Skip to content
Part 35 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Ranakun da suka rage daurin aurena da ya Safwan ƙara kusantowa suke fargaba kuma daɗa lulluɓe ni take.

Mami kam ko a jikinta ko da wasa kuma ba ta kuma ce min komai ba sau biyu tana kama ni ina share hawaye sai ta yi kamar ba ta gani ba abin da dai ta maida hankali gyara da ake min kamar ba gobe daga Haj Yar Shuwa.

Ana saura sati guda zan tafi Malumfashi in kwana biyar, sai in sauka Kaduna a ɗaura aure a taho da ni.

Daddy ya bayar da mota a ka kai ni can na iske kayan akwati da Mami ta haɗa.
Gwoggo Maryama sai gayyato abokan arzikinta har ma da makota suna gani ana ce mata yarki ta yi goshi don ko yammatan ma sai wadda ta yi sa’ar gaske za ta samu rabin haka.

Ita kam addu’o’i ta dage da su tana sadaka na Allah ya sa iyakar auren da zan yi kenan ya yanke min wahala.

Su Rahina har da shirya walima ita da yayarta ɗiyar Gwoggo ta Kano.

Ana gobe za mu tafi Kaduna kamar daga sama sai ga Zainab.

Mun yi murna ba ƙarama ba na ganin juna Samha ta yi girma sosai.

Ɗakin su Bilkisu da aka fara zama yammata gwoggo ta ce su bar mana.

Daga ni sai Zainab dare ya tsala amma ba mu da alamar barci zaune muke na girgiza kai da na ga tana rufe akwatunan auren

“Ma sha Allah Billy kin yi goshi, ga miji na nuna ma sa’a kin samu.”

Na tabe baki “Kayya Zainab ke dai, ni kuma haka Allah ya rubuta min.”

Ta dube ni da rashin fahimta “Me ya faru?

Yawan aure don shi ma wannan ga shi can ya mutu, baƙin cikina datse igiyar alaƙata da Mami da zai yi.”

Zainab ta toshe min baki “Ki zubar da mugun yawu don Allah, in sha Allah mutuwa za ta raba, ai kin jarabtu Bilkisu.

Ya Safwan mutumin kirki ne halayen shi na ƙwarai ne ina yawan jin Baba na yabon halayensa.

Me zai sa ki riƙa yi wa kanki muguwar fata.

Na share hawayen da suka taho min na kwance mata zama na gidan Mami yadda ta kasance har zuwa yau.

Na ƙare da cewa “Mutumin nan bai ce yana so na ba su suka ce sun ba shi, tunda aka yi maganar bai taɓa kallona ba wace irin rayuwa kike tunanin zan je in fuskanta?

Ki yi shiru Billy daina kuka, in sha Allah alheri ne, na yarda da son da Mami ke miki na Allah ne da ta san za ki wulaƙanta hannun ɗanta da ba za ta yarda da hadin ba.

Ki sha kuruminki mu shiga Kaduna kasuwa za mu bazama mu sayi kaya mu kuma bada ɗinkunan cikin akwatin nan, ba irin ki maza ke raina wa ba kwana nawa zai zo yana yar murya wuyarta dai ya gane ko ke wace ce, ni har na fara hango ga ki can kin riƙe shi har wuya.”

Haka muka kusa kwana Zainab tana cika ni da kalaman ƙarfafa gwiwa, zuwa safiya kuma na ji ni wasai na bar wa Allah komai.

Ɓullowar hantsi muna ta shiri za mu tafi sai ga matar Gambo.

Muka yi murnar sake haɗuwa da juna cikin mamaki na tambaye ta wanda ya faɗa mata ina garin.

Ta ce su Inna ta ji suna fadi. Na ce Inna ba tana Abuja ba ta ce ta dawo tana nan, ta faɗa min fitinar da Inna ta faɗa ita da ya’yanta sai dai su hadu su yi ta faɗa ga matar Hassan da ba su jin daɗin ta.

Na ce “Ke ma ta ce tunda na tafi ba ki raga mata, me zai sa ki ɗauki hakan? Kai ma fa ka haifa ba za ka so a yi maka haka ba.”

Ta ce “Haka ne, amma baƙin cikin abin da suka yi miki ya sa na ɗauki matakin hakan kuma tunda yaya Hassan ya auro daidai su na fita harkar su.”

Mun daɗe muna hira har sai da duk yan tafiyar suka kintsa ta yi min sallama na ba ɗanta kudi.

A Kaduna biki ya kankama A part ɗin Maman Ahmad da har ta kwashe kayanta aka yi wa su Gwoggo Maryama masauki da jama’arta sai sannan Zainab ke ce min sun rabu da Baba, a yadda suka ji don ba Baban ya faɗi musu ba ya kamata tana zuba mishi magani a abinci.

Sai kallon su Rabi’ah yammata muke suna shagalinsu ita da ƙawayenta.

