Skip to content
Part 57 of 67 in the Series Lokaci by Fareeda Abdallah

Har gida aka kai ma Umma labarinta. Abu ɗaya da yaso sanyayar mata da jiki shi ne jin aikin Hajja Falmata da tsada, domin sati ɗaya kacal a sauƙaƙe tana karɓan naira dubu arba’in ne. Amma jin irin kyawun ayyukan da take yi, da turbar shawarwarin zaman aure da iya gogayya ako wace kalar rayuwa ta zaman duniya yasa zuciyar Umma kwaɗaituwa da aikin.

Ba tare da sanin Samira ba ta saida duk ɗan tanadinta na auren ta biya kuɗin aikin gyaran jiki a gurin Hajja Falmata na sati huɗu, a sauƙaƙe ta biya dubu ɗari da hamsin bayan ta kora ma Hajja Falmata duk irin rayuwar da Samira tayi a baya da kuma halin da suke ciki a yanzu.

Wannan shi ne babban dalilin da yasa ta nemi a ɗaga batun auren. Kafin tafiyar Samiran da kanta ta aika aka kira mata Isiya, yazo har gida a ɗarare cikin jin kunya suka yi maganganu masu muhimmanci, sannan Umma ta shiga ciki ta tura mishi Samira.

Kamar baƙin juna, haka suka kasance. Sun kasa yin wata tsayayyiyar magana a tsakaninsu bayan gaisuwa, sai dai a fakaice lokaci bayan lokaci suke satar kallon juna su sakarwa juna murmushi.

Ko don Samirar ta daɗe bata ganshi bane ko kuma laushi ne da zuciyarta yayi oho! A idanunta sai take mishi kallon kamar ba wannan Isiyan da take mishi kallon rashin wayewa a baya ba. A yanzu wani kyakkyawan matashi take kallo a gabanta cikin kyakkyawar shiga ta shadda mai matsakaicin kuɗi da sabuwar hula da takalmi. Mai kwarjinin da in dai mace ba girman kai ta ɗora ma kanta ba babu inda baza ta shiga da shi a matsayin mijin aurenta ba.

A haka suka cinye mintuna talatin ɗin da Umma ta basu, ko da ya tashi tafiya ya karkace ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu biyar ya miƙa mata ƙin karɓa tayi.
“Na gode ƙwarai, Allah ya ƙara ma arziki albarka. Amma don Allah ka bar kuɗinka. Ka ga akwai hidima mai yawa a gaba duk da ba na so ka wahalar min da kanka.”

Kalaman da ta faɗa mishi kenan da taushin murya kuma a kunyace, ko kafin yace wani abu ta nufi hanyar fita tana cewa,

“Allah ya mayar min da kai gida lafiya Mijina. A gaida su Mamanmu.”

Wayyo Allah na… daɗi kashe Isiya mana… daman can duk miyagun halayen Samirar kwance take malala a zuciyarshi. Irin gwaggwaɓar canjin da ya gani yau a tare da ita yasa shi jin soyayyarta ya ƙara ninkuwa ninkin ba ninkin a zuciyarsa. Daƙyar ya iya ficewa daga zauren gidan shi kaɗai yake ta sakarwa kansa lallausan murmushi bayan ya ba ƙaninta kuɗin da ta ƙi karɓa an shige mata da shi cikin gida.

A daren ranar kuma ya aika mata da waya mai matsakaicin kuɗi ƙwarai da layin kira a ciki. Ko da ta duba wayar, akwai lambobinsa guda biyu a ciki yayi mata saving da Isiya.

Da murmushin farin ciki da ƙaunarsa a fuskarta ta canja sunayen daga yadda ya rubuta, ɗaya ta maida shi ‘Mijina’ ɗaya kuma ‘Jagora abin alfahari’

Ko da ta duba account balance ɗin sabon layin nata, ya zuba mata kati har na dubu biyu. Don haka ba tare da ɓata lokaci ba ta shige ɗaki ta danna ma lambarshi kira, abinku da wacce ta daɗe da sanin sirrin yadda ake tafi da zuciyar ɗa namiji, kuma ta haɗu da sabon shiga wanda bai taɓa faɗawa a tarkon kowa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ta ƙara rikirkita zuciyar bawan Allah da zaƙaƙan kalamai.

Faɗi yake a fili,

“Don Allah Matata ki bar ni haka… kar ki hana bawan Allah barci cikin nutsuwa alhalin ke kina gida kina barci hankali kwance.”

