Skip to content
Part 6 of 18 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

Kimanin sati guda ke nan da dangantaka ta yi tsami tsakanin Usman da Anty Sakina, cikin mako daya tak! Zaman doya da manja ne kawai ke wanzuwa. Babu wani abu da ke haɗa su face yin sallama da kuma amsawa, sai kuma a dawo lafiya idan ya ce da ita zai fita ko kuma ita ɗin za ta fita. Babu abinci a gidan, don haka ba ya saka ransa idan ya dawo ta kawo masa balle ya tambaya. A waje yake cin abincin kowanne lokaci, safe dare da kuma rana.

To da ma dai ita Anty Sakina ke kawo kayan abincin da suke ci, a wajen aikinta take ɗaukowa a matsayin rancen da ake ba wa ma’aikatan idan suna buƙata, sai a riƙa cire kuɗin kaɗan-kaɗan a cikin albashinsu. Don haka yanzu kuwa da haka ta faru tsakaninsu sai ta ƙi karɓa. Takan yi girki amma kaɗan take daidai cikinta, ba ta yi da shi.

A ranar Lahadin cikar makon ne Usman ya je wani kanti a nan cikin unguwarsu ya sayo wasu kayan abinci da suka haɗa da ƙaramin buhun shinkafa, da carton ɗin macaroni, sai garin semonvita leda uku ya kawo mata. Kwance take kan kujera a falo tana barci, ya shigo da kayan. Taɓa ta ya yi tare da cewa, “Tashi mana.”

Farkawa ta yi ta buɗe idon tana daga kwancen ta ce, “Ya ya dai me ya faru ne, lafiya?”

Zama ya yi kusa da kafafuwanta sannan ya ce, “Tashi zaune mana, ga waɗannan kayan, a yi maleji da su bashi na karɓo su wajen Danliti mai kanti. Yanzu abin da nake so da ke ki yo mana ragowar cefanen sai a ci gaba da yin girki kamar yadda aka saba.”

Kallon shi kawai ta yi fuskarta ba yabo babu fallasa, babu fishi kuma babu fara’a ta nisa tare da cewa, “Sai yanzu ka gaji da ɗaukar alhakin ne? To ai tunda ka ciyo bashin waɗannan kayan ragowar ma sai ka koma ka ciyo bashinsu. Ni babu inda zan je na sake karɓo kaya.”

“Kin ga Sakina ba na son wannan taurin kan naki, komai ya riga ya wuce kawai, kin yi abin da kike so ban kula ba ya kamata a ce kin huce kin sauko daga dokin zuciyar da kika hau.”

“Hmm! Usman ke nan, ce maka aka yi fishi nake? Kai ne ba ka so a faɗa maka gaskiya, duk abin da ka yi daidai ne. Kai gwani ne ba ka yin kuskure, don haka ba ka ɗaukar maganar kowa. Ban yi haka don na yi maka gori ko tagayyaraka ba, hakkinka ne na bar maka ka sauke. Maganar gaskiya ba zan sake ɗauko komai ba a matsayin loan, idan kana bukata alfarma ɗaya zan yi maka, ita ce idan an yi albashi ka ba ni kuɗin sai na sayo maka.”

“Oh My God! Don Allah ki bar cewa kin daina ɗauko mana kayan abinci, wai me na yi miki ne duk kin sauya a cikin ƙanƙanen lokaci?”

“Hmm! Babu abin da ka yi mini, ba ka yi wani laifi ba, ina son ka sani hakkin ciyarwa ba a kaina yake ba, a kanka yake. Kai Allah ya ɗorawa wannan, don haka ina ga ai ba abin tayar da hankali ba ne idan na ce ka sauke nauyin da ke kanka ko?”

“Haka ne maganarki amma da can ai ba haka muke ba ko, kina abin arziki kina samun lada, yanzu kuma za ki bari shaiɗan yana neman hure miki kunne. Ya kamata ki yaƙi shaiɗan ɗin nan ko da na cikin mutane ne, kawai ki ci gaba da abin alkairin da kike, darajarki ce take ƙara ɗaukaka a wajen Ubangiji.”

Cikin sigar siririn murmushi ta ce, “Wallahi har ka sani dariya ban yi niyya ba, ikon Allah yanzu kuma kai ne har kake yaba mini, kake cewa ina yin abin arziki. Usman ka sani ni ma ina da wayo fa,  ba shashasha ba ce. Na ji zan ci gaba da abin alkairin, to amma kai me kake da naka albashin na alkairin? A ma’aikatar tsaro ta tarayya kake aiki fa, ni kuma ƙarƙashin jiha nake a ma’aikata mafi ƙasƙanci. Albashinka ya fi nawa, ya linka nawa sau kusan biyar, amma ba ka iya wadata gidanka da cefane ko da marar daɗi ne. Sai dai nawa kuɗin za a ci, yaushe rabon da ka sayo mini sabon zani? Komai ni nake wa kaina, sunan ina da aure, idan ba na aikin tsirara zan rika fita ke nan ko kuma bara zan riƙa yi ina ciyar da kaina, ko kuwa gidanmu zan riƙa zuwa suna ba ni?”

