Skip to content
Part 54 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Duk yadda ta so ta tsayar da tsiyayar hawaye a idanunta kasawa tayi. Da ta ɗaga idanu ta kalli Mannira, sai ta tuna rabuwarsu a ranar da wannan mummunar ƙaddarar zai faru. Mannira jininta ƙanwarta da take matuƙar so wacce suke kwana ɗaki ɗaya suna tashi tare ita ce haka? Ta yi wani irin rama sosai, tayi baƙi, ta zabge, fuskarnan ya zama firit sai hancinta da ya ƙara tsawo kamar biro.

Tana zaune a kan gado anyi mata matashi da filo ta jingina bayanta, ta ƙurawa waje ɗaya idanu tana kallo hawaye na tsiyaya a idanunta kamar ma bata san da shigarsu cikin ɗakin ba.

Abinda yafi tayar wa da Nauwara hankali shi ne kalmar ‘rape (fyaɗe)’ da taji likitan yana faɗa yana maimaitawa a cikin taƙaitaccen bayanin da yake musu.

“Mafi akasari victims ɗin da mummunar ƙaddarar fyaɗe ya afkawa suna kasancewa a irin wannan yanayi na withdrawal. Za su janye kansu daga cikin mutane, kuma su dinga ɓoye damuwarsu, wanda a ƙarshe idan ba an dage da kulawa da su ba hakan zai iya haifar musu da depression mai ƙarfi. Shi yasa nake shawartarku da ku dinga ƙoƙarin ɓoye damuwarku a gabanta, kuma ku dinga ƙoƙarin kwantar mata da hankali, kuna nuna mata wannan abinda ya faru da ita ba komai ba, baƙin ciki ne na ɗan taƙaitaccen lokaci da zai zo ya wuce kamar ba’a yi ba.

Bayan dogayen shawarwari da ya bayar, yayi musu sallama da fatan Allah Ya bata lafiya ya fice daga ɗakin nurses na biye da shi riƙe da files a hannunsu.

Bayan gama sauraren jawabin da ficewar likitan, da sassarfa Nauwara taje ta rungume Mannira tana wani irin kuka mai cin rai. Khamis kuwa sai waje aka fita da shi saboda yadda jikinshi ya ƙara rikicewa, dama jiki ya sata ya shiga ɗakin ba tare da sanin Abba Yusuf ba. Sai kuma ya ci karo da bayanan likita waɗanda suka ƙara ɗaga mishi hankali.

Da matsanancin tausayin ƴanmatan Anty Iklima ta ƙarasa kusa da su ta dafa kafaɗar Nauwara tana lallashinta da nuna mata muhimmancin yadda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau.

Daƙyar ta iya ɗaga rinannun idanunta tana kallon Aunty Ikilima ta ce,
“Waye ya yiwa yar’uwata wannan cin mutuncin? Don Allah ki faɗa min ko waye! Wallahi sai na kashe koma waye da hannuna…”

“Assha! A’uzubillahi! Kul! kada ki ƙara furta irin waɗannan kalaman ko da wasa. Balle ma Yaya Yusuf yana matuƙar bakin ƙoƙarinshi wajen ganin an gano ko su waye suka aikata hakan a gare ta. Baki ga yadda ƴan sanda da ma’aikatan hisba ke ta sintiri a cikin asibitin nan ba? Matsalar da ta kawo jinkiri ita ce har yanzu Mannirah ta kasa faɗin ko su wanene da kuma takamai-mai abinda ya faru da ita bayan fitowarta daga makaranta.

Sannan lambar wayar da aka kira Daddynku da ita, an rasa takamaiman ko wanene mai shi saboda an sauke layin daga kan waya, kuma bayanan dake kan layin ba wasu masu yawa bane. Amma in shaa Allah ina da tabbacin za a dace. Allah zai toni asirin ko su wanene, mu cigaba da addu’a.”

A madadin kalamanta su kwantar ma da Nauwara hankali, kuka kawai suka ƙara sanya ta. Ta kifa kanta a jikin gado tana rusawa kamar ƙaramar yarinya Anty Iklima tana aikin lallashi.

Daƙyar ta iya dannar zuciyarta tayi shiru bayan Abba Yusuf ya rantse mata da girman Allah idan bata nutsu ba yanzunnan zai saka direba ya mayar da ita gida.

Yinin ranar tana maƙale da Mannira tana bata kulawar da ta da ce kamar yadda likita ya koyar da su. Ko nan da can ta kasa matsawa. Tana zaune a kan kujera kusa da ita tana ta bata labarai masu daɗi da saka nishaɗi, wasu ma tun na zamanin yarintarsu ne.

