Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Zuma Da Madaci by Bilkisu H. Muhammad

Yabo Da Godiya

Sun tabbata ga Allah (S.W.T) Mai kowa, Mai komai wanda Ya ke sauwake min alamurana ba tare da wani tsumi ko dabarata ba. Ina gaisuwa ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) Dan Aminatu da Abdullahi.

Godiya

Gare ku masoyana, makaranta littattafaina dare da rana ina yaba kokarinku, Allah ya bar kaunar da ke tsakaninmu abadan daiman.

*****

A dokance ya shigo gidan, cikin sanda ya ke tafiya zuciyarshi na harbawa da sauri da sauri. Hangota ya yi kwance a kan tabarma. Ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya tare da murmushi, ya karasa gare ta ya zauna cikin tankwashe kafafu. Ya zuba mata manyan idanunshi, sai dai rumfar da gashin kanta ya yi wa fuskar ya hana shi ganin kyakkyawar fuskar da tsawon kwana arbain bai yi tozali da ita ba. Yana murmushi ya kai hannu don yaye gashin, karaf ta riko hannun gabadaya ya yi mutuwar zaune, zuciyarshi ta dinga bugawa har lokacin ba ta saki hannun nashi ba.

Ya runtse idanunshi yana kiran, Hasbunallah.

Shirun ya yi yawa, a hankali ya bude idanun nashi da alamar cikin magagin bacci komai ya faru. Ya sauke wata ajiyar zuciya cikin dabara ya zare hannunshi daga cikin nata.

Kin sauya mini tunani, zuciyata ta zamo duhu ta makance, numfashina na fita da zafin kunar sonki.

Abbas! Abbas!! Ina son Abbas!

Ya ji tana fada. Ras gabanshi ya yi wani mugun bugawa, ya ji kansa ya sara. Da sauri ya kai hannu ya dafe kan nashi idonshi daya ya shiga zubda ruwa, kanshi ya shiga juyawa.

Ta sake yin wani juyi gabadaya ta zube hannayenta a cinyarshi.

Nauyin baccinta kan ba ni tsoro ga yawan surutai.

Kalaman kaka ya tuno lokacin da tana yar shekaru goma da haihuwa ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga. Ya yi murmushi mai ciwo. Motsin kaka ya ji da sauri ya mike cikin rashin saa. Ya yi karo da tukunya.

Wa ke tare da ni? Ta fada a tsorace.

Yana matukar tausayin tsohuwar, sai dai a yanzu shi ne abin tausayi, don yana matukar tausaya wa kanshi rayuwar da zai yi nan gaba.

Ya yi tattaki zuwa gabanta kamar yadda ya saba, direwa ya yi a kan gwiwarsa. Hannu biyu ya saka ya riko duka hannayenta, hakan ya tabbatar mata da wanda ta ke tare. Ta fadada murmushinta.

Boyayyen masoyi. Ta ce.

Ya jinjina kai tamkar tana ganinshi.

Ina ka shiga kwana biyu, mai muka yi maka ka zartar da wannan hukuncin mai tsauri haka?

Ya mike har lokacin bai saki hannayen nata ba.

Kaka ba zan sake ba, ni kaina na wahala duk inda na ke kuna cikin raina. Yanzu ki ba ni labari, ya na sami Amatallah?

Ta yi murmushi, Tana nan cikin koshin lafiya.

Ya sake tambaya, Ya karatunta?

Kaka ta ce, Ta zafafa wani fannin, har ba ta barci daga ta tsoma kafa cikin ruwan sanyi sai ta sha ruwan tea wanda ta cika sahi da wannan abin mai kamshin tsiya, wai duk don kada ta yi barci.

Ya ji dadi har cikin ransa.

Kaka ina ji a jikina burin Amatalla zai cika muddin ina raye, za ta zamo cikakkiyar likita wadda alummar musulmi za su yi alfahari da ita.

Ta ya ya haka za ta faru muddin ba ka bayyana mata kanka ba? Dukkan ganinka zai rushe lokaci ya yi da za ka gaya min game da kai.

Ya sunne kai kawai.

Sunanka kawai nake bukata ka kada kai, suna ba asali ba, na aminta da aslainka, mune ya kamata kayi wa wannan binciken, sunanka kurum za ka gaya mini daga nan sai ka bar komai a hannuna.

Ya ce, Ba yanzu ba.

Alamarin ya daure mata kai.