Dogon numfashi ya ja ya fesar da wata zazzafar iska tare da girgiza kai sannan ya ce, “Shike nan na ji korafinki kuma zan gyara. Yanzu dai ki yi haƙuri ki ƙarasa yin cefanen, sannan ina son mu koma kan wancan tsarin, zan riƙa ba ki kuɗin idan an yi albashin, shike nan ko?”

Haka dai ya kalamunce ta da bakinsa da iya zancensu na ma’aikatan ɗamara har ta amince ta sauko. To da ma dai fishi ba halin Anty Sakina ba ne sam, Usman ɗin ne yake neman ya sauya mata hali ta karfin tsiya, sakammakon ɓacin rai da baƙin cikin da yake kunsa mata ya sa a wasu lokutan take bayyana fishinta. Koda ta yi kokarin danne zuciyarta sai ta ji ta gaza, dole sai ta dan bayyana sannan take samun sauki.

Misalin karfe 3:00pm na rana bayan Usman da Anty Sakina sun gama sasantawa, ya fita daga gidan ya kira Humaira, tana ɗagawa cikin fara’arsa ya ce, “Ranki ya daɗe ‘yan mata ya gari ya kike?”

Murmushi mai sauti Humaira ta yi sannan ta ce, “Lafiya lau ya aiki? Yau kuma ni ce ranki ya daɗe ɗin, wannan ai sunanku ne na masu iko.”

“Ina wane mu, ai wannan suna sai ku mata sarakai ba, asalin sunan naku ne mu arzikinku muke ci. Na ce ko za mu iya haɗuwa ko kuma an jima da dare?”

“Anya kuwa gaskiya yanzu dai ina aiki kuma idan dare ya yi bana fita ko ina.”

“To ya ya za’ayi ke nan?”

“E to gaskiya sai dai gobe ke nan.”

“To babu damuwa goben kawai ki zo gida.”

Cikin sigar firgici ta ce, “Kai haba gida fa ka ce, har ka manta da abin da ya faru ranar nan? Gaskiya ba zai yiyu ba. Kamar yadda Anty Sakina ta ce, idan ka gan ni a gidanka to ka tabbata tana nan kuma ita ta neme ni.”

“Kin ga ki kwantar da hankalinki kin ji, gobe fa Litinin tana aiki, kuma kin sai karfe 2:00pm na rana take dawowa. Kawai ki zo da wuri kamar goma kafin rana ta yi, Sai mu yi abin da za mu yi, kin gane gidan zai fi sirri, da hotel na shirya za mu tafi ko ya ya kika gani?”

“Gaskiya ni dai ina jin tsoro wallahi.”

“Haba na ce miki babu wata matsala, ko waccan ranar ma ai ke ce kika ce za ki jira ta. Amma kin ga gobe Litinin muna gamawa za ki yi yafiyarki kawai, idan kin taho ki yi mini waya kin ji.”

“To shike nan zan duba na gani, amma dai gaskiya akwai matsala.”

To wannan ɓangaren ke nan, sai mu ce Allah ya shirya.

Ita kuwa Anty Sakina bayan Usman ya kalamunce ta ya shawo kanta ya fice daga gidan, ita ma fitar ta yi ta karasa sayo musu kayayyakin girkin kamar yadda ya roƙe ta. Sannan kuma ta haɗo kayan shayi da crates ɗin kwai guda biyu da man girki. Bayan ta dawo ta ɗauki cylinder gas ta je aka yo refilling, 3KG ta zubo. Yamma ta yi likis lokacin da ta dawo, kicin ta faɗa ta yi musu girki me rai da lafiya.

Bayan ta gama girkin ta yi wankanta ta yi kwalliya, babu laifi yanzu damuwarta ta ɗan ragu, duk da cewa Usman ɗin ba fasa halinsa ya yi ba. Bayan sallar magariba ya shigo gidan, sallama ya yi fuskarsa a sake shi ma babu alamun ɓacin rai. Zaune ya iske Anty Sakina bisa sallaya tana lazimi, bayan ta amsa masa sallamar ta ɗora da cewa, “Sannu da zuwa.”

Ya amsa mata, “Yawwa sannu dai, ya ya gidan ya aiki.”

“Lafiya lau.” Ta faɗa tare da mikewa, ya ce, “Ina zuwa?”

Ta amsa masa da cewa, “Abincinka zan ɗauko maka.”

“Bar shi tukunna sai an jima na yi wanka.”

Wankan ya shiga ya watso ruwa ya fito, ya sauya kayan jikinsa, lokacin Isha ta yi, alwala ya yi ya tafi masallaci. Ita ma Anty Sakina, sallar ta gabatar da yake da ma tana da alwala. Bayan ya dawo ta ɗauko masa abinci da ruwa har ma da lemo. Ya yi mamakin ganin abin da ta haɗa, abinci ne sosai har da nama duk da cewa ya san halinta, kaifi ɗaya ce, idan ta ce za ta yi abu to babu shakka za ta yi din. Ba ta taɓa amsawa cewa za ta yi wani abu ba, daga baya kuma ta ce ta fasa ,wannan ba halinta ba ne. Yana yabanta ta wannan ɓangaren.

