Skip to content
Part 18 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Sai a sannan ta fahimci cewar a fili ta yi maganar. Kallonsu ta yi da ɗan murmushi.

“Kama kawai yarinyarnan naga ta yimin da wani bawan Allah da na taɓa gani shekaru can baya. Sai kuma na tuna ba yadda Allah ba ya halittarSa. Kana arewa sai ka samu mai mugun kama da kai a Kudu.”

Suka yi ƴar dariya.

“Umma ina wuni. Anti Ina wuni.” Suka tsinci zazzaƙar muryar Humaira.  Duban yarinyar Umma ke yi tana mai jin wani yaam a jikinta, tun kallon da ta yi mata faruwar wani lamari da ya shuɗe ya faɗomata a rai. Ta daure ta amsa gaisuwarta gami da ƙaƙalo murmushi. Anti Khalisat da fara’arta ta amsa. Tuni kuma su Amira suka ja hannunta suka yi sama inda anan ɗakinsu yake.

Bayan gama gaisuwa ne, Anti Khalisat ta dubi Umma wacce har lokacin jikinta ke a sanyaye.

“Ita ce ai yarinyar wanna kurmar da nake ba ki labari, ta gidan Malam.”

“Allah Sarki, kenan su ne ƴan kauyen cinnaku?”

“Su ne.” Tausayi ya kama Umma.

“Allah Ya bata lafiya.” Suka amsa da ameen. Bayan tashin Anti Khalisat, Umma ta maida hankali ga Adam da ke kihingiɗe saman kujera ya dora tafin ƙafarsa guda a kai.

“Adamu baban kowa, ya muke ciki ne? Kaga yau fa Yaya ba zai maka ta sauki ba, ka fusatashi da yawa.”

Cike da damuwa Adam ya shafi sumar kansa.

“Umma aurennan fa lokaci ne da shi, ba yin kaina bane.”

Ta gyada kai.

“An sani lokaci ne, sai dai kai idan aka kyaleka ma, niyyar yinsa sam ba ka ɗauko ba.”

Ya yi ɗan murmushi yana mai kauda maganar.

“Ya su Amira suka riski sabuwar makaranta? Sun kuwa maida hankali?

Ta harareshi kadan.

“Ai ba ni za ka tambaya ba ɗan na iya, su za ka ke ka tambaya. Wato dai a dole idan an dauko magana mai muhimmanci burinka ka sauya ko? Toh ya yi kyau.”

Ganin ranta ya sosu ya sanya shi miƙewa zaune sosai gami da riƙon hannunta.

“Umma, domin Allah ku bar damuwa sosai akan rashin aurena. Wallahi ku yarda lokaci ne, da zarar na ga wacce zuciyata ke so da kauna, ba fa sai ance nayi ba. Sannan ko kammala gini ban yi ba shima ina da bukatar ƙarin lokaci. Bana son ku yimin auren dole, akwai matsaloli da dama da sukan jawo. Ku kara bani dama na kammala shirina, na muku alkawari da yardar Allah da zarar na samu wacce nake so da kaina zan muku batun aure. Addu’arku ke ɗawainiya da ni, saɓon Allah bai ta6a burgeni ba, ban taɓa jin zan iya aikatawa ba. Don haka ku kwantar da hankalinku. Idan har Adam ne, In sha Allah ba zai jawo muku abin kunya ba.”

Ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin sauƙin radadin da ke zuciyarta, maganganunsa sun shigeta. Haka ya ci gaba da kalallameta gami da nunamata tsarinsa, tun tana ɗan basarwa har ta gamsu ta kuma yi mishi addu’a da fatan samun mace ta gari. Ya amsa da amin yana mai jin wani nishaɗi.

*****

Kallonta yake ganin yanda duk ta birkice lokaci guda ya ba shi mamaki.

“Mum, meyafaru?” Ta girgiza kai tana dariyar yaƙe.

“Nothing my son, wow! Kaga yanda ka yi kyau?”

Jin haka ya yi murmushi gami da shiga dakin sosai ya karasa saman madubinta yana karewa kansa kallo.

“Really?”

“Dama ai kai mai kyan ne, son kowa kin wacce ta rasa. Mijin babbar yarinya.” Suka yi dariya. Wayarta ta yi kara, direban ne ya dawo don haka suka fita tare. Motar Fu’ad sabuwa fil na nan tafe daga Lagos Hayat ya sanya a kawomishi.

Sai da ta saukeshi a Office kafin ta fice gidansu.

