Skip to content
Part 1 of 10 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

❝Imɑm Shɑfi’i yɑ ce: “Zinɑ bɑshi ce, ‘yɑ’yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑ yi dɑ ‘yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑn yi dɑ ‘yɑrkɑ kyɑutɑ.❞

بسم الله الرحمن الرحيم

“Assalama alaikum, salama alaikum mutanen gidan nan ba kwa amsa sallama ne? Ko babu kowa a gidan ne?”

Mai yin sallamar ta ɗan numfasa ta ji ko za a amsa mata, amma dai shiru. Sai ta matsa ta ci gaba da rafka sallama,

“Salama alaikum, salama alaikum, ikon Allah! Wataƙila dai babu kowa a gidan, amma kuma sai su fita su bar gida a buɗe babu kowa haka?”

Rufe bakinta ke da wuya sai ta ji motsin tafiya daga cikin falon gidan bayan da ta matso kusa da ƙofar. Maigidan ne ya taso daga barci, short nicker ne a jikinsa kawai ko singlet babu, ya leƙo yana sakin miƙa, barcin ma bai gama sakin idonsa ba. Yarinyar da ke ta kwaɗa sallamar ta yi saurin sunkuyar da kanta kasa tare da juyawa, ganin a yanayin da ya leƙo. Juyawar shi ma ya yi da sauri lokacin da ya fahimci wacece ta zo. Jallabiya ya sako sannan ya sake fitowa ya ce,

“Humaira ce a gidan namu, sannu da zuwa. Bisimillah shigo mana.”

Ta ɗago kai tare da bin bayansa cikin falon suka zauna bisa kujeru mabambanta. “Ina yini.” Ta gaishe shi haɗe da tambayar, “Ina Anty Sakina, ba ta nan ne?”

Ya amsa mata da cewa, “E, yanzun nan ta tafi gidan kitso, lafiya dai ko?”

“Lafiya lau da ma na zo nan kusa da ku ne gidan su wata ƙawata shi ne na ce bari na biyo mu gaisa.”

“Gaskiya ya yi kyau wallahi kin kyauta kuwa. Ya mutanen gidan?”

“Duk suna nan lafiya ƙalau, bari na koma idan ta zo a faɗa mata cewa na zo.”

“Ba za ki jira ta ba? Ai za ta dawo ki ɗan jira ta kaɗan mana.”

Ta ɗan yi murmushi tare da cewa, “A’a, bari dai na tafi tunda ba ta nan, watarana na dawo.”

“Kada mu yi jayayya da ke, ni fa na ce ki jira ta ko.”

“Hmm! To shi ke nan.” Ta fada cikin sigar murmushi tare da sunkuyar da kanta kasa.

“Yawwa ko ke fa, da a ce ba ki samu kowa ba ne a gidan shi ne za ki ce haka. Bari na kawo miki ruwa ko?” Ya faɗa yana murmusawa haɗe da miƙewa ya nufi kicin ya ɗauko lemo da ruwa ya ɗoro a bisa faranti da cups ya kawo ya ajiye gabanta ya ce,

“Bisimillah.”

Ta yi murmushi tare da cewa, “Kai wallahi da ma ka bar shi a ƙoshe nake.”

“Ban gane kin ƙoshi ba, wannan ai ruwa ne ba abinci ba, duk wanda ya yi tafiya kuma dole yana buƙatar abu mai sanyi. Ko don ba antynki kika samu a gidan ba?”

Cike da jin kunya haɗe da murmushi ta ce, “Wallahi ko ɗaya ba haka ba ne.”

“Kin ga ba na son haka don Allah ki ɗauki ki sha.” Ya fada tare da buɗe lemon Five Alive ya tsiyaya mata a cup ya miƙa mata ya ce, “Karɓi ki sha.”

Alatilas ta karɓa, kunya duk ta baibaye mata fuska ta kurɓi kaɗan ta ajiye. Ya dube ta ya ce, “Ya ya school yaushe za ku yi hutu ne?”

