Shi idan yaji tana magana akan faɗan iyayenta jinta kawai yake yi, domin shi a ganin sa faɗa tsakanin mata da miji abu ne mai kyau muddin kowa a kan gaskiyar sa yake, domin kuwa haka a keyi a gidan su, hakan yasa bai taɓa mai da hankali akan hakan da take yawan faɗa masa ba. Shi dai kawai yafi mai da hankali akan rashin kulawa da basa bata da har take shiga matsala haka, ace wai iyaye su haifi ƴa amma su kasa ciyar da ita dan uwarsu. Yana jin yarinyar a ransa kamar ƙanwar. . .