Wata dariyar sakalci mai cike da jan hankali ta sakar mishi a kunnuwansa kafin ta katse kiran. Duk da haka bata ƙyale shi ba, sai da ta aika mishi da zafafan saƙonni guda biyu, ɗaya cike da kalaman soyayya tana ƙara jaddada mishi yadda take ƙaunarshi a zuciyarta. Ɗaya saƙon kuma cike da fatan alkhairi da kyawawan addu’o’in Allah ya ɗaukake shi ya kare mata shi daga sharrin maƙiya da mahassada.

A ɓangarensa zuciyarsa tumbatse da farin ciki yake amsa addu’ar a fili yana dariya kamar sabon kamu.

Maza biyu da suke zaune a ƙofar shagonsa suka kalle shi suka tuntsure da dariya haɗe da tafawa.

Firgigit! Ya dawo da hankalinshi yana kallonsu da tambayar lafiya.

“Ka san Allah? Ka bi a hankali, idan ba haka ba tun kafin ayi auren za ka fara sambatu kana kiran Matata Samira…”
Suka sake kwashewa da dariya.

Shi kuwa a kunyace ya saki murmushi yana sosa ƙeya, a zuciyarsa yake ƙara tabbatar da gaskiyar maganarsu. Shi yasa duk ya ƙosa ayi auren ko zai samu nutsuwa da kwanciyar hankali, don har yanzu a tsorace yake, duk gani yake kamar ba da gaske Samira tana ƙaunarshi kuma da kanta ta amince za ta aure shi. Tsoron shi Allah, tsoronshi wata rana ta canja ra’ayi.

*****

Bayan sati huɗu. Umma ta tabbatar bata biya kuɗin gyaran jikin Samira a banza ba. Da gaskiyar bahaushe da yace ko kana da kyau ka ƙara da wanka, eh lallai ga Samirarta da ta fara yamushewa saboda yawon banza bayan kyawu na musamman da aka tsatso a jikinta an ƙara mata da wani kwarjini na musamman.

A taƙaice dai, Samirar kamar an canja ta ne gaba ɗaya. Ba kyawun da tayi a jiki da fuska kaɗai ba, hatta yanayin maganarta ya canja. Ya koma a sanyaye kuma a tausashe sosai cike da nutsuwa, ga wani ƙasaita na musamman da ke fita cikin ko wace saɗara na maganganunta kamar wata ƴar sarauta.

Ita kanta Samirar, farin ciki da murna ya gagara ɓoyuwa a fuskarta. Minti ɗaya biyu za ta kalli Umma ta sakar mata lallausan murmushi,

“Na gode ƙwarai Ummata. Allah ya saka miki da aljannah mai maɗaukakiyar daraja. Haƙiƙa zuwa na gidan Hajiyar nan na ƙaru da ilmummuka na zaman rayuwar duniya da sirrin riƙe miji irin waɗanda ban taɓa cin karo da su ba. In Allah ya yarda bazan taɓa baki kunya ba.”

Maganganun da take ta yawan maimaita ma Ummanta kenan bayan dawowarta.

Ango da yazo shi kanshi ya kasa daina kallon amaryar tashi saboda tsabar mamakin canjin da ya gani a tare da ita.

“Ummm na ce ba? Wai wankan inji ne aka dinga miki acan gidan ko me aka yi miki? Kin ga yadda kika canja gaba ɗaya kuwa?”

A shagwaɓe ta ɗan kumbura bakinta zuwa gaba tana kallon cikin idanunsa, sai wani mar-mar take yi da gashin ido kamar za ta saka kuka.

“Ban yi kyau ba ko?”
Ta jefa mishi tambayar a shagwaɓe.

“A’a! Kawai dai kyau yayi kaɗan wajen bayyana ainihin yadda kika koma Matata. Wallahi kin fi kyau kyau, kin ƙara kwarjini da cika ido na musamman kamar wata sarauniya…”

“To ai daman Sarauniya ce, amma sarauniyar ba ta kowa bace sai ta Sarkinta Is’haƙ, jagorana… mijina… Abin alfaharin zuciyata…”

A tare su biyun suka sakarwa juna murmushi.

*****

Takanas-ta kano Umma ta ɗauki ƙanwarta da tazo bikin Samira tun daga Maraɗi suka je gidan Hajja Falmata domin sake yi mata godiya.

“Babu komai Maman Samira. Ai ɗa na kowa ne. Fatanmu Ubangiji Allah yasa ta shiga ɗakin mijinta a sa’a ya basu zaman lafiya.”
Amsar da Hajja Falmata ta basu da fara’a sosai a fuskarta.

