Kwanci tashi ba wuya a gurin mahaliccin sammai da ƙassai. Watanni biyu suka zo suka shuɗe a haka, ta wani ɓangaren al’amura na tafiyar hawainiya ba yadda aka so ba. Wani ɓangaren kuma al’amura sunyi sauƙi sosai kuma komai ya fara lafawa, ana cigaba da tuƙawa cikin godiya ga Allah da rufin asirin Ubangiji.
A ɓangaren Ziyada da Khamis, tunda ya samu tabbacin an san inda take kuma ana kiranta a wayar Aunty Ruƙayya ayi magana da ita, bai taɓa kalmar lambar wayar ya kira da nufin a bata suyi magana ba. Saƙo ɗaya da ya aika mata da shi shi ne,
“Ziyada, idan baki manta ba ni Khamis saki ɗaya nayi miki. Kuma na mayar da aurenmu a gaban Abokina Jamilu tun bayan kwanaki biyu da sakin ya afku. Don haka har yanzu a matsayin matata kike, idan kuma baki yarda ba, kina iya kiran Jamilu ki tambayeshi, na san baza ki rasa lambarsa ba.”
Wannan maganar tashi ba komai ya saka Ziyada ba sai dariya, domin shi da zancen banza ɗaya ta ɗauke su. Aure ne dai ko? Yarjejeniya ta amincewa gudanar da zamantakewa tsakanin miji da mata. Ita matar ta ce ba ta yi, akai kasuwa. Ko ana dole ne?
Takanas-ta kano Aunty Karima tayi takakkiya zuwa Lagos suka tasa Ziyada a gaba da nasiha da lallami iri-iri kan tayi haƙuri ta koma gidan uban ƴaƴanta. Ita kuwa ta baɗa ma idanunta toka ta ce kamar yadda Ummanmu ta rasu ta haƙura, ta haƙura da auran Khamis har abada.
Da suka nemi matsa mata suna tunasar da ita ko don darajar ƴaƴanta ta dubi Allah da Ma’aiki SAW ta koma ihun kuka ta fashe musu da shi, tana faɗin don sun ga babu iyayensu a raye shi yasa baza su goya mata baya kan abinda ta tabbatar shi ne daidai a rayuwarta ba.
Bayan sun rarrasheta daƙyar tayi shiru, nan ta zauna ta fara warware musu kaɗan daga cikin irin zamantakewar auren da tayi da Khamis, har zuwa kan taƙaddamar da suka yi ya sake ta akan abinda bai taka kara ya karya ba.
Hankulansu yayi mummunar tashi, domin buɗa irin waɗannan manyan maganganu na miyagun halayen Khamis abu ne da bata taɓa yi ga ɗaya daga cikinsu ba. Duk a tsammaninsu Khamis ya daɗe da shiryuwa, duba da yadda kullum idan zance ya tashi Ziyada idan bata faɗi alkhairinshi ba sai dai ta ce,
“Uhmmm! Shi daman zaman tare zo mu zauna zo mu saɓa ne. Allah ya ƙara mana haƙuri da juriya.”
Sun sha kukansu ba kaɗan ba, sannan suka sha alwashin ko ana ha maza ha mata za su goya mata baya. Yara ne dai Allah ya raya su yayi musu albarka.
Mijin Aunty Ruƙayya da ya kasance babban ɗan kasuwa kuma dattijo na gaske ta janyo cikin case ɗin. Bayan ya saurari duk wasu bayanai daga bakin Ziyadah cewa yayi baza’a yi gaggawar miƙa lamarin zuwa kotu ba.
“Duk abinda kika ga ya kai ga kotu kai tsaye to anyi duk mai yiwuwa ne an kasa samun maslaha. Za muyi iya yinmu, idan ya bata takardarta cikin sauƙi to falillahil hamd, idan kuma bai bata ba to babu yadda muka iya dole za mu miƙa maganar gaban Alƙali ya amsa mata takardarta. Irin wannan zaman ma ai ya wuce na haƙuri, ya kai ga cutarwa da hallakar da kai. Ziyada ba yarinya ba ce, tunda har ita da kanta ta yanke shawarar ta gama zaman aure da shi to lallai haƙura da al’amarin shi ya fi. Yara Allah yayi musu albarka.”
Duk da tarin harkokin da suke gabanshi haka ya katse komai yayi musu booking ɗin jirgi zuwa Kaduna shi da Aunty Ruƙayya. Basu nemi Khamis kai tsaye ba, gidan Abba Yusuf suka nufa yayi musu tarba ta mutunci da girmamawa.
Ko da suka natsa suka sanar da shi abinda ke tafe da su bai katse musu hanzari ba. Sai dai duk yadda yakai ga ɓoye rashin jin daɗinsa abun ya gagara.
