Skip to content
Part 56 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Da maɗaukakin ɓacin rai a fuskarsa yake kallon Yaya, sai sakin zafafan numfarfashi yake yi kamar mai shirin haɗiyar zuciya. Yadda kasan zai fashe da kuka haka ƙirjinshi ke hawa da sauka, muryarshi na rawa saboda ɓacin rai ya ce,

“Yanzu Yaya saboda Allah me kake nufi da maganganunka? Kai da kanka kake min zancen in nemo wata matar in aura bayan ka san abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba? Na zaci kai da Jamilu kuka tsara zantuttukan da sukai tasiri a zuciyata na sallami Ziyada? So kake inyi ta zama cikin ƙunci da kaɗaici sai ka ce wani marar galihu? Ƴaƴan da zan dinga gani suna ɗebe min kewa kafin mahaifiyarsu ta gama fushi ta dawo su ma kana neman haramta min riƙonsu?”

Da halin ko in kula Yaya Yusuf ya taɓe baki, alamun duk maganganun Khamis basu shige shi ba. Don ma ya ƙara tabbatar mishi da hakan sai cewa yayi,

“Ai kuma sai kayi Khamis. Waɗannan tambayoyin da ka jero min duk matsalolinka ne ba tawa ba. Ni dai na riga na gama magana. Shawara ce ta hanyar da za ka bi ƴaƴanka su koma gabanka na baka kyauta, ruwanka ne ka ɗauka, ruwanka ne karka ɗauka duk matsalarka ce.

Sannan ina mai ƙara jaddada maka, kayi taka-tsantsan da ni Wallahi Khamis. Kada ka ɗauka wai wasa nake maka da nace zan saka idanu ƙwarai aduk takunka da motsinka. Ruwanka ne ka cigaba da zama a mutumin ƙwarai kamar yadda ka fara bayan afkuwar waɗannan munanan ƙaddarorin da ko a mugun mafarki ba na ƙaunar tuna su.

Ruwanka ne ka canza hanya ka koma ruwa tsundum! Amma ina rantse maka da girman Allah mummunan motsi ɗaya zan gani daga gare ka wanda bai gamshe ni ba in ɗauke ka can-cak in miƙa ka gidan gyaran hali na Boska. Idan baka san ina ne ba kaje ka binciki tarihinsu ka gani, gagararrun yara da magidanta tsaf suke musu wankin ƙwaƙwalwa, zuciya da gaɓɓan jiki su zama mutanen kirki a cikin ƙanƙanin lokaci. Ɓace min da gani, mutumin banza kawai, wanda ya girma ya gama kama shi ta ko wane ɓangare amma har yau bai san ya girma ba.”

Haka ya fice fuuuu cike da matsanancin ɓacin rai da baƙin ciki kamar zai tashi sama. Ko kafin mai gadi ya gama wangale mishi get har ya finciki motar da wani mahaukacin gudu, ƙiris ya rage ya mutsuke ƙafafun mai gadin Allah ya taimaka yayi sufa ya dira can gefe ɗaya hannayensa biyu ɗore a kai idanu warwaje, ko kallon tsiya bai samu daga Khamis ba ya fice daga gidan da mahaukacin gudu.

“Allah ya kiyaye mai ƙararren kwana. Mummunar Tsautsayi da asara ya Allah ka kare bayinka talakawa.”

Mai gadi yayi addu’ar a fili hankalinsa a tashe, har lokacin bai samu zarafin sauke hannuwa daga kansa ba. Ƙirjinsa sai bugawa yake yi fafafat! Ya daɗe a cikin wannan yanayin kafin ya miƙe daƙyar ya maida ƙofar gef ɗin ya rufe. Zuciyarsa cike da tunanin yau in da Allah ya ƙaddara Khamis ya bi da mota ta kan ƙafafunshi da ya zaiyi? Ko an kaishi asibiti dai an riga an cuce shi.

A ɓangaren Khamis kuwa bai ma san me yayi ba, yana tuƙa mota yana jan tsaki da ƙwafa akai-akai. Sai a wannan lokacin wani matsanancin tsanar Ziyada da masifaffen haushinta ya turnuƙe zuciyarsa.

A ganinsa duk wannan bala’in ita ta jefa shi a ciki. Da ace ta yi haƙuri ta zauna ko da yaje da Nana Bilkisu cikin gidan, da duk wannan masifar bai afka ma zuri’arsu ba.

