Sosai muhseena tayi kokarin boye damuwarta alokacin da ta shiga gidan, adalilin bata son mahaifiyarta ta Samu damuwa.
Sai dai duk da haka Hajara sai da ta gane damuwar muhseena. A hankali Hajara ta zauna kusa da ita tana kallonta cike da kauna tace " muhseena me ke faruwa ne naga gaba daya babu walwala atare da ke, ko wani abun ya faru ne a makarantar."
Muhseena ta girgiza Kai tace ' aah Inna babu komai" ta girgiza Kai tace " aah muhseena idan kin boye abinda ke damunki to fuskarki ta bayyana don Allah ki gaya min damuwarki". Idanunta sukayi rau rau. . .