Tsawon shekaru goma sha kana hidimta wa jikata ya dace a ce na san waye kai, ai makanta ba kurumta ba ne

Ya katse ta, Boyayyen masoyi shi ne sunana.

Kada ka ci gaba da boye kanka, ina jiye maka abin da zai iya faruwa watarana. To ka gaya mini me ye manufarka a kan jikata?

Kanwata ce.

Ta langwabar da kai, To

Kaka! Kaka!! Muryar Amal ta katse su.

Bat ya bace wa gurin tamkar walkiya, kaka dai ta kasa motsi tamkar wacce aka dasa. Shekaru goma sha abu daya ake. Ta sauke ajiyar zuciya, boyayyen masoyi ya tsaya mata a rai kam tamkar wani mayen karfe.

*** *** ***

Ta mike daga kan darduma gari ya fara haske, ta fito tsakar gidata yi tuntube da wani abu, da sauri ta kai kallonta gurin. Wata katuwar bakar leda ta gani shake da kaya. Ta durkushe a gurin zuciyarta ta tsananta harbawa, ta dinga bubbude kayan. Dogayen riguna ne masu azabar kyau har kala hudu da kayan kwalliya, sai awarwaraye da yari da sarka masu kyau, sai daukar ido suke. Ta cije lebe zuciyarta ta shiga kuna, ba ta san saadda ta yi fatali da kayan ba.

Ba zan sa ba, ba na so, na tsane su, mahaukaci, aljani, igiritu!

Cikin muryar kuka ta ke maganar tana kuma ci gaba da watsi da kayan.

Kaka ta nufo gurin cikin lalube, Ke Amal me ye haka?

Kaka shi ne shi ne, yana son kashe ni Kaka, na ce ki daina karba yana son yi mana yawo da hankali,yana son haukata ni, ba boyayyen masoyi ba, boyayyen makiyi ne. ki ce da shi in ya isa ya bayyana kanshi.

Kina ina? Rike mini hannu za mu yi magana.

Ta tsagaita kukanta ta riko ta kamar yadda ta bukata, ta lalubo hannun Amal tana matsawa.

A yanzu babu shi har yanzu akwai sauran lokaci da zarar ya yi mini umarni zan sanar da ke, ke kuma a ranar za ki fidda ni kunya, a ranar za ki nuna mishi halacci.

Ta yi turus, Halacci? Halacci fa ki ka ce, wane irin halacci ki ke so na nuna mishi?

Kaka ta sanyaya murya, Dubi irin yadda ya ke dawainiya da ke.

Baki bude ta ke kallon Kaka, Au da man rokonshi muka yi? Gaya mini kaka ko neman taimakonshi ki ka yi? Tun daga yau na daina amfani da komai nashi.

Ta mike tsaye tana dube-dube tana ji a jikinta kamar yana tare da su.

Na yi maka nisa, kullum kara min kinka ka ke yi da hannunka wallahi. Yanzu ba ka burge ni

Ke Amal! Ashe ba ki da hankali? Ashe ke mahaukaciya ce? Wannan wane irin butulci ne, ina ma ina da ido ki ga yadda zan shake ki in tumurmusa ki, wallahi albasa ba ta yi halin ruwa ba.kaka ta fada tana huci, tana ci gaba da bambamin fada, ta shige daki ta zauna a kan tsohuwar katifarsu.

Amal ta yi sak duk jiinta ya gama yin laasar, lokaci guda ta shiga da na sani lallai Kaka ba karamin kauna ta ke wa boyayyen masoyi ba.

Cikin rashin kwarin gwiwa ta mike ta shiga gurinta ta zauna a kusa da ita tana duban fuskarta wadda ke tamke. A hankali ta ce.

Na tuba, kada ki yi mini fushi zan shiga tashin hankali, ke ce komai tawa.

Ta kai hannu za ta riko hannunta, Kaka ta fizge hannun nata tare da juya mata baya. Ta sake wani marairaicewa kamar za ta yi kuka.

Ba ni da kowa ballantana na je na sanar mishi da halin da na ke ciki Kaka, ina son ki dake ni in har haka zai sanyaya miki rai.

Inda zan yi gunduwa-gunduwa da ke zuciyata ba za ta yi sanyi ba muddin ba za ki fahimce ni a kan boyayyen masoyi ba. A duniyar nan ko ba na raye ba ki da wadanda suka wuce Hajiya Fati da kuma boyayyen masoyi. Wannan kurum na ke son ki fahimta.

Amal ta dinga kada kai.

Na ji na amince, na kuma tuba.