Ni kam daga ni sai Zainab muke ta namu shirin wanda ƙarfafa min gwiwa take wai har da Zainab a sai min magungunan mata na ce ke wallahi sun ishe ni Mami kamar ta kashe ni da su.

Ta ce ai ta san makamin da ta riƙe shi ya sa ta yi banza da ya Safwan yana shan ƙamshin shi shi namiji.

Washegari tun hantsi muka bar gidan ni da Zainab kasuwa muka nufa sayayyar material masu kyau da tsada muka yi muka bayar da ɗinki kuma duk ita ta biya. Sai cikin kayan akwatin ta zaɓi kala sha biyar muka kai ɗinki wurin gwanaye.

Da muka bayar muka tafi da zummar washegari za su kawo gida.

Wani Boutique muka wuce sakin baki na yi ina kallon Zainab irin kayan da take zaɓe da ta gama kuma ta kira Najib yana ɗagawa abin da ya fara ce mata “An ce baby ta zo ko?

Ta gwalo ido “Gobe fa daurin auren ta ya Najib.”

Ya ce “To sai me? Na shigo an ce min kun fita.”

E ya Najib ga mu nan a Ibrahim Taiwo.”
Ya ce “Ku jira ni ina kusa da wurin.

Ta sauke wayar tana duba na “Allah ya kawo mai biyan kuɗin kuɗaɗena sun huta.
Ta hango wata riga ta tashi ta tafi wurin, ba a yi minti goma ba ya ƙaraso tana ganin ya shigo ta je ta taro shi suka iso inda nake zaune na gaji ga kiran da ake ta mana mu dawo za a yi min wankan lalle ni da Rabi’ah.

Kaina ya tsaya “Da ke za a haɗu a yi min abin da aka yi min ko?

Na daga kai muka haɗa ido “Fushi nake da ke baby.”

Na ce “Fushin me? “Ga ni Baba ya hana ni ya ba wani ke? Kuma ki share ni ki manta son da nake miki.”

Shiru na mishi muna kallon juna ganin ba shi da niyyar kauda idon shi na sunkuyar da kaina Zainab ta ce “Ka yi haƙuri ya Najib.”

Ya naɗe hannayensa a ƙirji yana min kallon nan nasa “Kun gama ne? Zainab ta ba shi amsa da cewa “E ya Najib mun gama kuɗin dai ne ba mu biya ba.”

Ya ce “To ku biya ku same ni mota.”

Har ya juya ta ce “A ya Najib ka tafi kuma ba ka biya ba.”

Ya harari kayan “Ta wuce ita aka saya ma kayan da za ta sanya ma wani ba zan biya ba.”

Ta ce “Yi hakuri ya Najib.” Atm ɗinsa ya miƙa mata tare da faɗa mata pin ɗin ta je ta biya. Shi ya kaimu gida bayan mun biya mun dauko Amir.

Matar Najib tsohon ciki na gan ta da shi.

Dangin Daddy da Mami sun zo ɗaurin aure ana ta nuna musu ni don tambayar da suke. Sai ga Abu ma yayar Aminu ta zo har da Maman Aminun da matar wan shi

Da daddare an tafi kai Rabi’ah Baba ya kira mu ni da Gwoggo gudunmawarta ta ba shi ya yi mata bayanin ba yanzu zan tare ba don gidan da zai sanya ni yana gyare-gyare zan zauna gidan Mami sai ya kammala a yi tarewar biki.
Ya sa min albarka tare da addu’ar Allah ya albarkaci aurena.

Sai da aka gama yinin bikin Rabi’ah wadanda suka zo tare da Gwoggo suka tafi gida tare da sha tara ta arzikin da Daddy da Baba suka yi musu.

Mun dawo gidan Rabi’ah Zainab ta ce zo ki ga hotunan angonki ki ga irin kyan da ya yi. Na yi saurin kauda fuskata ina faɗin “Da ma ya zo ne?

Ta ce “Me kike nufi? Na ce “Su Daddy dai sun matsa mishi.”

Ta ɓata fuska ” Wai saboda Allah me ya sa kike haka?

Na murguɗa baki “To wace amaryar da ake so kika ga ana yi wa haka?

Ta harare ni “Ki faɗi alheri ko ki yi shiru na gaya miki.”

Na ce “Na yi.

Mutum huɗu ne masu min rakiya Gwoggo Maryama sai Maman su Zainab sai Zainab ɗin kanta sai matar Baba Ali ƙanen Baba.

Tarba mai kyau muka samu wurin Mami da sauran yan’uwanta da ba su tafi ba.

Na ja Zainab ɗakina muka yi ta hirar mu.
Kwana ɗaya suka yi suka juya, baƙin da suka yi saura ma suka tafi aka bar mu daga ni sai Mami.

