Skip to content
Part 33 of 35 in the Series Nima Matarsa Ce by Yargidan Imam

Sosai muhseena tayi kokarin boye damuwarta alokacin da ta shiga gidan, adalilin bata son mahaifiyarta ta Samu damuwa.

Sai dai duk da haka Hajara sai da ta gane damuwar muhseena. A hankali Hajara ta zauna kusa da ita tana kallonta cike da kauna tace ” muhseena me ke faruwa ne naga gaba daya babu walwala atare da ke, ko wani abun ya faru ne a makarantar.”

Muhseena ta girgiza Kai tace ‘ aah Inna babu komai” ta girgiza Kai tace ” aah muhseena idan kin boye abinda ke damunki to fuskarki ta bayyana don Allah ki gaya min damuwarki”. Idanunta sukayi rau rau alamar Zata yi kuka tace ” Inna damuwar Kabir ce ke damuna kawai”. Gaban Hajara ya Fadi ta Kara kallonta tace “me ya faru tsakaninki da Kabir din.”

Muhseena tace ” Inna Kabir ya zo garin nan jiya amma bai zo guna ba Kuma bai sanar min ya zo ba ko da babu dalilin da ya hana Shi zuwa wajena ai ya kamata ya gayá min cewa ya zo garin, gaba daya tun komawarsa ya canja min sosai yadda yake nacin Kiran wayata ya rage Kuma yadda Muke dadewa muna hira yanzu bai tsayawa da mun gaisa ya ji lafiyata da damuwata sai yayi min sallama.”

Hajara tayi jugum gabanta na cigaba da faduwa zuciyarta na cike da adduar Allah yasa ba fargabar su bace zata tabbata.

Muhseena ta cigaba da cewa ” haka zalika har zuwa yanzu ya ki yarda yayi min cikakken bayani Akan maganar auren mu” ta waigo ta dubi Hajara Ido cikin Ido tace ” Anya kuwa Inna ina da rabon auren mutumin kirki irin Kabir , Anya kuwa mafarki na zai Zama gaske ina ji araina kamar ko yaushe nasaba ta zatayi sanadiyyar rushewar farinciki na da mafarkina”.Ta karasa magana hawaye na fita daga idanunta.hajara ta kasa cewa komai sai Kai ta Sadda kasa tana cike da fargaba idan har Kabir bai auri muhseena ba hakika ba muhseena ba hatta su sunyi asarar mutum mai nagarta.

Ta dawo da kallonta ga yarta ta numfasa tace ” babu wani hukunci da zamu yi saurin yankewa ba har sai mun ji daga Kabir, ki kwantar da hankalinki idan ya kiraki ki tsaya kuyi magana sosai”. Tana gama fadin haka ta tashi ta fita daga dakin saboda bata son karama muhseena damuwa ta hanyar fadada ta ta damuwar.

Muhseena ta koma ta kwantar da kanta Akan katifa jikinta ya Fara daukar zafi.

******

Ranar da mujaheeda ta koma office, aranar Sam Alh jibrin ya kasa boye bacin ransa domin ko tsayawa ya kasa yi yayi Mata bayanin abubuwan da suka gabata a kamfanin bayanta, duk da ta bukaci hakan maimakon hakama office dinsa ya koma ya zauna Yana cike da fushi da bakinciki sai ya Kai gauro ya Kai mari . Dai dai lokacin murtala ya shigo office din shima fuskarsa babu yabo babu fallasa ya lalubi kujera ya zauna Yana kallon Alh jibrin ba tare da yace uffan ba,

Daga bisani Àlh jibrin ya dawo shima ya zauna Yana huro iska damuwa daga bakinsa.

Murtala yace ” sai hakuri oga, ni Kaina banyi tsammanin Haj zata dawo office ba,ni Nama rasa abinda take son Samu a aiki a kamfanin nan idan ba dorama Kai wahala ba Kai da dukiyar Ka ai sai Ka koma Ka zauna Ka cigaba da bada umarni”. Alh jibrin ya saki tsaki yace ” yarinya ce me shegiyar kafiya Kuma nima me kafiyar ce domin yanzu na Fara sai inda karfina ya kare, da kanta zata tattara tabar kamfanin nan, Ka duba kaga irin alherin da muka samu da bata office din yanzu Kuma ta dawo zata sa ni a damuwa da tambaye tambayen banza na ya akayi da kaza ya akayi da kaza.’