Ta kwantar da kai a jikin Kaka, yayin da Kaka ta dora hannu a kanta tana shafar lallausar gashinta, cikin furta.

Ban taba ganin mutumin kirki irinsa ba, babu abin da bai yi miki ba a rayuwa. Ya yi miki wanki, wanka, tsarkin kashi ban taba ganin inda namiji ke wa mace kitso ba sai a kan boyayyen masoyi, ya kan kama ki ya wanke miki gashi, ya zauna ya kitse shi tsaf.

Kaka a mafarkinki hakan ke faruwa?

Uhm, Amal har yanzu akwai kuruciya a tattare da ke.

Kaka duk lokacin da ki ke ba ni labarin boyayyen masoyi na kan dinga daukar mafarki kurum ki ke yi, in ba haka ba ya ya za a yi duk wadannan abubuwan su dinga faruwa amma ko sau daya idanuna ba su taba nuna min ba? Na fi tsammani da gamo ki ka yi

Kaka ta katsse ta, Ranar da za ki gano shi na nan, ranar zai zo.

Kaka yaushe ne wannan ranar zai zo?

Sai ba na duniya.

Ta kai mata duka.

Mutuniyar wofi, na ce kin ci gidanku, ni daga ni kada ki karasa ni.

Ta gantsare saboda shigar dukan da ta ji.

Wash! Kaka za ki balla ni.

*** *** ***

Amalil Islam shi ne sunanta na ainahi, irin matan nan ne wadanda daidaiku ake samu a duka Africa. Kyakkyawa ce ta gaske, kalarta wani iri in ta shiga cikin bakake ka kan ganta fara, in kuma cikin farare ta shiga ta kan dan dusashe, amma kalarta yayin da ta ke cikin fararen ta kan fi su daukan hankali.

Kai kanka in an ba ka zabi da gudu za ka zabi kalarta ka bar fararen. Kalarta wata iriyar kala ce da Ubangiji ya yi mata baiwarSa. Tana da matukar kunya da kamun kai. Kallo daya za ka yi mata ka fahinci ba mace ce mai son kwaramniya ba, sanyi-sanyi haka ta ke, jamaar unguwa na matukar mutuntata duk kuwa da kankantar shekarunta, musamman ta yadda ta ke tafiyar da alamuran rayuwarta.

Duk kwakkwafinka ba za ka ce ga yadda surar jikinta ta ke ba, sai dai ka ce kyakkyawa ce, sakamakon koyaushe jikinta na sanye da wani zumbulelen hijabi wanda ke barazanar share kasa.

*** *** ***

Amal! Amal!!.

Ya kutsa sitroom cikin kiran sunanta. Babu kowa sai Hajiya Fati wacce ke kishingide a doguwar kujera da sira a hannu.

Sallamar ke nan ko? Ta ce da shi.

Oh Mom, sorry. Amal na ke nema.

Ta dube shi a yatsine, Wai ba za ka dinga barin yarinyar nan tana hutawa ba?

Mom ba ta son abin da zai taba Amal. Ya yi murmushi, Wani taimako na ke so ta yi min.

Ta tabe baki, Kullum ba ka da aiki sai bautar mini da yarinya, ina son ka sani Amal ba yar aikinka ba ce.

Cikin muryar lallashi mai hade da barkwanci ya ce, Na sani AmalilIslam yar Mom ce, lelen Mom, kuma rainonta, horonta shi ya sa na ke dangantata da duk abin da zan aiwatar ko na ke bukata, kin ga ai na girma Mommyna ta yaye ni, ba zan iya zuwa kai tsaye na ce, Mom ta yi mini girki wa abokaina ba, dole sai dai na je ga magajiyarta, wannan magajiyar ita ce Amal Amalil Islam, ki saka a ranki a wannan matsayin na ajiye diyarki ba matsayin baiwa kamar yadda ki ke zargi ba.

Ta dinga murmushi cikin nuna shi da yatsa.

Ka cika sarkin tsari, sai ka je gida Kaka ba ta dade da fita ba, sai dai ina tsammanin akwai yan kitso cike a gidan.

Ya cije lebe, Oh shit! Wannan shi ne matsalarta daga kitso sai a ce ga ta can an zo ta yi kaunshi, mts!

Haka ya fita yana mita, ta bi shi kurum da ido karfin hali

*** *** ***

Ina ga ka kyale ta tagama a nutse, har yanzu akwai sauran lokaci.