Murmushi ya yi da ya ga abincin, ya buɗe tare da dubanta ya ce, “An gaishe ki, ko ke fa, yanzu haka bai fi ba, amma da kin bujuro da wani rikici marar dalili.”

“Hmm! Na bujuro ko dai kai ka bujuro da rikicin.”

Ya yi dariya ya ce, “To dai bisimillah ki saka hannu mu ci kawai.”

Ita ma dariyar ta yi sannan ta ce, “Caɓɗijan! Lallai kam yau da an yi ruwa da ƙanƙara. Anya ba mafarki kake ba?”

“Ban gane mafarki ba, don mun ci abinci tare shi ne mafarki.”

“A’a to ai na ga abin ne banbarakwai, yaushe rabon duniya da ayyaraye, tun ina amarya da ka yi na marmari sai ka watsar. Don haka ni ma yanzu ba zan iya cin abinci da kai ba, kowa ya ci nasa shi kaɗai din.”

“Ki daina wannan maganar, ke akwai ki da tone-tone wallahi. Don kin samu ma ban ce ki ba ni a baki ba, kawai ki sa hannu mu ci kin ji.”

“Ni kam Alhamdulillah na ci nawa na koshi, sai dai idan a bakin zan baka, da ma aikina ne.”

“Shike nan tunda kin ce kin koshi zan ci da kaina na gode.”

Nan ya buɗe cikinsa ya riƙa antaya girki yana ta santi tamkar bai taɓa cin girki mai daɗin wannan ba.

Wani ɗan gajeren tunani Anty Sakina ta faɗa, cikin tunanin take cewa a ranta, “Da ma wannan bawan Allahn ya ɗore a haka yadda yake a yau ɗin nan, fitar daren nan ya daina. Ni ban ga abin da na rage shi da shi ba, ba yabon kaina nake ba, ban ga tsiyar da yake nema ba a wajen matan banzan nan da yake kulawa, Allah ka ganar da shi.”

Bayan ya gama cin abincin, hira ya dauko yake ce mata, “Wai yaushe ne za ki promotional exam dinki?”

“Sai a July ne saura watanni biyu, ka san mu ‘yan July ne.”

“Okay ai gara a yi maza a yi mana promotion din nan, ni wallahi kuna bani tausayi. Malaman makaranta kuna matukar kokari, hayaniyar yara da korafe-korafe. Wai kanku baya muku ciwo ne? Abin takaici kuma shine gwamnati ta yi biris daku, ba a baku wani muhimmanci balle girmamawa.”

“Hmm! To ya ya za a yi, sai hakuri. Kuma aikin naku kamar namu din ne, korafe-korafen ne da hayaniya.”

“Hakane amma ai mu kin ga manya ne, idan mutum ya zo da gargar ubansa muke ci.”

Dariya ta yi sosai, ya cigaba da cewa, “Ya kamata ace gwamnati ta yi wa malamai wani tsari me kyau na inganta rayuwarsu da ta iyalansu har ma da tsarin aiki. Ni da zan samu dama sai na maida malamai sune na farko a albashi kuma sai kudinsu ya fi na kowa yawa sannan a rika basu allowances akai-akai kuma a rage musu yawan aikin da suke. Gaskiya na yarda da maganar da turawa ke cewa, The Reward For Teachers Is In Heaven. Allah ne kadai zai biya ku, ko nawa aka baku ba a biya ku ba.”

“Wallahi kuwa, fatanmu dai shi ne Allah ya ganar da al’umma da kuma mahukunta, su farka su karkato da hankulansu bangaren ilimin. Koda ba a duba matsalar malamai ba, to shi tsarin bada ilimin da kayan aikin koyarwa har ma da muhallin koyo da koyarwar suna cikin mawuyacin halin da ya kamata a basu kulawar gaggawa.”

“Wannan haka yake, na taba saurare a cikin wani shirin gidan telebijin, wata makarantar firamare dake cikin birnin jahar nan, a aji guda daya kawai akwai yara dalibai sama da dari hudu fa casa’in (490). Kin ga wannan ba karamin kalubale bane, kuma dole matsalolin malamai ma abin dubawa ne. Akwai karancin malamai wanda hakan baya rasa nasaba da rashin ingancin albashi da ake basu. Shiyasa mutane suke kauracewa aikin koyarwar, koda fannin suka karanta.”

“Hmm! Kai dai ka bari kwai, addu’a ita ce mafita.”

“To Allah ya yi mana maganin wannan matsalar dama dukkan matsalolin dake addabar kasar nan.”

<< Ƙuda Ba Ka Haram 5Ƙuda Ba Ka Haram 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×