Ko da suka tashi tafiya haka Hajjar ta haɗo su da turarukan jiki da na wuta masu kyau da daɗin ƙamshi irin nasu na ƴan Maiduguri. A matsayin gudummuwarta, ta kuma alƙarwarta musu in Allah ya yarda ana gobe biki da aka shirya za’ayi walima za ta tura yaranta su shirya amarya, ranar ɗaura aure kuma da kanta za ta dakatar da komai taje ta shirya Samirar.

Haka suka baro gidan farin ciki kan farin ciki na dukansu.

Umma marainiya ce gaba da baya, tun da daɗewa Allah yayi ma iyayenta rasuwa. Sannan familynsu ba masu yawan dangi bane sosai, duk da haka ƴan’uwanta sunyi mata kara fiye da yadda tayi tsammani.

Filin ta guda ɗaya da ta siya tun da daɗewa ba tare da sanin mahaifin Samira ba tasa a kasuwa. Babban burinta tayi ma Samiran kayan ɗaki masu kyau na matsakaitan kuɗi, domin ƙanwarta ta je har gidansu Isiya da a yanzu Samira ke kira Yaya Ishaƙ ta duba ɗakunan da aka gina don saka Amarya.

Da yake gidan akwai fili sosai a ciki mahaifinshi ya yanka mishi wadatacce, cikin ƙanƙanin lokaci da taimakon ƴan’uwansa da duk sun fi shi ƙarfi aka tayar mishi da ginin self content. Ɗaki da falo da bayi da kicin duk a haɗe, kuma babu laifi ɗakunan wadatattu ne masu girma. Sannan aka zagaye ɓangaren ta yadda Amarya za tayi harkokinta ba tare da sa’idon iyayen miji ba.

Ana tsaka da cinikin filin Umma an kasa samun kyakkyawan farashi sai ga Rahma da Mijinta Salim kamar daga sama, ba zuwansu ne abin farin ciki da mamaki ba, irin gwaggwaɓar kaɓakin arzikin da Rahma tazo musu da shi shi ne abin farin ciki.

Ba tare da ɓata lokaci ba ko nauyin ciki ɗan watanni biyar da ke jikin Rahma ta buƙaci a raka ta inda za’a ajiye aminiyarta. Tare suka tafi da Inna Fatume, ƙanwar Umma, Da Iyallu da tsananin jin daɗi da hutu yake ta ƙara taka muhimmiyar rawa gurin ɓoye tsufa da shekarunta.

Suna can suna dudduba ɗakunan Inna Fatume sai ganin maza majiya ƙarfi tayi sun shigo suna auna yanayin girman ɗakunan. Ashe masu shirya kayan gida ne Salim ya turo, lallai aiki ga mai ƙare ka.

Basu jima ba suka koma gida, bakin Inna Fatume har kunne take ba Umma labarin halin da ake ciki. Ko da yamma tayi, Inna Fatume da sauran ƴan’uwa da abokan arzikin Umma suka koma ganin ɗakin so ma sha Allah.

Kayayyaki ne aka zuba ma Samira masu bala’in kyau da tsada, babu ne kawai babu a ɗakunan nan, kicin, bayi. Kaya dai kamar na ƴar gidan masu bala’in kuɗi.

Ko da labari ya iske Umma, tsananin farin ciki yasa ta kasa magana, sai hawaye ke zirara mata. Ta rungume Rahma tana yi mata godiya da saka albarka. Sannan ta kama hannun Rahma ta damƙa a cikin na Samira ta ce,

“Rahma Aminiya ce da take ƙaunarki domin Allah. Ko bayan raina, da ita kaɗai na yarje miki kiyi ƙawance. Ina roƙon Allah ya kawar da shaiɗan a tsakaninku.”

“Amin ya Allah Umma.”
Suka amsa a tare, fuskokinsu cike da murmushi.

Bayan ficewarta Samira ta kalli Rahma tayi shiru, har lokacin bata saki hannun Rahma ba. Idanunta ciccike da hawaye, babu abinda take tunani sai irin yadda a baya ta sami dama duk da dai dukiyar haramun ce amma daƙyar take iya taimakon Rahma a wulaƙance. Sannu a hankali wasu zafafan hawaye suka gangaro daga cikin idanunta
“Don Allah ki yafe min Rahma. Ke Aminiya ce ta ƙwarai, mai kyakkyawar zuciyar da take iya saka alkhairi da sharri…”

Da sauri Rahma ta toshe mata baki tun kafin ta ƙarasa faɗin abinda ke bakinta, ta hurga mata hararar wasa.