Sai kuma ya watsar da zancen Ziyada ya fara jujjuya maganganun Yaya Yusuf a ranshi, a fili yake shan alwashin matuƙar ba Ziyada bace za ta dawo a matsayin matar aurenshi to fa shi da aure sunyi hannun riga haihata-haihata.

Babu Ziyada, Nana Bilkisu da yaso kamar ranshi zai fita ita ma babu ita, bai ma san a wace duniya take a halin yanzu ba. Ai kuwa shi da mace sai dai a haɗu a huta ya kashe ƙishin ruwanshi, amma zancen aure babu har gaban abada idan akwai.

Shi a karan kanshi ya sani sarai babu wata ƴa mace da za ta iya haƙurin zama da shi irin zaman da Ziyada tayi da shi. A wannan zamani dai yasan da ƙyar ne ya samu kwatan-kwacin mai iya ko da rabin haƙurin Ziyada. To kuwa me zai kai shi janyo ma kanshi wata matar ya tona ma kanshi asiri?

Ire-iren tunanikan da yayi tayi kenan tare da shan alwashin komawa ruwa tsundum na halayenshi. Tunda dai ya riga yayi biyu babu ko ɗaya, to fa lallai bai kamata ya bari ya sake rasa ɗaya su zama uku ba. Rayuwa ce har yanzu da sauran ƙuruciyarsa tunda har yanzu bai cike arba’in a duniya ba. To bature ma ai cewa yayi rayuwa tana farawa ne daga shekaru arba’in, don haka zai ƙara zage dantse ne ya mori ƙuruciyarsa sosai ya tsikari duniya da tsinke har zuwa sadda tsufa zai mishi sallama sannan ya watsar da komai ya koma ga Allah yayi ta istigfari. Allah mai gafara ne mai jin ƙan bayinsa.

Daman abu biyu ke ɗan saka mishi waigi, na ɗaya matarsa Ziyada, na biyu ƴaƴansa. To yanzu duk basa nan, holewa da raƙashewa ai sai abinda yayi gaba. Da waɗannan tunane-tunanen ya ƙarasa gidan Big Aunty wacce ya shafe watanni masu yawa bai waiwayeta ba.

Kuma da yake Khamis yana cikin yaranta maza da take matuƙar ji da su domin yana mata hanyar samun manyan kuɗaɗe ko da ya faɗa mata sabbin zubi yake so, don yana cikin ɓacin rai da ƙunci. Ba tare da ɓata lokaci ba ta haɗa shi da wasu ƙananun ƴan mata da basu wuce sha bakwai-bakwai ba, ya kwashe su suka nufi masaukin baƙi. Kwana yayi yana kashe ƙishin ruwansa da su.

A cewarsa, ya same su fiye da yadda yayi tsammani, don haka shi da kanshi ya shirya musu sakayya da karo ɗaya yanke talauci. Ko kafin gari ya gama wayewa har ya haɗa musu wani babban connection da wani mashahurin ɗan siyasa, tun a mota yayi ta jaddada musu in dai suka saki jikinsu ya su samo rabon da zai wanke duk wani dauɗar talauci da yake tare da su.

Haka suka rabu suna ta mishi godiya kamar za su kwanta mishi.

******

Ingantaccen hadithi ne na fiyayyen halitta SAW yake cewa lallai shaiɗan yana zagayawa a jikin ɗanAdam kamar yadda jini yake zagayawa a jikinsa.

A cikin kwanaki ƙalilan, duk wani ɓurɓurin shiriya da ya fara bin jikin Khamis ya kama gabansa. Bin mata da kawalcinsu babu abinda ya ragu, sai ma ƙaruwa da yayi ninkin ba ninkin.

Abu ɗaya dai da baya yi tun Ziyada da yaranshi na nan har yanzu bai fara ba shi ne kai ƴanmata gidanshi ya hole da su. Amma fa hotels hotels da mai tsada da mai arha babu wanda bai sani ba a faɗin garin kaduna. Kwalliya, tsafta, da gayunsa ya ƙaru fiye da da, babu wanda zai ga Khamis ya ce shi ne mahaifin su Batula ma balle har a kalli Nauwara da Mannira a jingina mishi su a matsayin ƴaƴa saboda tsabar sanin sirrin gyaran jiki da yayi.

