Skip to content
Part 20 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Ya farfaɗo, Alhamdulillah.”

Fadin Dr Ashir yana duban dattijon marar lafiyar a lokaci guda kuma yana amsa wayar Adam da ya nemi ba’asi.

Dattijon ya yi mishi ƙuri yana dubansa, a hankali ya ji ya soma dawowa hayyacinsa. Ba da jimawa ba ya tuno da yanda motarsu ta yi dabo a titi ta faɗa can gefe. Bai manta salatin da kowannensu ke yi ba. Alokaci guda ya tuno da sadda mahaifinsa ya rike hannunsa gam yana kalmar shahada.

“Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ku kaini wurin Babana, ku kai Ni na ganshi.” Fadin Dattijon yana rike da kansa, lokaci guda idanunsa suka kaɗa suka yi ja. Kansa ya shiga sarawa ya sa hannu biyu ya dafe. Ganin haka da azama Dr ya katse kiran Adam, ya tunkari dattijon yana rikeshi.

“Sannu Baba. Allah Ya ba ka lafiya.”

“Ina Baba? Bai mutu ba? Ina ƴaƴana da Matata Nasiba?”

Jin haka Dr Ashir ya juya yana kallon Nos.

“Kiramin Matar da suka zo tare.”

Da saurinta ta fita waje. Baraka wacce dama zaman jira take ta mike ta shiga ɗakin. Ganin Dattijon da ta kira da Bala zaune da duwawunsa. Sai ta soma hamdala tana washe haƙora.

“Alhamdulillah, Bala sannu ya jikin?”

Tun shigowarta dama idanunsa a kanta. Ya girgiza kai.

“Sunana Buhari ba Bala ba.”

Ta ji abin banbarakwai. Ta dubi Dr Ashir shima dubanta ya yi kafin ya maida hankali ga Dattijon yana nazari. Can ya shiga yi mishi tambaya.

“Toh Malam Buhari, daga ina?”

Buhari ya ji tambayar kamar rainin hankali. Cikin hali na dauriya irin na marar lafiya ya amsa.

“Haba likita, tunda na zo nan ai nasa kana da labarin abinda ya sameni saboda ba za ka duba ni ba sai da sa hannun ƴan sanda. Ina cikin wadanda suka yi hatsari a hanyar zuwa Kano daga Yobe. Tare muke da Babana Malam Zubair da iyalina sai abokiyar zaman Mahaifiyata. Su na ina? Ya jikinsu?”

Sai a sannan Dr Ashir ya fahimci inda zantukan Buhari suka dosa. Baraka ta bude baki za ta yi magana ya yi saurin dakatar da ita.

“Suna nan lafiya. Ina zuwa. Biyoni Baba.”

Daga haka ya juya ya fita, Baraka na biye da shi tana waigen Bala wanda ya juye zuwa Buhari lokaci guda. Shima kurr ya yi mata da idanu har ta fita daga ɗakin.

A dakin ganin marar lafiya suka zauna. Cikin nutsuwa ya soma jefomata tambayoyi.

“Baba, ki ka ce mijinki ne?”

Tana sharar hawaye ta gyada kai.

“Eh, mijina ne, yau shekarunmu kusan talatin da aure sai dai Allah bai bamu zuri’a ko guda ba.”

Ya girgiza kai.

“Allah Sarki, a wane gari kuke?”

“Mu ƴan Kano ne unguwar Ƴankaba.”

“Ina ƴan uwan mijinnaki?”

“Almajirin mahaifina ne, tun yana saurayi yake tare da mahaifina. Da na kai munzalin aure aka aurar da ni gareshi, muna tare har zuwa yanzu da iyayena suka rasu.

Ya yi shiru yana juya maganar.

“Meyafaru likita? Ka fadamin.”

Ta katse tunaninsa.

“Toh, sai dai kiyi hakuri. A iyakar bincike gaskiya mijinki ya yi hatsari ne a baya wanda ya jawo ya yi loosing memory dinsa.”

“Mene hakan?” Ta nemi ba’asi da rawar murya.

Kwankwasawar da akai gami da buɗe ƙofar, Adam ne.

“Please come in.” Fadin Dr Ashir.

Ya Kai duba ga matar, duk da cewa aikin ba fanninsa bane amman bai san dalilin da yasa suka tsaya mishi a rai ba. Tana ganinsa ta ganeshi ta soma gaishe shi gami da yi mishi addu’a.

“Ya mai jikin?” Ya katse ta. Ganin ta yi shiru tana duban Dr Ashir sai ya nemi ba’asi gun Dr Ashir. Tiryan tiryan ya karanta mishi matsalar Buhari na mance komai a sakamakon hatsarin da ya yi shekarun baya, sai a yanzun ne ya dawo hayyacinsa. Kuka sosai Baraka ke yi tana ambaton Allah.

“Kiyi hakuri Baba, zo muje wurinsa.” Fadin Dr Adam. Suka mike gaba daya suka koma wurin Malam Buhari da ke kwance yana hira da marar lafiyan da ke ɗayan gadon yana ba shi labari game da yanda suka yi hatsari shi kuwa yana jajantawa. Sallamarsu ce ta katse maganarsu. Suka ƙaraso Malam Buhari na faman kallonsu.