“Allah ya sani, ko kusa ban taɓa tsammanin auren Ziyada da Khamis mai ƙarewa bane a daidai irin wannan lokacin da duk su biyun ya kamata su watsar da komai su rungumi tarbiyar ƴaƴansu. To amma ako wane lokaci ina maimaita ma Ziyada ni zan kasance mai adalci ne ga lamarinta. Khamis ƙanina ne, na san duk irin miyagun abubuwan da yake aikatawa har ma da wanda ita Ziyadar bata sani ba. A zamantakewar aurensu tabbas haƙurinta shi ya kawo su har i yanzu ba tare da auren ya mutu ba. Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, Ubangiji ya haɗa kowa da rabonsa na alkhairi.”
Ya ƙarasa addu’ar tare da sanya hannu a fakaice ya ɗauke wasu ƙananun ƙwallah da suka taru a kwarmin idanunsa.
Maganganunsa, ba ƙaramin kashe ma su Aunty Ruƙayya jiki yayi ba. Amma duk da haka basu janye daga ƙudurin da ke tafe da su ba. Maganganun Yayansa ya ƙara tabbatar musu da gaskiyar halayen Khamis da Ziyada ta faɗa musu kaɗan daga ciki, in dai kuwa haka ne, rabuwar auren shi yafi alkhairi.
Ba tare da ɓata lokaci ba Abba Yusuf ya ɗaga wayarsa ya kira Khamis, yayi mishi umarnin duk inda yake yabar abinda yake yi yazo yana nemansa a gaggauce.
“Yanzu haka ina gida ne Yaya, kaina ke min ciwo. Lafiya dai ko…?”
Tun ma kafin ya ƙarasa tambayar har Yaya Yusuf ya katse wayarsa. A dole ya miƙe daga kwanciyar da yayi ya shirya jikinsa a sanyaye ya ɗau makullin motarsa ya fice daga gidan.
Kusan haka rayuwarsa ta koma, tun bayan mummunar ƙaddarar da ta afka ma Mannirah ya dawo hayyaci da nutsuwarsa daƙyar da taimakon likitoci yayi wani irin sanyi kamar ba shi ba. Duk harkokinsa ya dakatar da su, tun abokan shashancinsa na nemansa a waya yana ƙin ɗagawa har ma daga bisani ya sauke layin daga kan wayarsa.
Rayuwarsa ta koma daga gida, sai masallaci, sai Chemis ɗin abokinsa Jamilu da yanzu yake wa kallon babban Amininsa. Sai kuma lokaci bayan lokaci yana leƙawa gidan Yaya ya duba ƴaƴansa biyu. Shi yanzu bakam yayi yana jiran Ziyada ta gama fushinta ta dawo ɗakinta, tunda dai ya faɗa mata ya mayar da ita. Kawai abinda bazai iya ba shi ne tashi tun daga Kaduna har zuwa Lagos bikonta, idan ta gaji da zama don kanta za ta dawo. Abinda ya bar ma ransa kenan.
Ko da ya isa gidan Yaya, ya iske Aunty Ruƙayya da Mijinta lokaci ɗaya ya faɗaɗa fuskarsa da murmushi.
“Ziyada tana ciki ne Aunty?”
Ya jefa mata tambayar bayan gaisuwa da ya gudana a tsakaninsu. Shi duk a tsammaninsa sun dawo da Ziyada ɗakinta ne.
“A’a! Ziyada tana Lagos Khamis. Takardar sakinta muka zo karɓa…”
A zabure ya miƙe tsaye kamar wanda aka zurkuɗawa allurar bazata tun kafin ta aje numfashin maganarta.
“Saki kuma bayan na faɗa muku na mayar da ita ɗakinta?”
Ya jefa mata tambayar yana harhaɗe girar sama da ƙasa.
“To Wallahi Tallahi idan sama da ƙasa za su haɗu ba uban da ya isa yasa in rabu da matata uwar ƴaƴana.”
Ya sake faɗa a fusace yana ƙanƙance idanu cike da bala’i.
Duk yadda Alhaji Sharif mijin Aunty Ruƙayya yaso ya zauna suyi magana ta fahimtar juna ya ƙi. Sai safa da marwa yake yi yana faɗin duk munanan maganganun da suka zo bakinshi. Idanunshi a rufe, kamar bai san suwa ke gabanshi ba. Rantsuwa yake yana ƙarawa kan babu shegen da ya isa ya kashe mishi aure.