*****

Lallai ita zuciya ako wane lokaci ta kasance tana umarni ne da mummunar aiki. Amma a yayin da bawa yayi ƙoƙarin fin ƙarfin zuciyar, yayi matuƙar dauriya gurin yaƙar shaiɗanin da ke tattare da shi, ya nisanci shaiɗanun mutane, ya zama ako wane lokaci yana mu’amala da mutanen kirki. To tabbas zuciyarsa za ta tsarkaka, za ta rabauta daga saƙe-saƙen ɓarna da son aikata miyagun aiki. Zuciyar bawa za ta gyaru, dukkan jiki zai gyaru kamar yadda yazo a cikin ingantaccen Hadithi na fiyayyen halitta SAW.

Kamar dai haka ne ya kasance da Samira wacce yawon bariki yasa aka yi mata laƙabi da kankana. Da fari, shiryuwar da tayi ba don Allah da Annabi bane, sanadiyyar fin ƙarfinta da aka yi da kuma maganin da ake bata ne yasa ta ƙyamaci duk miyagun ayyukan da take aikatawa.

Amma sannu a hankali da yawan nasiha, kyakkyawan mu’amala daga mahaifiyarta, janta a jiki sosai daga ƴa zuwa kamar matsayin ƙawa kuma abokiyar shawara, biya mata buƙatunta daidai gwargwado da bai sha ƙarfin mahaifiyarta ba. Kyakkyawar mu’amala daga ƙannenta da a baya suke yi mata kallon tsoro ko kuma wata dodo yasa zuciyarta ta fara yin laushi sosai.

Umma ta kasance macece mai yawan ibada da miƙa al’amuranta ga Allah! Shi yasa sannu a hankali komai ke zuwa mata a sauƙaƙe. Na daga cikin shawarwarin da mai magani ya bata shi ne yawan jan Samira a jiki. Da kiyaye yawan tunatar da ita mummunan rayuwar da tayi a baya, a dinga ƙoƙarin nuna mata ba wani babban abu bane in dai za ta tuba. Lallai Allah mai gafara ne ga bayinsa matuƙar bawa zai yi tsarkakken tuba. A dinga kawo misalan mata da yawa da suka aikata mummunan abu fiye da nata, amma da suka tuba, kuma suka yi haƙuri da kaɗan ɗin da suka fara samu sannu a hankali sun samu ci gaba da ɗaukakar da basu taɓa tsammani ba.

Duk waɗannan matakan Umma ta bi su, har ma da waɗanda bai ambata mata ba. Na daga cikin matakan da ta bi don jan Samira a jikinta shi ne komawa ɗakin Samira da kwana, duk daren duniya ƙarfe huɗu na dare za ta tashi Samirar daga barci, da tausasan kalamai take cewa,

“Daure ki tashi Yayansu. A daidai wannan lokacin har zuwa ketowar alfijir Allah da kanshi yake sakkowa sama yana cewa ina bayi na masu buƙata in biya musu? Ina bayi na masu damuwa in yaye musu? Ina bayi na masu neman gafara in yafe musu? Da waɗannan dalilan kin ga barci bai kamace mu a irin wannan lokacin ba. Daure ki tashi kiyi nafila ko raka’a huɗu, idan kin idar sai kiyi ta istigfari, kiyi karatun Alƙur’ani ko sumuni ɗaya, gaf da kiran sallan farko sai kiyi ma Allah kirari da tsarkakan sunayensa, ki nemi gafaran zunubanki ki miƙa ƙoƙon buƙatunki. Ko ke ba ki da matsalar komai a rayuwarki?”

A sanyaye take gyaɗa kai alamar A’a!

Tun tana tashi daƙyar tayi alwala tayi sallar tana gyangyaɗi. Sannu a hankali har ibadar ya kama jikinta, Umma na tashinta za ta tashi ba tare da nauyin barci ko ƙuncin zuciya ba. Har aka kai matakin da a wasu lokutan ma ita take fara tashi kafin Umma ta tashi.

A zaman istibra’in da tayi na tsawon watanni uku ko sau ɗaya Isiya bai ziyarce ta ba. Kuma daman babu waya a hannunta balle ya kira ta. Sama ko ƙasa ta nemi wayoyinta guda biyu ta rasa, kuma ko da tayi cigiya Umma bata amsa mata da wani gamsasshen amsa na inda wayoyin suke ba. Duk iya bincikenta kuma bata ga inda Umma ta ɓoye ba, tun tana naci da baƙin rai har ta gaji ta fawwala ma Allah. Sannu a hankali ma har ta saba da rashin wayoyin, kuma tana jin daɗin rayuwarta a haka ba tare da wani takura ko ɓacin rai ba.

