Skip to content
Part 19 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Ta yaya? Yaushe kuka ɗinke har haka?”

Tiryan-tiryan Adam ya bata labarin komai tun daga farko. Umma banda murmushi ba abinda take zabgawa karshe ta yi hamdala ga Allah.  Sosai ta yi mishi nasiha akan ya cire komai a ransa ya rungumi Fu’ad tamkar ciki daya suka fito.

“Ba ruwanka da alaƙarsu da mutane biyun nan (Hayat da Salma), Ka kaunaceshi domin Allah. Da zuciya daya, Allah Ya yi muku albarka.”

“Ameen Umma.”

*****

Gaisuwa irin ta kurame Maryam ke mishi, har sai da Yaha ta ce.

“Baba ana gaidaka.” A sannan ne ya ɗan yi firgigit. Ya amsa yana mata alamar ya amsa da hannu. Murmushi Maryam ta yi wanda karara ya kara ganin kamanninshi da ita. Kirjinsa dokawa yake har suka mike suka fita bai iya yi musu addu’ar a zo a gani ba. Ita kanta Maryam sai da ta kara juyowa ta dubeshi kafin su fita. Kanta ciwo yake, ta yiwa Yaha alamar su tafi don ba za ta iya zaman kwakkwarar mintuna anan ba balle awanni. Daga ta tuna fuskar Dattijon sai ta ji ta rasa sukuni. Ta kuma kasa gane abinda ke sanyata jin abinda take ji.

A bangaren Engineer kuwa, kuryar ɗakinsa ya shige ya tura kofar. Hannu yasa ya jawo tsohuwar ajiyarsa cikin tsohon akwatin da ya zo da shi tun dawowarsa daga ƙasar waje. Hannu na rawa ya bude ya fiddo wasu hotuna. Mace ce mai kananun shekaru ta ci riga da wando. Gashinta ya zubo a gadon bayanta. A gefenta, shi ne tsaye sanye da kananun kaya ya sanya hannu a aljihun wandonsa. Ta saƙala hannu a wuyansa su na dariya. Hoton sun dauka ne a saman London bridge. Haka ya dinga kallon hotunansu kala-kala. Maidawa ya yi ya adana su kafin ya zauna saman ƴar kujerar da ke a ɗakin yana zubar da hawaye. Ya sani sun yi wata irin rabuwa da ita, kamar yanda ya san sun rabu ne tana da juna biyu. Sai dai kuma labarin abinda ta haifa bai riskeshi ba. Amman bai san ina ta ke ba, ina zai ganta balle ya nemi gafararta ba. Sun riga da sun gogawa junansu baƙin fenti.

Kuka yake, shekaru sama da talatin, abinda ke cin zuciyarsa kenan yana nukurkusarsa. Yasan shi mai laifi ne, damuwarsa kenan ta shekara da shekaru. Dakyar ya daure ya share kukansa, fitowar da zai yi falo ya soma ganin bibbiyu, karshe ya zube a tsakanin dakin da falo. Baba Hindu ce ta sawo kai falon da sallamarta. Ganin ba ya falon ta juya don dama magana take so su yi, ta tabbata bayan gida ya zagaya. Jikinta ya bata mutum ne kwance a hanyar daki, ta juyo domin tabbatarwa. Ganin kamar Engineer ya sanya ta saurin ƙarasawa, ai kuwa shi ne.

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Bello! Bello!”

Tana jijjigashi tana kuka. A guje ta fice ta dawo tsakar gidan. Ganinta haka su Abulle suka mike.

“Ku kira Malam, ga Bello ya faɗi!”

Jin wannan ya tashi hankalinsu, a guje Yusuf ya sheƙa ya kira Malam. Sai gashinan tare da su Lawwali. Mota aka sanyashi suka fice asibiti.

*****

A bangaren Adam kuwa, dukkan wasu bayanai ya tattaro ya yiwa  Hashim akan maganarsa ta aure, dakyar da siɗin goshi ya yi nasarar shawo kansa.

“Kada kuma naji wani zancen daga baya. Ka cika alƙawari, da zarar ka samu ka kawo ayi maganarta.”