No Anwar, ba zai yiwu ba, dole ta sallami kowa aikina ya fi wannan muhimmanci.

Anwar ya tabe baki tare da daga kafada.

Well, go ahead.

Yana tsaye a kofar gida Abba ya kutsa kai gidan, daga soro ya tsaya yana jin hayaniyar mata ya ja tsaki.

Wannan shi ne matsalar gidan koyaushe gidan bai rabo da dandazon mata tamkar gidan biki, ba su ma ko ganin yanayin gidan. Ya dinga bin koina na gidan da kallo, koina a babbabure daga kasa har jikin garu, rashin daben kasa ya taimaka gurin zaunewar ramuka a kasan gidan. Rashin tsawon katangar gidan ya taimaka gurin kara wa gidan muni. Kai da ka ke waje za ka iya hango na cikin gidan, sai dai kallo daya za kai wa gidan ka tabbatar akwai wadatar tsafta ga wani kamshi da ya zauna a gidan.

Shinshinar kamshin turaren jikinshi ya tabbatar mata da cewar yana daf da inda suke. A hankali ta maida idanunta ga soron gidan.idanunsu suka gauraya, ras ta ji gabanta ya yanke, da sauri ta basar tamkar ba ta ganshi ba. Ya yi murmushi abin a jininta ya ke, yar talaka amma halayyarta tamkar yar sarauta. Tana burge shi, yana shaawar yanayinta, ya sani in zai kwana a gurin ba za ta taso ba muddin ba magana ya yi ba.

Kokarin kara kwata satar kallonsa za ta yi suka sake hada ido, da sauri ya kira ta da hannu, sai da ta karasa kitson da ta kama ta taso a nutse.

Yana kallonta cikin takaici ya jinjina kai, yarinyar na son bai wa kanta wahala, ji don Allah cikin yan uwanta matan ma ba ta aje hijabi ba. Irin yadda ya kafe ta da manyan idanunsa ya sanya ta maida kai kasa, kunyarta ya yi yawa, ya fada a ransa.

Ina son ki sallami jamaarki ki kuma lissafa mini abin da ki ka rasa zan biya ki. Ina son sayen wannan ranar pls.

Ya karasa cikin muryar lallashi. Ta dago kai cikin dubansa har yanzu idanunshi na kanta.

Ta sake dauke kai, duk da ba ta ce komai ba, fuskarta ta nuna ba ta ji dadin furucinsa ba.

O.K, kina so ne in je na yi musu magana da kaina?

Da sauri ta kada kai.

Ki yi mini magana mai ya sa ki ke son sake min ki ko ma tamkar ba Amalil islam dinmu ba? Ko kin fada soyayya ne?

A razane ta dago mamaki da tsoro suka lullube ta. Shi ke nan ta mutu ta shiga ukunta, duk jikinta ya gama yin laasar.

Gaya min waye shi? Ya tambaya cikin daga gira.

Ta yi saurin basar da zancen, Ba na jin dadi ne, amma zan yi duk abin da ka umarce ni.

O.K, ina son ki kure dukkan basirarki don fitar da ni kunyar abokaina.

Ya saka hannu cikin aljihu kudi ya fitar shi kanshi bai san adadinsu ba, Ga wanan ki sayi duk abin da za I bukata.

Ya juya ya soma taiya, a gaf da kofar da zai fidda shi waje ya tsaya ya kuma juyo,Da karfe hudu nake tsammanin zuwansu.

Tabbas soyayya na sanya uka, farin ciki ta sa a rasa. Kwance ta ke a kan katifa tana faman juyi dulk duniyar ta yi mata zafi, mai ya sa ta ke jin Abbas a ranta tamkar ta mace? Mai ya sa zuciyarta ke son zautar mata da kwakwalwa tare da son tursasata a akan abin da ta sani ya fi karfinta har abada, har abada Abbas ya yi mata nisa, dangi, asali, dukiya, ilimi mutum ne shi mai tsada. Namiji ne shi wanda duk wata isasshiyar mace ke mafarkin samu. Yana da aji da girman kai, ga naira.

Abbas ya fi karfina, zuciya ki daina dora mini abin da ko a mafarki ba zai kasance ba.

Amal. Muryar Kka ta atse ta. Kokarin saita muryarta ta ke ta sani duk da Kaka ba ta gani ta kan fahinci duk wani yanayi da ta ke ciki, walau na farin ciki ko sabanin haka.

Wai ba yanzu ki ka gama ce mini za ki yi wa bakin yayanku girki ba?