Ban ga kuma ya Safwan ba don da na daidaici lokacin shigowar shi nake shigewa ɗaki, har sai da na yi kwana uku da daddare ina kwance wata yar ajinmu ta kira ni tana min tsiyar an ce musu na yi aure shi ne ban fadi ma kowa ba, haƙuri na ba ta da cewar abin ne ya faɗo ba shiri, na tambaye ta an fara karatu don mun koma ta ce ba a yin komai amma dai yau da safe Madam
Sanga ta shigo wai za ta yi test.

Na gwalo ido “Ta yi?

Ta kwashe da dariya “Ba ta yi ba amarya.”

Na ja ajiyar zuciya “Gobe in sha Allah zan shigo.”

Muka yi sallama.

Da safe kuwa da na tashi shiri na fara sai da na fito na karya na koma ɗaki sanya dogon hijab na ɗauki jakata.

Ina fitowa falo gabana ya fadi ganin ya Sadauki zaune na kauda kaina na ce wa Mami.

“Sai na dawo Mami.”

Ta ce “A dawo lfy.

“Ke koma ciki.”

Muryar ya Sadauki da na ji ta sa gabana bugawa na tsaya cak ban juyo ba a “Ya haka kuma makaranta fa za ta ka ce ta dawo.”

E Mami ta dawo wa ta tambaya da za ta tafi?
Mami ta kasa cewa komai don mamakin da ya lulluɓe ta wai a gaban ta Sadauki ke wannan abu.
Kuncinta kawai ta dafe har na juya zan koma dakin wayata da ke cikin jaka ta ɗauki ƙara
ya ce cikin dakewa “Wa ya ba yarinyar nan waya Mami?

Ta ce “Ban sani ba ubana.”

Ni dai na wuce su na koma dakin cike da jin haushin wannan gadara.

Da rana na kira Ruƙayya Babangida ta ce min ba a yi komai ba.

Da daddare ina daki na ji shigowar shi Afnan na gefena tana barci.

Na ajiye wayata na gyara kwanciya na fara lumshe ido kiran Mami ya shigo ta ce in fito in same ta na zumbula hijab na fita tun daga nesa na hango su shi da Aunty Farha gaba na na ji ya buga sakewar da na saba yi da ita sai na ji na kasa, cikin fara’a ta taso ta ruƙo ni muka zauna tare ta dubi Mami “Don Allah Mami za mu tafi da Nana, idan Dear ya fita gidan isa ta yake ga Afnan tana nan.

Mami ta jinjina lamarin “Ya za a yi ta bi ki gidanki Farha? Ai ba a yin haka.”

“A’a Mami ni fa Nana ƙanwata ce don Allah ki bar mu mu tafi.”

Ta ce “Ba a yi bikin tarewa ba ɗaura aure kawai akai.”

Ta marairaice “Ai an kusa gama aikin Mami duka kwana nawa ya rage ki ba mu abar mu?

“To ni abin ya fi karfina bari in faɗa wa Daddy sai ki shiga ki tambaye shi.”

Ta miƙe ta haura sama tsalam ta mike daga wurin zamanta ta zauna masangalin kujerar da yake zaune yana latsa wayarsa kai ba ka cewa ma ya san me ake a cikin falon.

“Za su ba mu amaryarmu Dear mu yi tafiyar mu.”

Kai da ba ka nan in ka tanka ya tanka har Mami ta dawo Daddy na biye da ita.

Farha ta gabatar mishi da buƙatarta shi kuma a al’adar shi saboda surukuta ya ce

“Ba laifi ai ka kusa kammala aikin nata gidan ko?

Ya Safwan ya ɗaga kai.

Ya dube ni “To kintsa Bilkisu ku je ki taya ta zama kafin a gama nakin.

Na miƙe har ina haɗa hanya na faɗa ɗaki faɗuwa kawai na yi na fasa kukan da na yi saurin toshe bakina kar a jiyo ni duk da dai da nisa da inda suke.

Ban ji turo ƙofa ba sai dai ji na yi an kamo ni na ɗaga idona da ke jiƙe sharkaf da hawaye Mami ce ja na ta yi zuwa bakin gado

“Share hawayenki Bilkisu.”
Abin da ta fara ce min kenan.

Na share da hijab ɗi na “Ki nutsu ki saurare Ni. Da farko za ki ga kamar ban kyauta miki ba ina kallo aka ba Sadauki ke ba tare da ya ce yana so ba.

Tsananin son da nake miki ya sa na bari aka yi miki hakan, kuma ko ba mu raye za ku yi alfahari da hakan.

Sadauki shi ne zai miki irin ruƙon da nake fata a yi miki ya wanke miki baƙin cikin da kika sha a baya, kema kuma ke ce irin macen da nake ma Sadauki addu’a. duk da ban ji daɗin tafiyarki a haka ba ba a yi miki biki irin na yar gata ba ina miki fatan alheri ko da wace niyya ta gayyace ki farar zuciyarki da ba ki nufin kowa da sharri Allah zai taimake ki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 34Mutum Da Kaddararsa 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×