Da murmushi Adam ya dubeshi yana dan shafar sumar kansa.

“Zan cika da yardar Allah.” Daga haka suka yi dariya. Kiran wayar Hashim da aka yi ta dauke hankalin Adam daga gareshi zuwa ga su Humaira da ke gefe su na wasan Ludo a wayar Anti Khalisat. Ya shagala wurin kallonta sai jin salatin Hashim ya yi wanda ya haɗa da miƙewa tsaye lokaci guda. Ganin haka gaba daya yaran suka kalleshi.

“Lafiya?” Adam ya nemi sani.

“Baba Engineer ne ba lafiya, su na asibiti yanzu haka.”

Salati suka yi, Hashim ya karasa ciki ya sanar da su Umma. Gaba daya suka ruɗe, tare da Umman da Adam suka wuce sai Shuraim suka bar Anti Khalisat da yara.

Malam da Lawwali suka soma gani tsaye sun yi cirki-cirko a kofar dakin da Engineer ke ciki. Suna ƙarasawa Hashim ya nemi sanin abinda ya faru ga Engineer.

“Ina zamu sani Hashimu? Hindu ce ta riskeshi a sume, yanzu dai muna jira mu ji yanda likita zai ce.”

Sai a sannan hankalin Umma ya kai ga Baba Hindu da ke gefe zaune saman benci tana matsar kwallah. Kasa hakura tayi da zaman gidan ta biyo su Malam.

Karasawa ta yi suka gaisa gami da fatan Allah Ya ba Malam lafiya. Adam kuwa ji yake kamar ya shiga ya gani, yana kaunar mutumin sam ba shi da matsala. Ba jimawa likita ya fito gaba daya suka yi kansa. Hannu ya ɗagamusu yana murmushin rage musu damuwa.

“Ku kwantar da hankalinku, ya farfaɗo yanzu dai mun mishi allura ya samu bacci. Waye makusancinsa anan?”

Da ɗan murmushi Malam ya amsa.

“Dukkanmu makusantansa ne.”

Likita ya jinjina kai gami da kai duba ga Hashim ganin ya fi su karamin shekaru sannan kuma ba yaro bane. Watakila zai fi fahimtarsa.

“Ko zan iya ganinka a ofis?”

“Toh, muje.”

A can ofis likita ya soma bayani.

“Babanka yana fama da wata damuwa wacce take ƙara yawaita a duk lokacin da ya matsawa kwakwalwarsa da tunani.  Wannan dalili ya sanya abin yana barazanar taɓa mishi zuciya, wato ya jawomishi ciwon zuciya.”

Tunda aka furta damuwa Hashim ya ji dokawar abu a kirjinsa. Ya dinga maimaita kalmar Innalillahi. Likita ya koro jawabin abubuwan da zasu kiyaye kafin ya rubuta magani.

Hashim bai ɓoyewa su Malam ba, su kansu abin ya ɗan razana su. Malam Kabiru ya jima yana zargin hakan, ya jima yana ganin damuwa sau da yawa a fuskar dan uwansa musamman idan zai tuno da rayuwarsa ta London. Nan da nan zai tashi hankalinsa ya dinga tambayarsa dagaske za’a yafemishi zunubban da ya dauka a can? Tun ya na hanashi ire-iren kalamannan har akwai radda ya ce.

“Wai ni Bello, da ka je can shirka ka yi? Ko kuwa rai ka kashe ka gudo? Faɗamin takamaiman laifin da ka aikata.”

Sai da ya rantse mishi akan ba ɗaya da ya aikata aciki sannan hankalinsa ga kwanta. To har suka tashi daga wannan zaman bai ji damuwar Bello ba

Bayan Kwana Uku

Ta yi jifa da wayarta gefe tana miƙewa tsaye, nan da nan kishi ya kaɗa kwayoyin idanunta, Inna ce ta kirata akan sai dai ta yi hakuri don a cewar Gagarabadau ba abinda za’a fasa na auren Halima da Hayat. To kusan a ɓangaren Hajiya Murja ma duka haka ta samu amsa daga bokayenta. Sai wani daya da ya ga sun matsa ya ce zai san abin yi.