Tun Mannira tana ƙure ta da kallo kamar bata santa ba, hawaye na tsiyaya a idanunta. Har hawayen ya tsaya, tayi shiru kamar ba ta gane abinda take cewa, har ta fara ƙoƙarin amsa magana ƙasa-ƙasa. Amma sam ba walwala a tare da ita ko kaɗan.

Shi kanshi likitan a lokacin da ya dawo ya gansu sai da ya jinjina ma Nauwara, kuma ya ce ta cigaba da bada himma. In dai aka cigaba da tafiya a haka cikin ƙanƙanin lokaci za ta manta da damuwar komai ta rungumi ƙaddarar da ya afka mata.

Cikin ikon Allah a kwanaki biyar Mannira ta ɗan ƙara warwarewa sai ɗan abinda baza’a rasa ba na damuwa da ƙuncin zuciya, wannan kuma ya zama kamar dole ne. Amma sosai ta rage yawan kuka, sai dai tayi a ɓoye. Yanzu har ana iya zama ayi hira a gabanta, jefi-jefi kuma tana ɗan amsawa. Sai dai sanyin jikinta ya ninninku fiye da tsammani.

Da salon dabara da bugun ciki haɗe da iya zama da mutane Anty Iklima tayi amfani har ta samu Mannirah ta faɗa mata duk abinda ya faru a tsakaninta da Muhsin. Abin ya girmame mata, ta kuma tausayawa Mannira nesa ba kusa ba. Cin amana irin haka a wajen wanda ka yarda da shi, ba ƙaramin giɓi yake janyowa a rayuwar mutum ba.

Saboda haka ta ƙudiri aniyar yin iyaka bakin ƙoƙarinta wajen ganin cewa hakan bai jawo wani naƙasu a cikin rayuwar yarinyar ba.
Bata kuma yi ƙasa a gwiwa ba ta sanar da Yaya Yusuf duk abinda Mannirah ta fada mata. Har kwatancen gidan da suka kaita da duk abubuwan da suka faru waɗanda suka gudana kafin hankalinta ya ɗauke, sai da ta faɗa mishi.

Hankalinshi ya tashi sosai, kuma ranshi yayi mummunan ɓaci da irin wannan yaudara da cin amanar da mafiyawancin samari suka daɗe suna amfani da ita gurin lalata ƴanmatan da suka aminta da su. Su kuma da yake sakarkaru ne da yawan ƴan matan sun ƙi ganewa. Nan take a gaban Aunty Ikilima ya dauki waya ya kira Cp, wanda dama can yasan da zancen case ɗin. Baiyi ƙasa a gwuiwa ba ya zayyane mishi duk wasu bayanan Muhsin, iyayenshi, inda suke zaune, da komai, kamar dai yadda Mannira ta bayyana.

Da ƙwarin gwuiwa Cp yayi mishi al’kawarin tsayuwa ka’in da na’in wajen ganin an ƙwatowa Mannirah haƙƙinta, ta hanyar gurfanar da Muhsin da abokansa a gaban kuliya manta sabo. Da wannan suka yi sallama, Abba Yusuf na ta yi mishi godiya kamar ma har an kamo Muhsin an gama komai.

*****

Kwanaki uku tsakani Yaya Yusuf ya amsa kiran da Cp yayi mishi a babbar headquarter ɗinsu ta ƴan sanda. Kai tsaye aka nufi Ofis ɗin CP da shi bayan ya isa gurin.

CP Lawal Lawal, abokin Yaya Yusuf ne da suka yi primary da Secondry tare, kuma cikin hukuncin Allah ko bayan rabuwarsu sai suka riƙe zumunci da abotar da ke tsakaninsu har zuwa yanzu da Lawal Lawal yake da matsayin CP shi ma Yaya Yusuf yake riƙe da babbar muƙami a aikin gwamnati.

Da fara’a sosai a fuskarsa ya tashi daga kan kujerar da yake zaune lokacin da Yaya Yusuf ya shiga ofishin. Ya tarbe shi da murna sannan ya bashi hannu suka yi musabiha tare da gaisuwa irinta shaƙiƙan aminai.

CP Lawal bai tsaya ɓata lokaci ba ya fara korawa Yaya Yusuf bayani game da case ɗin Mannira da yai ruwa yayi tsaki kamar ƴarsa ta cikinsa.
“A taƙaice wannan abu da suka aikata shi ne karo na shida ga ƴan mata mabanbanta. Ba a kan Mannirah kaɗai ya fara aikata haka ba. Bugu da ƙari kuma su kansu iyayen Muhsin nemanshi suke yi ido rufe, saboda kafin ya gudu sai da ya wawushe dukiyar Uban miliyoyin kuɗaɗe, ya kuma kwashi gwala-gwalan mahaifiyarshi ƙara gaba. Abin dai babu daɗin ji sam!”