Murtala ya Kara sakin tsaki yace ” yanzu meye abin yi oga” ya numfasa yace ” Kaina ya kulle yanzu banyi tunanin komai ba tukuna, Amma zanyi tunani don bazan bari wani yayi min wasa da arzikina ba” murtala yace ” ina fa oga, ni ma ina bayanka”.gaba daya haka suka uni a kamfanin cikin damuwa gami da kulle kullen yadda zasu Kara bulloma al’amarin.

Karfe daya saura kwata na ranar lahadi Haj murjanatu tana zaune a falon gidan Haj Nana tana jiran ta Gama shiryawa ta fito. Har Haj murjanatu ta Fara gajiya da Zama sannan Haj Nana ta fito cikin kwalliya ta Riga da zani na atamfar Holland tana fara’a ” Ayi hakuri Haj kinsan bazawara da kyale kyale”. Haj murjanatu tace ” kyale kyale na banza tunda ba bazawari kike nema ba” tayi dariya tace ” Raba ni da bazawari mu da aure ai mun sami yanci kinsan dadewa a bautama yanci ne”. Haj murjanatu ta Mike tace ” uhmm muje kinji Haj”. Tare suka jero har wajen motar Haj murjanatu yau ita kadai ta tuko motar ta domin in dai zata yi irin wannan tafiyar ta sirri to bata daukar direba.

Ita ke tuka motar Haj Nana na gefenta, ta dan dubeta kadan tace ” yaya wajen mujaheedan ba dai wata matsala ko”. Haj murjanatu ta ce ” lafiya din kenan tunda ban ji wani abin ba, amma kema kinsan ai shurun bazai dore ba in dai wannan kafaffen yaron ne sai ya Kara kilama yayi abinda yafi Wanda yayi a baya,Shi yasa nake son nayima hanci tufka” Haj Nana tace ‘ Ai kin ma yi nawa na dauka tun ranar data koma washegari zaki zo muje.”

Haj murjanatu tace ” wasu uzurori ne kawai suka sha Kaina yasa ban neneki mun tafi ba”. Haka dai suka cigaba da hira har suka Kai gidan mallam me guru.

Sunyi sa’a Basu tadda wasu mutane masu yawa ba, domin nan da nan layi ya zo kansu suka shiga.

Bayan sun gama gaisawa ne Haj murjanatu tayi masa bayanin abin da ke tafe dasu.ta Kara da cewa ” nasan idan nace araba tsakaninsu yata zata cutu , Kuma Bana bukatar hakan don haka nake son ta mallake mijinta yadda ko da bisa kuskure ba zai taba iya bata Mata rai ba, atakaice dai mallam ina son ya Zama rakumi mujaheeda ta Zama akala sai yadda tayi dashi.”

Mallam me guru yayi murmushi yace ” wannan ba Wata matsala bace zata mallake Shi ” daganan ya janyo carbinsa da sauran tarkacen kayan surkullensa ya bukaci sanin sunan sa ta gaya masa .ya Jima Yana Dan bincikensa kafin daga bisani ya dago ya dubeta yace ” zata mallake Shi, amma ina son ki sani rayuwar aurensu tana cike da kalubale akwai Kuma abubuwa da dama da zasu faru masu Sosa rai Wanda ko da ta mallake Shi hakan bazai hana faruwa ba”

Cikin faduwar gaba Haj murjanatu tayi saurin duban Haj Nana sannan ta dawo da kallonta ga mallam tace ” Ai rigakafin damuwar ta tace yasa na ke son ta mallake Shi idan Kuma har mallakar ba zatayi maganin hakan ba ai babu amfanin mallakar”. Mallam yace ” Tabbas mallakar ba zata Hana duk abinda zai faru ya faru ba,Kuma ita kanta mallakar akwai ranar da zata warware sai dai idan za’a cigaba da sabuntata”. Haj murjanatu tace ” don Allah mallam wane abubuwa ne marasa dadin zasu faru ” ya girgiza Kai yace ” bangani ba ,Amma tabbas akwai matsala domin ita kanta matsalar na hangota acan wani gari amma Kuma banga katamaiman abinda zai faru ba.”