Ya yi daidai da fitowar Hayat daga wanda sanye da doguwar jallabiya sai tawul a hannu. Goge jikinsa yake yi yana kallonta, kusan kwanakinnan duk abinda ke faruwa kenan gareta. Karasawa ya yi ya zauna a gefenta. Ta rike hannuwansa gam.

“Ya zan yi Hayat? Wata za ta shigo cikin rayuwarmu ba yanda na iya. Ya zan yi? Ka bani shawara.”

Ya rungumeta na ƴan mintoci yana shafa bayanta kafin ya ɗago kanta yana mai riko haɓanta.

“Haba Salma, wai mene zai dameki akan abinda ma ba ya gabana?  Meyasa za ki tada jijiyoyin wuyanki? Damuwarnan bana sonta.”

Ta sauke ajiyar zuciya, hawaye har ya silalo daga kwarmin idanunta. Kafin ta ce wani abu wayarta ta yi ƙara. Kusan lokaci guda suka dubi wayar, Hayat ne ya mike ya daukota a ƙasa. Sunan da ya gani ya tabbatar masa Halima ce, maimakon ya dauka sai ya mikawa Salma. Idanu ta zaro tana duban saman screen din. Sai kuma ta kafa wayar a kunnenta.

“Me kuma ya faru? Mene ne? Inace mun yi dake sai nan da sati?”

Dariya Halima ta yi.

“Ina laifin wanda ya tunasar da kai? Ai ba shi da laifi Salma. Don haka tuni nake maki da kuma gargadi da babbar murya. Ni ba kanwar lasa ba ce, wallahi sai kin gwammace kiɗa da karatu muddin kika yi kokarin salwantar da rayuwata don ba yau na sanki ba. Kar tasan kar.”

Salma ta dubi hayar wanda yake sauraronsu zuciyarsa na tafarfasa. Zai yi magana ta yi azamar toshe bakinsa da hannu. Gami da girgiza masa kai.

“Naji, zan kiyaye.” Shi ne kawai abinda ta fadi daga nan ta katse wayar.

“Kar ka fadi wani abun. Na fa fadamaka abinda ya yi kwanaki, so kake ta koma ta cewa su Hajiya ai gadon ba na Fu’ad bane? Ko so kake ta ce mu muka kashe Haisam? Ka kwantar da hankalinka, zan san abin yi a tsanake.”

Hayat ya jinjina kai ransa na wani irin suya. Ya tsani Halima don ba yanda ya iya ne ya danne ashariyar da ta taho bakinsa. Juyawar da zasu yi suka yi ido hudu da Fu’ad da ke tsaye cak yana kallonsu fuska a daure. Gaba daya hanjin cikinsu ya cure ya harɗe wuri guda. Shikenan ta faru ta kare!

“Mum ina son magana da ke.” Yana faɗin haka ya juya ya fice.

“Shikenan Fu’ad ya ji komai!” Cewar Salma.

Girgiza kai Hayat ya yi.

“No, bai ji ba, da ace ya ji ciki zai shigo. Kedai yanzu je ki ji da me ya zo amma ki saita kanki.”

Ta gyada kai,dakyar ta iya danne kashin da ke kokarin suɓutomata wanda razani da murɗawar ciki suka tunkuɗoshi.

A falon ta tarar da shi a tsaye.

“My Son.”

Har lokacin fuska ba fara’a ya juyo a harzuƙe har sai da ta ji numfashinta ya dauke na wucin gadi alokaci daya karamar tusa ta suɓucemata. Shi kuwa tunawa da ya yi cewar mahaifiya take a wurinsa sai ya sassauta, ya yi kokarin samarwa kansa nutsuwa. 

“Please Mum, please ina rokonki, ki dinga bani time mana. Ace duk sadda nake da magana da ke kina wani abin daban. Yau ma na zo da niyyar ganinki na ganki da wancan mutumin. For God sake Mum ki bari bana so.”

Salma wacce ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa ta dafa kujera.

“My son har na ɗan tsorata, nayi zaton wani mummunan abun ne ya afku gareka.”