“Na zaci tun tuni mun daɗe da manta abinda ya faru a baya mun fuskanci gaba? Kuma ca nake tun ranar ƙarshe na rabuwarmu da ke a wancan lokacin na furta na yafe miki? Zan roƙe ki karo na farko kuma na ƙarshe, don Allah daga yau kar ki sake maimaita min irin waɗannan maganganun matuƙar ba so kike in nuna miki ɓacin rai na ba.”

“Angama! Zan kiyaye in sha Allah Uwargida kuma Amaryar Salim Kanta. Allah yasa ke kaɗai za ki cigaba da zama sarauniya a zuciyarsa da gidansa har abada.”

Da fara’a sosai a fuskar Rahma ta amsa addu’ar cikin jin daɗi.

“Ameen thumma Ameen ƙawalliyata.”
A tare suka yi dariya. Rahma ta buɗe za tayi magana wayar Samira ta fara ƙara alamun ana kiranta.

Da ɗan hanzari ta miƙe tsaye ta ɗakko wayar acan saman durowa, daga yadda fuskarta ya faɗaɗa da murmushi ya tabbatar ma da Rahma ango Isiya ke kira. Mamaki ne ya ƙara kama ta, a zuciyarta take ayyana lallai ruwa ya daki babban zakara. Samira ƴar gayu da gwalli da ƙwalisa da ta bala’in raina aji da ajawalin Isiya a baya wai yau ita ce teke cikin farin ciki haka don ya kira ta? Har ma take shirye-shiryen zamowa matarsa ba tare da tilastawa ba? Tuna rayuwar gaba ɗaya ba a hannunmu take ba, kuma Ubangiji shi yake jujjuya zukatanmu a tsakankanun yatsunsa yasa tayi saurin watsar da tunanin haɗe da yin istigfari.

Ta dawo da hankalinta kan Samirar a daidai lokacin da suke sallama da Isiya bayan ta bashi uzurin tana da baƙuwa, babbar Aminiyarta ta iso daga ƙasar Egypt.

“Rowar Angon ake min baza’a bani shi mu gaisa ba?”

Rahma ta faɗa tana murmushi.

“A’a wace ni, ai kin wuce haka ƙawata. Bari in sake kiranshi.”

Ko da ta kira shi, suka gaisa a mutunce da Isiya har ta mayar ma da Samira ƙare ma wayar kallo take yi. Mamaki ne ya sake kamata sosai na ganin irin ƙaramar wayar da Samirar take riƙewa. Ta kasa haƙuri ta bar zancen a ranta sai da ta ce
“Gaskiya ƙawata wannan wayar ta yi miki ƙarama da yawa, bari in kira My dear idan zai dawo ya taho miki da wata wayar ko ta 200k ce kiyi maneji…”

“A’a don Allah”
Samira ta katse ta da sauri.
“Ke kike ganin wannan wayar ta yi ƙarama. Wallahi ba ƙaramin daɗin amfani da ita nake ji ba. Don Allah ki bar ni da ita.”

Ta sake faɗa hankalinta kwance. Sai kuma ta ƙara faɗaɗa murmushi kafin ta cigaba da cewa

“Kuma ita wannan wayar da kike gani kyautar mijina ne. A ganina, akwai rashin kyautawa kawai lokaci ɗaya yaga na canja ta ba tare da saninshi ba. Don Allah ki barni da ita, idan ya samu kuɗi na san shi da kanshi zai canja min.”

Shiru Rahma tayi kamar bata gamsu ba, sai kuma can ta ce
“To shi kenan. Amma kina whatsapp da facebook?”

“A’a! Harkar social media Wallahi duk ta fice min arai. Kin ganni a hakan nan rayuwa nake cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, babu abinda ke damuna.”

“Ma sha Allah! Amma dai idan baki buɗe facebook ba ko whatsapp ya kamata ki buɗe, tunda shi iya contacts ɗin ki za kiyi chats da su, kuma akwai ajujuwa na darussa da dama da zan saka ayi adding ɗin ki. Za ki ƙaru da abubuwa da yawa na gyaran jiki da zamantakewar aurenki.”

“To shi kenan. Zan tambayi izinin Mijina, idan ya amince zan buɗe. Sai inyi miki magana…”

“Kira shi dai yanzu mu nemi izinin.”
Rahma ta katse ta da sauri.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Lokaci 56Lokaci 58 >>

1 thought on “Lokaci 57”

  1. Allah sarki Rahma mai kyakkyawan hali
    Allah ya hada mu da mutanen arziqi da zuciya mai kyau
    Allah ya sa muma mu kasan ce masu Hali da zuciya mai kyau

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×