Gaban Haj murjanatu ya cigaba da faduwa ta shiga matsananciyar damuwa ta Kasa magana har sai da mallam yace ” kina bukatar mallakar?” 

Ta dubi Haj Nana Ido cike da neman shawara ta daga Mata Kai alamar eh, ta dawo da kallonta gare Shi tace ” eh” yace ” to Ku je Ku dawo jibi lokacin na Gama hada komai” tace ” toh” ya gyara zamansa yace ” zaki taho da dubu dari da hamsin” tace ” babu damuwa”.daga nan suka tattara suka tafi.

A cikin mota daker Haj murjanatu ke tuka motar Haj Nana ta dubeta tace ” ki kwantar da hankalinki Haj babu abinda zai faru in sha Allah.”

Ta girgiza Kai tace ” Haj auren mujaheeda da Taufiq shine babbar barazanar da nake fuskanta arayuwata, Bani da wani abin so sama da mujaheeda tabbas idan aka jarabceni akanta Zan wahala kwarai, ” Haj Nana tace ” Dama mafi yawan lokuta anfi jaraftar Ka da abinda kafi so” Haj murjanatu ta numfasa tace ” ya zanyi Haj” tace ” Kada kisa aranki har ya dameki ba lalle bane abinda mallam ya fada ya tabbata Allah Shi kadai yasan gaibu”. Haka Haj Nana ta cigaba da kwantar Mata da hankali Amma harta kaita gida ta aje ta wuce bata Sami nutsuwa ba harta koma gida.

Duk tunaninta bai wuce ya zata bulloma al’amarin Taufiq ba, domin dai tana da yakinin ko matsalar ce shine zai zamo me kirkirota.

A cikin kwanaki biyun nan kafin ta koma wajen Mallam me guru gaba daya damuwa ta nunata don hatta Alh Mustapha labaran ya Lura akwai abinda ke damunta amma Yana tsoron tambayar ta don bai San irin amsar da zata bashi ba.

Ranar da ta koma ta amso maganin Kai tsaye gidan mujaheeda suka wuce ita da Haj nana.sunyi sa’a Taufiq baya gida hakan yasa suka saki jiki.haj murjanatu ta dakko killin magani ta Mika Mata cikin son Karin bayani ta karbi maganin tana jujjuyawa ” mummy na meye” ta tambayeta ta dan gyara Zama tace “maganin tsari ne na amso muku ke da Taufiq saboda rayuwar nan ta lalace kana can Baka damu da kowa ba amma an damu da kai, Shi yasa na karbo muku.”

Mujaheeda tayi murmushi tace ” nagode mummy, to ya zaayi dashi” tace” yauwa kinga wannan a cikin abincinsa Shi kadai zaki sa masa wannan Kuma naki ne hayaki zaki dinga yi dashi duk bayan magriba” ta gyada Kai tace ” to shikenan in sha Allah zanyi” Haj Nana tace ” Kada dai kiyi wasa dashi ki tabbatar kina yi har ya kare shima ki tabbatar kullum kinsa masa a abinci Kuma Kada ki bari wani yaga sanda zaki zuba don ba zasu gane na meye ba sai kiga sun yi wata fassara da ban” tace” to shikenan ko Kuma na ba yaya Taufiq nasa kawai ya dinga zubawa da Kansa don Shi baida mantuwa ni ko ina iya mantawa.”

A gaggauce Haj murjanatu tace ” aah kada ki bashi kadama ki nuna masa ko gaya masa na kawo Miki magani kinsan Maza Basu wani yarda da irin wannan magungunan gargajiya ba” mujaheeda tace ” eh Kuma fa hakane mummy.”

Haka dai Haj murjanatu ta ninke mujaheeda a bai bai domin tasan matukar ta gaya Mata gaskiya ba zata taba yarda ta amshi maganin ba balle har tayi amfani dashi tasan halin yarta Sarai.

Sun Jima a gidan sosai kafin su tafi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Nima Matarsa Ce 32Nima Matarsa Ce 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×