Skip to content
Part 14 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Karar Kwana 

Yau kam Iliya hankalinsa a tashe yake, garin kamar an yi shara sam babu fasinja. Yau ya kamata a ce ya kai wa mai Keke Napep ɗin da yake aiki da ita balas, amma gashi ko dubu biyu bai haɗa ba. Ga matarsa haihuwa ko yau ko gobe. Dukan kan Napep ɗin zai yi cike da takaici sai ya an ce, ‘ss!’

Yana waigawa kuwa sai ya ga wani mutum me matsakaicin jiki sanye da suite shuɗiya. Fuskar mutumin sanye take da gilashi, don haka ba zai iya tantance yanayin idanunsa ba, sai dai da gani mai kuɗi ne. Domin ko takalminsa kawai ya wadatar a matsayin hujja. Hannunsa riƙe da wani ɗan ƙaramin akwati, da alama ofis zai je.

Cikin wata murya da Iliya ya kasa tantance Bafulatani ne ko buzu ya ce,

“Mai Napep za ka je Millennium City?”

A hanzarce Iliya ya ce,

“Ai ko sama ka ce za ka sai in kai ka Yallaɓai.”

Murmushi kawai mutumin ya yi ya shiga sannan ya ce,

“Drop zan ɗauke ka. Amma sauri nake sosai don na makara. Ina fa ta za ka iya kai ni a ƙasa da mintuna talatin.”

“Ai cikin minti sha biyar ma za mu iya kai wa matuƙar dai za a yi min biya mai kyau.”

Murmushi mutumin ya sake yi a karo na biyu sannan ya ce,

“Wannan ba matsala ba ne. Kai dai ka isar da ni wurin da wuri kawai.”

To faɗuwa ta zo daidai da zama, tsohuwa ta karye. Dama neman kuɗi yake ruwa a jallo. Gashi kuma ko ba a faɗa ba wannan mutumin mai kuɗi ne sosai. Don haka sai yai ta ba wa Napep wuta ba ƙaƙƙautawa. su shiga nan su fita can, kafin wani lokaci sun shigo Millennium City. Babu abin da Iliya ke tunani face irin kuɗin da zai samu da kuma irin bushashar da zai yi da su.

Mutumin ya Kwatanta masa inda zai kai shi. Bayan sun isa wurin, sai mutumin ya ce da shi,

“Na fa gode sosai da ƙoƙarin da ka yi na kawo ni akan lokaci. Nawa ne kuɗinka?”

Iliya na ‘yar fara’a ya ce,

“Ai Yallaɓai ka ba da abin da ka ga ya dace kawai.”

Murmushi mutumin ya sake yi sannan ya ce,

“Kai kuwa abokina ka yi karatun boko ne?”

“A’a Yallaɓai, me ka gani?”

Iliya ya tambaya cike da mamaki.

“Na ga kana da kirki ne. Shi ya sa kawai na tambaya.”

Mutumin ya ba shi amsa.

“Ban yi karatun boko ba Yallaɓai. Na dai yi yaƙi da jahilci, don haka na iya karatu da rubutun Hausa. Kuma Yallaɓai ai ba lalai sai wanda ya je boko ba ne kawai yake da kirki.”

Girgiza kai kawai mutumin ya yi yana murmushi sannan ya ce,

“Maganarka gaskiya ce.”

Sannan ya zaro kuɗi daga cikin aljihunsa ya ƙirga, sannan ya miƙa masa da cewa,

“Ga dubu takwas nan. Ina fata sun yi ko?”

Mamaki ma ya hana shi magana balle ya yi masa godiya. Hannu na karkarwa ya karɓi kuɗin sannan ya rusina har ƙasa ya fara godiya. Mutumin ya ce mishi ya tashi ai ba komai. Daga nan suka rabu, mutumin ya shige wata masana’anta da ke wurin shi kuma Iliya ta juya ta tafi. Saboda tsabar murnar samun waɗannan kuɗaɗe, bai ko ankare da cewa mutumin bai ɗauki ɗan ƙaramin akwatin da ya shiga napep ɗin da shi ba.

Bayan ya ɗan yi nisa kaɗan sai ya tsaya da nufin ya lissafa kuɗin. Tsayawar shi kenan sai ya ji kamar wani abu na motsi a seat ɗin baya. Don haka sai leƙa domin ya ga ko menene. Leƙawarsa ke da wuya sai ya ga wannan akwati. Nan fa ya ɗauki akwatin yana dudduba shi. Wata zuciyar na ce mishi ya mayar wa da mutumin da abinsa, wata kuma na ce mishi kawai ya tafi da shi. A ƙarshe dai Shaiɗan ya ci galaba a kan shi ya zaɓi tafiya da wannan akwati.

Napep ɗin ya koma ya nufi gida a guje. Ya mutane sai tare shi suke yi a hanya amma ko kallon su bai yi ba. Ko da zuwa gida, sai ya rufe ƙofar sannan ya kira matar suka shiga ɗaki suka rufe ƙofar nan ma. Nan ya labarta mata abinda ya faru, amma sai ya ce mata tsintar akwatin ya yi. Nan fa suka fara ƙoƙarin buɗe akwatin. Suna buɗewa kuwa sai suka ga babu komai a ciki face bom ƙwaya ɗaya yana nuna lokaci, saura minti ɗaya ya tashi. Kafin su buɗe ƙofar su fita bom ɗin ya tashi da su da maƙwabtansu gaba ɗaya.

*****

A can wani ɓangare na Millennium City, Ishaq na zaune yana duba na’urar da ke hannunsa mai kama da waya. Kwatsam sai ya ga alamar da yake ta fatar gani. Bom ɗin ya tashi. Nan fa ya cika d matsananciyar murna har da yin tsalle.

<< Bakar Kaddara 13Bakar Kaddara 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.