Kaka na gaji ne. ta fada a sanyaye, ta fahinci Abbas bai dauke a komai ba sai don ta dinga fidda shi kunya yayin da ya yi baki, daga lokacin ba ta da sauran muhimmanci a gare shi.

Ki tashi na ce ko ba naa son shiririta.

Ta mike cikin sharar kwalla.

A kicin ta ke faman kai komo ta sauke ta dora, gabadaya aikin ya kwabe mata, sai yanzu ta fahinci ta debo da zafi.

Karfe uku ya yi fakin a harabar gidan, kai tsaye ya wuce sashinsa inda gabadaya kamshin girkin Amal ya gama cika gidan. Ya yi murmushi tare da ambatar.

Amalil Islam.

Bathroom ya shiga ya yi wanka ya shirya kansa cikin wasu fitinannun kaya english wear riga da wando, wandon blue ne, rigar yellow. Ya fito tamkar wani basarake, ya feshe jiki da turare, ya dauko agogonsa yana kokarin dauraw ya nufi sashin kicin. Ya dade tsaye a kanta yana kallon yadda ta ke aiwatar da komai cikin nutsu yanayin komai cikin rashin kuzari in ka dubi uban aikin da ta ke ba za ka zaci ita ta yi su ba.

Kamshinsa tuni ya isar mata ji ta yi gabadaya kafafunta sun yi mata nauyi. Ya zaga gabanta.

Sannu da hidima.

Kanta a kasa ua shiga binta da kallo, tun daga sama har kasa. Yana mamakin katoton hijabinta wanda ke barazanar share kasa. Ya kunshe dariya a ciki.

Wai ke wannan abin ba ya damunki ne?

Da sauri ta dago kai tana son sanin wani abu ne ya ke nufin zai dame ta. Idaunsu suka gauraya, zuciyarta ta ji tana bugawa da karfi, gabadaya kwarjininshi ya rikitata.

Ta yi saurin mai da kai. Ya saki murmushi.

Ina nufin wannan kayan zafin, hijab din ya yi girma da yawa, in kina so zan siya miki na zamani masu ado a jiki.

Ba ta kula shi ba, kokarin sauke tukunya ta ke a kan gas.

Ki yi mini magana. Ya fada cikin kashe murya. Ya sake dawowa gabanta yana laluben fuskarta.

Amal. Ya kira sunanta.

Kai tsaye ta sake dagowa.

Ga yadda ki ka hada gumi har kan hanci, wannan na nuni da cewa za ki yi kishi, masana sirrin mata sun fassara duk macen da ke gumin hanci za ta yi zafin kishi, kin ga kyanki mijin mace daya, da ni ki ka dade.

Kalamansa sun sanya numfashinta tsayawar wucin gadi.

Kwarai, ni mijin mace daya ne, sai dai ni din mai tsada ne.

Ya kai hannu yana son dauke gumin da ya yi dandazo akan dan siririn hancinta, muryar Hajiya Fati ta katse shi daga barin abin da ya ke kokarin aikatawa. A dabarance ya dan ja da baya cikin shafa keya.

Ta karaso gurin tana dubanshi da fuska a tamke, tana mita.

Amal kin debo da zafi da kin bi ta tawa in kin yi abinci kala biyu ya wadatar.

Mommy ba komai, ai na ma kusa karasawa.

Shi kam gogan tuni ya dade da bai wa kafarshi iska.

Yanzu gaya mini mai zan kama miki?

Mom ban da abinki wannan ai ba ta san ciwon jikinta ba.

Nur da ke kokarin shigowa kici din ta ce, duk da hararar da Hajiya Fati ke watsa mata bai sanya ta rufe baki ba.

Ba kya ganin kullum cikin aiki ta ke ba dare ba rana kamar jakalliya, ta saba ta taso cikin wahala komai za ki ce ba za ta taba ganewa ba.

Amal ta dube ta kurum, sanye ta ke da wasu fitinannun english wears wanda bai kamaci diya musulma ta saka su ba. Irin rigar nan ce wadda aka fidda mata wuya kato, hakan ya taimaka gurin bayyanar da rabin nonuwanta, ga kan nan ya sha gashin doki, sai siket wanda ya yi balain matse ta.

Ki yi mini shiru ki kuma bace mini da gani.

Oh sorry na mance, ashe fa yar lelen Mom na taba.