Daga ƙarshe dai haka su Aunty Ruƙayya suka fice ransu a ɓace. Cikin fushi Alhaji Sharif ya kira babban lauyansa suka yi maganganun da ya dace. Kasancewar tun farko sun shirya za suyi kwanaki uku a kaduna kafin su koma Lagos, domin Aunty Ruƙayya ta ziyarci ƴan’uwa. Washe garin ranar da safe Barr Salawuddeen lauyan Alhaji Sharif yaje har gida ya ɗauki Ziyada zuwa wani babban kotu a Lagos ta shigar da ƙarar Khamis.
Zuwa la’asar, har sammaci ya iske Khamis a ƙofar shagon Uncle Jamilu. Hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba, abu ne da bai taɓa tsammani ba ace ƙiyayyarsa a zuciyar Ziyada har yayi zurfin da za ta iya ture komai da kowa ta iya maka shi a kotu. Duk da rikicewa da yayi, sam bai saduda ba, ko a fuska bai nuna alamun nadama ba.
Kamar wani taɓaɓɓe ko zararre, nan ƙofar shagon Uncle Jamilu ya dinga sambatu yana shan alwashin ko kotun ƙoli-ƙoli za ta kai shi babu wani tsinannen Alƙali da ya isa ya raba shi da matarsa. Idan kuma akwai uban da ya isa, to su zuba su gani, shege ka fasa tsakaninshi da ita.
Gwanin ban tausayi, haka Jamilu yake ta bin shi da idanu. Duk yadda yaso Khamis ɗin ya zauna suyi magana a nutse su samu mafita amma sam ya ƙi saurarensa. A ƙarshe ma haka ya wuce fuuu da takardar sammacin a hannunsa yana zage-zage kamar mahaukaci.
Jamilu ya raka shi da idanu, baki da hanci buɗe. A zuciyarsa yake ayyana lallai in ba wani ikon Allah da tsarewarsa ba mummunan abu kaɗan ne zai ƙara faruwa da Khamis ƙwaƙwalwarsa ta samu gagarumar matsala. Ta bakin masu iya magana ne da suka ce, some-somen hauka zubda yau.
“Allah ya tsare.”
Ya ƙarasa tunanin da addu’a a fili, sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana tunanin ta inda ya kamata ya ɓullo ma al’amarin.
Cikin shagonshi ya shiga, ya zare wayarsa da take maƙale a caji ya zauna akan kujera. Sannan ya lalubo lambar Yaya Yusuf ya danna mishi kira. Maganganu suka yi mai yawa kuma na fahimtar juna a tsakaninsu, kafin suka tsayar da magana kan cewa a daren ranar idan Allah ya kaimu Yaya Yusuf zai je unguwar ya samu Uncle Jamilu su je su samu Khamis a gida.
******
Bayan doguwar nasiha da tsoratarwa haɗe da jan kunne a fakaice, sai da yaga jikinsa yayi sanyi tuɓus! Sannan Yaya Yusuf ya shigar mishi da maganar ya daure yayi ma Ziyada abinda take so ba tare da an kai ga shiga kotu ba.
A zabure ya ɗago kai yana kallon ɗan’uwan nasa, bakinsa na rawa ya ce
“Yayyyyyaaaa…. Kkkkkkana nufin in sake aikata kuskuren sakin Ziyada a karo na biyu kenan fa?”
“Ƙwarai kuwa Khamis. Amma idan ka sake sakin nata ba ina nufin aurenku ya ƙare kenan har abada ba. Kar ka manta, idan ta gama iddah hankalinta ya kwanta ta huce daga duk wani fushi da ɓacin ran da take ciki game da kai za ka iya sake shiga layin manema.”
A wannan gaɓar Uncle Jamilu ya karɓi maganar, bayan ya ɗan gyara zama ya ɗora da cewa
“Kuma a wannan lokacin da kake faɗa Yaya ina da tabbacin sai ta fi dubanshi da daraja.”
Ya mayar da kallonsa kan Khamis a tausashe ya cigaba da cewa,
“Abokina kai da kake da manyan makamai biyu na sake yaƙar zuciyar Ziyada a karo na biyu? Ko ka manta ne? Ina da labarin matsananciyar soyayyar da kuka gudanar kafin kuyi aure. A zamantakewarku ma ni shaida ne kan irin matsananciyar soyayyar da Ziyada take maka. Kuma har bayan barinta gidannan, babu wani ƙwaƙƙwaran abu guda ɗaya da ta taɓa yi maka wanda zai bayyana mana matsanancin ƙiyayyarka ƙarara a tare da ita. Sannan ƙarin makami na biyu da za kayi amfani da shi gurin yaƙo zuciyarta shi ne ƴaƴan da ke tsakaninku. Kar ka manta, iyaye mata suna da rauni sosai akan ƴaƴansu, ko yanzu don ta riga ta hau dokin zuciya ne. Idan ta huce ko su Nauwara da Mannira sun isa su karya mata zuciya ta dawo gidanka a karo na biyu. Kawai dai ka daure zuciyarka a yanzu ka bata takarda salin-alin ba tare da an kai ga tonuwar asiri ba.”
