Skip to content
Part 13 of 28 in the Series Na Kamu Da Kaunar Matacce by Fatima Dan Borno

A natse Munaya take rubuta abubuwan da za ayi na shirin bikin Anti Zuwaira. Wani abun mamaki ashe Anti Zuwaira cewa mazajen take yi, Uncle Zayyad dai yayanta ne da ya rasu. Abba da kansa ya kira mahaifin Mubaraak ya basu haƙuri akan ya janye maganar Munaya da Mubaraak.

A ranar Mubaraak kamar zai yi hauka. Hatta anti Zuwaira ta fahimci yana cikin damuwa. Tambayar duniyar nan ta yi masa ya ce mata babu komai.

Da Hajjo da Munaya da Amina aka barwa ragamar shirya bikin. A ranar da Anti Zuwaira ta ɗauki Munaya a mota suka je gidan su Zayyad taga abin mamaki. Suna nan zaune suka ga gaba ɗaya Hajiya ta fita hayyacinta. Kwanciya ta yi babu lafiya. Hakan yasa Munaya ta kasa jurewa ta ce,

“Me ya sami Hajiya ne haka?”

Suhaima ta ce,

“Tun ranar da ta shiga ɗakin Yaya Zayyad wai ta ji alamun mutum a ɗakin, sannan taga an kwashe tsofaffin kayansa an ajiye sabbi. Shikenan bata sake lafiya ba.

Zuwaira ta juyo da sauri ta dubi Hajiya. Wani irin farin ciki ya tsirga mata. Da alamun burinta yana gab da cika. Kai ta ji daɗin labarin nan. A fili kuma sai ta nuna damuwarta,

“Hajiya wannan ba komai bane face gizau. Wanda ni tuntuni yake yi mini hakan. Dan Allah kada ki saka damuwa a ranki. Ko jiya da aka kai lefena sai da na yi ta kukan rashin Zayyad. Mu yi masa addu’a kawai.”

Duk suka taru suka yi ta ƙara mata ƙarfin guiwa, har ta samu ta rage damuwar da take yi.

Shirye-shirye ya yi nisa. Yau kuma Zuwaira ta kai ziyara wurin Shugaba. Kanta a ƙasa take yi masa bayani,

“Mai girma Shugaba yau na samu abun farin ciki. A daidai lokacin da muke shirye-shiryen bikina da Gawa na huɗu, nake samun labarin Zayyad ya sake dawowa duniyar nan a karo na biyu, kamar dai yadda ka tabbatar mini da dawowarsa. Na yi farin ciki, na Gaza ɓoye farin cikina har sai da mutane da yawa suka gane.

“Ya kai mai girma Shugaba. Lokacin naɗin sarautana ya zo kenan. Ranar da na daɗe ina jira yau gashi ya zo. Ban taɓa samun labarin dawowarsa ba, kamar yadda ka faɗa sai yau. A bani umarnin abin da zan yi na gaba, domin in mallaki ƙasusuwan nan. Ina cirosu kai tsaye zan kwashe su, in kai shi China wurin sarkin sarakuna. A ranar insha Allahu za a bani kambun da zan gagari kowa.”

Tana maganar tana murmushi mai nuni da cewa tana cikin nishaɗi. Shi kuwa ya haɗa rai ya ce,

“Muna da labarin dawowar Zayyad. Sai dai shima hatsabibi ne, ya dawo ne domin ya cika wani burinsa a kanki. Ya dawo ne saboda shugabansa ya dawo da ruhinsa domin su haɗa ƙarfi su yi wani aikin, kafin daga bisani ya koma ƙabarinsa ya kwanta mu kuma mu tado shi, sannan mu kwashe ƙasusuwansa. Me ya sa kike da gaggawa ne? Kina, son sarauta kawai dan ki dinga wulakancinki yadda kika so ko? Kinsan akwai mutane masu yawa da suke ƙwadayin sarautar nan, amma kuma babu wanda ya iya kawo abubuwan da ake buƙata sai ke. Ki kwantar da hankalinki Zayyad ba zai sake wata uku a duniyar nan ba zai kammala aikinsa ya koma. Ki ƙara haƙuri, ƙila ba za ki kai shekaru ukun da na ambata maki ba.”

Ta sunkuyar da kanta ƙasa, kafin daga bisani ta yi masa Sujjada. A ƙalla ta kai mintuna uku goshinta na ƙasa. Sai da yasa abu ya shafi kanta sannan ta tashi.”

“Sarkin sarakai ya taimakeka shugaba.”

Ta juya. Da Mubaraak ta ci karo a daidai wurin fitowa daga ɗakin da ta hana kowa shiga. Bata taɓa wasa ko gigin barin makullin ba. Ta, tsorata da ganinsa a bakin ƙofar. Ya dubeta cike da mamaki,

“Me kike yi a ɗakin nan tun ɗazu? Wai me ne ne a cikin ɗakin ma?”

Yana tambayarta yana ƙoƙarin cusa kansa. Da sauri ta dakatar da shi,

“Dakata! Wannan ɗakin da kake gani, anan Yayana ya yi rayuwa har ya mutu. Babu komai a ciki sai tarkacensa. A duk ranar da na ji kewarsa nan nake shiga.”

Har cikin zuciyarsa ya gamsu. Suka juya tare.

*****

Munaya da Hajara da Amina sun shiga kasuwa sun yi siyayya. Gaba ɗaya suka fito a gajiye da nufin su tsallaka su, shiga cikin motarsu. Munaya bata an kare ba, wata mota ta kwasheta. Dukkansu suka juyo a razane, suka fasa ƙara tare da watsar da kayayyakin da ke hannunsu suka nufi in da take a kwance. Kanta ke fitar da jini, da kuma dantsen hannunta da wani abu mai kama da ƙarfi ya shige ciki. Tsananin azaba ya hanata kuka sai daman runtse idanunta take yi tana ji kamar zata mutu.
A gigice mutane suka taimaka a ka sakata a motar Hajara, domin kuwa mai motar da ya bugeta ya gudu.

Wani babban asibiti ta kaisu. Da sauri aka yanki kati sannan aka shiga da ita wurin Dokto. Gaba ɗaya ta gigice sai runtse idanu take yi saboda azaba.

Ya kama tsintsiyar hannunta yana dubawa cike da tashin hankali. Har cikin zuciyarsa yake jin tsantsar tausayinta. Ya zama dole ya yi mata allura kafin, ya yi aiki a hannun.

“Sorry…”

A take ta ji wani irin sanyi, tare da faɗuwar gaba. Dan haka ta ɗago idanunta ta kafe shi da su. Tsananin firgici da tashin hankali suka mamayeta. Tana ƙoƙarin buɗe idanu tuni ya zuba mata ruwar allurar. Ta dinga gani dishi-dishi. Daga nan bata sake sanin in da kanta yake ba. Ya yi ajiyar zuciya, daga bisani ya kira taimakon wasu nasis. Cikin ikon Allah ya gyara mata hannun da kuma kanta. Duk in da ta ji ciwo sai da ya gyara tsaf! Sannan ya koma ya zauna ya dafe kansa.

‘Yar mutan Bornonku ce.

<< Na Kamu Da Kaunar Matacce 12Na Kamu Da Kaunar Matacce 14 >>

2 thoughts on “Na Kamu Da Kaunar Matacce 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×