Ta dubi Amal sama da kasa ta watsar tare da jan wani dogon tsaki. Kofi ta dauka ta fice tana faman kunkuni, Hajiya Fati ta maida kallonta ga Amal, gabadaya tausayinta ta ke ji.

Ki yi hakuri, watarana za su yi nadama, za ta tsuguna a gabanki tana neman alfarmarki, ranar zai zo ki da babu ni a duniya.

Amal ta yi yake, Momy kada ki damu, ni kam ban taba sanya abin da ta ke mini a zuciyata ba, na sani babu abin da ya ke dauwamamme, za ta daina za kuma mu zamo daya.

Hajiya Fati ta dafata tana murmushi, ba ta taba ganin yarinya mai shiga rai irin Amal ba, ubangiji ya dasa mata kaunarta tun tana jaririyarta.

Yadda nake jini a raina wataran su ma za su ji haka, ina alfahari da ke, burina kullum Nur ta dinga koyi da dabiunki, na rasa mai ke damunta, mai ke dawainiya da ita. Nur ta zame min matsala bakidayanta, na sani kamatadini tidani, abin da kayi shi za a yi maka, amma ban san yadda aka yi abin da ban yi ba yarana ke yi. Wallahi Amal ban taba daga murya sama da ta mahaifana ba.

In ka ga Hajiya Fati na hira da Amal sai ka yi zaton saanni ne, in ta bai wa Amal labarin damuwarta ta kan ji sanyi, musamman in ta ji Amal nata yi mata addua.

Amal ta numfasa, Ki yi hakuri Mummy, wannan shi ne taki jarrabawar, kaddarar kowa da yadda tasa ke zuwar masa.

Yana makale a jikin falwaya, hannunshi nade a kirjinsa. Ya hango ta fito daga makotansu za ta shiga gida, ya ji kamar ya je ya ta ya gaya mata yadda ya ke ji game da ita, ya gaya mata ba zai iya ba in babu ita, ya shaida mata ita ce rayuwarsa, ruhinsa, farin cikinsa. Zai rasa komai in har ya rasata, rayuwarsa ta ginu ne a kan sonta.

A hankali ya rabu da jikin falwayar gadan-gadan zai nufe ta.

Amalil islam. Ya ji wata murya ta kira ta, haka ne ya sanya shi tsayawa.

Amalil islam. Aka kara fada.

Wata matashiyar budurwa ce ba za ta wuce saarta ba ta karaso da gudu ta rike mata hannu.

Aisha Aliyu ke ce?

Cikin farin ciki ta fada.

Ni ce. Ta ce, Amal an yi hutu kin yi wahalar gani. Ina ne gidanku?

Za ta yi magana ta ji muryar Nur tana fadin.

Aisha Aliyu wanderful, da ma kina zuwa unguwar nan?

Da sauri Amal ta kai kallonta gare ta, sanye ta ke cikin riga da wando pakistan sun kamata sosai, sai wani siririn gyare a tsokani sharia da ta yane kai da shi. Ta karaso inda suke tsaye.

Um, ka ga manyan kwari, kina hutawa irin wannan kashe gayu?

Suka cafke, Shegiya mai ya kawo ki unguwarmu? Nur ta tambaya.

Aisha ta ce, Ai ni yau na yi saar fita, na ga aminiyata.

Wayarta ta hau ruri, ta latsa kore ta karo a kunne.

O.K ina zuwa, yi hakuri inti daya.

Ta katse wayar cikin kallon Amal, Gaya mini gidanku in wuce.

Nur ta kafe Amal da ido tana dariyar mugunta.

Ko nan ne gidanku? Ta nuna gidan su Nur.

Da sauri ta kada kai, Ba nan ne gidanmu ba, ga gidanmu nan.

Ban son tsokana fa, please gaya mini, sauri na ke.

Uhm Aisha ke nan, wallahi nan ne gidanmu.

Caraf Nur ta café, Babu kama ko, to ko za ki shiga ne ki ga tsohuwarta don goge shakku?

Ai ni ji nake yi nan ne gidanku, don rannan Zainab ta yi mini kwatance.

Tana dai shiga ne tana aiki a ba ta abinci. Nur ta sake fada.

Ko kadan Aisha ba ta ji dadin kalaman Nur ba.

Rayuwa ce, mu ma da haka nuka fara, yanzu ga shi komai ya zamo labari. Amal mu je na gaida Ummanki.

Ta janyo hannunta suka shige. A gaban boyayyen masoyi komai ke faruwa, ya yi murmushi mai ciwo, Amal dinshi daban ta ke,

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×