Ya taɓe baki gami da girgiza kai. Jan hannunta ya yi har suka zauna a falon.

“Game da employees namu ne. Salary dinsu ya yi kaɗan Mum, wannan ai mugunta ce. Na fadamaki wannan mutumin mugu ne kin ƙi yarda, ta ya ya muna samun incomes fiye da tunaninmu amman ace ba’a kyautatawa ma’aikata?

No Mum, wannan ba yi bane.”

Abinda ya matse ta, ya matse ta. Don haka ta mike tsaye.

“Ka yi duk yanda ya dace My Son, I trust you.”

Daga haka ta fice, yana kira amma fadi take.

“One minute Son.”

Haka har ta shige dakin. Hayat mai jiran tsammani ta fadawa bai ji ba a gaggauce tana shigewa toilet. Ganin haka shi kuma ya fito. A falon suka yi kiciɓus da Fu’ad.

Fu’ad ya dauke kai ya maida kan wayarsa, har Hayat ya yi gaba ya tsinkayi muryar Fu’ad.

“Your Dad is sick. Yau 3 days kenan, an yi admitting dinsa a asibiti.”

Ya dubeshi, kusan sai su yi watanni ba su ce da juna uffan ba. Jin ya ce mahaifinsa ba lafiya sai ya yi turus.

“Are you serious? Wa ya sanarmaka?”

Fadin Hayat cike da kulawa.

Ba tare da ya dauke idanunsa daga kan waya ba ya ƙara ba shi amsa.

“No need ka san waya sanarmin, kawai dai yanda na ganka a nan ya ban tabbacin ba ka da labari. Koda dai, ba ka da damuwa sosai.”

Ran Hayat a ɓace ya fice zuwa sashinsa. Wato har mahaifinsa ya kwanta ciwo amman a rasa me sanarmasa? Dama ko wayarsa yanzun bai fiye ɗagawa ba, shiyasa kwana biyu bai kirashi ba. Kwafa ya yi.

“Duk laifin wannan bawan Misrawan ne! Shege mai shiga tsakanin uba da ɗansa.”

Yana maganar Hashim, wayarsa ya ciro ya yi kiran Malam Kabiru don yasan duk ya fi su sanyin zuciya. Gaisuwar mutunci suka yi kafin ya ce.

“Yanzu Malam ashe Baba ba lafiya amman aka rasa wanda zai faɗamin? Fisabilillahi yanzu ba wanda ya damu da ni?” Ya furta yana mai kwantar da muryarsa.

“Ka yi hakuri Hayatu, ban yi zaton ba ka sani ba sai dai nayi mamakin rashin ganinka dama. Jikin Bello da sauki Alhamdulillah, yanzu haka yana gida don an sallameshi. Sai da ya kwana uku a asibiti.”

Salati Hayat ya yi kafin ya yi addu’a

“Allah Ya ba shi lafiya, Yasa kaffara ce. Ina nan zuwa gobe.”

Malam Kabiru ya amsa.

“Toh Allah Ya ba ka iko. A gaida iyalin.”

“Zasu ji.” Daga haka suka yi sallama yana mai jin takaicin Hashim.

‘Albasa kam ba ta yi halin ruwa ba.’ Ya furta a ƙasan rai, har abin ya kai shi ga mance nashi tarin laifukan, ya take komai ya hango na wasu.

*****

Zaune suke a Emergency, su na zirga-zirga da amsar marasa lafiya da dubasu. Kukan wata mata ya dauki hankalinsu, tana yi tana jijjiga dattijon mijinta wanda ke zaune saman wheelchair kansa na fidda jiki da alama bai ma cikin hayyacinsa. Ganin haka likitoci har biyu suka yi kansa.

“Idan ka mutu nima za ka rasa ni Bala! Wayyo ni Baraka!”

Aka shigar da mutumin daki, za ta shiga aka dakatar da ita. Adam ganin haka ya maida hankali ga Dr Fati.

“Dr, ji da wannan baiwar Allahn. Console her please.”

Ta gyara zaman gilashinta tana murmushi.

“Toh Dr Adam gwanin masu tausayi.”

