Sai da suka gama cin abincin kafin Adam ya kalli Haura da tun ɗazu ta gama cin nata abincin ta na dai zaune ta na kallon Salim. Ya ce "Karfe nawa ne ya ce zai zo?" Haura ta amsa da "Sai dai na sake tambayar sa amma bai faɗa min ba" Adam ya ɗan saci kallon Amera sai suka haɗa ido, ya kawar da kai. Ya ce "Ki ce masa yazo da wuri domin a kwai gurin da nake son zuwa yau" Haura ta amsa masa. Ya tashi ya bar gurin ba tare da ya sake cewa komai. . .