Duk yadda ta so ta tsayar da tsiyayar hawaye a idanunta kasawa tayi. Da ta ɗaga idanu ta kalli Mannira, sai ta tuna rabuwarsu a ranar da wannan mummunar ƙaddarar zai faru. Mannira jininta ƙanwarta da take matuƙar so wacce suke kwana ɗaki ɗaya suna tashi tare ita ce haka? Ta yi wani irin rama sosai, tayi baƙi, ta zabge, fuskarnan ya zama firit sai hancinta da ya ƙara tsawo kamar biro.
Tana zaune a kan gado anyi mata matashi da filo ta jingina bayanta, ta ƙurawa waje ɗaya idanu tana kallo hawaye na tsiyaya a idanunta kamar. . .
Allah sarki Mannira. Amma na ji dadin hukuncin da aka yi wa su Muhsin. Allah ya gyara system na mu na Najeriya ya shirya mana zuri’a