Haka dai suka taso shi gaba da lallami da nasiha in wannan ya saki wancan ya karɓa har suka samu daƙyar yana ƙwallah ya sake furta kalmar saki ɗaya ga Ziyada, ya kuma rubuta a rubuce ya miƙa ma Yaya.
Jikinsa a saɓule ya shige cikin ɗakinsa ba tare da ko sallama ya iya yi ma ɗaya daga cikinsu ba. Yaraf! Ya zube akan gado, hannayensa biyu dafe da kanshi da yake ji yana mishi wani matsanancin ciwo kamar ana buga mishi guduma. Allah ya gani, yana matuƙar son Ziyada, yana kuma son cigaba da zama da ita. Amma a wannan gaɓar ya sani dole amfani da shawarwarinsu Yaya shi ne hanya mai ɓullewa, in dai ba yana so a shiga kotu asirinshi ya tonu a idanun duniya ba.
Washe gari da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe Yaya Yusuf yaje har gidan Alhaji Sharif da ke Kaduna ya kai mishi takardar sakin Ziyada.
Da taƙaitaccen fara’a a fuskar Alhajin ya karɓi takardar ya warware ya karanta, sannan ya maida kallonshi kan Yaya Yusuf ya ce
“Ma sha Allah! Lallai yayi kyan kai. Sai muyi fatan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a tsakaninsu.”
“Amin”
Yaya Yusuf ya amsa da sanyin murya. Har yayi shiru sai kuma ya ƙara da cewa
“Idan kuma da rabon sake zama a tsakaninsu Allah ya tabbatar.”
Tsakanin Aunty Ruƙayya da ta shiga falon a lokacin, da Alhaji Sharif da yake zaune babu wanda ya samu zarafin amsa addu’arsa. Domin dai Allah ya sani Khamis ɗin ya gama fice musu arai gaba ɗaya, amma basu san me gobe za ta haifar ba.
Haka Yaya Yusuf ya fice daga gidan jikinsa a sanyaye. Allah ya sani ko kaɗan bai so rabuwar Khamis da Ziyada ba. To amma ya ya iya? Khamis ɗin shi ya ɓata rawarshi da tsalle.
*****
Bayan wannan gwagwarmaya da dagar da aka sha kuma kwanaki kaɗan tsakani Khamis ya sake ɓallo wata rigimar tsakaninshi da Yaya Yusuf. Wai yaranshi na hannun Ziyada yake so a amsar mishi, kuma yana so su Mannirah su koma Hannunshi da zama.
Shi kaɗai ya zauna yayi tunanin matuƙar yana so hankalin Ziyada yayi gaggawar juyowa gare shi to mataki na farko da zai bi shi ne ya amshe ƴaƴanshi daga hannunta. Kuma ba ma ƴaƴan hannunta kaɗai ba, har na hannun Yaya Yusuf ya kamata ya karɓe, a tunaninsa, karɓan ƴaƴan a daidai wannan lokaci shi zai sa Yaya Yusuf yayi duk mai yiwuwa wajen ganin Ziyada ta koma gidansa ko don ta kula da tarbiyar ƴaƴanta. Tunda ai tana matuƙar jin maganarsa.
Sai da Yaya Yusuf ya gama saurarensa tsaf! Sannan ya rufe idanu ya zuba mishi rashin kirkin da ya jima yana dakon yi, tun sa’adda mummunar ƙaddara ta afka ma Mannirah.
Faɗa yake kamar zai ari baki, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. A cewarshi, ina mutum mutumin banza kamar Khamis zai iya riƙe yara har biyar babu mata a gidanshi?
“Ca nake saboda sakaci da wasareren tarbiya irin taka ce kwanaki kaɗan da barin Ziyada gidanka kayi sakacin da har wannan mummunar ƙaddarar ta afka Mannira?
Idan ‘ya’yanka kake so su koma gidanka da zama, to lallai ka samu nutsattsiyar mace wacce kowa ya yarda da tarbiyarta ka aura.
Idan kun zauna na ɗan lokaci na gamsu da yanayin zamanku to zan mayar maka da ƴaƴanka gidanka. Sannan ni da kaina zan amso su Batula a hannun Ziyada in dawo maka da su gabanka, daman hakkin kula da su a kanka yake.
Idan har ba aure ka sake yi ba kuwa to lallai ka cire zancen sake zama da ƴaƴa a gabanka ba tare da uwa a tare da su ba…”
Yawwa Yaya Yusuf, Irin ku ake so. In ba Khamis da rashin godiyan Allah ba wai zai karbe yayan sa lallai.