Skip to content
Part 21 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

“Sunanta Rumaisa. Ita ce matar da na soma aura a zamana a London.”

Abinda ya furta ya sanya suka shiga kallon kallo a junansu sai dai ba wanda ya katse shi. Hakan ya sanya ya ci gaba.

“Idan ba ku manta ba na fadamaku a zamana a London nayi ɓarna kala-kala. Sai dai Alhamdulillah Allah Ya tsareni daga aikata zina. Babu wannan a cikin ɓarnar da ɗan uwanku ya aikata. Abokina daya a London, Suwaid. Shi ya koyamin shaye-shaye domin ba irin abinda ban taɓa sha ba a zamana a can. Ya kasance mu ne can wurin party mu ne can, a farko hakan bai hanamu neman ilimi ba kuma bai sa mun yi wasa da karatunmu ba sai daga baya. Ya kasance karatunmu ya ja baya, sai a yi zaman aji sau biyar ma bamu damu da shiga ba. Rumaisa ƴar ajinmu ce. Kusan duk abinda muke yi akan idanunta. Nakan ji nauyi na haɗa ido da ita ina shan taba ko giya. Ba ta cemin komai sai da ta kalleni ta girgiza kai ta wuce. Wasu lokutan har hawaye nakan gani a fuskarta wanda ke nuni cewa ba ta ji dadin abinda nake aikatawa ba.

Tun ina iya yi a bainar jama’a, sanadin Rumaisa yasa na soma jin kunya, ko zamu yi shaye-shayenmu, nakan ja Suwaid mu fice daga makarantar gaba daya.

A hankali sai ya kasance tun Rumaisa na yi mana shiru da zuba ido, har daga baya ta soma yi mana magana. Takan yi ƴar nasiha, idan aka kwana biyu mu ci gaba da halayyarmu sai dai ba’a bainar jama’a ba.

Ba mu tashi girbar abinda muka shuka ba sai da muka ɓata shekaru biyu a makaranta bamu tsinana komai ba. Wannan ne ya soma sanyaya zuƙatanmu. Muka koma baya alhalin classmates dinmu sun yi gaba. Ba mu kadai bane, sai dai duk wanda ya san zafin karatun zai ji ciwon abin. Wasu kuwa ko a jikinsu.

“Kun ga abinda nake gudarmuku koyaushe ko? Kun gani ko?”

Shi kadai Rumaisa ta furta a sadda aka kafe sunayenmu cikin wadanda ba mu yi nasara ba.

Dakyar dai da taimakon Allah muka kammala karatu, bani da niyyar komowa gida kamar yanda Suwaid ma ba shi da wannan niyyar. Ba mu hango komai a rayuwar Nigeria ba illah talauci da bakin ciki kala-kala. Alokacin soyayyar Rumaisa ta mamaye ko’ina a zuciyata. Har na kasa hakuri na furtamata lokacin da zamu rabu, ita tana ajin karshe mu kuwa muna aji na biyun karshe. Babu ja in ja ta amince muka kulla soyayya, ya kasance duk da tana ajin karshe amman duk sadda ba su da lecture muna tare da juna hakanan gareni. A hankali aka soma saninmu tare har ake mana taken Love birds sai dai mu yi murmushi.

Bayan Rumaisa ta kammala karatu, ta koma gida.

Mahaifinta dan kasuwa ne, Alhaji Sadik Ahmad. Yana rike da matsayin mataimakin gwamna a wancan lokacin kuma ita kadai ce diyar da Allah Ya basu, sauran duk da ke gidansa ƴan riƙo ne kamar yanda ta shaidamin a baya.

