Har suka isa asibitin ihu take yi ta na faɗin zata mutu, waiyoo ƙirjinta zafi, ya cuceta, ya ce baya sonta. Sannan har lokacin jini na fitowa daga bakinta, gaba ɗaya ta fita a haiyacinta shi kansa Adam a tsorace yake ganin yadda take yi kaman zata mutu.
Adam
Zaune yake a gaban likitan yana sauraron bayanin da yake masa. Sai da ya gama gaba ɗaya kafin yayi ƙarfin halin faɗin "Ciwon zuciya fa likita? wannan ƙaramar yarinyar ita ce ciwon zuciya zai kama? To a garin yaya?" Yayi tambayar da tsoro da mamaki. Likitan ya ce "Wannan. . .