“Saura sati biyu mu fara exams, ita ce ma final year dinmu.”

“Kai Masha Allah, na taya ki murna Allah ya ba da nasara. Amma za ki zo mana hutu nan kafin ki ci gaba ko?”

Humaira ta yi murmushi tare da sunkuyar da kanta, ya ci gaba da cewa, “Gaskiya sai kin zo kin yi hutu a nan, tun tuni nake son ki zo ki yi hutu tare da mu ga shi har kin kammala. Saboda haka idan kika zo sai an samu admission sannan za ki koma ko kuma ma kawai ki zauna tare da mu.”

Maganar yake tare da sakin murmushi idanunsa a kanta yana kare mata kallo. Nisawa ta yi haɗe da murmushi sannan ta ce, “Hmm! To shi ke nan zan zo dai na yi muku sati guda.”

Dariya ya yi sosai kana ya ce, “Haba sati ɗaya sai ka ce ana korar ki.”

Yana maganar yana ci gaba da kallon ta babu kakkautawa bare kiftawa, duk lokacin da ta ɗago kai sai su haɗa ido da shi. Kirjinta cike yake taf! Da dukiyar fulani, tamkar balan-balan aka hura. Hijabi ne a jikinta amma duk da haka sun turo hijabin hatta da nipples shape din ana gani. Hakan ta sa yanayinsa ya fara sauyawa, idonsa ya kada ya yi jajir. Abin da ya fara jefa firgici a zuciyar Humaira ke nan.

“Akwai abinci fa idan kina bukata duk da cewa na ga kin ƙi sakin jikinki sai ka ce wata baƙuwa. Don Allah ki saki jikinki ki je kicin akwai abinci.”

“Hmm! Allah na ƙoshi fa, da a ce zan ci da kaina zan je na duba ba sai ka ce mini ba.”

“To ai ni na ga sai ɗari-ɗari kike da ni.”

Ya faɗa tare da miƙewa ya sake komawa kicin. Farfesu ya zubo mata yavce, “To ga wannan shi ai ba abinci bane da za a ce an ƙoshi.”

Ya ajiye tare da zama a kusa da ita kan kujerar da take zaune two seater har jikinsa yana taɓa nata. Gabanta ne ya yanke ya faɗi darrr! Sunkuyar da kai ta yi, ya dafa kafaɗunta ya ce,

“Humaira me kike buƙata na shirye-shiryen exams ɗin da kuma partyn candy, ki faɗa mini.”

Cikin rawar murya cike da fargaba haɗe da tsoro Humaira ta ce, “Don Allah ka bari na tafi tunda har yanzu ba ta dawo ba.”

Tana faɗa ta yunƙura za ta miƙe ke nan, ya riƙo hannunta tare da juyo da ita gabansa ya ce, “Kar ki yi mini haka Humaira, ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru. Ina son mu ɗan zauna tare.”

“Haba Yaya Usman, kai fa mijin yayata ne bai kamata ka yi mini haka ba. Ba ka ma jin tsoron ta shigo ta gan mu tare a kan kujera ɗaya. Gaskiya ka sake ni na tafi gidanmu don Allah.”

Riƙe yake da hannunta har ya fara ɗora yunƙurin kai ɗaya hannunsa bisa kirjinta, ture hannun ta yi. Ya dube ta ya ce, “Ba yanzu za ta dawo ba, domim ba ta jima da fita ba. Humaira ina son ki.”

“Don Allah ka sake ni yaya Usman, wai ka san me kake cewa kuwa? Ni fa ƙanwar matarka ce, matsayin ƙanwa nake a wajenka bai kamata ka yi mini haka ba. Gaskiya ba zan kara zuwa gidan nan ba.”

“Haba Humaira yanzu ba ni da alfarma ke nan a wajenki?”

“Kana da ita, amma kuma kai ma ka san abin da kake son aikawata sam bai dace ba ko?”