Yaya Yusuf yayi shiru, hannunsa tallabe da kunci, zuciyarshi duk babu daɗi. Sai tunani yake ta ina yarinya nutsattsiya kamar Mannirah ta haɗu da tantirin ɗan iska kuma mayaudari irin Muhsin? Daƙyar ya iya buɗe baki ya ce
“To yanzu ya kake ganin za ayi? Ko kana nufin ya ci bulus kenan? Ire-iren waɗannan shaiɗanun yaran bai kamata a barsu su cigaba da aikata irin wannan mummunan ɓarnar ba.!”

Cp yayi wani taƙaitaccen murmushi yana kallon Yaya Yusuf ya ce
“Calm down abokina. Ina baka kana roƙa… Wato abinda ya faru shi ne wani abu da bature yake yiwa laƙabi da ‘karma’ shi ya faru. Zancen da nake yi maka a yanzu haka Muhsin yana hannun hukuma…”

Cike da ɗoki da zumuɗi a muryarsa ya katse Cp da cewa
“Alhamdulillahi! Amma kuwa na ji daɗin jin wannan maganar. Ta yaya akai haka? A ina kuka samu nasarar cafke matsiyacin?”

“Uhmmmm! Wato yaronnan da kake gani tantiri ne fiye da tsammaninka. Kafin mu kai ga damƙe shi yana wawasan kuɗin iyayen tuni suka tsallaka zuwa ƙasar America. To sai dai wani abu da ya manta ko kuma tsautsayi ne oho! Shekaru fiye da hudu da suka gabata, ana nemanshi a ƙasar America bisa zargin cewa sun yiwa wata ɗaliba a makarantar da suke fyaɗe shi da abokanshi. Tun a wancan lokacin aka samu nasarar damƙe abokan nashi, shi kuma ya samu nasarar gudowa Najeriya ba tare da sun kama shi ba. To kaga da wancan laifin wanda bai gama mutuwa ba, yanzu kuma sai ya sake dirar musu da hodar Iblis wadda aka kama su da ita a airport. To dai in taƙaita maka zance yanzu manyan laifuka uku ake tuhumarshi da su acan ƙasar America. Kaga na farko fyaɗe, na biyu guduwa da yayi, ga kuma na uku shiga ƙasar da kayan da aka hana. Kuma kasan yadda ƙasar America take da matukar tsauri ta bangaren fyaɗe da kuma safarar miyagun ƙwayoyi, ko kai ɗan gidan uban waye baka isa ka tsallake hukunci ba.

Sannan ina mai tabbatar maka da cewa, da zarar mun kammala haɗa sauran cases ɗin shi da muke da su anan, za mu miƙa su can kotun ƙasar da ake gudanar da case ɗin shi. Kai kanka kasan bayan faruwar haka tsattsauran hukunci ne zai biyo baya wanda yafi ma wanda za a zartar musu anan Najeriya, in sha Allah!!”

Yaya Yusuf yayi shiru yana tunani, Allah ya sani ba haka yaso ba. In da so samu ne zai fi son ace an hukunta waɗannan tsinannun yara a gabanshi, ya kuma tabbatar da idanunshi. Amma kuma idan ya duba ta wani ɓangaren sai yaga cewa wata-kila hakan yafi zama alkhairi. Saboda yadda ƙasarmu ta gama ɓaci da cin hanci da rashawa, ga iyayenshi masu kuɗi ne na gasken gaske. Mawuyacin abu ne kaga an yankewa ɗan masu kuɗi hukuncin da ya dace da laifin da ya aikata, in dai a ƙasarmu ne sai addu’ar Allah ya sakawa waɗanda aka zalunta kaɗai.

Don haka ya kaɗa kai tare da fatan Allah yasa hakan ya zama shi ne mafi alkhairi.

Cp ya amsa da Amin. Bai fice a gaggauce ba sai da suka ƙara yin hira suna tattaunawa kan irin waɗannan cases ɗin da suke faruwa akai-akai musamman cikin kwanakin nan, da yadda idan ba tsananin sa’a aka ci ba sam hukuma ba ta ɗaukar matakin da ya dace akan mai laifi, ko da su ƴan sanda sun jajurce wajen kamo mai laifin da tattara bayanai su tura case ɗin kotu, a ƙarshe maganar tana shan ruwa ne ba tare da ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran hukunci ba, matuƙar mai laifin yana da waɗanda suka tsaya mishi.