“Sannu Baba, Ina wuni, ya jikin?”

Da dan murmushi Malam Buhari ya amsa.

“Ah Alhamdulillah, jiki ya yi sauki.”

Shima Adam sai ya murmusa.

“Haka ake so. Baba daga wane gari kake?”

“Ni ɗan Yobe ne sai dai asalin iyayena ƴan Ɗambatta ne. Neman ilimi da kuma abinci ya kawo Mahaifinmu Malam Zakari Yobe.”

Baraka da ke jin abin kamar almara sai sharar hawaye take ta kasa cewa uffan. Lokaci daya Bala ya koma wani daban da ba ta da masaniyarsa. Adam ya ɗan yi shiru, so yake ya tuna a inda yake jin sunan Malam Zakari. Can kuma sai ya kara jefamasa tambaya.

“Malam Zakari dai wanda aka fi sani da Malam Zakari Dambatta?”

Da wani zumuɗi Malam Buhari ya mike zaune.

“Eh ɗannan, shi ne. Shi ne Malam Zubair mahaifina, mazaunin unguwar Shagari. Ba wanda bai san shi ba a Unguwarnan.”

“Kasan Malam Kabiru Abdullah?” Fadin Adam yana katse hanzarinsa.

Malam Buhari ya yi ƴar dariya.

“Ikon Allah, toh ai shi wannan da kake fadi sun yi zaman mutunci da mahaifina, ɗalibinsa ne kuma aboki.”

Jin haka Adam ya mike tsaye gami da duban Dr Ashir yana murmushi.

“Akwai sanayya sosai.”

“Alhamdulillah.” Fadin Dr Ashir.

Bai cewa Malam Buhari komai a kansa ba gudun kada ya ruɗar da shi. Ya san ba komai zai gane ba, karshe ya fita. Dr Ashir ya ja Baraka gefe ya bata umarnin kada ta mishi maganar ko shi waye a wurinta, ta kyaleshi tukunna har a yi mishi bayani. Daga haka Dr Ashir shima ya gudu daga dakin saboda ba ya son tambayoyin da Malam Buhari zai mishi a yanzun.

*****

“Wace ce?” Ya yi tambayar yana kallon Secretary.

 “Ta ce sunanta Hanan.”

Fu’ad ya ɓata fuska.

“Idan ka bari ta shigo Ofis dinnan, a bakin aikinka.”

“Idan na riga da na shigo fa?”

Suka tsinci muryarta. Haka kawai sai ya ji kunyar irin kalar macen da ke nemansa a Ofis. Bai taɓa sanin yana da kunya ba sai ranar. Riga wacce ta matse jikinta ta sanya wanda mamanta kamar ka taɓa da allura su fashe tsabar girman da suka yi. Wandon ma ba’a maganar matsewar da ya yi mata. Secretary zai fitar da ita Fu’ad ya dakatar da shi.

“Je ka kawai.” Hanan ta matsa akan hanya ya shiga, ta tura kofar da kafa. Da sassarfa ta ƙarasa gareshi. Tana kokarin rungumeshi ya yi saurin dakatar da ita da hannu.

“Stop right there!” Ya faɗi a tsawance hakan ba karamin haushi ya ba Hanan ba. Ta ji takaici amma ta danne.

“Wa ya nunamaki Ofis dinmu?”

Ba za ta ce Haidar ba saboda taimakonta ya yi, sai da ta yi dakyar kafin ya amince ya ba ta address bayan ta daukar mishi alkawarin ba za ta bari Fu’ad ya sani ba.

“Abinda kake so ai duk inda yake ba za ka bari ya kufcemaka ba. Ina maka son da ba zan iya rayuwa babu kai ba, kai kuma ka kasa ganewa. Kana korata, kana nuna tamkar ba ka sanni ba bayan ka shigo rayuwata ka koyar da ni so da kaunarka. Meyasa Fu’ad? Meyasa zaka yimin hakan?”

Tana maganar da muryarta ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa yayinda yatsarta ke zagaye gaban rigarta. Ya yi azamar kauda kai yana ambaton Allah. Hanan shaidaniya ce ta gasken gaske. Ya mike tsaye ba tare daya kalleta ba ya ce,

“Na fadamaki babu ni babu ke! Ki fita daga rayuwata tun kafin na soma zaginki a bainar jama’a ina wulakantaki.”

“Hakan zai fi min dadi idan har za ka kulani, za ka shiga harkata. A yanzu ka daina ko daukar wayata, sai na maka text ya fi a kirga amman ba za ka ma nuna ka gani ba. Sai na nuna maitata a fili duk sadda muka hadu amman ka nuna bana gabanka. Ya kake so na saka rayuwata?”

