Tana shiga da motarsa ta fara cin karo a ɗan madaidaicin harabar gidan wanda ya yi mata kyau gashi ɗan ƙarami amma a wadace ya ke. Sai da ta tsaya ta ƙarewa motar kallo sosai ta na jin yadda ta yi kewar motar har cikin zuciyarta, jakarta ta buɗe ta fiddo da abun rubutu ta fara za na abun da take son zanawa sannan ta wuce ta na jin wani irin farinciki na ratsa ta, har wani lallausan murmushi take saki ita ɗaya. Tabbas ta tabbatar nan gidan Sir ne domin irin wannan daɗin da farincikin dole sai. . .