“Ki bar wannan maganar, ni da ke ne fa yanzu. In dai har ba ki mini wannan alfarmar ba, to kin nuna mini iyakata a wajenki.”

Duk maganar nan da suke bai sake ta ba, riƙe yake da ita, sai ma shafa jikinta da yake yi. Hakan yasa ita ma ta fara jin wani abu a ranta, wasa ya fara yi da ƙirjinta. Idanunta ne suka fara lumshewa, jikinta ya fara saki ta ce, “To yanzu me kake so na yi maka?”

Sumbatar ta ya fara, hijabinta ya zare mata daga jikinta, wata ‘yar karamar riga ce armless ta kama ta sosai irin body hug ɗin nan. Ya shafi ƙirjin sannan ya zura hannunsa. Ya ci gaba da sumbatar ta, ya kama harshenta ya yi masa wata tsotsa da karfi, gabaɗaya ta kwanta a jikinsa tana nishi. Shi kuwa ya ci gaba da yake suna akan kujera. Zuwa can da ya ga ta fara suma,  jikinta ya mutu sai ya ɗauke ta sama ya yi cikin ɗaki da ita bai ajiye ta ko ina ba sai kan gado.

Cire mata rigar ya yi, skirt ɗin lace ne a jikinta shi ma ya cire. Haka ya ci gaba da shafa jikinta. Ya fara yunƙurin aiwatar da abin da ta gaza gane mene ne.

“Me za ka yi ne, gaskiya ban da wannan ka yi hakuri.” Humaira ta fada tana kokarin mikewa.

Idanuwansa sun kaɗa sun zama ja kamar gauta, ya ce, “Kar ki yi mini haka mana.”

“Gaskiya a’a ya isa haka yaya Usman, ka rufa mini asiri.”

“To shi ke nan na ji.”

Haka nan dai ya hakura ya bar ta ba tare da ya cim ma muradinsa na raba ta da budurcinta ba. Miƙewa ya yi ya mayar da kayansa ya fito falo ya zauna, ita kuwa tana can kwance kan gado shame-shame ta gaza koda mikewar. Mintuna kamar biyar zuwa bakwai ya sake komawa ɗakin barci ya iske ta ta fara, ya tashe ta ta hanyar jijjigata, ta farka.

“Barci kike ji ne?”

Ya tambaye ta, girgiza masa kai ta yi alamar e, ta ma gaza yin magana. Sam ba a taɓa yi mata haka ba, ya gajiyar da ita ba kaɗan ba.

Ya ce, “To mayar da kayanki tukunna sai ki kwanta ki yi barcin.”

Ko hannunta ba ta iya ɗagawa, shi ne ya saka mata kayan a jikinta sannan ya kamo ta suka dawo falo ya shimfiɗe ta a kan kujera three seater. Barcin ne kasa-rika ya sake ɗauke ta. Shi kuwa munafikin sai ya fito waje ƙofar gidan ya zauna yana ta latsa wayarsa.

Bayan kamar awa guda yana nan zaune a ƙofar gidan sai ga Anty Sakina nan ta dawo daga gidan kitson da ta tafi.

“Yau kuma zaman waje kake sha’awa?”

Anty Sakina ta tambaya, shi kuwa sai ya kada baki ya ce, “A’a baƙuwa dai muka yi ne shi ya sa na fito nan na ba ta waje na ga ta ƙi sakewa ne. Da cewa ma ta yi za ta tafi tunda ba kya nan.”

“Wace ce ta zo, Mummy ce ko kuma wa?”

“A’a ba Mummy ba ce Humaira ce, wai gidan wata abokiyar karatunta ta zo shi ne ta karaso a gaisa.”

“Hmm! Kai ma dai, Humairar ce ta ƙi sakewa saboda kai? To mu je cikin.”

Ta shige gaba ya biyo bayanta, gabansa sai faɗuwa yake a ransa yake cewa, “Allah ya sa kada ta fahimci wani abu, Allah ya sa jikin yarinyar nan ya dawo daidai.”

