Skip to content
Part 22 of 41 in the Series Rumfar Kara by Rufaida Umar

Kuka sosai yake yi yana ambaton Allah. Faɗi yake.

“Na yarda ɗannan, na yarda da kaddarata ce hakan. Bar nunamin madubi. Allah Yay maka Rahma Malam, Allah Ya ji kanki Nasiba. Allah Sarki Hassan da Al’amin.”

Buhari ke wannan maganar yana kuka bayan gama ƙarewa kansa kallo a madubi wanda Dr Ashir ya nunamasa. A baya ya dauka tamujewar fatarsa sakamakon hatsarin da suka yi ne, sai dai furfurar da kuma girman da ya gani ƙururu a madubin ya sauya tunaninsa. Wannan bai girgizashi ba sai da ya ji shekarun da ya kwashe a wannan halin da kuma yanda abubuwa suka kasance. Ya share hawaye bisa lallaɓawar da Dr Adam ke mishi kafin ya dubi wacce aka kira da matarsa ta yanzun, Baraka.

“Kinga ikon Allah ko? Bansan da aurenmu ba. Amman in Sha Allah na miki alkawarin kasancewa da ke har karshen rayuwarmu. Ki yafemin.”

Baraka ta dauke hawayenta tana murmushi. Wannan kadai ya ishe ta kwanciyar hankali, idan da ace Buhari ya ƙi aminta da zama da ita, ina za ta kai maraicinta?

“Ba komai Malam Buhari. Allah Ya barmu tare.”

Ta ƙarashe tana ƴar dariya, Dr Adam suka murmusa. Miƙewa Dr Adam ya yi yana duban agogo.

“Ok, bari naje. Lokacin aikina ya yi. Baba sai na zo kenan ko?”

Buhari ya kalleshi yana murmushi.

Toh ɗana, sai ka zo muje wurin Malam din. Na gode sosai Allah Ya bar zumuncinmu.”

Aka amsa da amin daga nan ya fice.

*****

Cikin tashin hankali ta sake kiransa a karo na goma sha biyar nan ma bai ɗauka ba wannan ya sa ta yi wurgi da wayar saman kujera tana cin magani. Zuwan Maryam ya fi komai dagula mata lissafi, Maryam ba abinda ba ta sani ba game da sirrinsu. Matukar wannan sirri ya je kunnen iyayen Hayat toh kuwa ta tabbatar ba mai daga musu kafa, har inda take za’a zo a kamata. Watakila itama hukuncin kisa ya hau kanta.

Wayar ce ta ƙara daukar ƙara. Hannu na rawa ta dauka.

“Hayat ya ake ciki? Kar ka kyaleta! Ka kashe ta!”

“Salma ni za’a kashe? Bu…uban can! Ni kike so a kashe kenan? Wato wannan shi ne hukuncin da kika yanke dama?”

Muryar Halima ce ta doki dodon kunnenta. Ta runtse idanu gami da dafe kai alamun abin ya soma bata ciwon kai.

“A’a Halima, ba ke ba. Meyasa zan sa a kashe ki? Ko kin mance alkawarin da na daukar maki cewar ba zan dau wani mataki mummuna ba?”

“Ki ɗauka ma Salma! Wallahi Halima walki ce kuma daidai nake da ƙugun kowane ɗan iska!”

Salma ta dinga zuba rantsuwar ba ita take nufi ba, har a karshe ta yi suɓutar baki ta ambaci sunan Maryam.

Gaba daya wutar jikin Halima ta dauke.

“Wace Maryam ki ke magana akai?”

Fadin Halima cikin rawar baki.

“Maryam dai da kika sani. Maryam din Haisam.”

Wata ashariya Halima ta lailayo har sai da Salma ta fidda wayar a kunne kafin ta mayar.

“Ai wannan ba ku kadai ya shafa ba, domin bayyanar Maryam tonuwar  asiranmu ne. Me kuke ganin zamu yi?”

Salma ta gyara zama tana kara manna wayar a kunnenta. Makiyin maƙiyinka, masoyinka ne hakan yasa ta ji ta wartsake.

