"Sir ka faɗa mata abun dake tsakanin mu da kai ko? Ta yarda zaka aure ni?" Haura ta faɗa hawaye na zubowa daga idanunta, sannan yanayin muryar da ta yi maganar kana ji kasan bata jin dadi, ji take ina ma ya ce mata eh Nadiya ta yarda zai aureta. Kafin ma Habib ya magantu Nadiya ta ce "Abun da ke tsakanin ku! Dama kin san shi ne?" Nadiya ta faɗa cikin wata murya mai sanyi domin abun da take ji game da haura ba zai faɗu ba. Habib yayi saurin faɗin "Bebb Kinga abun. . .