Unguwar Mandawari suka nufa, sun ɗan yi tafiya cikin lunguna direban ya tsaya kasancewar mota ba za ta shiga sauran wuraren ba. Ta ja tsaki, a ganinta me za’a yi da unguwa irin wannan? Ta fito gami da sanya gilashinta a fuska, tafiya ta shiga yi cikin lungunan tana jin takaicin yanda yara da manyan layin ke bin ta da kallo har ta iso kofar gidansu wanda idan wani ma bai fahimta ba sai ya dauka hanya ce da ka ɓulla wannan ta sanya an sha shigo musu gida a dauka hanya ce ba gida ba.

Tun daga zauren gidan ta soma cin karo da tinkiyoyi har uku da ke daure, ga kashinsu duk a ƙasa. Tana ƙarasawa zaure na biyu ta ci karo da kejin kaji. Wani wawan tsaki ta ja. Ji tayi ta taka wani abu mai taushi, ta yi azamar duba bayan takalmin, kashin tinkiyoyin nan ne suka cure a wuri guda har ta kai ga takawa. Murje takamin ta yi a cikin ƙasa tana mai jin wani malolon bakin ciki.

“Kai Allah Ya sauwake, wannan wace irin rayuwa ce?”

Muryarta ya dau hankalin facalolin gidan da mahaifiyarta da kuma abokiyar zaman mahaifiyarta.

Kallonta suke don basu gane ko wace ba, Innarta da ke zaune saman tabarma ta saki nono ba riga sai sani da ta daura tana kasa kayan miyan siyarwa ta ɗago kai tana kallonta. Salma ta gama kaiwa maƙogwaro sai dai ta daure ta karasa tana murmushin yaƙe. Ko a dangin ba ta zumunci da kowa sai masu da shi. Sai ta gane mijinki wani ne ko dan uwanta wani ne fitacce sannan ta ke kulla zumunta da su. Tun dawowarsu ba ta nunawa Fu’ad hanyar gidansu ba don gani take rainata kawai zai yi. Shima tun daddara hanashi zuwa ga nasa dangin uban ya ce babu shi babu nata, alokacin ma ko a jikinta don gaba ta kai ta gobarar titi.

“Salame?” Fadin Inna tana ɗora hannu a haɓa baki sake. Wannan ya sa Laminde kishiyarta ƙara kallon matar, sai sannan ta gane dagasken Salame ce. Bushira da Beebalo matan yayanta maza suka kalleta baki sake. Bushira ta santa, Amarya Beebalo kam bata da labarinta.

Tana yamutse fuska ta karasa ga Inna.

“Sannunku.” Inna da rawar jiki ta mike tana washe baki, ko banza ta san yau kakarta ta yanke tsaka. Yau kam za ta samu kudi tunda ga Salma.

Bata ko bi takan Laminde ba dake miko gaisuwa ba balle Bushira ta yi gaba zuwa ɗakin Inna.

Inna da azama ta bi bayanta.

“Sannu da zuwa, bari na kawomaki ruwa.”

Da hannu ta dakatar da ita.

“Ba wannan ya kawoni ba don Allah. Zauna magana na zo da shi.”

Inna ba ta ko damu da yanda ta yi furucin kamar ba ita ta haifeta ba, komawa ta yi ta zauna tana ƴar dariya.

“Ya kuke? Ina Hayat din da jikana?”

Salma ta yamutse fuska.

“Kalau. Wata matsala ce ta kunnomin.”

Turus ta yi.

“Toh naji, dama dai ashe da gaske Alhaji Mansur yake da yace kin dawo har kin je gidansa. Wace matsala ce ta sa ki ka zo yau?”

Innar ta furta tana mai maida hankali gareta sosai. Ganin kallon da Salma ta watsamata ya sanya ta shanye sauran zancen da ta yi niyyar saukowa don nuna isa matsayinta na uwa. Ta tuna ko wace Salma, dama can ba wani girma take bata ba balle yanzu da burinta ya cika na samun abinda take so. Tiryan-tiryan ta koramata batun Halima, dama ba abinda Innar bata sani ba sai ƙalilan.

“Tirƙashi!” Fadin Inna tana dafe haɓa.

*****

Amira ke  koyawa Humaira aikin da aka bata tana mata dalla-dalla yanda za ta fahimta, sai ga shi nan kan kace me tana ganewa sosai. Kiran da Amir ya yi musu na su fito a ci abinci ya sanya suka mike. A kasan suka tarar dasu gaba daya saman tebur.