“Bansan me zamu yi ba Halima, domin Maryam na wurin da ƙaryar mutum ya ce zai shiga ya illata ta. Tana gidan su Hayat, idan da asirin muke ji, su kam akwai tsayawa tsayin daka a addu’a. Wannan ne abin tsorona. A yanzu dai so nake na samu tabbacin har yanzu Maryam tana nan a kurma da bebiyar da na sa aka maidata. Idan har ba ta sauya zani ba to sai na san ta inda zan ɓullowa lamarin.”

“Hakane, yanzu ke zaman me kike a Kanon da ba za ki je Yoben ki ganewa idanunki ba?”

Salma ta girgiza kai.

“Akwai matsala Halima, Boka ya tabbatarmin cewa muddin ɗaya daga cikinmu ya yi ido hudu da Maryam, a ranar za ta soma magana. Ke ba ma mu kadai ba, muddin Maryam ta yi ido hudu da fuskar da ta sani to fa kashinmu ya bushe.”

“Tirƙashi! Wanna mummunan labari kika bani da ya dakusar da farin cikina. Batun Maryam ba ku kada zai shafa ba, nima ya shafeni kamr yanda ku ka sani. To ko zamu sa a cinnawa gidan wuta ne?”

Salma cike da jin dadin yanda Halima ta dage da batun nemo mafita, yasa ta soma zargin har ta watsar da batun auren Hayat. Hakan yasa da karfin gwuiwa ta ba ta amsa.

“Ba zai yiwuwa ba domin ni bana son aikin da za’a yi saurin ɗagowa. Nafi kaunar yin abinda ba kowa zai fuskanta ba.”

“Hakane. Amman abinda ban sani ba, ta haihu kuma abinda ta haifa yana raye?”

Cike da bakin ciki Salma ta amsa.

“Haka nake zato kamar yanda aka dubamin a ƙasa, shiyasa nake son jin komai daga Hayat. Bari mu jira mu ji.”

“Yauwa gwara mu sani. Toh ya ake ciki da maganarmu? Ina ta kwana?”

Ji ta yi kamar ta watsamata garwashi a kirji, ashe dai bata manta ba. Ta ja guntun tsaki.

“Kya bari dai a kashe wannan boss din ko?”

Wata shewa Halima ta yi.

“Ina fa? Ai gwara na shigo a kashe Boss da babba da karamin. Kar ki ɗauka bana ƙirga ranaku, yau saura kwanaki biyu kacal idan ban yi kuskure ba. Don haka ki fita idona, idan ba haka ba zan haɗamaki zafi biyu. Nifa duk wutar da ba ni kadai za ta ƙona ba ba ta fiye girgizani sosai ba. Bikin Magaji bai hana na Magajiya. Aure da Hayat daram!”

‘Don b…ubanki ba.’ Salma ta zage ta a zuciya, a fili kuwa ta amsa.

“Shikenan, za ki ji ni dai.”

“Ba matsala, yanzu dai duk yanda ake ciki game da Maryam sai ki kira mu san abin yi.”

Hararar wayar Salma ta yi tana ji kamar ta shaƙe Halima ta huta.

“Toh Nurse Halima.”

Fadin Salma da gatse. Halima ta kece da dariya.

“A baya kenan wannan, a bayan ma akwai dalili!”

Daga nan ta katse wayar don tsabar bakin ciki.

*****

A asibiti kuwa Hayat banda gumi ba abinda yake haɗawa. Zafi biyu yake ji, ga na rashin sanin taƙamaiman wanda zai tambaya game da Maryam, ga kuma na rashin lafiyar Mahaifinnasa. Ba wanda ya fi damunsa irin batun Maryam. Burinsa ya san dalilin zamanta a gidan.

Aka gama duba Engineer likita ya yi ta musu fada akan lallai su kula da lafiyarsa matukar suna son ya ci gaba da rayuwa a doron ƙasa. Jininsa ne ya hau ba kaɗan ba wannan ta sanya likita riƙe shi a asibitin don ya samu kwakwalwarsa ta huta.