Murmushin ma bai iya ya yi ba, tausayin matar ya ji sosai. Yana kallo Dr Fati ta isa gareta ta riketa.

“Kiyi hakuri, In sha Allah zai samu sauki.”

Tana kuka take fadin.

“Wallahi Dakta daga can wurin aikinsa na gini aka kawoshi rai a hannun Allah wai faɗowa ya yi. Ina zaune sai shigomin da Bala aka yi.”

Abin ya ba Fati tausayi, yanzu dattijon nan ne har yake da kokarin yin aikin gini?

“Ki hakuri, addu’arki yake buƙata saboda kuka ba zai amfaneshi da komai ba.”

Ta gyada kai tana sharar kwalla.

“Toh Dakta, na daina.”

Sai da ta kama hannunta ta zaunar kafin ta dawo ta labartawa Adam abinda ya faru. Ya kara jin tausayinsa.

“Yanzu a shekarunsa yake aikin gini? Wannan zai iya kaiwa 60yrs. Koda bai kai ba to yana dab da kaiwa.”

Ta gyada kai hannunta a harɗe tana kallon matar.

“Gaskiya dai kam. Watakila rashi ne ya sanya shi aikin.”

Fitowar likita daga dakin ne ya dauki hankalinsu, ya dubi matar.

“Ke kika kawo dattijon nan?”

Ta mike da sauri tana gyada kai.

“Eh ni ce likita.”

“Ok, biyo ni.”

Ta bishi har inda su Dr Fati ke zaune. Bayan sun zauna ya dubeta.

“I’m sorry, yana bukatar gwaji da ƙwaƙwalwa saboda gaskiya kansa ya bugu hakanan ba wani abun tashin hankali bane sosai. In Sha Allah muna saka ran farfadowarsa. Sai dai dole a yi mishi gwajin sakamakon buguwar da kan ya yi. Za ki je yanzu ki bude muku file daga nan sai ki kawomin ina jira.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! To yanzu likita har nawa ne zan kashe? Oh Ni Baraka.”

Sai sannan Dr Adam ya dubeta. Miƙewa ya yi.

“Zo muje Baba.” Ta dubeshi, ganin ba ta mike ba, Dr Fati ta sanya baki sannan suka wuce tare. Shi ya taimaka mata da bude file. Suka dawo ga Dr Ashir. Bayan ya miƙa sai ya mishi magana da harshen turanci.

“I will pay for his treatment. If everything is needed, please let me know.”

Daga nan ya yi gaba. Sai bayan ya matsa daga wurin ne Dr Ashir ke sanarwar matar, nan ta fashe da kuka tana ta godiya gami da yiwa Dr Adam addu’a.

Washegari

Daidai kofar gidan ya yi parking, fitowa ya yi daga motar suka ci karo da Hashim wanda Shima zuwansa kenan. Mugun kallo suka watsawa junansu kafin duk su dauke kai. Ganin Hashim ya shige sashin Engineer, bakin ciki ya kama Hayat. Koda ace Baban zai mishi faɗa, ba ya kaunar a yi shi a gaban Hashim. A cewarsa kara rainashi zai yi duk da basu fi sa’annin juna ba. Wannan dalilin ne ya sanya shi kuma ya yi sashin Malam.

Da sallamarsa ya shiga, fitowarta kenan daga banɗaki da nufin shigewa ɗaki. Kunnenta ba ya ji hakan ya yi dalilin da ba ta lura da shi ba sai shi ke ƙaremata kallo. Kirjinsa ne ya shiga lugude, ya ji wani gumi na ratsomishi. Juyawa ya yi da sauri ya fita yana waige. Ko shekaru nawa za’a kwashe ba za ta ɓace daga idanunsa ba, ba kuma zai kasa ganeta ba. Bai ko lura da inda yake jefa kafarsa. Haka har suka ci karo da Humaira wacce dawowarta kenan daga boko. Hakan ya yi sanadin faɗuwar filas din abincinta.