A ƙarshe suka rufe hirar tasu da yiwa ƙasarmu addu’a Allah ya shiryi mutanen cikinta ya tabbatar mana da shugabanni adalai. Daga haka suka yi sallama Yaya Yusuf yayi ma Cp godiya sosai. Shi kuma Cp yayi mishi alƙawarin idan wani abu ya taso zai sake nemanshi domin ya ji inda aka kwana.

Cikin ikon Allah sati biyu tsakani aka yankewa Muhsin hukuncin zama a gidan yari har na tsayin shekaru talatin da biyu acan ƙasar America. Akwai kuma gagarumar tara da aka yanke ma iyayenshi da na abokanshi biyu za su bada ga Mannira da sauran yaran da aka zalunta aka ketawa haddi. Sauran abokan cin mushen Muhsin guda biyu kuma aka yanke musu hukuncin zaman shekaru ashirin a gidan yari.

Wannan labari ba ƙaramin faranta ran iyalan Alhaji Yusuf yayi ba da ma ɗaukacin sauran ahalinsu na kusa sosai da suka san da zancen abinda ya faru.

Hakan ya ƙara taka muhimmiyar rawa gurin kawo sauyi mai kyau cikin rayuwar Mannira. Wadda ta kasa sakin jikinta a ko’ina, koda-yaushe tana cikin ɗar-ɗar. Hakan yasa Abba Yusuf tare da taimakon Aunty Karima wacce taje taga halin da suke ciki ta kuma yi jimami kwarai da gaske, suka sama mata wajen da take zuwa counselling. Har makaranta ma sai da aka canza mata wadda tafi kusa da gidan Abba Yusuf ɗin. Duk da cewa ba sanin zancen aka yi ba a tsohuwar makarantarsu, amma kuma jita-jita bata da daɗi, za ta kuma iya sanyawa ta kasa samun nutsuwar yin karatun da ya zama ƙiris ya rage ta ƙarasa.

Alhamdulillahi! Matakan da suka ɗauka na ƙara inganta rayuwarta ya taimaka ƙwarai wajen samar mata natsuwa da kwanciyar hankali sosai.

Zama a gidan Abba Yusuf ɗin ma sai ya fiye mata zaman gaban iyayensu. Saboda ba ta samun kulawar da take samu a gaban Abba Yusuf da tarbiya.
Ga Nawwara nan duk iya zamiyarta da silalewa, amma ta kasa zagaye bayan idon Abba Yusuf tayi facaka yadda take so.

Babu yadda Amina bata yi da Nauwara ba akan ta dinga bin ta suna zagayewa ta baya suna harkar gabansu kamar yadda suka saba.
Amma Nawwara ta kasa sakin jikinta ko kaɗan. Allah ya sani ta riga ta gama tsorata da Abba Yusuf, Gani take yi duk inda ta motsa idanunshi yana kanta.

Don haka take taka-tsantsan sosai da lamarin zama a gidanshi. Saboda ta san fushinshi ba ƙaramin bala’i zai sauke mata ba, tana kuma tsoron irin hukuncin da zai yanke mata idan ya same ta da karya dokokin da kusan kullum sai ya jaddada mata kamar bitar karatu.

A gefe guda kuma bayan zugar Amina ga takura da matsin lambar da Mumcy take mata. Tun tana bin ta da lallami da daɗin baki har ta fara fito mata ta bayan gida da ƙananun barazana iri-iri. Domin Nauwara na ɗaya daga cikin yanmatan da take matuƙar ji da su da alfaharin samunsu a ƙarƙashinta.

Balance suke kai mata ba na ƙananun kuɗaɗe ba. Da wannan dalilin yasa ba za ta taɓa bari ta kuɓuce mata tana ji tana gani.

Kawai dai tana ɗan ɗaga mata ƙafa ne komai ya ƙara daidaita a al’amuran Nauwarar, kamar yadda kullum Amina take tausarta.

“Ita har ma ta isa tace za ta bar ƙungiya cikin sauƙi haka? Ki dai ɗan ɗaga mata ƙafa Mummy. Kin san yanzu tana gidan wan babanta ne. Har yanzu bata gama gane yadda al’amuran gidan suke tafiya ba, kuma kin san ta da bala’in tsoro. Ni da kaina zan sake janyo miki ita cikin harka dumu-dumu. Ba ke kaɗai ba Mummy, ko ni ƙaruwar da nake yi da ita ai bazan yi sanyar da za ta saɓule cikin sauƙi haka ba.”
Ire-iren maganganun da Amina take yawan maimaita ma Mummy kenan a cikin kwanakin.

***

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 53Lokaci 55 >>

1 thought on “Lokaci 54”

  1. Allah sarki Mannira. Amma na ji dadin hukuncin da aka yi wa su Muhsin. Allah ya gyara system na mu na Najeriya ya shirya mana zuri’a

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×