Sai dab da Magriba suka bar asibitin. Kai tsaye Hayat ya koma gida don jin abinda ke faruwa.  Yaha ya yi kiciɓus da ita ta fito daga sashin Engineer za ta shige, yarinyar da ke gefenta ita ce ta ja hankalinsa. Yana kallon yarinyar ya ji wata irin faɗuwar gaba. Humaira ta ƙura mishi idanu tamkar ta jima da saninsa. Ta durkusa ta gaidashi. Ganin Yaha itama gaidashi ta yi. Ya ma kasa amsawa.

Da yatsa ya nuna Humaira.

“Wace wannan?” Ya furta cikin faduwar gaba. Yaha ta dubi Humaira kafin ta dubeshi.

“Sunanta Humaira, diyar baƙuwar Malam ce.”

‘Ta faru ta ƙare! Maryam ta haihu kenan!’ Ya yi furucin a zuciyarsa.

Ganin zasu shige ya dakatar da Yaha.

“Ke Yahanasu, zo ina son magana da ke.”

Ta amsa da toh gami da umartar Humaira da ta shige ciki. Humaira ta nufi cikin gidan, Yaha ta bi bayan Hayat da ya koma jikin motarsa.

“Ya sunan baƙuwar Malam din?”

“Maryam.”

Ya ɗan yamutse fuska gudun kada Yaha ta zurfafa tunani.

“Ikon Allah, itama wata yar uwar tamu ce banda labari?”

Yaha ta murmusa, ita mamaki ma ya bata yanda ya tsaya jin abinda ba damuwarsa ba. Tiryan-tiryan ta ba shi labarin Maryam wanda ta sani, ba abinda ya fi saka shi nishadi face jin da ya yi cewar ba ta magana ballantana ta ji har kuma ta mayar. Sai dai maganin da Malam ke mata ya ɗan sanyayar da jikinsa, wannan ya ba shi tabbacin tsugunne ba ta ƙare ba kenan. Akwai sauran rina a kaba. Ganin ya shiga dogon nazari ya sa Yaha dubansa a tsanake itama tana mamakin chanjawarsa.

“Yaya ko ka santa ne?”

Ta nemi sani, ya hau muzurai gami da soma magana da faɗa-faɗa.

“Ni abokin wasanki ne? Idan na yi tambaya laifi ne? Ko kina nufin ni bare ne a wurin Malam?”

Ta kasa gane manufar faɗan, hakan yasa ta ba shi hakuri sannan ta yi gaba. Shi kuwa ya ja guntun tsaki, ji ya yi ba ma zai yi sallar anan ba wannan ta sanyashi shigewa mota. Sai a nan ya lura da kiran da Salma ta dinga narka mishi. Ya yi jifa da wayar don yanda kansa ya dau chaji yana bukatar saman nutsuwa kadan.

*****

Cikin tafiyar kasaita yake kutsa kai asibitin har ya karasa ga ofis din Adam. Sai da ya Ƙwanƙwasa aka ba shi iznin shiga kafin ya shiga da sallama.

Dr Adam ya yi baya da kujera yana kallonshi da murmushi. Kallo daya za ka yi mishi ka gane a jigace yake bai saba da wahalar ba. Top din rigarsa ya bar ta a mota, daga shi sai ta cikin fara ƙal, necktie ya sassautashi ya yi nashi wuri. Maɓallan gaban rigar kuwa ya ɓalle biyar na ƙasa yayinda ukun sama suke a bude wanda har kana iya hango farar singilet din da ya sanya.

A matukar gajiye yake, yana ƙarasawa ya faɗa saman resting chair.

“Sannu.” Fadin Dr Adam kamar ya yi dariya. Ya mike ya dauki ruwa a fridge ya miƙa mishi. Fu’ad ya karɓa da sauri ya kwankwaɗe.  Sannan ya dubeshi.

“No Dr, gaskiya ba zan iya wannan aikin ba, akwai wuya.”

Murmushi ya kara suɓucewa Adam.

“Kuma haka za ka daure ka yi ba. Wannan ke nuna cewa ka zama cikakken namiji kuma jarumi mai neman na kansa. Ba ka ci gaba da zama spoiled brat ba, komai sai an maka.”