Ta ce muddin ina sonta toh sai dai na bar London na zo Nijeriya, anan ne kuma na nunamata ba zai yiwu ba. Muka rabu baram-baran zuƙatanmu ba dadi. Bayan tafiyarta na shiga kunci da damuwa, soyayyarta ta yimin karfi wanda idan har ba maganin maye na sha nayi bacci ba to fa bani da nutsuwa. Kokarina a makaranta ya soma ja baya har sai da Suwaid ya shawarceni akan na dage da karatu domin shi kadai ne zai sa na yi kudin kece raini wanda zan raba kyautatawar da Rumaisa ta yimin a rayuwa.

Idan ba ku manta ba dama sanadin Gwamnati muka je karatu a ƙasar, sai dai tun sadda abokan karatun da aka kawo mu da su suka yi graduation, ba’a kara bi ta kaina ba da ni da sauran wadanda suka yi wasa da damarsu. Mahaifin Suwaid yana da arzikinsa daidai gwargwado kuma su din mazauna garin Minna ne sai dai asalinsu buzayen Nijar. Ba ya cikin ƴan scholarship na gwamnati. Da taimakonsa da na Rumaisa nake karatu. Koda zamu rabu mun yi mamaki da har ta biyamin dukkan wani abinda ya kamata na ajin karshe. Wannan ya kara sanyamin kewa da kaunarta. Na dai daure bana shan komai sai idan zan kwanta shima don nayi bacci ne. Ranar da ya kama na bikin kammala karatunmu, muna tsaye muna hotuna da ƴan uwan Suwaid da suka zo ana dariya. Nikam ko a jikina wai don nawa basu zo ba saboda a ganina koda ace akwai hanyar zuwansu toh fa zan ji kunya ne don ba su da arzikin gogawa da iyayen Suwaid da ma saura da nake gani a makarantar. Sallama na ji an yimin a daidai lokacin, ban ɓata lokaci wurin juyawa ba saboda muryar da naji. Rumaisa ce tana ta zabgamin murmushi. Ta yi kyau kamar ba ita ba ta kara ƙiba. Ranar wuni muka yi tare, mun yi kuka mun yi dariya. Ta bani dalilanta na ƙin aurena a baya, ta tsorata da yanda na ke ɓoye kaina, tana tsoron jin wani mummunan abu dangane da asalina saboda na ƙi faɗa mata ko ni waye, shi ne ma dalilin da ya sa ta dage akan sai dai muyi aure a Nijeriya.

Na yarda da dalilinta, na kuma amince na ba ta tarihin rayuwata sai dai da alkawarin ba za ta ce sai na koma Nijeriya ba. Ta gamsu don ba irin lallaɓawar da ba ta yimin ba ni kuma na nuna idan har ba haka ba toh sai dai  kada a yi auren.  Itama ta zo da nufin Masters ne, zuwa lokacin za mu ga yanda za ta ɓullowa iyayenta da batun aurenmu. Bayan shekara daya, a sannan na samu a wani ƙaramin kamfani na sarrafa kayan electronics a ƙasar. Suwaid shima ya samu aiki a kamfanin gine-gine.

Rumaisa ta kammala ta haɗa takardunta itama, lokacin ta aikawa mahaifinta saƙo akan ta samu miji sai dai Maraya ne, kuma tana sonshi a haka, idan suna son farin cikinta su zo su auramata shi idan kuwa a’a to zasu nemeta su rasa. Fatima ƴar gata ce. Duk abinda take so Mahaifinta Alhaji Sadik Ahmad yana da kokari wurin yi mata. Ya tako ya zo har London tare da mahaifiyarta Yasmin Mohammed.

Kafin haɗuwata da su ta tsaramana  yanda zamu yi musu bayani, Suwaid ya gamsu da hakan. Ni kuwa na ƙi aminta karshe dai na yarda da tsarinsu. Suka ci galaba a kaina na nunawa iyayenta ni maraya ne asalima karatun da nake a nan gwamnatin garinmu Yobe ne suka dauki nauyina, da na kammala na samu aiki nayi zamana.

Suka aminta da hakan, a karshe suka yi mana fatan alheri suka ce na tafi zasu neme ni.

