Sai a sannan ta fahimci cewar a fili ta yi maganar. Kallonsu ta yi da ɗan murmushi.
"Kama kawai yarinyarnan naga ta yimin da wani bawan Allah da na taɓa gani shekaru can baya. Sai kuma na tuna ba yadda Allah ba ya halittarSa. Kana arewa sai ka samu mai mugun kama da kai a Kudu."
Suka yi ƴar dariya.
"Umma ina wuni. Anti Ina wuni." Suka tsinci zazzaƙar muryar Humaira. Duban yarinyar Umma ke yi tana mai jin wani yaam a jikinta, tun kallon da ta yi mata faruwar wani lamari da ya shuɗe ya. . .