Ta ƙarashe tana mai ɗora hannu a gadon bayansa lokaci guda tana matsawa. Sosai yake jin matsar har cikin ɓargonsa ya juyo da sauri ya bata wani irin runguma mai karfi, daman daurewa ya ke yana yaƙi da zuciyarsa. Ta yi amfani da wannan damar ta haɗe bakunansu wuri guda ta shiga jan harshen tamkar ta samu alawa.

“Ka sani Allah Ya tsani Zina. Ka yi yaƙi da zuciyarka. Kar ka manta, wannan jin dadin na dan lokaci ne, azabar Allah kuwa dauwamammiya ce.”

Da wani irin karfi ya angizata sai ga ta sharaf a ƙasa. Ya dubeta da idanunsa wadanda suka yi jazur sannan ya kama hannunta ya ɗagata. Ya shiga jan ta kamar wata kaya har ya fidda ita daga Ofis dinta.

“Kar ki ƙara zuwa inda nake, I hate you!”

Ya furta bayan ya tattara ragowar sautin da ya rage na muryarsa. Daga nan ya banko kofar ya rufe da mukulli ya fada banɗaki yana ambaton istigfari a ƙasa ransa.

Hanan ranta a ɓace ta juya ga ma’aikatan da ke zaune suna kallonta, sai kuma suka dauke kai, ta yi kwafa ta fice a fusace. Me zasu yi ba dariya ba.

*****

“Bello.” Fadin Gwaggo Hadiza kai tsaye tana duban Engineer wanda ke kishingiɗe saman darduma a falonsa.

“Na’am.” Ya amsa yana kallonta ransa duk ba dadi.

“Ka ganmu duk anan gaba daya babu bare cikinmu ko?”

Ya kara duban mutan dakin kamar mai son tantancewa da zaƙulo baren. Daga ita sai Hannatu sai Lawwali, Rakiya da kuma Malam Kabiru. Yan uwan juna kenan.

“Babu.” Ya amsa.

Ta gyada kai.

“Toh Alhamdulillah, kamar yanda ka ce babu bare a cikinmu, ka san cewa tunda muke bamu taɓa ɓoyewa juna komai dangane da junanmu ba. Amman me ya yi zafi har haka Bello? Mene damuwarka har haka da za ka kasa faɗawa ɗayanmu? Kabiru shi ne karami amman ilimi da kaifin basira ya maidashi kamar babba a cikinmu. Duk shakuwar da za ka yi da mu toh ya biyo bayan wacce ku ka yi da shi. Girma ya kama mu, kana dai gani tafiyar ma sai da sanduna nake yi, amman yau ace ka faɗi ka mutu saboda damuwar da mu ƴan uwanta bamu da masaniya a kai, ta ina zamu soma nema maka gafarar Allah? Yanzu wannan ciwon da ka yi bai ishe ka ishara ba Bello? Idan da ace ka mutu fa? Wace damuwa zamu ce ta kashe ka? Bamu sani ba. Ka ƙi buɗe baki ka yi mana bayani, kana zaton anan duniya akwai wani da zai fahimceka bayan mu? Wallahi babu shi. Don haka ina so idan har ni Hadiza na isa da kai, a yau ba anjima ko gobe ba, ka faɗamana ainahin damuwarka domin mu sani.”

“Assalamu Alaikum.”

Hayat ya yi sallama ya shigo, suka amsa. Da sauri Hadiza ta ɗaga mishi hannu.

“Fita muna magana!” Ta yi maganar a tsawance, dama can tana da daukar zafi don ma yanzu girma ya sa ta rage. Hayat ya juya ya fita. Shi yanzu a tsorace ma yake, ya shigo da biyu ne don ya ji ko akwai wani bayani da Maryam ta kawo gidan. Ba ya kaunar shiga sashin Malam Kabiru don yasan a can ne zai ci karo da ita wannan ta sanyashi wucewa ga Gwaggo Hindu ya zauna kamar gaske.

A daki kuwa Engineer ya gyara zamansa.

“Da farko ina mai baku hakuri bisa abinda na ɓoyemuku shekara da shekaru. A yau in Sha Allah ko mene zan fadamaku shi sai dai ina roƙonku da ku yimin kyakkyawar fahimta. Rakiya.”

Ya kira sunan autarsu a mata.

“Na’am Yaya.”

Ya yi mata nuni da ɗaki. Shiga nan a can ƙasan gado za ki ga akwati da na dawo da ita daga Landan, kawomin.”

Ba musu ta amsa ta mike, kowannensu kirjinsa na dukan tara-tara. Tsoron abinda zai fito daga bakinsa suke. Sai dai sun gwammace kiɗan da karatu.

Ba jimawa Rakiya ta dawo, ya umarci ta bude akwatin. Nan ma ta yi yanda ya ce, envelope ya ɗauko ya ciro hotuna ya mikawa kowannensu sauran kuwa ya ajiye a gabansa. Shiru suka yi suna kallonsu. Shi din ne tare da wata baiwar Allah kyakkyawa da ita.

Ganin sun nutsu suna kallon hoton, Gwaggo Hadiza har da gyara zaman gilashinta ya soma magana.

<< Rumfar Kara 19Rumfar Kara 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.