‘Ikon Allah.’ Fadin Humaira a zuciya, ta san cewa ta ta6a gani a gidansu Anti Nuriyyah sai dai kuma ba ta taɓa gani an ci abinci samansa ba duk kuwa da cewar an fadamata abinci ake ci a kai.

Tun tahowarsu yake kallonta, murmushi ta sanyashi. Ya gama lura da yanda ta ke a dan tsorace sai dai yana hango wani karfin hali da dakiya tattare da ita. Ta wani dake gudun kada ta kwafsa.

“Ku zo ku zauna ku ci abinci.” Fadin Anti Khalisat, Umma kuwa kalaman Haisam suka fado a ranta a wancan lokacin.

“Idan Mijinki ya dawo ki ce masa Haisam Zakariyya ya zo. Ki fadamasa ya ji tsoron Allah! Ya kuma sani cewar zan yi ƙararsa.”

Ba ta manta sadda ta tambayeshi a daidai harabar gidan.

“In Sha Allah zan isar da saƙonka, ka yi hakuri kar ka ce na maka katsalandan. Me Hayat ya yi maka?”

Ba ta mance kallon da ya yi mata da jajayen idanunsa ba wadanda ɓacin rai suka rina.

“Kar ki damu, watarana abin ɓoye zai fito fili. Wuyarta na shigar da zancensa kotu.”

“Umma.”

Ta yi dan firgigit ta dawo hayyacinta tana duban Adam. Humaira wacce tsoron kallon da Umma ke bin ta da shi ya mamaye ta, tuni ta yi ƙasa da kanta yanda har ba ta son ɗagowa, wata fargaba ta ke ji.

“Umma meyafaru ne ki ke tunani irin haka? Tun dazu Anti ke magana ba ki ji ba.”

Ta yi murmushin yaƙe gami da girgiza kai.

“Bakomai, ya akai?”

Ta ƙarashe tana maida akalar zancen ga Anti Khalisat. Shi kuwa Adam ya maida dubansa ga Humaira, tun ɗazun ita Umma ke kallo  bai kuma san dalili ba, yarinyar har ta tsargu ta sunne kanta. A hankali ya kai hannu ya taɓa yatsun hannunta. Ta dubeshi tana satar kallon Umman wacce ta maida hankali ga cin abinci.

“Ci abinci mana.” Ya furta a tausashe yana sakarmata murmushi. Ta maida mishi martanin murmushin kafin ya dauke hannunsa su soma cin abinci sai dai ba ta son ta kalli Umman, takan ji kamar ba ma kallonta take yi ba, harara ce.

*****

Bisa umarnin Malam, Yaha ta yiwa Maryam rakiya bangaren Engineer domin ta gaishesu. Tun ganin da suka yi mata suka sha jinin jikinsu, suka amsa gaisuwarta ta kurame da yi mata addu’ar samun lafiya. Yaha ta yi mata jagora zuwa wurin Engineer. Alokacin yana kishingide yana sauraron labarai a rediyo. Sallamar Yaha ce ta katseshi hakan yasa ya rage murya yana mai amsawa. Ta shigo tana mai umartar Maryam ta shigo. Tun shigowarta ya ji gabansa ya faɗi. Itama Maryam zubamishi idanu ta yi, kirjinta na dukan tara-tara tana mai ambaton Allah a zuci. Kanta har wani sarawa ya soma, toh ga Engineer ma kusan abinda ya faru kenan. Da yatsa ya shiga nunata. Yaha da bata kawo komai ba ta soma bayani da ƴar fara’arta.

“Dama Malam yace na kawota ku gaisa, ita ce marar lafiyar da ya ba ka labari.”

‘Allah, Kar Ka sa tunanin da ke zuciyata ya zama gaskiya.’ Fadin Engineer yana duban Maryam kamar sabon makahon da ya samu ido lokaci guda.

*****

“Ba tirƙashi za ki cemin ba, mafita za ki nemomin. Ya zan yi? Mene abin yi? Shigowar Halima rayuwar gidan aurena, zai zama kamar tarwatsa rayuwar da na gina ta zamantakewata da Hayat ne. Bana son yin wannan gangancin.” Tana maganar a harzuƙe tana duban Innarta sa’ilin da ta fidda gilashin idanunta.

“Shikenan naji. Kar ki damu wannan abu ne mai sauki. Kudi za ki kawo a yau ba gobe ba zan shirya naje wurin Malam Mudan.”

Salma ta dan harareta.

“Inna na sanki sarai da kudi, me za ki ce ayi akan maganar?”

‘Ƴar gwafar uba!’ Inna ta furta a ƙasan ranta, a fili kuwa ta rausaya kai da alamun tausasawa.