Duk yanda suka so su yi bincike a kaina a can Nijeriya, Rumaisa ta ce ba ta amince ba, koda suka matsa ta dinga yi musu hauka kala-kala. A dole dai sai da Mahaifinta ya binciki makarantar Oxford ya gane ina shaye-shaye. Ya kirani daga ni sai shi ya ce sai dai nayi hakuri wannan zai sa ba zai bani auren Rumaisa ba. Sai a lokacin na kara tabbatar da irin matsanancin don da nake mata. Na dinga roƙonsa amman ya nuna sam.

Kwanaki biyu tsakani aka nemi Rumaisa sama ko ƙasa aka rasa, duk saboda an hana ta aurena ta gudu. Mahaifinta yasa aka kama mu ni da Suwaid. Ya ce sai mun fito mishi da ƴarsa. Sai da muka yi kwanaki goma cif a bayan cell dinsu sannan Rumaisa ta bayyana. Can wani hotel aka ganta don ya sa an kafa cigiyarta. Ta tubure ba za ta dawo ba sun rasa ta kenan tunda sun rusa farin cikinta na aurena, acewarta basu san adadin shekarun da ta kwashe tana yaƙi da soyayyata ba. Babu wani ja in ja suka yarda don dama a kwanakin da ta yi gaba daya sun fice hayyacinsu. Mu kuwa azaba kala-kala mahaifinta ya sa aka yi mana, bayyanarta tasa aka fito da mu.

Bayan wannan da kwanaki bakwai aka daura aurenmu. Suwaid shi ya zama wakilina. Muka tare a wani kerarran gida karami wanda a zuwansa garin ya siya. Ya damƙamin takardun matsayin kyauta don na rike ɗiyarsa da amana. Na ji dadi nayi ta godiya. Zamantakewarmu ta yi dadi duk da cewar wasu lokutan mukan samu saɓani sai dai ko kadan Rumaisa ba ta taɓa gorantamin game da wani dukiya da iyayenta suka mallakamin ba. Suwaid aka mishi transfer na wurin aiki zuwa New York, zan iya cewa wannan ne sanadin da mua’amalarmu ta ja baya don har na baro London bamu ƙara haduwa da juna ba sai dai a lokacin da ya tafi ba jimawa mukan turawa juna saƙonni shima daga baya muka daina.

Sai da muka shekara biyar da aure Rumaisa ba ta haihu ba. A wannan lokacin ni kuma ba abinda nake sha’awa irin ganin ɗa. Hakan yasa na sauyawa Rumaisa, ta kasa gane kaina. Nakan yawan nunamata maitata ƙarara akan son haihuwa. Manyan asibitocinsu kuwa ba wanda ba mu je ba sai dai ba labari. Na soma kaiwa dare a waje ban shigo gida ba, ta rasa kaina.

A wannan yanayin muka hadu da Halisa. Halisa ba Bahaushiya ba ce. Haifaffiyar garin Sudan ce amman a Nijeriya suke zaune cikin garin Kaduna. Tana gaban kakanninta bayan rasuwar iyayenta.  Zuwan da ta yi London ta zo wurin Kanin mahaifinta da ke zaune da iyalinsa don dora karatunta na Masscom daga Degree zuwa Masters.

Tun bana kula Halisa har tausayinta ya soma rinjayar zuciyata. A hankali muka fahimci juna da Halisa har na yarda muka kulla abota daga baya ya koma soyayya. 

Na shiga ɓoyewa Rumaisa batun Halisa, kaiwa dare kuwa sai abinda ya karu. Ban kuma ɓoyewa Halisa cewa ina da mata ba ta nunan ita fa ni take so kuma za ta zauna da ni a kowane yanayi. Wannan ya kara daga darajar Halisa a zuciyata.