A ranar da ta gama Istibra’i, a ranar Isiya ya aike mata da kayayyakin buƙatu na kwalliya da ƙamshi masu kyau da matsakaicin farashi. Amma shi bai je ba.

Da farko yadda iyayen suka shirya bayan gama Istibra’i da sati biyu za’a ɗaura musu aure. Saboda an gama binciken lafiyar Samira da Isiya babu wani ƙwaƙƙwaran lalura daga ɓangarenta ko nashi da zai kawo tarnaƙi gurin kasancewarsu ma’aurata.

Gaf da za ta gama Istibra’i Umma ta nemi al’farma a ɗaga lokacin bikin zuwa bayan gama Istibra’inta da kwanaki arba’in sai a ɗaura auren.

Jikin ƙanin mahaifinsu a sanyaye yake cewa ga Umma.

“Ummansu, bakya tsoron wani mummunan lamari da ba’a fata ya gitta a gagara ɗaura auren? Me zai hana a ɗaura auren in yaso daga baya kun gama duk shirye-shiryen da za kuyi sai ta tare…”

“Babu abinda zai faru sai alkhairi in Allah ya yarda Baffansu.”
Ta katse shi da sauri, fuskarta da ɗan taƙaitaccen murmushi. Kafin yayi magana ta ƙara da cewa,

“Kayi haƙuri, mu bar maganar auren zuwa kwanaki arba’in ɗin. In Allah ya yarda jinkirin zai zama alkhairi.”

“To shi kenan. Allah yasa haka.”

“Amin.”

Haka nan yayi mata sallama ya fice daga gidan ba don ranshi ya so al’amarin jinkirta auren daga ranar da aka sanya tun da farko ba. To amma ya zaiyi? A shaidar da yayi ma Umma ya san da gangar baza tayi abinda zai rusa maganar auren ba. Tunda tun farko tsarinta ne komai ya tafi yadda basuyi zato ba, ita ɗin jajurtacciyar mace ce da tayi tsayuwar daka akan tarbiyar ƴaƴanta tun kafin ɓacewar ɗan’uwansa.

Idan basu yaba mata ba, to fa babbar rashin adalci da zalunci ne zai sa su zage ta. Duk irin rayuwar da Samira ke gudanarwa tun ɗan’uwansu na nan suna da labari amma basu taɓa tsawatarwa ko yunƙurin aikata wani abu da zai girgiza duniyar shaiɗancin Samirar ba.

Balle kuma bayan ɓacewar ɗan’uwansu da rashin zumunci da gudun wahala yasa suka ƙara janye jikinsu gaba ɗaya don ma kada Umman tayi kuskuren tunkararsu da wani matsala ko buƙatar yau da gobe. A yanzu kuwa dole su ɗaga mata ƙafa matuƙar ba so suke duniya ta zage su ba.

****

Hajja Falmata ƙwararriyar macece da tayi suna ta shahara sosai a ɓangaren gyaran jikin Amare da zawarawa. A bayan gyaran jikin ma, wayayyiyar mace ce ta ga jiya taga yau a rayuwar duniya, shi yasa a gidanta har councelling na mata take yi akan yadda za su tafiyar da rayuwarsu. Waɗanda suka mu’amalanceta ko suka taɓa harka da ita sun shaide ta akan sanin sirrin zaman duniya, mata da yawa sunyi ittifaki in dai kika kaiwa Hajja Falmata kuka akan matsalar rayuwa musamman ta zamantakewar aure, za ta baki kyawawan shawarwarin da sannu a hankali in dai kika bi su kuma kika yi aiki da su tabbas za ki cimma hanya mai ɓullewa.

A ɓangaren gyaran jiki kuwa kafin komai sai ta girka amarya ko bazawara da magungunan sanyi masu kyawun gaske, sai ta fatattaki sanyi a jikin mace kafin duk wani gyara ko shan magani ya biyo baya.

Kuma aikinta ƙaramin shi ne na sati ɗaya, sati biyu, uku, har zuwa sati huɗu amare da zawarawa na yi a gidanta. Domin babban gida take da shi da ma’aikata da komai, kuma wani abin burgewa shi ne mijinta babban malami ne kuma limamin babban masallaci a cikin garin kaduna. A taƙaice dai harkokinta tafe yake kan tsarin addinin musulunci.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 55Lokaci 57 >>

1 thought on “Lokaci 56”

  1. Oh oh Khamisu wannan jaraban ina zaka da shi?? Allah ya shirya
    Samira kuwa na ji dadin yadda komi na tafiya dai dai

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×