“Kai ka kai!” Ta furta tana ja da baya gami da dubansa. Shi kuwa kallo daya ya yi mata ba’a hayyaci ba ya gifta ta ya fice, motarsa ya faɗa sai gidansa dake nan cikin garin Yobe. Ita kuwa Humaira ganin ta haɗu da mutum yana zazzare ido ya bata tsoro, ga shi ko magana bai mata ba ya kada kai ya fice kuma ta ji karar tashin mota. Ai ba ta bi ta kan foodflask dinta ba ta shige gidan a guje. Yaha da ke kokarin leƙowa ta duba wanda ya yi sallama ta ci karo da Humaira.

“Ke lafiya?”

Humaira na maida numfashi tana mata nuni da kofar gidan. Ganin ta kasa magana Yaha ta ture ta ta fita wajen don ta ganewa idanunta. Sai dai ba ta ga kowa ba sai motar Hashim.

Dawowa ta yi amman tuni Humaira ta faɗa ɗakin Mamarta. Yaha na mitar abinda ya firgita Humaira ta kwashe flask din abincin da ta watsar ta shigo ciki. Sai da ta ajiye kafin ta leka ta tambayi Humaira abinda ya tsorata ta? Humaira ta dubi Mamarta da ke Sallah kafin ta amsa tana haki.

“Wani ƙaton mutumi ne a zaure muka yi karo, kuma…kuma sai bai yi magana ba ya wuce. Kuma sai na ji an tayar da mota shi ne na tsorata.”

Yaha abin ya bata mamaki, dagaske kenan Gwaggo take da ta ce ta ji sallama.

“Toh amman waye?” Fadin Yaha a fili, karshe ta ce,

“Uhm, Allah Ya kyauta toh. Ke kuma matsoraciya ai da ba mutum bane ba zai yi sallama ba.”

Daga haka ta fita. Sai bayan Hashim ya shigo suke labarta mishi ya yi dariya.

“Hayat ne fa, na ga zuwansa sai dai ko wurin Baban bai shiga ba ya tafi. Meke faruwa?”

Babu mai amsar a cikinsu don haka aka bar zancen.

*****

Hayat kuwa yana isa gida ko fitowa daga motar bai yi ba ya shiga laluben wayar Salma, hannunsa har rawa yake. Tana ɗagawa ta ce.

“Mene ne kuma?” Ya san haushinsa take ji akan zuwan da ya yi Yobe alhalin su na cikin matsala.

“Salma akwai matsala!  Ta dawo rayuwarmu.”

Cikin dan rudewa Salma ta nemi ba’asi.

“Wa kenan?”

Ya amsa kai tsaye.

“Maryam! Maryam da kika sani. Tana gidan Malam.”

Hanjin cikin Salma suka kaɗa. Kanta ya daure har ta rasa gane wane Malam din. Cikin rawar murya ta ce.

 “Kai tsaye, waye Malam?”

“Malam Kabiru, baban Bilkisu!”

“Shikenan! Shikenan mun shiga uku!”

Shi ne kawai abinda Salma me nanatawa a gigice, shi kuwa har ya katse kiran, koda ya shiga falon kasa  zama ya yi. Ya tuɓe babbar rigarsa ta malun-malun. Banɗaki ya shiga domin rage nauyin mara.

*****

“Ya farfaɗo, Alhamdulillah.”

Fadin Dr Ashir yana duban dattijon marar lafiyar a lokaci guda kuma yana amsa wayar Adam da ya nemi ba’asi.

Dattijon ya yi mishi ƙuri yana dubansa, a hankali ya ji ya soma dawowa hayyacinsa. Ba da jimawa ba ya tuno da yanda motarsu ta yi dabo a titi ta faɗa can gefe. Bai manta salatin da kowannensu ke yi ba. Alokaci guda ya tuno da sadda mahaifinsa ya rike hannunsa gam yana kalmar shahada.

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ku kaini wurin Babana, ku kai Ni na ganshi.” Fadin Dattijon yana rike da kansa, lokaci guda idanunsa suka kaɗa suka yi ja. Kansa ya shiga sarawa ya sa hannu biyu ya dafe. Ganin haka da azama Dr ya katse kiran Adam, ya tunkari dattijon yana rikeshi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 18Rumfar Kara 20 >>

1 thought on “Rumfar Kara 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×