Fatan da yake ta yi ke nan a zuciyarsa, suna isa falon Anty Sakina ta ga Humaira kwance kan kujera tana sharar barci babu hijabi sai ‘yar ƙaramar riga, wajen cibiyarta ma duk a waje. Ta yi sauri ta ɗauki hijabin ta rufe ta da shi sannan ta waigo da wani irin kallo mai cike da tuhuma ga Usman. Sunkuyar da kansa ya yi yayin da zuciyarsa ta ci gaba da bugawa da sauri, cikin inda-inda da in’ina ya riƙa cewa, “Au au au barci ma ta yi ke nan.”

Cike da mamaki Anty Sakina take dubansa, yanayinsa akwai alamun firgici da rashin gaskiya. Juyawa Anty Sakina ta yi kan Humaira ta kama ta tana tashin ta da cewa, “Ke Humaira, Humaira tashi mana.”

Humaira ta farka tare da cewa, “Na’am Anty sannu da dawowa.”

Anty Sakina ba ta amsa mata sannun da ta yi mata ba, sai ma tambaya da ta fara aika mata kamar haka, “Tun yaushe kika zo ne?”

Usman ne ya yi saurin cewa, “Ai ba ki daɗe da tafiya ba ita kuma ta shigo. Ina jin ta gaji ne sosai shi ya sa ta yi barci, kin san ana ɗan yin rana a garin.”

Kallonsa kawai Anty Sakina ta yi ta kauda kai, gaskiya ba ta aminta da shi ba. Yanayinsa ba haka ta saba ganinsa ba, duk ya bi ya rikice ya daga hankalinsa.

Sannan kuma tunda Humaira take zuwa gidanta ba ta taɓa yin barci ba, waɗannan ne abubuwan da suka fara jefa zargi a zuciyarta.

Duban Humaira ta sake yi tare da cewa, “Ko dai ba ki da lafiya ne?”

“Anty lafiyata lau wallahi, kawai dai barcin ne ya zo mini, ni ma na yi maimakin ganin kaina ina barcin.”

“To shi ke nan ya ya gidan ya su Abba da Mummy da su Zainab da Haidar?”

“Kowa yana nan lafiya.”

“Me ya sa ba ki mini waya ba da kika zo, inda kuma ban dawo da wuri ba fa, sai ki zauna ki ci gaba da barcin?”

“Hmm! Anty wallahi ba ni da credit ne a wayata, da ma na zo nan kusa da ku ne na kawo wa wata ƙawata littafanta saboda saura sati biyu mu fara exams.”

“To shi ke nan ya yi kyau, amma daga yau idan kika zo ba na nan kada ki sake zaman jira na. Kawai ki kira ni a waya ma kafin ki karaso.”

Usman wanda ya kasance tamkar mutumin da ke gaban Alƙali ya yi tsuru-tsuru, nisawa ya yi sannan ya ce,

“Haba don Allah! Ya ya kike mata kamar da faɗa ne? Ziyara fa ta kawo miki. Mutum ya yi aikin lada kuma a riƙa yi masa faɗa. Wannan ba daidai ba ne, to mene ne idan ta zo ba ta same ki ba ta yi jiran ki? Gidan ‘yar uwarta ne fa, don Allah ki rika sassautawa ranki, haba!”

“To na ji amma yana da kyau ta faɗa mini za ta zo, idan unguwar da na tafi nesa ne sai ta zauna jira na, kuma su can gida hankalinsu a tashe?”

Ganin yadda suka fara musayar kalamai tsakanin Anty Sakina da Usman ya sa Humaira ta ce, “Anty bari na tafi tunda mun gaisa.”

Ta faɗa tare da yunƙurawa ta miƙe ke nan sai ta yi talau kamar za ta faɗi, ta koma ta zauna kan kujera.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Ƙuda Ba Ka Haram 2 >>

1 thought on “Ƙuda Ba Ka Haram 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×