice. Abdul ne ya haɗa masa Tea me kauri marar zafi sosai miƙo masa, bai wani sha da yawa ba ya ce ya ƙoshi sai da Su Ammi suka matsa masa sannan ya ɗan ƙara, Abdul ya ba shi magani.
Alhamdulillahi ya samu ɗan kuzari da ƙarfin jiki, tun da har ya tashi ya yi Sallah. Daga Masarauta aka shiga zo masa ya jiki, sai wajen seven na dare sannan ya samu kansa, ya matsa wa Abdul a sallame sa, Abdul ɗin ya ce “An ƙi ɗin” ya yi murmushin mugunta ya ɗaga kafaɗu, ya ce “idan ka gama komai zan koma masarauta”.
Yana gama faɗar haka ya miƙe ya sanya takalman da aka ajiye masa, ya buɗe ƙofar ya kashe ma Abdul ido ya fice.