Jin haka Fu’ad ya yi murmushi ya mike zaune yana gyara zaman rigarsa da maɓallai.

“Kuma fa you are right. Zan yi making my own identity nima. The Great Engineer, Fu’ad Haisam Zakariyya.”

Suka yi dariya. Kwanƙwasa kofar ya dauki hankalinsu. Suka kalla a tare, Adam ya bada iznin shigowa. Dr Fati ce ta zo sanar mishi da batun marar lafiya. Ganin Fu’ad sai ta tsaya suka shiga gaisawa har da barkwanci don ba yau ne ranar farko da ta ganshi ba. Ta lura ɗan tsokana ne hakan yasa ta su ta zo ɗaya. Bayan sun gaisa ta fita tare da Dr Adam. Aka bar Fu’ad shi ɗaya. Komawa ya yi mazaunin Dr Adam yana bin nameplate din da kallo. Dr Adam Bello. Bai yi mamaki ba, asalina murmushi ya yi. Ya san yanda ya ƙi jinin Hayat.

Laptop din da Adam ya janyo ya bude gami da kunnawa. Hoton da ya soma bayyana a saman screen shi ya ja hankalinsa. Ya kura ido yana kokarin tuna inda ya san fuskar. Yan biyu ne sanye da kaya iri daya, sun rungumo Adam ta baya suna dariya akai hoton. Da alama dai hoton bai wani jima ba.

“Oh!” Ya furta a fili sa’ilin da ya tuna twins din Umma ne sai dai ba zai iya tuna sunayensu ba. Ya yi shiru yana nazarin halittar Amira. A hankali ya dinga wassafa kyawunta, bai san mintunan da ya kwasa wurin kallonta ba a karshe ta lumshe idanunsa. Murmushi ya ke yana jin wani yanayi da nan da nan ya shiga karyatawa. Sumar kansa ya shafa.

‘Yarinya ce fa! Kar kuma ka ɓata lokacinka, diyar maƙiyinka ce. Ba za ka sameta ba.’

Fadin wani bangare na zuciyarsa. Ya yi azamar kauda tunanin gaba daya. Sai dai ya kasa samun nutsuwa. Connecting System din da wayarsa ya yi da sauri ya kwashi hotunan Adam, karshe ya ɓige da ɗiban na Amira wanda yawanci tare take da Amir. Har ya kammala ya kashe Laptop din ba alamar zuwan Adam.

Sai da akai sallar Magriba kafin Adam ya shigo.

“Sorry.” Abinda ya furta kenan, ya ajiyemishi takeaway da ya sa aka kawomishi. Sannan ya shiga ya dora alwala. Suna cikin cin abinci wayar Adam ta yi ƙara. Ganin Baba Hashim ne ya ɗaga ba tare da wani jinkiri ba.

Bayan gaisuwa yake sanar mishi da batun rashin lafiyar Engineer.

“Toh wai Uncle kodai za’a yi mishi transfer ne zuwa Akth?”

Daga can Uncle ya amsa.

“A’a Son, ba zai yiwu ba. A dai yi hakurin a karasa treatment din anan tunda asibitin yana da kyau sosai.”

“Hakane, Allah Ya ba shi lafiya, Yasa kaffara ce .”

Daga nan suka yi sallama. Fu’ad ya jefamishi tambaya.

“Still dai jikin Grandy ne?”

Adam ya gyada kai yana mai kokarin haɗiye lomar bakinsa.

“Yaushe za ka koma?” Ya jefamishi tambayar.

“Zuwa gobe, saboda akwai mutumin da zan kai ga Malam.”

“Allah Ya kaimu, sai muje tare.”

Murmushi Adam ya yi, yana jin dadin wannan sauyi da kuma zumuncin da suke yi da Fu’ad.

Tare suka fice daga ofis din kowa ya kama hanyarsa.

*****

Misalin karfe takwas, Adam da Fu’ad suka kama hanyar Yobe. Cikinsu har Buhari, Baraka da kuma kanin mahaifin Baraka saboda kafa shaida akan abubuwan da suka faru a baya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Rumfar Kara 21Rumfar Kara 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×