“Haba Salame, ki hakuri mana har na kammala magana.”

Salma wacce sunan da Inna ta furta ya gama ƙular da ita ta yi kwafa.

“A duk duniya ke kadai kike kirana da Salame ban yi ashariya ba. Kema nakin wataran baƙantamin yake.”

“Ah ni Sa’a, Allah Ya huci ranki.”

Salma ta tura baki.

“Ina jinki, me za’a yi mata?”

Inna ta gyara zama.

“Anzo wurin, Halima gogaggiyar yar bariki ce sai dai yanzu ya kamata ki nunamata kema ba kanwar lasa ba ce. Ba zamu yarda ta shiga gidan Hayat ba. Zan je na sanya a haukata ta.”

Salma ta ɗan yi shiru tana nazari can kuma ta yi murmushi kafin ta zarce da dariya gami tafa hannuwanta. Innar ma dariya ta yi tana mai jin sanyi. Ido ta gwalalo ganin yanda Salma ta zura hannu a jakarta ta fiddo kudi  har dubu ashirin ta miƙamata.

“Ga wannan na aikin ne. Wannan kuwa.” Ta ƙara daukar dubu goma.

“Naki ne, kiyi kudin mota aciki.”

Da rawar jiki Inna ta karɓa ta hau sanyamata albarka. Salma karemata kallo take yi.

“Wai ni Inna mene amfanin yawon da kike a gidannan ban riga? Wannan sai ki sa surukanki su rainamu.”

“To ai wai gani nayi an saba kuma ma girma ya zo me za’a ɓoye.”

Tsaki Salma ta ja.

“Nidai kada na kara zuwa na ganki haka.”

“Ai kuma shikenan, yanzu ya za’a yi idan na gama da Gagarabadau?”

“Zan sa direba gobe ya zo ya dauko ki. Ban ce kuma ki tahomin da kowane shege ba a gidannan don sanda nayi fadi tashin samun miji mai maiƙo, ba irin zagin da basu yimin ba. Da Baba na raye da ba abinda ma zai kawo ni gidannan, ba irin tsanar da  bai yimin ba da yana raye.”

Inna ta kwantar da murya.

“Yo wa ya isa ma ya bi ni? Ai ni walki ce daidai nake da kugun kowa. Su kansu sun sani ba a kawomin wargi.”

Ta gaskata hakan sanin da ta yiwa Innar tun ma a can baya. Miƙewa ta yi tana kakkaɓe jikinta kamar wacce ta zauna cikin shara. Madubin idanunta ta maida, Inna ta adana kudaden sannan ta yi mata rakiya har wurin mota. Ta dawo tana yaɗawa Laminde habaici.

“Ɗiyata ta yi goshi, na wasu har gobe suna fama da sauran dumame. Bakin ciki ya kora mutum ɗaka.”

Laminde tana daga ɗaki tana cika da batsewa sai dai ta yi kwafa ba tare da ta ce uffan ba.

*****

Wayarsa dake ringing ya fiddo. Ganin mai kiran ya sanyashi murmusawa. Yana ɗagawa Fu’ad ya soma ɓaɓatun wai ya je Yobe bai faɗamasa ba, ai da ya biyoshi.

“Afuwan Lil, ba wani jimawa zan yi ba ai. Gobe ma ina hanya in Sha Allah.”

“Ok ok, naji, Nima ɗaga Ofis ne na biya mu gaisa, ban sameka ba na kira Dr Ibrahim sai yake cemin ka je Yobe. Ya su grandies da Umma?”

Adam ya ɗago kai ya dubi Umma da hankalinta ke ga talabijin ita da yara.

“Gatanan. Za ku gaisa ne?”

Cikin sauri Fu’ad ya amsa.

“Yes Please.” Dama tsoron kada Adam ya ƙi shiyasa bai ce ya bata wayar ba.

Umma ta kalli wayar tana ware hannu alamar tambaya. Ta karɓi wayar ta kara a kunnenta.

“Assalamu Alaikum.”

Daga can Fu’ad ya amsa, sannan ya gaisheta. Ta amsa a mutunce, karshe ta miƙawa Adam wayar, sallama suka yi ya kashe.

“Waye ne?” Ta nemi ba’asi da murmushi.

Shima da murmushin ya amsa.

“Fu’ad.”

“Wanda dai na sani?” Ta tambaya da mamaki.

Ya gyada kai kafin ya labarta mata yanda suka yi. Ta cika da dimbin mamaki sai dai ta ji dadi sosai.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 17Rumfar Kara 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×