Ina son auren Halisa ina kuma tsoron gargaɗin da iyayen Rumaisa suka yimin akan kada na mata kishiya. Wannan ta sa na yanke shawarar auren Hasiya a ɓoye, itama ta amince.  Kasancewar ƙanin mahaifinta ya dauki rayuwar boko da tsanani wannan ta sa bamu ci wuyar shawo kansa ba aka yi mana aure. Gida na kamawa Halisa take zaune, sai da mukai sati tare da Halisa kafin na tunkari Rumaisa. Da kaina na fadamata a nufin ko me zai faru ya faru don a lokacin son Halisa ya rufen ido irin yanda ban taɓa tsammata ba.

Magana dai ta isa ga iyayen Rumaisa, wanda shi ne silar rabuwarmu. A bata so, ta nunamusu ta ji tana sona a hakan. Ni kuwa goron da mahaifinta ya yimin game da duk kyautatawa da suka yimin ya sanya na ji gaba daya Rumaisa ta ficemin a kai. Na ji na hakura da ita har abada, dama ba haihuwa mukai ba balle na takura akan zaman namu, bayan tafiyarta na tsinci wasikar da ta bar min. Anan nake jin labarin cikinta na watanni uku. Hankalina ya tashi sai dai komai ya kuracemin. Da wannan bakin cikin na abinda na aikatawa Rumaisa da kuma batun cikin da bansan da shi ba, na koma shaye-shaye. Wataran na sha na yiwa Halisa duka, wataran kuwa na ce ta fita ta bar gidan ba za ta kwana ciki ba saboda ta yi sanadin rabuwata da Matata.

A hankali kuma komai ya tafi, na rabu da shaye-shaye da taimakon Allah da kuma yawan nasihar Halisa. Mace ce mai hakuri da takatsantsan. Wannan ne dalilin da na kara yin watsi da komai sai dai London ya fita raina tun a sannan. Rashin sanin taƙamaiman abinda zan ce a gida idan na koma ya sa na hakura da komawar.

Sai da muka shekara hudu da Halisa kafin ta samu juna biyu, na dauki hakan matsayin jarrabawar Ubangiji. Bayan ta haihu da shekara goma sha daya na yi mafarki da Mahaifinmu yana kuka da fadin ba ya son ganina tunda har zan iya mancewa da shi da tarbiyyar da ya bamu da komai. Ba ya son ganina.

Wannan ya fi komai daga hankalina hakan yasa na tattaro na dawo Nijeriya.

*****

Engineer na kai wa nan ya dubesu a kunyace, matan gaba daya hawaye ne a fuskokinsu, hakanan mazan idanunsu sun kaɗa. Ya kara da fadin.

“Bansan ina Rumaisa ta shiga. Ban kuma san inda zan sameta ba. Wannan shi ne damuwata tun bayan dawowata Nijeriya, inda nake da tabbacin nan ne garinsu kuma da gidansu, na je na tambaya an ce sun bar garin ma gaba daya. Game da Maryama dake wurinka kuwa. (Ya nuna Malam Kabiru), jikina kawai ke bani cewar tsatson Rumaisatu ce. Sai dai bani da masaniya. Kafin rasuwar Halisa ta bi ta damu akan Rumaisa, takan yawan cemin bamu kyauta mata ba, ba ta ji dadin rabuwar kalar rabuwar da mukai ba. Ta kuma roƙeni duk sadda muka haɗu na nemamata gafararta. Ganin ya zamemin abu mai matukar wuya. Ku yi hakuri ku yafemin domin Allah. Ko bayan raina ku nema min gafarar…”

Ya soma tari sosai duk suka yi kansa suna salati. Ganin haka Rakiya ta fita nema mai kaisu asibiti. Hayaniyarsu ya fito da Hayat da su Abulle daga ɗaki. A motar Hayat din aka tafi kai Engineer sai dai rabin hankalin Hayat na ga hotunan da Rakiya ke faman tattarawa bisa umarnin Gwaggo Hannatu.

Bayan tafiyarsu ta adana wurin da ta dauko.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 20Rumfar Kara 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×